← Book details Naanah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 95 OF 125

Sashe 95

Naanah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Aunty Khadijah ta ce“tom gani nan” daga haka ta kashe wayar, tashi ta yi tana murmushin da bata san dalilin sa ba, Ta ƙarasa press ɗinta ta fiddo wata dakkakiyar shadda maroon colour sai sheƙi take. Ta zare kayan jikinta ta saka shaddar ta feshe jikinta da turaruka kala-kala, kwalliya sosai ta yiwa fuskarta sannan ta ɗauki wayarta bayan ta yafa mayafi ta fito daga ɗakin.

Umma na zaune tana lazumin bayan magriba taga Aunty Khadijah ta fito. Ta dinga kallon ta da mamaki ta ce

“Khadijah ina kuma zaki je?”

Murmushi Anty Khadijah ta yi ta ce“daman baƙo nayi Umma, shi ne zan je.” Umma ta jinjina kanta ta ce“to a dawo lafiya.” amin ta ce sannan ta juya ta fice tana murmushi, Amal dake zaune kan kujera tana danna waya ta kalleta sai kuma ta taɓe baki. Tsaye ta same shi jikin gate ɗin gidan, ta ƙarasa tana kallon sa saboda wadataccen hasken da yake wajen. Shima kallonta yake yana murmushi, Ta ɗan durƙusa ta ce

“Ina yini?”

Malam Garba ya yi murmushi yana gyara rawanin kansa ya ce“lafiya lau Hajiya Khadijatul kubra. Ya su Mama?” Anty Khadijah ta sake murmushi ta ce“suna nan kalau, ta ce ma na gaishe ka.” Malam Garba ya jinjina kansa ya ce“Allah sarki, ina amsawa sosai da sosai.” shiru wajen ya ɗauka, can kuma ya ce“daman fa zuwa nayi mu ɗan gaisa yauwa, naga kwana biyu kin janye ƙafa” Anty Khadijah ta girgiza kanta ta ce“Ayyah abubuwane suka min yawa. Na gode amma” Jinjina kansa ya yi ya ce“Ba komai. Aaa ba komai, bari na koma”

“Da wuri haka?”

Ta yi maganar tana murmushi, gyaɗa mata kai ya yi ya ce“Eh gara naje. Sai kuma wani lokacin” Anty Khadijah ta ce“To na gode.” Tana tsaye har ya bar wajen sannan ta koma cikin gidan.

****
Suna tsaye da Surry har mijinta yazo ɗaukanta. Ta kalli Nana wadda ke mata hira ta ce“Ga Albee ya zo, zan tafi. Kin dai ji duk abin da na faɗa miki ko?” gyaɗa mata kai Nana ta yi ta ce“tom sai monday.” Surry ta yi murmushi sannan ta bar wajen, Basu daɗe da tafiya ba motarsa ta yi parking. Sarai ta gan shi amma ta ɗauke kanta, Gajiya ya yi da jiranta ya fito daga motar, sanye yake da wasu English wears na Gucci masu kyau da taushi, wanda suka dace da weathern damunar da ake ciki, Gashin kansa ya zubo gefen kafaɗunsa dan bai daure shi ba. Har gabanta ya ƙaraso yana kallonta ya ce

“Sai na zo nace ki tawo?”

Kallon sa ta yi sai kuma ta sunkuyar da kanta tace“ban ganka bane.” Shiru ya yi yana kallonta dan ya san ƙarya take ta ganshi, Ya ce“to muje.” Ya yi maganar yana karɓar jakar hannunta, ita dai bata ce komai ba ta yi gaba, ta shiga motar tana jiransa. Bayan ya shiga ya ajiye jakar a jikinsa yana kallon ta fuskarsa a sake ya ce

“Kin daina fushin?”

Kallon sa ta yi, kamar ba zata yi magana ba sai kuma ta ce“Fushi kuma?” Ɗauke kansa ya yi ganin tana shirin raina masa hankali, Ita ma ta mai da kanta ga jikin glass ɗin ƙofar tana kallon garin wanda ya ɗan yi duhu kamar hadari na kwance. Har suka je gida babu wanda ya yi magana, yana gama parking bata jira shi ba ta sauka daga motar ta nufi cikin gidan. Da idanu kawai ya bita sai kuma ya zare key ɗin ya fito hannunsa riƙe da school bag ɗin tata ya nufi cikin gidan shima. Ko a parlour bai sameta ba, dan haka ya nufi apartment ɗinsa kai tsaye. Da daddare wajen ƙarfe 10:00 na dare ya fito ganin har sannan bata zo ba, kuma ranar kwananta ne. Kai tsaye apartment ɗinta ya nufa, a buɗe ya samu ƙofar ya shiga yana kallonta. Zaune take tsakiyar gadonta tana danna system ɗin dake gabanta, Ya zauna gefen gadon ya ce

“Nana baki ga dare ya yi bane?”

“Nagani.”

Ta ce ba tare da ta ɗago kanta ba. Abdusammad ya ɗan yi shiru ganin ko kallon sa bata yi ba, bai taɓa ganin ta yi masa haka ba. Hasali ma bai taɓa ganinta in a serious mood irin haka ba, Ya numfasa kafin ya ce

“Ina jiran ki naji shiru, tashi mu tafi.” sai a sannan ta ɗago ta kalle shi. Fuskarta a haɗe babu alamar wasa ko kuma yarintar daya saba gani, Bakinta sai sheƙi yake dalilin lip gloss ɗin data saka, wanda duk cikin shawarwarin da Surryn ta bata ne. Lokaci ɗaya yaji jikinsa ya yi sanyi, Ta ɗauke kanta ganin irin kallon da yake matan. Rufe system ɗin ta yi ta sauko daga kan gadon, Riga ce mara nauyi a jikinta, wadda ta tsaya iya gwuiwarta, fararen ƙafafunta sun fito sosai. Ajiye laptop ɗin ta yi a kan drawer ta juyo tana shirin barin wajen, Tsaye ta gan shi a gabanta. Sai da ƙirjinta ya buga, amma ta dake ta haɗe fuska babu alamar wasa ta ce

“uncle ka matsa.”

Janyota jikinsa ya yi ya fara ƙoƙarin kai bakinsa ga nata, ta sanya hannayenta duk biyun ta ture shi tana cewa“Ni bana son irin haka uncle. Ka daina min wallahi”

Ganin yanda ta yi maganar ya sanya shi yin murmushi, kamar wanda ya tuna wani abu sai ya saketa ya ce“shikenan zo mu tafi” Barin wajen ta yi sannan ta ce“to muje.” daga haka ta yi gaba yana biye da ita a baya. Sai da suka je tsakiyar parlour sannan ta ja ta tsaya. Ya juyo yana kallon ta yace

“Mene ne?”

Ɗan kwaɓe fuska ta yi ta ce“Na manta wayata.”

Ya ce“to zaki je ki dauko ne?” gyaɗa masa kai ta yi ta ce“Eh ina zuwa.” daga haka ta juya ta koma ɗakin, Yana nan tsaye har bayan mintuna biyar amma bata dawo ba. Ya juya yana kallon ƙofar sai kuma ya ƙarasa wajen, Sai dai me? Yana murɗawa ya jita a rufe, Ya ɗan bubbuga ƙofar ya ce

“Nana! Nana!”

Shiru babu amsa, tana zaune gefen gadon tana jinsa. Ya dinga kiran sunanta ta yi banza, har ya gaji ya bar wajen. Ta koma ta yi kwanciyarta ta ja duvet ta rufe jikinta, hannunta ta sanya ta kashe side lamp ɗin dake gefen gadon, nan take duhu ya mayaye ɗakin, Ta lumshe idanunta nan da na bacci ya ɗauketa.

08106608363
Nanameera.*🌹 NAANAH 🌹*

Arewabooks@Nanameera08
Wattpad@Nanameera08.

Page 57.

Tun daga wannan ranar kuma bata sake bari wani abu ya haɗa su ba, da safe idan ta tashi bata tsayawa jiransa take tafiyarta makaranta. Haka idan ta dawo ko zama a parlourn bata yi ballantana ya ganta. Gaba ɗaya ta zama kamar ba ita ba, koda ya shigo daƙinta bata yarda ta kula shi daga Eh sai A'a, duk abin da Surry take faɗa mata shi take yi, sosai kuma hakan ya dameshi. Dan yanzu ta tashi daga Nanar daya sani yarinya mai rigimar banza, ta zama wata daban wadda magana ma bata dameta ba. Idan kaji tana dariya to a waya ne ita da Amma ko kuma su Maimoon, Ɓangaren Zahra kuwa abun sai a hankali, yau a zauna lafiya gobe abu yaci tura. Kwata-kwata bata wani ganinsa da mutunci, ganin haka ya sanya shima ya tarkatasu ya watsar da lamarinsu gefe, idan ya shiga apartment ɗin kowacce da safe baya sake nemansu sai idan wadda take da kwana taje ɗakinsa, a haka har kusan wata guda ya shuɗe.

Ranar wata Juma'a around 9pm ya shigo ɗakin yana sanye da kayan bacci, Zahra na zaune gefen gado tana kitsema Noor dake bacci kanta. Ya ƙaraso ciki ya tsaya a bakin gadon yana kallon su, sau ɗaya ta kalle shi ta ɗauke kai, Ya numfasa sannan ya nemi gefen gadon ya zauna. Har ta gama mata kitson bai ce komai ba, Ta ɗauketa ta fita da ita daga ɗakin, After some minutes ta dawo ta zauna gefen gadon tana shirin kwanciya taji ya ce

“Zahra ina son magana dake.”

Fasa kwanciyar ta yi ta koma ta zauna tana kallon sa babu yabo babu fallasa ta ce“To ina ji.”

“Akwai abin da nake miki ba daidai bane da har ki ka sauya haka? Ko akwai abin da na rage ki dashi da ki ka koma kaurace min? Did i done something wrong to you?”

Abdusammad ya jera mata tambayoyin yana kallon ta a nutse. Wani murmushin takaici Zahra ta yi ta ce“Au tambaya ka ke doctor? Baka sani ba kenan? To bari kaji ba wani abun bane kawai na gaji da zama da kai ne! Wallahi na gaji. Bana son zaman nan”

Da mamaki yake kallonta, Can kuma ya girgiza kansa ya ce“Zahra ƙarya ki ke wallahi, ƙarya ne ki ce kin gaji da zama dani. Cause i know you love me, kamar yanda nake sonki, ke kan ki shaida ce na aureki ne saboda ina son ki. Na bijirewa dangina saboda ke, dan Allah Zahra kada ki ce zaki bar ni. Kada ki ce zaki gujeni”

Ya ƙare maganar yana ƙoƙarin rungumeta, Ture shi ta yi tana watsa masa wani kallo ta ce

“Kada ka sake kuskuren taɓa ni, bana so nace maka.”

Miƙewa tsaye ya yi wannan karon a fusace ya ce“idan na taɓa ki me zaki yi? Ko kin isa ki hanani na taɓa ki ne?”

Tashi tsayen itama ta yi tana kallon sa ta ce“Ai ko ba zaka taɓa ni ba, kuma idan ka manta bari na tuna maka. Yau ba kwanana bane, sai kaje wajen ita yarinyar daka aura ka kwanta da ita amma wlh ba dai ni Zahra ba!”

Ta ƙare maganar tana zabga masa wata uwar harara. Gyaɗa kai Abdusammad ya dinga yi cike da mamakinta ya ce

“Oh haka ki ka ce?”

Ta gyaɗa masa kai tana faɗin“Eh haka na faɗa!"

“To bari ki ji, ke baki isa ki hanani nayi abin da nayi niyya ba. Idan naso yin abu ban ga wadda zata hanani ba, kuma da ki ke maganar Nana, ita yarinya ce ƙarama. Bata san komai ba, dan haka ni ba azzalumi bane da zan cutar da ƴar mutane. Amma ke dole ne nayi yanda nake so dake!”
Chapter 95 · 0% Book details