Sashe 47
Naanah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Toh kawai ta ce ta juya ta fita. Ta karasa zare hijabin jikinta sannan ta ɗauki mayafin abayar dake kan gadonta ta rufe kanta dan tuni ta cire ɗaurin sego ɗin ta fito. Bata gan shi a parlon ba, sai taron mutanen gidansu Amma da suka zo. Ta ƙarasa tsakar parlon ta ɗan gaishesu sama-sama sannan ta kalli Amma a sanyaye ta ce“Ina Abban yake?”
“Yana balcony da Abdusammad”
To kawai ta ce sannan ta nufi waje jiki a sanyaye. Tsaye ta same su da uncle suna magana, ta ƙaraso a hankali tana wasa da fingers ɗinta, sai da ta gaishe da uncle ya amsa yana kallonta sannan ta kalli Abba muryarta na fita a hankali ta ce“Abba gani” envelope ɗin da ke hannunsa na hagu ya miƙo mata yana faɗin
“Yanzu na haɗu da malamin nan naku, shi ne ya ce na kawo miki”
Nana ta sanya Hannunta duk biyun ta karɓa sannan ta ce“Abba wane malamin?”
“I can't recall his name, but ina yawan ganinsa idan naje Aun”
Nana ta yi shiru sai kuma ta juya a hankali ta koma ciki. Abba ya bita da idanu sai kuma ya kalli Abdusammad ganin shi ma itan yake kallo yasa ya ce“gaba ɗaya ta zama wata so silent da ita. Ban taɓa tunanin akwai lokacin da Nana zata nutsu irin haka ba” murmushi kawai ya yi sannan ya ce“ai fa. Kamar ba ƴar rigimar nan ba”
Abba ya ɗan yi dariya sannan ya kawar da zancen ya koma kan maganar da suke ya ce“Ni ina ga kawai ka yi haƙuri. Tun da kaga Atta ta riga da ta dage, and sanin kanka ne ba zamu iya ja da ita ba. Idan har muka ce a'a zata ga kamar dan babu ran Yaya ne ya sanya” Abdusammad ya furzar da iska daga bakinsa sannan ya ce“amma Abba ni bani da niyyar ƙara aure, beside ma koma zan ƙara aure sai na rasa wadda zan aurar sai wannan yarinyar? She's too young wallahi gaba ɗaya fa da kaɗan ta girmi Nana. Ni bana son auren yarinya ƙarama wallahi”
Abba ya ɗan murmusa kafin ya ce“To ya zaka yi? Tun da dai har kana da matarka wadda kake so to ka bari ayi auren nan kawai. Bayan Atta kana ganin Hajiya ma ta dage, kuma dai ka san ba zata bari a fasa ba, bayan haka ma yau an saka ma yara lalle ai kaga aure ya tabbata” Abdusammad ya yi shiru can kuma ya ce“ai shikenan. Amma ni gaskiya bana jin zan iya tafiya da ita can, sai dai ta zauna anan kawai a samar mata schl ta shiga” Abba ya jinjina kansa ya ce“a'a da dai ka tafi da ita. Cause school ɗin can yafi nan”
Numfasawa ya yi kawai sannan ya ce“tom bari naje dare nayi” jinjina kai Abba ya yi sannan suka yi sallama ya tafi.
****
Nana na shiga daƙinta ta ajiye envelope ɗin gefen gado sannan ta sake ficewa daga ɗakin. Apartment ɗin su Maimoon ta je, ta samu basu nan wai suna gidan Mama. Babu yanda ta iya haka ta dawo gida dan ita ba wani son zuwa Apartment ɗin su Hamida take ba saboda faɗan Mama. Kai tsaye daƙinta ta shige, ta kalli envelope ɗin data ajiye saman gado sai kuma ta nufi kan drawer in da ta ajiye wayarta, missed call ɗin Khadijah ta gani. Dan haka ta ɗauki wayar ta koma ta zauna kan gadon tana dialing numbern nata, ringing biyu ta ɗauka, Nana ta sauke numfashi bata ce komai ba. Khadijah da ke zaune kan sofa ta gyara zamanta tana faɗin
“Ina ki ka shiga ina ta kiranki?”
A sanyaye Nana ta ce“na ɗan fita ne”
Khadijah ta jin jina kanta kafin ta ce
“To ya shirye-shiryen?”
“Yaushe za ki taso?”
Nana ta mayar mata da tambayar ba tare da ta amsa tatan ba. Murmushi kawai ta yi ta ce“Da gobe nake saka rai. Ina jiran Daddy ya dawo ne”
Ɗan haɗe rai Nana ta yi kamar tana gabanta ta ce
“Har sai gobe?”
Khadijah ta waro idanu tana murmushi ta ce“to yanzu da daren nan ki ke son na biyo Flight or what?”
Nana ta yi shiru can kuma ta ce“amma da sassafe zaki tawo?”
Khadijah ta girgiza kanta still smiling ta ce
“a'a zuwa azahar dai, zan biyo flight ɗin 9 kin ga idan na zo zan fara zuwa gidan Ammi”
To kawai Nana ta ce jin kira na shigowa wayarta ta ce“alright sai goben” okay Khadijah ta ce sannan ta katse kiran. Nana ta dinga kallon numbern Junaid da ke ruri akan screen ɗinta, sai kawai ta yi jifa da wayar kan gado ta yi kwanciyarta a gefe. Ganin bai tsaya da kiran nata ba ya sanya ta tashi ta kalli wayar sai kuma tayi tsaki. Ta sanya hannunta ta janyota ta dinga kallon screen ɗin sai kuma ta yi rejecting call ɗin ta kifa wayar kan cinyarta. Ta dafe kanta tana sauke numfashi, Above 5mins kafin ta ɗago fuskarta idanunta sun sake yin jajur kamar me shirin kuka. Ta ajiye wayar tana shirin tashi idanunta ya sauka akan envelope ɗin, Hannunta na dama ta kai ta ɗaukota ta dinga juyawa tana tuna maganar da Abba ya faɗa mata.
“Malaminmu? A Aun?”
Ta tambayi kanta. Sai kuma ta shiga ɓare envelope ɗin ta leƙa, tun da taga tarin takardu taji gabanta ya faɗi. Ta ƙarasa zaro su hannunta na rawa, A firgice ta miƙe tsaye hannunta riƙe da hotunan jikinta sai wani irin rawa yake kamar ana kaɗa ganga, Nana ta dinga girgiza kanta hawaye na biyo kuncinta. Ta ɗauki wayarta da sauri ta shiga dialing numbernsa tana hawaye, sai da ta kusa katsewa sannan ya ɗauka. Bata jira ya yi magana ba ta fara faɗin
“Dan Allah dan Annabi kada ka sake turo min da hotunan nan, wallahi zuciyata na gab da tarwatsewa. Idan har da gaske ka ke sona, so kuma na tsakani da Allah to ka taimaka min ka rufa min asiri” ta ƙare maganar kuka na kwace mata. Junaid da ke tsaye a balcony ya saki kyakkyawan murmushi muryarsa wasai babu alamar damuwa ya ce
“Da dana ke kiran ki shi ne ba zaki ɗaga ba ko?. Sai yanzu saƙona ya iso gare ki kenan, fatan dai ke kaɗai ki ka gani?”
Nana ta haɗiye wani miyau mai ɗaci ba tare da ta ce komai ba. Junaid ya ci gaba da faɗin
“Ki ɗauka wannan shi ne karo na ƙarshe da zan gargaɗeki akan maganar auren nan. Wallahi idan har aka kai gobe ban ji labarin fasa aurenki ba to ba saƙo zan bawa mahaifinki ya kawo miki ba. A'a shi da kansa zan bawa a matsayin kyautar auren ki”
Runtse idanu Nana ta yi saboda yanda zuciyarta ta yi wata irin bugawa, ta zauna gefen gadon hawaye na zubowa kan fuskarta. Cikin sabon yanayin daya risketa ta buɗe bakinta a sanyaye ta ce
“Shikenan zan fasa auren!”
08106608363
Nanameera.*🌹 NAANAH 🌹*
Arewabooks@Nanameera08
Wattpad@Nanameera08.
Page 30...
Nana ta sauke numfashi tana jiran abin da zai ce. Ɓoyyayiyar ajiyar zuciya Junaid ya sauke sai kuma ya ce“Taya zan tabbatar da haka?”
Runtse idanunta ta yi wanda ya bawa hawayen dake cikin idanun damar gangarowa kan fuskarta. Ta ɗan suɗe laɓɓanta na ƙasa kafin ta ce“zan faɗawa Abba bana son auren” jinjina kai Junaid ya yi sai kuma ya ce
“Ok. Na baki daga yau zuwa gobe, idan har ban ji an fasa auren ba to ki sani zan kawo ƙarshen wannan wasan namu”
Nana ta yi shiru tana shessheƙar kuka a hankali. Jin bata ce komai ba yasa ya ce “Zan katse wayar”
“A'a dan Allah... Ina son na tambayeka”
Junaid ya gyara zaman wayar da ke kunnensa yana saurarenta da kyau ya ce“ina ji”
“Da gaske kana sona kuwa?”
Nana ta yi maganar cikin wani irin sanyi daya zarce misali. Junaid ya ɗan murmusa ya ce
“Tambaya ki ke Nana?. Duk abin da nake bakya gani kenan?”
Ta girgiza kanta kamar yana gabanta ta ce“ance masoyin gaskiya baya son yaga masoyiyarsa cikin matsala. Amma me ya sa kai ka ke kokarin yin abin da zai zame mini matsala?”
Junaid ya yi shiru kamar me tunani. Jin haka yasa Nana ta ɗan yi wani murmushi mai haɗe da hawaye ta ce
“shikenan sai da safe”
Daga haka ta katse wayar ta ajiye gefenta. Rasa abin yi ta yi sai kawai ta fashe da wani irin raunataccen kuka, Dai dai nan aka buɗe ƙofar ɗakin. Aunty Ramlah ta dinga kallonta sai kuma ta ƙaraso ciki tana faɗin
“Nana kukan me ki ke?”
Girgiza kai Nana ta yi cikin kuka ta ce“Aunty ki kira min Ammana. Dan Allah ki kirata mutuwa zan yi”
Aunty Ramlah ta dinga kallonta sai kuma ta juya da sauri ta fice daga ɗakin. Nana ta yunƙura da kyar ta mike ta haɗe hotunan ta tusa ƙasan katifar gadonta dai dai nan Amma ta shigo ɗakin Aunty Ramlah na biye da ita. Amma ta dinga kallonta ganin yanda take kuka kamar ranta zai fita, Ta zauna gefen gadon ta dafata cikin rauni ta ce
“Nana mene ne kuma?”
Kasa bata amsa ta yi sai kawai ta shige jikinta tana sake rushewa da wani sabon kukan, Amma ta ɗora hannunta akan bayanta ta dinga shafawa a hankali. Gaba ɗaya bata jin daɗin yanda Nanar ta koma, ta rasa dalilin daya sanya taƙi kwantar da hankalinta. Suna nan zaune har bayan mintuna biyar sannan ta fara rage sautin kukan nata, dan haka Amma ta ɗagota tana kallonta ta ce“kukan me ki ke Nana?” cikin shessheƙar kuka Nana ta ce
“Amma dan Allah ina son magana da Abba. Dan Allah Amma, zuciyata zafi take min”
Ganin yanda take numfashi da kyar ya sanya Amma ta ce“to tashi muje na raka ki yana ɗakinsa” dakyar Nana ta miƙe Aunty Ramlah na kallonsu ta ce“ku je bari na jira anan” okay kawai Amma ta ce sannan ta riƙe hannun Nana suka fita daga ɗakin a hankali. Aunty Ramlah ta girgiza kai tana kokarin zama gefen gadon ta ce
“oh Allah ya yi mana maganin masifa”