Sashe 87
Naanah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
****
A hankali ta fara buɗe idanunta tana ƙarewa saman ɗakin kallo, leds ɗin a kunne suke har sannan duk da hasken daya gaureye ɗakin. Ta tashi zaune tana murza idanunta, Ba wai baccin ne ya isheta ba kawai tashin taji ta yi. Kallon gefenta ta yi inda Hasken ke shigowa da glass window ɗin dake wajen, Ta ɗauke kanta tana tura baki kafin daga bisani ta yaye bargon dake jikinta ta sauka daga kan gadon, kai tsaye kuma banɗaki ta nufa. Wanke fuskarta ta yi a jikin sink kafin ta ɗago kanta tana kallon madubi, Fuskarta ta ɗan kumbura dalilin baccin da tayi, ta kai hannu ta rufe bakinta saboda hammar data tawo mata. Sabbin brushes ɗin data gani ta ɓare ta ɗauki ɗaya sannan a ɗauka toothpaste ta zuba ta hau wanke bakinta. Bayan ta gama ta ɗauki mouth listener ta fesa sannan ta zare rigar jikinta ta fara wanka, Tana gamawa ta fito ɗaure da towel. Ta karasa jikin madubi ta fara dube-duben mayukan da suke wajen, can dai ta ɗauki wani olive lotion ta shafe jikinta dashi. Babu abin da ta saka bayan man ta buɗe press ɗinta, wata riga ta zaro a jakarta ta ɓare ta warwareta tana kalla. Doguwar riga ce mai manyan flowers a jiki, saman rigar an saka roba mai talewa, Ta daɗe tana juya rigar kafin ta sanyata a jikinta. Ba ƙaramin kyau rigar ta yi mata ba, Ganin babu dankwali a ciki ya sanya ta sauke gashin kanta ya sakko kafaɗarta. Sai ta yi kamar wata baturiya, Ta rufe press ɗin sannan ta nufi hanyar fita daga ɗakin. A balcony ɗin saman ta tsaya, ganin hanyoyin sun rabu. Kamar ta je ta duba sai kuma ta nufi ƙasa kai tsaye, Parlourn net kamar jiya sai tashin ƙamshi yake, Ta kalli hanyar benan Zahra ta taɓe baki lokaci ɗaya kuma ta nufi benan da taga Abdusammad ɗin ya hau jiya. Ba karamar benansu bane wanda ana hawa za'a tarar da parlour, wannan wata ƙofa ce ta glass gefenta da wasu maddane na sirri. Ta daɗe tsaye a wajen kafin ta ƙarasa ta fara knocking bell ɗin jikin ƙofar, Ganin ba'a zo an buɗe ba ya sanya ta koma knocking ɗin da hannu. After 5mins taji an fara buɗe ƙofar, Ta tura baki tana ɗauke hannunta daidai nan ƙofar ta buɗe. Fuskarsa ya zuro yana kallonta, Ta kalle shi ganin bai ce komai ba, daga gani ka san bacci yake dan idanun sa sun ɗan janye, kuma babu riga a jikinsa sai faffaɗan ƙirjinsa dake bayyane.
“mene?”
Ya tambaya a shaƙe. Kallon sa ta sake yi sai kuma ta sunkuyar da kanta tana wasa da fingers ɗinta, Ya yi shiru kamar mai tunani sai kuma ya matsa daga jikin ƙofar still looking at her ya ce“shige.” kamar jira take ta shige cikin, Ya Girgiza kansa sannan ya mayar da ƙofar ya rufe. Wata irin ajiyar zuciya Nana ta dinga saukewa a jere a jere, Idan kana neman inda aka kashe masa kuɗi to parlourn ɗakin ya kai. Ko makaho ya shafa ya san an ɓarnatar da dukiya a wajen, Wasu set ɗin kujeru ne white colour masu taushi ko a ido, Bango ɗakin mai zane-zanen abstract art na Paris,Ta sake lumshe idanunta saboda ƙamshin cherry blossom air freshener ɗin dake dukanta. Bai ce mata komai ba taga ya zo ya nufi bedroom ɗin, itama ta bishi da sauri. Colours ɗin da aka yi amfani dasu a parlourn sune a cikin ɗakin, Komai fari ne, rabin bangon ɗakin an yi zane irin na manyan artist, ga wasu manya manyan frames ɗinsa dake maƙale a kowace kusurwa ta ɗakin, Hotunan tamkar sa yi magana saboda girmansu. Gaban gadon ya ƙarasa ya zauna yana kallon ta, Ganin hankalinta baya wajen yasa ya ce
“Ke zo nan.”
Ƙarasawa gabansa ta yi da sauri ta zauna a gefen ta sunkuyar da kanta. Shiru ya yi kamar ba zai magana ba sai kuma ya ce“mene ne?”
Girgiza kanta ta yi a hankali, Ya sake cewa“saboda ki takurani ki ka zo kina min knocking da safiyar nan?” ɗago kanta ta yi ta kalleshi sai kuma ta sake sunkuyar da kan nata kafin ta ce“uncle ai rana ya yi fa.”
“Karfe nawa?”
Ya tambaya yana ƙoƙarin kwanciya, Kallon agogon bango dake maƙale a sama ta yi ta ce“ƙarfe 11:20 na safe.” Hannunta ta ji ya jawo ya kwantar da ita gefensa sannan ya ce“Oyah ki koma bacci sai an jima zan tashi.” kwaɓe fuska ta yi dan ita har ga Allah bata ji zata yi wani bacci ba, Ganin ta juya tana kalle-kalle ya sanya ya jawota jikinsa ya ɗora kansa akan fuskarta yana jin yanda take sauke numfashi ya ce“cewa nayi ki yi bacci.”
“Unclee!.”
Ta kira sunansa a shagwaɓe, Ɗaga mata gira ya yi alamar mene ne?. Ta tura baki ta ce“to ai bana jin bacci”
“Yanzu zan saka ki ji shi to.”
Girgiza kanta ta yi da sauri, Taja duvet ɗin ta rufe har fuskarta tana sauke numfashi, Ya yi murmushi sannan ya kashe hasken ɗakin nan take ya koma kamar ba rana ba, Jan duvet ɗin ya yi ya rufe jikinsa, Ya dinga kallonta ganin yanda take ta raba idanu..
“Ba zaki yi baccin bane?”
“Zan yi.”
Ta ce kamar zata yi kuka, Ji ta yi ya jawota jikinsa sosai ya ɗora hannunsa a bayanta wajen kanta ya fara shafawa a hankali kafin ya ce
“Sleep.”
Gyaɗa masa kai kawai ta yi, ya ci gaba da shafa kan nata ba tare da ya ce komai ba. Kasancewar daman baccin ba isarta ya yi ba, Ta fara lumshe ido, yana kallonta duk abin da take a haka har baccin ya yi awon gaba da ita. Sai a sannan ya zare hannunsa, Ya gyara mata kwanciyar sannan shima ya rufe idanun sa ya koma baccin.
****
Nigeria.
Atta ce tsaye a compound ɗin gidan tana gyara mayafin rigar jikinta, Abba ya yi shiru yana jin abin da take cewa. Papa ne ya ce“Atta ai gara ta zauna anan ta yi idda, kin ga idan Allah ya yi ma sai ta samu wani mijin ta yi aurenta.” wata uwar harara ta maka masa kafin ta ce“To bama so, iyayenta zan maidawa ƴarsu. Bayan yaro ya riga da ya saketa? To zaman me zata yi muku kuma ban da son zuciya.” Shiru Papa ya yi dan ya fuskanci ba fahimtarsa zata yi ba. Abba ya taka har gabanta sannan ya ce
“Atta dan girman Allah ki je kawai zan kawo yarinyar nan da kaina daga baya.”
Shiru ta yi tana kallon sa, can kuma ta tsuke baki ta ce“Ai gara na tafi da ita Ahmadi, kawai ka bari na tafi da ita.” Girgiza kai Abba ya yi yana kallon Haule dake tsaye ta sunkuyar da kanta ya ce“Ki barta anan ɗin, zan kawota da kaina daga baya.” Taɓe baki ta yi ba dan ranta ya so ba ta ce“Ai shikenan tun da kafi ƙarfina. A faɗawa Khadijah na tafi”
Murmushi Abba ya yi ya ce“Tom in sha Allah, Allah ya tsare hanya ya kai ki lafiya.” Da amin ta amsa sannan ta ƙarasa gaban Haule ta dafata ta ce“Kar ki damu kin ji. Zan aura miki wani wanda ya fi shi kin ji” Haule bata san sanda ta fashe da kuka ba, Ta rungumeta Atta tana kuka kamar ranta zai fita. Allah ya sani tana son Safwan, a ɗan zaman da suka yi tare ta koyi ƙaunarsa. Burinta kullum ta gan shi, koda ba zai kulata ba, ashe zaman nasu ba zai yi tsayi ba. Itama Attan kukan take, Da kyar Abba ya rarrashesu ta bar jikinta, ta shige mota bayan an saka mata kayanta. Drivern yaja motar suka bar compound ɗin, Ban da kuka babu abin da Haule ke yi, Abba ya kalleta cike da tausayinta ya ce
“Ya isa haka, Je ki ciki.”
Bata ce komai ba ta nufi apartment ɗinsa, dan daman tun shekaranjiyan anan take.. Sai da ta tafi sannan Abba ya kalli Papa wanda ya yi shiru tun ɗazu. Papa ya sauke ajiyar zuciya kafin ya ce“Allah ya kyauta.” Abba ya amsa da Amin sannan kowa ya nufi hanyar gidansa jiki a sanyaye.
****
Anty Khadijah ta dinga kallon sa da mamaki ganin har sannan bai ce komai ba. Ta gyara zamanta dan ita kaɗai ta zo wajen ta ce“Ina jin ka malam, ka ce na zo cikin gaggawa me hakan ke nufi? Ko akwai matsala ne?” Girgiza kansa ya yi ya ce“Babu wata matsala Khadijah, daman ina son sanar dake wani abu ne.” Anty Khadijah da kanta ya fara ɗaurewa ta ce“To ina ji Allah dai yasa lafiya” Jinjina kansa ya yi yana murmushi ya ce“ai lafiya ma idan ki ka ce to ɗaya kenan.” Ita dai ta dinga kallon sa, Ya ɗan yi gyaran murya kafin ya fara cewa
“Wato Khadijah tun ranar dana fara ganinki naji ina ƙaunarki, naji sonki ya ɗarsu a zuciyata. Irin son nan mai tsanani, Ina son kasancewa dake Khadijah, bana gajiya da kallon ki, wannan dalilin ya sanya nake yawan gayyatar ki nan, saboda ƙaunar da nake miki. Ina son ki bani dama na zama abokin rayuwarki, na aureki mu zauna ƙarkashin inuwa ɗaya.!”
08106608363
Nanameera.*🌹 NAANAH 🌹*
Wattpad@Nanameera098
Arewabooks@Nanameera08.
Page 53.
Wata irin zabura Anty Khadijah ta yi ta miƙe tsaye, Ta dinga watsa masa wani kallo bakinta na rawa. Miƙewa ya yi yana kallon ta, kafin ya yi magana ta ce
“Kai ɗin banza! Kai ka isa na aureka? Ashe ma mahaukaciya ce ta raine ni, wallahi kaci ƙarya! Dube ka, wani ƙazami dakai. To ko auren saurayi da budurwa ban auri lalataccen namiji ba ballantana yanzu.”
Ta ƙare maganar cikin bala'i, Shi dai bai ce komai ba sai kallonta da yake. Ta jujjuya a gabansa kafin ta ci gaba da faɗin