← Book details Naanah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 113 OF 125

Sashe 113

Naanah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Murmushi ya yi ya ce“Naji amma bana son yawo, Ki zauna waje ɗaya.”

To kawai ta ce, Ta sauka daga kan gadon ta nufi toilet, Yana zaune har ta fito daga wankan. Ta buɗe press ɗinta ta zaro wata Shayla Abaya sea green ta saka, Kasancewar yadin yana da santsi ya sanya duk motsin da ta yi sai jikinta ya amsa. Ta ƙarasa gaban madubi ta fara shafa mai, Ji ta yi an rungumeta ta baya, Ta sauke numfashi tana kallon sa ta madubi ta ce

“Uncle...”

Bai ce komai ba ya fara ƙoƙarin juyo da ita, Saurin girgiza masa kai ta yi ta ce

“Uncle ba fita zaka yi ba?”

Gyaɗa mata kai ya yi ya ce“Eh ai sai an jima Flight ɗin zai tashi, Zo ki ji”

Shiru ta yi tana kallon sa, Ya ɗan haɗe fuska ya ce

“Baki ji ba?”

Sauke idanun ta kasa ta yi, kamar zata yi kuka ta ce

“Dan Allah uncle ka yi haƙuri, wallahi bani da lafiya..”

Ta ƙare maganar tana rau-rau da idanu, Shiru ya yi yana kallonta, Can kuma ya gyaɗa kansa ya ce“Okay sai na dawo.”

“A dawo lafiya, Allah ya tsare.”

Ta ce a sanyaye. Da Amin ya amsa sannan ya fice daga ɗakin, Nana ta sauke ajiyar zuciya tana dafe ƙirjinta, a yan kwanakin nan har tsoro lamarin sa yake bata, Ta ƙarasa shiryawa a gurguje ta bar gidan ita ma.

Tana zuwa ta samu Amma zaune a parlon ita da Haule, Ta zauna bayan ta gaida su,

“Amma me ku ka dafa?”

Harararta Amma ta yi sannan ta ce“Me zaki yi da abin da muka dafa?”

Langwaɓar da kai Nana ta yi ta ce“Yunwa nake ji Amma!”

“Ke baki yi girki ba?”

“Nayi bana ci”

Ta amsa tana ƙoƙarin kwanciya. Ɗauke kai Amma ta yi ta ce

“Ki je kitchen akwai abinci”

Ƙarasa kwanciya ta yi sannan ta ce“to bari na tashi”

Ita dai Amma bata sake bi ta kanta ba suka ci gaba da maganar su da Haule. Bayan an sakko daga sallar juma'a suka je apartment ɗin Hajiya Babba, Gaba ɗayan su suka haɗu, Amrah, Haule, Hamida, Maimoon, Sai kuma Nanar. Su duka da ciki Nana ce kawai babu, Duk wanda ta kalla a cikin su sai ta fara dariya. Maimoon da Amrah ne kawai ke biye mata, Su ko sauran sai kallo da ido. Wajejen ƙarfe 3:00 na rana Atta ta fito parlourn ta zauna suna hira duka. Koda aka kawo abinci Maimoon ce ta zubawa kowa, Nana ta dinga kallon abincin sai kuma ta ajiye, Tun safen babu abin da taci. Atta ta dinga kallon ta sai kuma ta ce

“Ke ba zaki ci abincin ba?”

“Na ƙoshi?”

Ta amsa tana ɗauke kai. Taɓe baki Atta ta yi ta ce“To kar ki ci ɗin, Shi mijin naki idan ya dawo sai na faɗa masa, Ni babu ruwana ba zai zo ya ce na bar ki da yunwa ba!”

Tura baki Nana ta yi, Hajiya Babba da ta zo parlourn sannan ta kalle su ta ce

“Mene ne?”

“Wai ba zata ci abinci ba, Salon mijinta ya zo yana yi mana rashin ɗa'a”

Da ɗan mamaki Hajiya Babba ta dinga kallon ta, Can kuma ta ce

“Nana ɗauki abinci ki ci”

Kasa cewa komai ta yi. Ta ɗauki plate ɗin jallof rice ɗin wadda ta sha kayan haɗi ta fara ci a hankali. Ko loma huɗu bata yi ba ta ajiye spoon ɗin tana yamutse fuska. Hajiya Babba da ke lura da ita tun ɗazu ta ce

“Mene ne?”

Girgiza kanta ta yi ta buɗe bakin ta da niyyar yin magana sai ta fara ga amai, Durƙushewa ta yi a wajen tana kwarara aman kamar zata amayar da kayan cikinta. Hajiya Babba ta taso ta riƙeta, Atta ki tsayawa ta yi a wajen tana kallon ta, Duk suka yi shiru. Sai da ta gama aman sannan Hajiya Babba ta sanya ta tashi ta rakata ciki, Mai aiki ta gyara wajen, Koda ta shiga ɗakin banɗaki ta wuce ta zare kayan jikinta ta yi wanka. Bayan ta fito ta zauna gefen gadon tana jiran Hajiya Babba ta dawo, Koda Hajiya Babba ta dawo samunta ta yi ta yi bacci a wajen, Ta girgiza kanta sannan ta ƙarasa ta rufeta da duvet ta ƙaro gudun ac sannan ta ajiye rigar ta juya ta fice daga ɗakin.

08106608363
Nanameera.*Page 67.*

Koda Hajiya Babba ta dawo ƙasan zaune ta same su sun yi shiru suna sauraren Atta da ke faman magana, Tana ganinta ta ce“Khadijah me ya sami yarinyar ne?” Sai da Hajiya Babba ta zauna sannan ta ce“Ba komai Atta, Maybe ta ci abin da bata so ne, tana sama.” Shiru Atta ta yi kamar me nazari, Can kuma ta ce“To ni dai kada mijinta ya dawo ya ganta a kwance, Yanzu sai ya ce na bar ta da yunwa. Gwara ta zo ta faɗi abin da take so a dafa mata taci ko dan Allah?” Girgiza kai Hajiya Babba ta yi kafin ta ce“A'a Atta, kawai rabu da ita.” Taɓe baki Atta ta yi sannan ta mai da idanun ta kan su Maimoon ta ce

“Ina faɗa muku...”

****
Bai dawo gidan ba sai bayan sallar isha'i, Kai tsaye kuma apartment ɗinsa ya shiga, Ya yi wanka sannan ya fito ya nufi apartment ɗin Hajiya Babba. Koda ya shiga zaune ya same su a parlour suna hira, Ya ƙarasa ciki bayan ya yi sallama ƙasa-ƙasa ya zauna kan sofa, Murmushi Aliyu ya yi ya ce

“Buddy sai yanzu?”

Furzar da iska ya yi daga bakinsa kafin ya ce

“Na gaji wallahi, Da kwana zan yi to ina son gobe naje gurin can da wuri, Cause nan da 2 days nake son komawa.”

“A haba dai 2days? Bai yi wuri ba?”

Wani kallon sheƙeke Abdusammad ya yi masa sai kuma ya ɗauke kansa ya ce“Da yake baka san abubuwan da ke gabana ba. Ina Hajiya?”

Kafin ya yi magana ta fito daga kitchen hannun ta riƙe da ƙaramin bowl, Ta ƙaraso parlourn ta zauna kan sofa sannan ta ce“Kiran me ka ke min?” Langwaɓar da kansa ya yi yana murmushi ya ce“Kawai na zo na gaishe ki ne, kuma sai naga ban gan ki ba.”

Jinjina kanta kawai ta yi sai kuma ta kalli Maimoon da ke gyangyaɗi ta ce

“Aliyu ka raka yarinyar nan gida ko ta shiga ciki ta kwanta.”

Sai a sannan Aliyun ya kalleta, Baccinta take a zaune hankali kwance, Ya girgiza kansa sannan ya ce

“To Hajiya.”

Daga haka ya tashi ya ƙarasa kan kujerar da take, Tashin ta ya yi sannan ya riƙe hannun ta, Ya yi musu sallama sannan ya fice daga parlon, Ɗaya bayan ɗaya suka dinga ficewa. Ya rage sai Abdusammad kawai zaune, Hajiya Babba ta kalle shi ta ce

“Yaushe zaka tafi?”

“Nan da Sunday nake so”

Shiru ta yi tana tunani kafin ta ce“Har da Nana zaka tafi?”

Gyaɗa mata kai ya yi ya ce“Eh in sha Allah, Kin ga tana zuwa school ai.”

“To Allah ya kaimu lafiya”

Ta ce tana ɗaukan spoon ɗin da ke cikin naman, da Amin ya amsa sannan ya tashi ya ce“Sai da safe.”

“Ita yarinyar fa?”

Da ɗan mamaki ya ce“Tana nan ne?” Kallon hanyar sama ta yi ta ce“Tana can tana kwance” Toh kawai ya ce sannan ya nufi saman, Ɗakin Hajiya ya buɗe ya shiga, ya sameta kwance kan gadon ta rufe idanun ta amma ba bacci take ba. Kamar ba zai magana sai kuma ya ce

“Taso mu tafi”

Yanda ya yi maganar a shaƙe ya sanyata tashi zaune tana murza idanun ta. Ya juya ya fice daga ɗakin, Jiki a sanyaye Nana ta sauka daga kan gadon, Ta ɗauki mayafin rigar da Hajiya Babba ta bata ta ɗan yafa kanta sannan ta fara tafiya a hankali. A tsaye ta same shi a parlourn yana yi wa Hajiya Babba magana, Ta ƙaraso ta tsaya a gefe tana kallon su, Sai da suka gama sannan ya nufi waje, ta yiwa Hajiya Babba sallama sannan tabi bayansa. Koda ta fita samu ta yi har ya yi nisa abin sa, Ita dai ta ci gaba da tafiyarta a hankali har suka ƙarasa gidan. Ɗakinsa ya shige ita ma ta nufi nata ɗakin, Tana shiga ta faɗa toilet ta yi wanka sannan ta shirya cikin wata sleeping dress doguwar riga wadda ta tsaya mata iya gwuiwarta, Ta ɗaure gashinta da ribbon sannan ta fito daga ɗakin. Koda ta shiga ɗakin sa zaune ta same shi gefen gado yana danna system ɗinsa gefensa kuma wani ɗan madaidaicin tray ne mai ɗauki da kayan fruits, Ta ƙarasa ciki ta zauna gefen gadon ta yi shiru tana kallon sa. Har bayan mintuna goma babu wanda ya ce da wani ƙala a cikin su, Daga ƙarshe dai ta numfasa ta ce

“Uncle..”

“Uhm.”

Ya amsa ba tare da ya ɗago kansa ba, Sanyi jikin Nana ya yi, Dan indai taga ya yi mata haka ta san wani laifin ta yi, To amma ita bata san me ta yi masan ba. Dan haka ta yi ƙasa da muryarta ta ce

“Uncle ba zaka ci abinci ba?”

Girgiza kansa ya yi yana ci gaba da abin da yake, Ta dinga kallon sa amma bata sake cewa komai ba. After 5mins ya rufe system ɗin ya tashi hannunsa rike da plate ɗin ya fice daga dakin, Tana nan zaune har ya dawo ya nufi toilet, wanka ya sake yi sannan ya fito, Wani boxer kawai ya saka a jikinsa ya nufi kan gadon ya yi kwanciyarsa can tsakiyar gadon ba tare da ya kalli inda take ba. Tuni hawaye suka fara zubowa kan fuskarta, Ta jima zaune a wajen kafin ta tashi ta hau kan gadon ta ɗora kanta akan bayansa cikin shessheƙar kuka ta ce

“Uncle me nayi maka to?”

Bai yi magana ba, Duk da idanun sa a buɗe suke, Jin bai ce komai ba ya sanyata sake cewa

“Dan Allah ka yi haƙuri ba zan sake ba wallahi! Ba zan kuma ba uncle.”
Chapter 113 · 0% Book details