Sashe 111
Naanah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
“Kar ki matso kusa dani, Kin cuceni Anty! Kin cuceni, Wallahi ba zan taɓa yafe miki ba.”
Zahra ta ƙare maganar tana sakin wani raunataccen kuka, Kallon ta Anty Khadijah ta dinga yi, Ta taɓe baki tana girgiza ƙugu ta ce
“Na cuce ki fa ki ka ce Zahra? Na cuce ki a ina? Ni na saka ki? Dole nayi miki?”
Zahra bata iya cewa komai ba sai kuka kawai take, Anty Khadijah ta ɗan yi murmushi ta ce“Ai ni ba cuce ki ba, Duk abin da nayi saboda ke na yi sa, Saboda ina son na taimake ki ne, Dan haka mutuwar aurenki ba laifina bane. Sakacin ki ne ya janyo miki”
Ta ƙare maganar tana zabga mata wata uwar harara, Can kuma ta juya ta fice daga ɗakin rai ɓace. Silalewa a ƙasa Zahra ta yi tana ci gaba da kukanta, ta yi dana sanin yarda da maganganun Anty Khadijah, Ta yi dana sanin biye mata, Da duk hakan bata faru da ita ba. Da Noor bata mutu ba, Da Abdusammad bai saketa ba, da ace ta ɗauki duk maganganun da Umma take faɗa mata da yanzu tana zaune gidan mijinta cikin kwanciyar hankali, Ta sake fashewa da wani sabon kukan tana ɗora kanta gefen gado.
****
Bayan sallar isha'i ne suna zaune a parlon wanda suka haɗa da Abba, Papa, Sultan, Hamid, Aliyu, Daddy, Mama, Hajiya Babba, Atta da kuma Abdusammad. Papa ya kalli Abdusammad jin bai ce komai ba ya ce
“Abdusammad muna jin ka.”
Ajiyar zuciya ya sauke yana kallon su ɗaya bayan ɗaya, Can kuma ya ɗan numfasa kafin ya fara magana cikin nutsuwa.
“Na rasa ta ina zan fara, Na rasa me zan yi? Na rasa da wane ido zan kalle ku duka”
Da ɗan mamaki Papa ya ce
“Me ya faru Abdusammad? Wani abun aka yi?”
Shiru ya ɗan yi kamar me tunani, Can kuma ya girgiza kansa muryarsa a sanyaye ya ce
“Komai ma ya faru Papa, Nayi laifi, Laifin da ban gane girmansa ba sai daga baya. Laifin da ya zama sanadiyyar saka dangina cikin matsala, Na yi kuskure, Na rasa ta ina zan fara gyara shi”
Ya ɗan yi shiru yana sauke numfashi, Su dai babu wanda ya ce komai a cikin su sai kallon sa suke,
“Na san ba lallai ku gane abin da nake nufi ba, Ina magana ne akan auren da nayi. Duk abin da faru ya faru ne ta dalilin auren da nayi, Tabbas duk abin da babba ya hango yaro ko ya hau saman dutse ba zai hango shi ba. Ban kyauta ba, Na ƙarya doka da tunanin cewa auren dangi tamkar take haƙƙi ne. Ban nemi shawarar kowa ba, Ban yi tunanin abin da hakan zai jawo ba, Ban yi aiki irin na masu hankalina ba. Kawai na yi abu dai-dai da son zuciyata, Na auri wadda nake ganin ita nake so, Ita ce zan iya rayuwa da ita. Ita ce zata haifa min ya'ya mu yi rayuwa irin wadda na shirya, amma abin da na kasa ganewa shi ne aibun dake cikin bijirewa iyaye.”
Tsayawa ya yi da magana, Ya ɗan gyara zamansa yana mai da idanun sa kan Hajiya Babba sosai ya ci gaba da cewa
“Hajiya ban kyauta ba, Na bijire miki, na yi ba dai-dai ba. Ban ɗauki shawarar ki, Ban ma baki wannan damar ba, Na sani duk abin da faru ya faru ne dalilin bijire miki da nayi, Dan Allah dan Annabi ki yafe min...”
Ya ƙare maganar yana sunkuyar da kansa, Idanun sa suka circiko kamar me shirin yin kuka, Dafa shi Abba ya yi a sanyaye ya ce
“Abdul me ya faru ne? Mene ne haɗin auren ka da abubuwan da suka faru?”
Kallon Abba ya yi da jajayen idanun sa, Sai kuma ya girgiza kansa muryarsa a sarƙafe ya ce
“Abba komai ma ya faru ne sanadiyyar aurena. Zahra ita ce wadda ta fitar da hotunan Nana, Daman kowa ya san da wannan, Ita ce wadda ta fara tarwatsa rayuwar yarinyar har ta kai ga ta samu ciwon zuciya. Sannan da ban auri Zahra ba da ƴar uwarta ba taga Safwan ba, Kuma da Safwan bai auri Siyama ba da bai rasu ba Abba. Domin Siyama ita ce wadda ta shafa masa cutar Hiv ɗin da ta yi ajalin sa!”
A firgice duk suka dinga kallon sa, Hajiya Babba da tun da ya fara magana bata ce komai ba ta gyara zamanta muryarta a dake ta ce
“Siyama kuma?”
Kallon ta Abdusammad ya yi kafin ya gyaɗa mata kai ya ci gaba da cewa
“Eh Hajiya, Ita ce, Safwan ya faɗa min komai. Ya kuma nuna min komai, Siyama ita ce take ɗauke da cutar, sannan ita ta shafa masa, wannan dalilin ya sanya ya saki Haule gudun ta kamu da cutar ita ma. Hajiya na yi kuskure, Duk abin da Safwan ya yi ba shi da laifi, domin da bai ga nayi ba shima ba zai yi ba, Da bai ga na auri Zahra ba ba zai taɓa cewa zai auri Siyama ba. Da bama zai ganta ba, Sun asirce shi ne ita da mahaifiyarta domin kawai ya bijire muku, Duk abin da Safwan ya yi ba shi da laifi.”
Babu wanda ya iya cewa komai a cikin su, Atta kuwa tuni ta fara kuka tana girgiza kanta. Ajiyar zuciya Abba ya sauke jikinsa duk a sanyaye ya ce
“Ka daina faɗin haka Abdul, Duk abin da ya faru ba laifin ka bane. Ƙaddara ce! Ita kuma ƙaddara ba'a iya guje mata, Haka Allah ya tsara babu yanda zamu iya”
Girgiza kai Abdusammad ya yi ya ce
“A'a Abba wannan ganganci, Sakaci na ne, Wannan shi ne dalilin daya sanya Allah ya jarrabeni. Abba na muku ba dai-dai ba, Na rusa muku dangi da abin da ku ka daɗe kuna ginawa, amma duk da haka baku ce min komai ba. Baku yi fushi dani ba, Kun ci gaba da zama dani kamar ma babu abin da ya faru, Me ya sa Abba?”
“Saboda mun san wata rana dole zaka gane gaskiya kamar dai yau ɗin nan!”
Papa ya bashi amsa kai tsaye idanunsa zube akan sa. Juyawa Abdusammad ya yi ya kalle shi sai kuma ya jinjina kansa ya ce
“Haka ne, Cikin ikon Allah gashi na gane gaskiya, Dan haka zan yi duk mai yiwuwa wajen ganin na gyara abin da na ɓata. Zan karɓi abin da yake nawa, zan ɗauki girman da Allah ya bani. Ba zan sake aikata irin abin da na aikata ba har abada”
Murmushin jin daɗi Abba ya yi, Zuciyarsa wa sai dan daman ya san dole wata rana sai Abdusammad ya gane abin da ya yi, kuma ya karɓi laifinsa. Duk da bai yi tunanin abun nan kusa ba, Ita kanta Hajiya Babba zuciyarta ta fara sanyaya, Takaicin ta ya fara raguwa. Duk da daman ita bata taɓa rike shi a ranta ba. Ganin babu wanda ya ce wani abu ya sanya ya ci gaba da cewa
“Na rabu da Zahra, Ba dan na tozarta ta ba, sai dan ba zan iya ci gaba da zama da ita a haka ba. Zan zauna da Nana, zan kula da rayuwarta, Ba zan taɓa bari wani abun ya sameta ba in sha Allah.”
Da mugun mamaki duk suke kallon sa,
“Akan me ka saketa?”
Ya tsinkayi muryar Hajiya Babba tana tambayarsa, Sosai yaji san yi a ransa jin yanda ta yi masa maganar. Ya numfasa kafin ya ce
“Saboda ba zan iya ci gaba da zama da ita ba Hajiya, Zahra ta kashe min Noor, ita ce wadda ta saka guba a cikin abincin da sunan ke zata kawowa. Sai kuma Nooriya ta fara cin abincin wanda ya yi sanadiyar rasa rayuwarta, Dan haka ba zan zauna da ita ba. Ba zan iya ci gaba da kallonta da igiyar aurena ba, dole na rabu da ita!”
Salati da sallalami aka fara a parlourn, Kowa na fadar abin da ke ransa. Shi dai bai iya cewa komai ba ya sunkuyar da kansa, Cikin kuka Atta ta ce
“Amma wannan yarinya ba zamu yafe mata ba, Saboda mugunta shi ne har zata iya zuba guba a abinci? Na shiga ukuna! Wace irin rayuwa ce muke ciki ne? Me yasa mutane basu ɗaukan ran mutum a bakin komai?”
Babu wanda ya ce wani abu, Ta ci gaba da kukanta tana maganganunta. Can dai Hajiya Babba ta ce
“Ya isa haka, Ku bar aibata ta, Ni na yafe mata. Idan tana sane ta yi Allah ya shiryeta, Idan kuma cikin rashin sani ta aikata to ubangiji ya yafe mana baki ɗaya, Allah yasa mufi ƙarfin zuciyoyin mu.”
Da Amin Abdusammad ya amsa. Papa ya ce
“Amin. Dan Allah abar wannan maganar a nan, duk abin da ya wuce a bar shi a ya wuce ɗin. Tun da har ya saketa to kar a sake tada maganar, ita kuma wacce da zarar ta gama takabarta za'a sallameta ta tafi gida, Dama ba wani abu ya sanya muke kin auren bare ba, muna ƙi ne saboda irin haka. Baka san wa zaka je ka auro ba, Idan ma ka yaba da halayenta to baka san su wane danginta ba, Dole shi kuma kowane tsuntsu kukan gidan su yake. Duk halin kirkinta za'a iya jan ra'ayin ta, Dan haka ya sanya muke zaba muku mata a cikin dangi inda ka san su wane iyayenta da kuma ahalinta, Ba wai muna yi bane saboda mu cutar da ku, Mu a ganin mu gata ne muke muku a matsayin ku na ya'yan mu, Dan haka dan Allah dan Annabi ku zama masu biyayya, Su iyaye ba'a ja dasu. Koda abin da suka ce bai maka ba to ka yi musu biyayya tabbas zaka ga ribar hakan, Bijire musu babu abin da zai jawo sai dana sani, Dan haka ku kiyaye.”
Jinjina kai kawai suka yi kafin suka amsa da in sha Allah, Abba ya gyaɗa kansa cike da gamsuwa ya ce