Sashe 11
Naanah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Nana ta dinga kallonsa hawaye na sauka kan fuskarta, ganin yanda ya kafeta da idanu ya sanya ta sunkuyar da kanta tana ci gaba da shessheƙar kuka. Ɗauke kansa ya yi daga kallonta ya zubawa compound ɗin gidan ido, ƙoƙarin saita kansa yake amma zuciyarsa a cunkushe take, he just can't believe a ce Nana na kula wani, wanin ma a wajen estate, how? Furzar da numfashi ya yi daga bakinsa sannan ya juyo yana sake kallonta. Kuka take sosai, fuskarta ta yi jajur, ɗauke kansa ya yi sannan ya ce"baki shirya tafiya gida ba kenan?" kasa magana ta yi sai hawaye dake fama zuba kan fuskarta kamar an buɗe famfo, kwafa ya yi ya ce"wato ga ɗan iska yana magana ko? shi yasa ki ka min banza nayi ta yi ko? wane ne wanda na gan ki dashi? wane ne wanda ya baki yanki har da kalaman soyyaya a jiki? wane shi? A ina yake? har kin yi girman da ki ke ganin zaki fara soyyaya?"
Da sauri ta kalleshi amma bata ce komai ba, harararta ya yi ya ce"I'm talking to you, har kin girma?" Tura baki ta yi muryarta na rawa ta ce"n..nifa ba wani abun bane, ai kowa yana da wanda yake so, to nima shi nake so, kuma shi zan aura, naga..."
Wata irin tsawa ya daka mata ba tare da ya san ya yi hakan ba, ya dinga mata wani irin kallo yana huci kafin ya ce"shi zaki aura? Da gaske? Daman ke zaki yanke wanda zaki aura? ke ki ke da wannan alhakin bamu sani ba?"
Murguɗa masa baki ta yi ta ce"ai Abba zan faɗawa kuma na san zai yarda" Sultan kasa magana ya yi sai kallonta da yake baki buɗe ganin bai ce komai ba ya sanya ta ɗan ɗago kanta ta kalleshi, har sannan kallonta yake da alama dai abin faɗa ya rasa. Wayarsa xe ta fara ringing hakan ya dawo dashi daga tunanin da ya tafi, kallon screen ɗin ya yi ganin sunan Hameed ya sanya ya ɗauka, maganar 2mins suka yi ya kashe wayar bai sake bi ta kan Nana ba ya sauka daga motar, ganin haka ya sanya itama ta sakko ta nufi hanyar gidansu da sauri.
****
Babu kowa a parlon sai tv dake aiki ita ɗaya, kai tsaye ɗakinta ta shige tana zuwa ta faɗa kan gado ta fashe da kuka. Maganganun Junaid ne suka dinga dawo mata, sai kuma maganganun Sultan wanda suka sake tuna mata irin ƙalubalen dake gabanta, tana nan kwance har aka fara kiran sallahr magriba. Ta tashi ta shige toilet ta yi wanka sannan ta ɗauro alwala, sauya kaya ta yi zuwa doguwar riga mara nauyi sannan ta gabatar da sallahr, ta daɗe tana rokon Allah akan ya taimaketa ya kuma yi mata zaɓi nagari kafin daga bisani ta tashi ta naɗe laddumar ta fito daga ɗakin jiki a sanyaye ta nufi ɗakin Amma.
Zaune ta sameta kan ladduma tana jan carbi, ta ƙarasa ta zauna a kusa da ita ba tare da ta ce komai ba, sai da ta kai inda zata tsaya sannan ta juyo ta kalleta ta ce"kin dawo?" gyaɗa mata kai Nana ta yi, Amma ta dinga kallonta ganin yanda fuskarta ta yi jajur yasa ta sake cewa "meya sami fuskarki?" A sama Nana ta ji maganar dan bata yi tunanin Amma zata tambayeta ba, dan haka ta shiga kame-kamen abin cewa
"U...un... Wani kwaro ne ya hau min kan fuska shine ya cijeni kuma da zafi sosai"
Amma ta kalleta ba dan ta yarda da abin da ta ce ba, sai ta taɓe baki ta ce"Ya Ramlan?"
"Tana nan klao, ta ce tana gaishe ki"
"Ina amsawa"
Amma ta ce tana jawo wayarta daga kan drawer, shiru wajen ya ɗauka ita tana danna wayarta ita kuma tana tunanin ta inda zata fara sanar mata halin da take ciki. Above 5mins kafin ta gyara zamanta muryarta a sanyaye ta ce"Amma!" ɗago idanu ta yi ta kalleta sai kuma ta ce"ina jin ki lafiya?" gabanta na tsananta faɗuwa ta ce"daman ina son nayi wata magana da ke ne" Ajiye wayar hannunta ta yi tana mai da hankalinta gareta ta ce"okay Ina ji" Nana ta dinga wasa da fingers ɗinta tana tunanin ta inda zata fara, kusan 3mins bata ce komai ba, hakan yasa Amma ta jawo wayarta tana cewa"shikenan idan baki da abin faɗa tashi ki bani waje" girgiza kanta ta yi, sai kuma ta sauke nunfashi ta ce"daman... Daman akwai wani malamin makarantarmu ne, sanda muna Aun, to shi ne.. shi ne..!"
Amma ta dinga kallonta tana jiran taji me zata ce, ganin ta yi shiru ya sanya ta ce"shi ne me? Ina jin ki?"
Fashewa ta yi da kuka tana cewa"shi nake son na aura Amma! Ni shi nakeso, bana son auran zumuncin da ake yi mana, ni shi zan aura dan Allah ki faɗawa Abba"
Tashi tsaye Amma ta yi tana mata wani irin kallo cike da tashin hankali da kuma ɓacin rai ta ce"Nana kin san me ki ke faɗa? Har yaushe ki ka yi girman da har ki ka san ki ce ga wanda ki ke so? A nan gidan? Wane kalar hauka ne yake damunki? so ki ke ki ja min masifar da ba zan iya da ita ba ko me? wato a ce yata ta bijire ko? kina son a saka ubanki a bakin duniya ko? To bari kiji koda wasa kar na sake jin makamanciyar wannan maganar a bakin ki Nana, wallahi idan ba haka ba sai ranki ya yi mugun ɓaci! Sai na saɓa miki fiye da yanda ki ke zato. Kuma Allah nagode maka daya sanya ki ka faɗi wannan maganar naji, daman nan bada jimawa ba za'a ɗaura aurenku, ki bar gabana kafin ki dauko min maganar da ba zan iya da ita ba"
Da sauri ta ɗago idanunta wanda ke zubar hawaye ta kalli Amma, furucinta na ƙarshe shi ne abin da ya dagula nutsuwarta, aure! Aure za'a musu? Innalil lahi wa ina ilayhi raji'un, ta dinga maimaitawa cikin ranta, kafin ta tashi tana kallon Amma bakinta na rawa ta ce" ki yi hakuri, banida niyyar ɓata miki rai Amma, wallahi daman sai da na faɗa masa ba zaku yarda ba, amma ya ce na gwada, Amma naji ba zan sake miki maganarsa ba, amma dan Allah kada ki saka a min aure yanzu, banaso Amma, bana so dan girman Allah, ki taimakeni Amma!"
Wani irin wawan mari Amma ta sauke mata tana huci ta ce"kin ji an tambayeki abin da ki ke so? ko kuma wanda baki so? ko daman ni ce nake zaɓar lokaci da kuma wanda zaku aura? Idan baki bar ɗakin nan ba sai ranki ya yi masifar ɓaci Nana! Leave my side!"
Wata irin azaba ce ta yi mata yawa, ga zafin mari ga kuma zafin kalaman Amma, madadin ta fita daga ɗakin sai kawai ta durƙushe a wajen ta riƙe ƙafafun Amma cikin matsanancin kuka take faɗin
"Ki yi hakuri Amma, ki yi hakuri ki taimakeni Amma! Ki yi hakuri Ammaa..!"
Kasa cewa komai ta yi, kawai ta janyeta daga jikinta ta fice ta bar ɗakin, Nana ta dinga bin ƙofar da kallo tana wani irin kuka kamar ranta zai fita, ita ba rabuwarta da Junaid ne abin da ya fi damunta ba, maganar auren da aka yi shine tashin hankalinta. Wa zata aura? Wa aka zaɓa mata? Da wa zata yi rayuwa??..
****
Sultan ya dinga kallon Papa yana jin wata irin zufa na keto masa duk da ac dake ɗakin, ganin bai ce komai ba ya sanya Papa ya sake faɗin "lafiya dai Sultan?" girgiza kansa ya yi dan bakinsa ya gagara magana, Papa ya ce"saboda haka ina fatan ka zama miji nagari a wajen matarka, ka bata kulawa iyaka iyawarka, ka sota, ka ƙaunaceta, kamar yanda kaga muna yi da iyayenku" zazzafan numfashi ya sauke kafin ya shiga jinjina kansa. Papa ya ce"kana iya tafiya" ko rufe bakinsa bai yi ba Sultan ya tashi ya fice daga ɗakin da sauri, A corridor ya haɗu da Juwaira wadda take tafe hannunta riƙe da tray, sannu da zuwa ta yi masa amma ko ta kanta bai bi ba ya shige ɗakinsa ya rufo ƙofar. Dakyar ya ƙarasa gefen gado ya zauna yana sauke numfashi, bai san sanda hawaye suka fara zuba kan kuncinsa ba, ashe ba zai samu Nana ba? Ashe ba zai zama mijinta ba? Wane irin dangi ne wannan? Wace irin al'ada ce wannan? Kenan baka da yancin zaɓar matar da zaka yi rayuwa da ita? haka zasu ci gaba da rayuwa? Ya ilahi. Maganganun da Sultan ke yi kenan cikin zuciyarsa, a fili kuwa bakinsa kamar an rufe shi da gam haka yake ji, ya gagara cewa komai, ya gagara furta wata kalma ballantana yaji sauƙi a ransa. Daga ƙarshe ma kwanciya ya yi kan gadon yana kuka kamar ƙaramin yaro.
****Mami ta dinga kallonta ganin yanda take kuka kamar ranta zai fita ya sanya ta ce"Amrah zo nan" tasowa ta yi ta ƙaraso gabanta ta zauna kusada ita, rungumeta Mami ta yi tana faɗin"kukan na mene ne Amrah? Baki farin ciki?" kasa cewa komai ta yi, sai ma wani sabon kukan data fara, Mami ta dinga rarrashinta amma sam taƙi yin shiru, suna haka ya buɗe ƙofar ya shigo, Har ya zauna kallonsu yake da mamaki, ganin yanda take kuka ita kuma tana faman rarrashinta, Alhaji Abubakar kenan, mahaifin Amrah, kuma ɗan yaya a wajen Hajiya Khadijah, Mami kuma wadda ta kasance yarta ta biyu wato Fatima, yaransu kuma su ne Amrah da Sa'eed. Mami ta kalleshi ta ce"yauwa gara da Allah ya shigo da kai dan wallahi nagaji da rarrashinta" Daddy ya ce"me aka mata?"
"Akan maganar auren nan ne, tun da aka yi maganar shikenan take faman kuka"
Da mamaki Daddy ya ce"and kukan ne mene ne? wa ya ɓata mata?" Mami ta girgiza kanta ta ce"ban sani ba wallahi" tsaki ya yi yana mai da idanunsa kan Amrah ya ce"Ke Amrah!" ɗago kanta ta yi sanin halinsa yasa ta ce"na'am Daddy"