← Book details Naanah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 124 OF 125

Sashe 124

Naanah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Na yafe miki Khadijah, Dama ban taɓa riƙe ki ba, Na san idan har ubangiji na karbar addu'ar da nake to tabbas wata tana zaki shiryu, Kuma gashi yanzu naga wannan lokacin. Allah ya yi miki albarka, Da ke da sauran ƙannen ki, Allah ya ci gaba da kare mu daga sharrin shaidan, Allah yasa mufi ƙarfin zuciyoyin mu, Da mu da sauran al'ummar musulmai baki ɗaya.”

Anty Khadijah ta sauke numfashi sannan ta ce

“Amin ya arrahamar-rahimin”

****
Nana ce zaune gefen gado tana zuba kaya a cikin trolley ɗin da ke gabanta, A sanyaye take komai tana nishi, Sakamakon cikin da ke jikinta wanda ya fito sosai. Abdusammad ya buɗe ƙofar ɗakin ya shigo yana kallon ta, Zama ya yi gefenta ya ɗauki sauran kayan ya ce

“Let me help you”

To kawai ta ce sannan ta ɗan matsar masa da trolley ɗin, Sai da ya kammala zuba kayan sannan ya rufeta. Ya juyo yana kallon ta, Kallon sa ita ma take, Tana sanye da doguwar riga ta abaya baby pink. Murmushi ta ga yana yi, Ta ɗan haɗe rai ta ce

“Uncle me ka ke wa dariya?”

Gyaran murya ya yi yana son fuskewa ya ce

“Nothing”

Ta sake zumɓura baki gaba tana kafe shi da idanu. Kallon ta ya sake yi sai kawai ya ɗauke kansa, Bai san sanda dariyar ta suɓuce masa ba, Ya dinga yi mata dariya yana kallon ta. Ita ko ta cika ta yi fam dan ƙaramin abu ne yake ɓata mata zuciya yanzun, Gaba ɗaya cikin ya mai da ta wata masifaffiya. A fusace ta ce

“Ni ai ba mahaukaciya ba ce da zaka dinga kallona kana min dariya.”

Ta ƙare maganar kamar zata yi kuka, Girgiza kansa ya yi cikin dariya da raha ya ce

“Kin san me? Gani na yi hancin ya yi kamar na Hippopotamus, Idanun ki sun sha kwalli kamar me bada maganin gargajiya...” Ya ƙare maganar yana tuntsire da wata sabuwar dariyar. Kuka ta saka ta fara dukansa ko ta ina tana cizonsa, Ya ci gaba da dariyarsa can kuma ya riƙe hannayenta still smiling ya ce

“Na tuba madam, Kin yi min kyau ne fa.”

Fashewa ta yi da kuka ta shige jikinsa tana cewa

“Ai naga ba haka ka ganni ba, Kuma wallahi bana son cikin ma.”

Dariya kawai ya yi ya rungumeta a jikinsa, Can ya shafa cikin nata yana jin yanda yaron cikin ke motsi ya ce

“Hiii unborn, Ka samu ka fito duniya mamarka ta bar ni da rigima”

Tura baki ta yi bata ce komai ba, Ya tashi da ita a hannunsa yana faɗin

“Madam haka ki ka zama? Kin ji nauyin ki kamar bag ɗin shinkafa”

Shiru ta yi masa dan ta san so yake ta yi maganar, a kwanakin nan ya mai da ita kamar wata kakarsa, Kullum cikin tsokanarta yake. Wani lokacin ta biye masa wani lokacin kuma ta yi masa kunnen uwar shegu, A haka suke fito daga gidan ya sakata a mota sannan shima ya shiga kai tsaye kuma airport suka nufa dan Nigeria zasu je suna.

****
Cike estate ɗin yake da mutane, Na birni dana ƙauye, Ashe sunan matan gidan ake. Masu decorations na musamman aka ɗauko suka zo suka yi decorating wajen, Aka saka kujeru huɗu da bannern jarirai huɗu. Sai da masu jegon suka fito sannan aka fara gane su wane, Maimoon ce da Haule, Hamida da kuma Amrah, Sun ci kwalliya cikin wani uban su lace mai azabar kyau da tsada. Kowacce an yi mata make -up a fuska suna rike da jariran su, Suma mazan haka suka shirya cikin wata dakkakiyar shadda gezner brown colour, Sun yi ɗinki iri ɗaya har Abdusammad. Sai shige da fice kowa ke yi, Suna aka yi gagarumi dan haɗe shi aka yi, aka ce a bari duk su haihu sai ayi, Kasancewar Nana na da tazara dasu sosai yasa ba'a saka da ita ba, Maimoon Mace ta haifa, Hamida da Amrah ma haka, Haule kuma ta haifi namiji. Yar gidan Maimoon sunan Ummi aka saka mata, Suna ce mata Ummi, Ita kuma yarinyar Hamida sunan Hajiya Babba aka saka mata wato takwarar Nana, Suna ce mata Ikram, Ita kuma yarinyar Amrah sunan Mommynta aka saka ana ce mata Khairiyya, Shi kuma yaron Haule aka mayar masa da sunan mahaifinsa marigayi Safwan, Ake kuma kiransa da sunan. Taro aka yi bana wasa ba, aka ci aka sha aka watsa Naira, Da daddare kowa ya tafi sai ya'yan gidan kawai, Nana kuwa kuka ta dinga yi saboda gajiyar da ta yi, Ita sam bata saba kujiba-kujiba ba a gida, Daga kwanciya sai cin abinci take. Yau kuma ta zo ta sha uban wahala dan ko zama bata yi ba, Sai da Abdusammad ya siyo mata magani ta sha sannan ya samu ta yi bacci kan ƙafarsa. Sati ɗaya kawai suka yi ya cewa Hajiya Babba zasu wuce, Ta ce sai dai ya bar Nana a nan ya tafi ta haihu a gida. Da fari ƙin yarda ya yi, Saboda ya san Nanar ce ta kitsawa Hajiya Babba haka, Dan tun a New York take ce masa ya barta a gida, Sai da Papa ya shiga maganar sannan ya bar ta ya shige shi kadai, Ko sallama ko bai yi da ita ba. Ita ma bata damu ba saboda ganin ta da ta yi cikin yan uwanta tana shiga tana fita yanda take so.

**** Tunda cikin Nana ya shiga watan haihuwa babu wanda ya ƙara samun sukuni, Ko ciwon kai taji ta dinga kuka kenan tana raki, Dama tuni Amma ta koreta daga apartment ɗin ta, A cewar ta ba zata iya da iya shegenta ba, Ta yi zamanta a Apartment ɗin Hajiya Babba dan ita ce kawai ke yi mata yanda take so. Anan ma kullum sai sun yi faɗa da Atta, Duk dare Abba zai shigo ya ganta, Da safe ita kuma taje, Duk yanda take son magana da Abdusammad basa yi, dan iyaka kiran da zata yi masa ba zai ɗaga ba. Tana ji wasu lokutan suna waya da Hajiya Babba, Sai dai ta yi kasaƙe tana saurara ko zai ce a bata wayar, amma har su gama wayar ba zata ji ya ambaceta ba, Tun Hajiyar bata fahimta har sai da ta gane, Ranar wata asabar ya kira wayar suna zaune a parlour tare tana cin abinci. Bayan sun gama hira Hajiya Babba ta ce masa

“Arɗo kana sanin halin da Nana kuwa ke ciki? Yaushe zaka zo ne?”

Tun da yaji Hajiya Babba ta yi maganar to ya san Nanar na kusa, Dan haka ya yi gyaran murya ya ce

“Ba sai naji ba Hajiya, Kawai ki gaisheta, nan ba da jimawa ba zan zo. Akwai yarinyar da muka daidaita da ita ina son na zo mu yi zancen dake, bana son a ɗau lokaci mai tsayi.”

Bata san sanda ta fara dawo da abincin data zuba a bakinta ba, Hawaye suka fara ambaliya akan fuskarta. Girgiza kai Hajiya Babba ta yi dan ta san ya yi ne dan ya kunno ta, Musamman data saka wayar a handsfree. Jiki a sanyaye Nana ta tashi sum sum ta bar parlourn, Tana zuwa ta shige ɗakin Hajiya Babba ta saki wani raunataccen kuka ta fadi a wajen, Ihu ta dinga yi tana birgima, Hajiya ta kashe wayarta ta tashi ta bi bayanta, A kwance ta sameta tana kuka kamar ranta zai fita, Ta ƙarasa ta ɗagota ta ce

“Ke mene haka? Da wasa fa yake miki”

Bata yi magana sai kukanta da take yi, Hajiya Babba ta ce ta tashi su koma ƙasa, Ta miƙe tana ƙoƙarin tafiya ta dafe mararta saboda wani irin murɗawa da taji ta yi. Ƴar ƙara ta saki wanda ya sanya Hajiya Babba ta kalleta ta ce

“Mene ne?”

“Marata zata cire Hajiya, Shikenan zan mutu...”

Ta fara kuka kamar wadda ake duka, Ganin abun nata na gaske ne ya sanya Hajiya ta koma ƙasa ta ɗauki wayarta ta kira Sultan da Abba, Koda ta koma kwance ta sameta sai ihu take tana juye-juye wanda ya tabbatar da naƙuda ce ta zo mata. Abba ne ya ɗauketa ya kai har mota aka wuce da ita asibiti, Iyaka tashin hankali sun gan shi akan Nana, Dan ban da ihu babu abin da take. Duk wani makusancinta sai da ta kira sunansa, Abdusammad kuwa ta kira shi yafi sau ɗari. A haka har Allah ya hukunta ta haifi yaranta Mata guda biyu, Farare sol dasu kamar iyayensu. Gaba ɗayan su da Abdusammad suke kama, Idanun su ne kawai irin na Nana. Zo ka ga murna cikin Family ɗin Muhammad Shuwa, Kafin ka ce kwabo an cika asibitin da jama'a, Aliyu da kansa ya kira Abdusammad ya sanar da shi haihuwar bayan ya gama raina masa hankali. Ai ko awa bai ƙara ba ya fara shirye-shiryen dawowa Nigeria.

****
Kwana ɗaya da haihuwar ya zo, lokacin har an sallamesu sun dawo gida, Tana apartment ɗin Hajiya Babba har sannan. Duk yanda Amma ta so tafiya da ita kasawa ta yi dan kar aga zaƙewarta, Musamman da taga yanda Atta ke zuba rashin ta ido akan duk wanda ya yi maganar uwar ya'yan ko kuma ya'yan. Around 2:00 pm ya shigo parlourn bakinsa ɗauke da sallama, Atta na ganinsa ta saki guɗa tana murmushi ta ce

“Ga uban Ya'yan Allah ya kawo shi, Kai wannan ɗa ka ban mamaki. Ka ga yara Masha Allahu”
Chapter 124 · 0% Book details