← Book details Naanah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 125

Sashe 22

Naanah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Tare zamu fita da Abba, zan sanar dashi" cewar Abdusammad yana tashi daga wajen, okay kawai ta ce sannan ita ma ta nufi upstairs. Ɗakin da Nana take ta fara shiga ta sameta zaune ta yi shiru, ta dinga kallonta kafin ta ce“Nana baki shirya ba?” ɗan murmushi ta yi ta ce“yanzu zan shirya” okay kawai Zahra ta ce sannan ta juya ta fita, koda ta sake dawowa bata sami Nana a wajen ba sai ƙarar ruwa da taji wanda ya tabbatar mata da tana bayi, ta ajiye mata welfolded Abayar a gefen gado sannan ta fita. Ƙarfe 11:45 na safe Nana ta fito parlon sai zuba ƙamshi take, ta shirya cikin ash colour ɗin Abayar me manya flowers a jiki, ta yi rolling mayafin abayar akanta ta yi wani irin kyau. Zahra ta dinga kallonta tana murmushi kafin ta ce“kaga shuwar asali irin wannan kyau haka?” tura baki ta yi ta ce“ayyah Aunty Zahra banso wallahi” dariya Zahra ta yi tana gyarawa Noor hular kanta ta ce“to naji” shiru ta yi can kuma ta ce“yauwa aunty Zahra ina wayarki?” kan kujera ta nuna mata tana faɗin “gata can” okay kawai Nana ta ce sannan ta ƙarasa ta ɗauka, face id ne akai dan haka ta miƙa mata ta ce“ki cire min zan yi hoto” murmushi kawai Zahra ta yi sannan ta cire mata, ta karɓa ta fice daga parlon tana murmushi. Garden ɗin gidan ta ƙarasa ta shiga dial ta saka numbern Junaid wadda ta gama haddacewa sannan ta danna kira, sai da ta kusa katsewa sannan ya ɗaga, Junaid da ke tuƙi ya ce

“Hello wake magana?”

Ajiyar zuciya Nana ta sauke jin muryarsa, ta ɗan yi shiru har sai da ya sake magana ya ce

“hellooo”

“sir ni ce”

Junaid ya gangara gefen titi yayi parking sannan ya ce

“Nana ina ta kiran ki baki ɗaga wayata why?”

Numfasawa ta yi ta ce

“bana gida ne, ina wajen uncle ɗina”

Nannauyar ajiyar zuciya ya sauke ya ce

“okay, yanzu ya ake ciki?”

Sai da ta sake leƙawa ta tabbatar da babu wanda ya tawo sannan ta ce

“zamu fita da matarsa, zan kira ka idan mun je gidan sai ka zo”

Jinjina mata kai ya yi ya ce

“okay, shikenan zan kira ki”

Girgiza kanta ta yi da sauri ta ce

“no kar ka kirani, ni zan kira ka”

Okay ya ce sannan suka yi sallama ya kashe wayar. Ta sauke ajiyar zuciya sannan ta goge call log ɗin ta shiga Snapchat, ko hoto biyu bata yi ba Noor ta ƙaraso wajen da gudu ta ce"Aunty Nana ki zo in ji Ummi” okay ta ce sannan ta riƙe hannunta suka bar wajen, Zahra da ke bayan motar ta kalleta ta ce“hoton ya isa haka ai Nana zo mu tafi” murmushi kawai ta yi sannan ta zagaya ɗaya side ɗin ta shiga motar tare da Noor, drivern ya ja motar suka bar compound ɗin.

08106608363
Nanameera.*🌹 NAANAH 🌹*

Page 14...

Abba ya ɗan yi murmushi kafin ya ce"like how kenan tayaya ka ke tunanin haka zai yiwu?” Abdusammad ya ɗan kalli compound ɗin gidan inda bishiyu ke kaɗawa da sauri da sauri saboda iskar da ake da sauri da sauri, ya sauke numfashi sannan ya ce“Abba so nake abar maganar auren nan dan Allah, yara ne ƙanana fa” ɗan murmushi irin na manya ya yi kafin ya ce“to mene ne dan an yi aurensu yanzun? sun kammala karatun secondary, to mene ne abin da za'a jira?” Abdusammad ya girgiza kansa ya ce“a'a Abba, at least ya kamata ace ko degree sun haɗa, kaga sannan sun ƙara hankali sai a musu auren” shiru Abba ya yi bai sake magana ba, shima Abdusammad ɗin bai damu da rashin maganar ba ya ci gaba da danna wayarsa.

****
Barraks road,
Gibson jalo.

A babban compound ɗin gidan motar ta yi parking, Zahra ta sauke ajiyar zuciya sannan ta fito daga motar, ita ma Nana ta fito tana ƙarewa babban compound ɗin gidan kallo, bishiyu da flowers sun cika ko ina, Zahra ta zagayo tana riƙe da hannun Noor ta ce“muje Nana” okay kawai ta ce sannan suka nufi hanyar balcony ɗin gidan. Bakinsu ɗauke da sallama suka shiga, Ta ajiye wayar gefenta ta tashi tana murmushi ta ce“laaa aunty sannu da zuwa” Zahra ta yi murmushi tana kallon budurwar mai matukar kama da ita ta ce“Safeena kina zaune, yauwa” daga haka ta nufi kan kujera ta zauna. Safeena ta ɗan kalli Nana ta ce“welcome sis” murmushi Nana ta yi ta ce“thank ya ki ke?”

“Alhamdulilah”

Ta ce tana komawa ta zauna, ita ma Nana tafiya ta yi ta zauna kan ɗaya daga royal cushion ɗin dake zagaye da ƙaton parlon, Safeena ta kama hannun Noor tana faɗin “wow aunty ashe Noor ta girma” ta ƙare maganar tana ɗorata kan cinya. Murmushi Zahra ta yi ta ce“eh yar taku ta girma mana, Ina Aunty Khadijah da Umma?”

“Umma tana sama fa, ita kuma Aunty bata nan sun fita da Siyama”

Okay Zahra ta ce sannan ta miƙe ta nufi saman da sauri, Nana ta bita da kallo sai kuma ta ɗan jingina da kujerar tana sauke numfashi. Zahra ta tura kofar bedroom bakinta ɗauke da sallama, Umma dake zaune ƙasan gado tana jan carbi ta ce“wa'alaiki salam, Fatima” ta ƙare maganar tana gyara zamanta, fuskarta ɗauke da murmushi ta ƙarasa ta zauna gefenta ta ce"Ummata”

“ya mai gidan naki?”

Sai da ta kwanta kan cinyarta sannan ta ce“lafiya kalau, ya ce an jima zai bi yo ya gaisheku”

Jinjina kai Ummar ta yi sannan ta ce“Ina Noor ɗin?”

Murmushi Zahra ta yi ta ce“tana ƙasa wajen Safeena”

Okay Umma ta ce. Shiru ne ya biyo baya kowa da abin da yake tunani can kuma Zahra ta ce“laa Umma wai ina Aunty Khadijah?”

“ta fita kin san halinta dai ba son zama take ba, tuni ta fice”

Murmushi Zahra ta yi ta ce“hajiya Aunty Khadijah kenan, Allah ya kawo mata miji ta yi aurenta dai”

“to san auren take Zahra? Ai bai dameta ba, tafi son ta yi ta yawo daga nan sai nan” girgiza kai Zahra ta yi ta ce“a'a Umma tana so mana, ai kowa ce mace na son ta yi aure duk da ta taɓa yi amma zawarci ai bashi da daɗi” taɓe baki Umma ta yi ta miƙe sannan ta ce“ai duk kun fita hankali, ita ce babba amma babu abin da ta iya sai shirme” daga haka ta nufi ƙofa ta fice daga ɗakin, jim Zahra ta yi a wajen tana tunani kafin ta miƙe ta fito ita ma.

Umma ta dinga kallon Nana fuskarta ɗauke da fara'a har ta ƙaraso wajen ta ce“wa nake gani kamar Nana?” zamowa ta yi daga kan kujerar ta gaisheta, Umma ta zauna kusa da Safeena tana faɗin “lafiya kalau Khadijah, haka ki ka girma?” sunkuyar da kai ta yi a hankali, Umma ta sake cewa“ina mamanki?”

“tana gida”

Ta yi maganar a sanyaye, jinjina kai Umma ta yi ta ce“Allah sarki na kwana biyu rabon da na ganta” ɗan murmushi Nana ta yi bata ce komai ba dai dai nan Zahra ta sakko daga saman, ta ƙaraso wajen Nana tana faɗin “umma kin ga yanda Nana ta girma ko?”

Jin jina kai Umma ta yi ta ce“yanzu nake faɗa nima, kamar ba ita ba ce ki ke zuwa da ita ba lokacin tana ƴar ƙarama, bata fi girman Noor ba” Zama Zahra ta yi sannan ta ce“wallahi amma yanzu ta zama ƙatuwa ta kamoni a jiki” langwaɓar da kai Nana ta yi kamar zata yi kuka ta ce“kai Aunty”

“ƙarya nayi? Yanzu fa kin yi girmana wallahi sai dai a ce idona ya fi naki buɗewa, kin ga Umma aurensu fa za'a yi nan da 6weeks”

Riƙe haɓa Umma ta yi ta ce“Allah alhakamu, har lokaci ya zo? Daɗina dasu auren wuri na huta kafin yaro ya fanɗare, to wa zata aura a cikin samarin gidan? Ko sun daina auren Zumuncin?”

Ummar ta jera mata tambayoyin a tare. Murmushi Zahra ta yi idanunta zube kan Nana ta ce“Safwan zata aura, ina zasu daina auren zumunci Umma?”

Waro idanu Umma ta yi ta ce“Ikon Allah wane Safwan ɗin? Ban san shi ba” Girgiza kai Zahra ta yi ta ce“a'a dai baki gane shi ba, Safwan fa ɗan autan su Daddyn Noor” jinjina kai Umma ta yi ta ce“eh na gane shi kuma, wani mai kama da Abdusammad ko?”

“eh shi fa kin gane shi ma” cewar Zahra tana murmushi. Kallon Nana Umma ta yi ta ce“Allah ya sanya Alkhairi Khadijah ya baku zaman lafiya, amma ki yi ta haƙuri, aure sai da haƙuri”

Jiki a sanyaye Nana ta ce“to Umma in sha Allah”

“Ni kam suna burgeni wallahi Aunty, ko nima zaki sama min miji a cikin estate ɗin ne?” Safeena ta yi maganar cike da zolaya, riƙe baki Zahra ta yi tana faɗin “kee rufa min asiri, su basu auren haɗi” ta ƙare maganar cike da raha, Safeena ta ce“assha da dai kin duba, a yan samarin nan nasu a sama min ɗaya na aura, wallahi suna mugun burgeni bama ni kaɗai ba, ko a cikin jama'a zaki ji ana maganar dangin. Haka rannan wata course mate ɗina wai zata min ƙarya ai tana dating da ɗaya daga cikin ya'yan gidan na ce to wallahi ƙarya take dan Yayata babban ɗan gidan take aure” tuntsirewa da dariya Zahra ta yi ta ce“wato ke ga gwana ko?” murmushi Safeena ta yi ta ce“ai gaskiya ce, ke fa Allah ne ya baki shi wallahi, daman ance matar mutum ƙabarinsa amma idan ba dan haka ba ya za'a yi ki aure shi” ɗan haɗe rai Zahra ta yi ta ce“to kar ki faɗa min magana kuma”

Zazzaro idanu Safeena ta yi tana murmushi ta ce“nii to Allah ya baki haƙuri Hajiya” ta ƙare maganar tana gyarawa Noor gashin kanta.
Chapter 22 · 0% Book details