Sashe 43
Naanah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Murmushi kawai ya yi dan ya san ta dai faɗa ne amma ba har ranta ba. Ya ɗago fuskarta da hannunsa ɗaya yana ƙare mata kallo ya ce“Zahra kenan, ki daina damun kan ki kinji. Ni Abdusammad Muhammad Shuwa banida niyyar ƙarin aure, ban da niyyar yi miki kishiya. A tsarin rayuwata mace ɗaya kaɗai ta wadaceni, muddin na samu mai kyakkyawan hali kamar dai ke ɗin nan” ya ƙare maganar yana jan kumatunta cike da zolaya. Bata san sanda dariya ta kufce mata ba, ta kifa kanta akan cinyarsa tana yi a hankali. Shima murmushi kawai yake dan yaji daɗin ganinta cikin farin ciki.
****
Bayan sallar magriba babu daɗewa ta fito parlon tana sanye da wasu English wears riga da wando wanda basu kamata ba, gashin kanta a gyare kamar koda yaushe ta tufke da riboom ya sauka har gadon bayanta. Ta ƙaraso parlon jiki a sanyaye tana kallon Amma da ke zaune a kusa da Abba tana nuna masa abu a waya, Amma na ganinta ta mike tana faɗin “gata nan ma” da idanu Abba ya kalli Nana sai kuma ya ce“yauwa daughter zo nan” babu musu ta ƙarasa ta zauna in da Amma ta tashi tana kallonsa. Abba ya dinga kallonta ganin yanda ta rame kamar ba ita ba ya ce“Nana lafiyar ki? Akwai abin da ke damunki?”
Ƙirƙiro murmushi ta yi ta ce“Babu komai Abba, kawai nagaji ne” shiru ya yi yana nazarin maganarta can kuma ya ce“anyway tashi muje ki rakani” to kawai ta ce sannan ta mike ta koma daƙinta. Wayarta da ke gefen drawer ta dauka dan yanzu sam bata yarda ta yi nesa da ita, ta buɗe press ta ɗauki wata Dubai chiffon Abaya mara nauyi ta ɗora kan kayanta sannan ta fito parlon. Tsaye ta same shi hannunsa riƙe da car key da alama ita yake jira, tana fitowa ya kama hannunta suka fice daga parlon.
A cikin wata Lexus jeep black colour suka fita daga gidan, Abba da kansa ke driving dan baya buƙatar wani a tafiyar tasu. Nana ta dinga kallon titi ba tare da ta tambayeshi inda zasu je ba, saɓanin da, da idan zai fita da ita ta dinga tambayarsa kenan har sai ya gaji. Abba ya ɗan yi mamaki rashin tambayar tata dan haka ya gyara zamansa yana murza steering motar a nutse ya ce
“Nana”
Ɗago idanunta ta yi ta kalleshi a sanyaye ta ce“na'am Abba”
Yana ƙoƙarin shan kwanar round about ɗin ya ce“tell me me ki ke so? Like abubuwan da ki ke so irin na amare” Nana ta ɗan yi shiru can kuma ta ce“a'a Abba bana son komai” sai da ya juyo da fuskarsa ya kalleta dan ba ƙaramin mamaki hakan ya basa ba. Ya mai da idanunsa kan titi yana faɗin “Na riga da na gama shirya komai, akwai waleema da za'a yi bayan ɗaurin aure wanda duk abokaina zasu halarta, and I want to you to be there saboda akwai waɗanda muka haɗu dasu a makkah time ɗin da muka ce Hajj dake last two years sun ce suna son su ganki, basu san kin girma haka ba” ya ƙare maganar yana murmushi. Nana da ke saurarensa ta jinjina kanta ba tare da ta ce komai ba, Abba bai damu da rashin maganar ta ta ba ya ci gaba da faɗin
“And ina son ki kula sosai Nana, aure ba ƙaramin abu bane, ki yi kokarin zama yarinyar kirki a gidan mijinki, idan ki ka yi haka zan yi alfahari dake. Kin san ke kaɗai ce yata, ke kaɗai Allah ya bani a matsayin kyauta, so duk wani abu da iyaye ke yiwa ya'ya ko kuma suke so daga gare su ni akan ki nake da wannan burin. U're my last hope Nana, Dan Allah kada ki bawa Abbanki kunya, na sani kina da sauƙin hali amma bakya ji Nana, bakya son zaman lafiya. Dan Allah dan Annabi ki bar wadannan ɗabi'un a matsayin yarinta, ki sani idan ki ka yi aure kin riga da kin girma. Ke ba yarinya ba ce kamar da. Zaki zama uwa ne, dan haka dole ki sauya kin ji ƴar albarka, kada ki bari nayi kuka da ke Nana. Idan har ban samu kwanciyar hankali daga gareki ba ki sani babu wani wajen da zan samu kuma, daga gani har mahaifiyarki ba zamu so koda dana rana ɗaya a kawo mana ƙararki ba. Hakan zai sosa ran mu and na san ba zaki so ran mu ya ɓaci ba ko?”
Abba ya ƙare maganar yana kallonta dan tabbatar da abin da yake son sanin, Allah sarki Nana ban da kuka babu abin da take, dan ba ƙaramin tausayi Abba ya bata ba. Me ta aikata ne? Taya zata iya kaucewa abin da yake gabanta domin ta faranta ran iyayenta? Ya zata yi da Junaid da Aunty Zahra? Wadannan tunanin su ne suke hanata bacci duk dare. Waɗannan tunanin su ne abin da ke neman haifar mata da ciwon zuciya, Ta kifa kanta a tsakanin cinyoyinta tana sake rushewa da wani irin kuka.
Abba da mamaki ya cika shi ya gangara gefen titi ya yi parking ya juyo gaba ɗaya yana kallonta fuskarsa cike da damuwa ya ce
“Nana why? Mene ne? Maganar dana faɗa ce ta saka ki kuka?”
Abba ya jera mata tambayoyin yana ƙoƙarin ɗagota.
Madadin ta bashi amsa sai kawai ta rungumeshi tana sake fashewa da sabon kukan, Abba ya dinga shafa kanta yana cewa ta yi shiru amma sam bata saurarensa. Sai da ta yi mai isarta sannan ta fara sauke ajiyar zuciya tana shessheƙar kuka, Ya ɗago fuskarta yana kallonta ya ce“mene ne?”
Cikin shassheƙar kuka ta ce“Abba tsoro nake ji, wallahi tsoro nake ji Abba” ta ƙare maganar wani kukan na tawo mata, Murmushi irin na manya Abba ya yi sannan ya ce“ki yi haƙuri kin ji, ki daina jin tsoro ina nan babu abin da zai sameki” Abba ya yi magana cikin sigar rarrashi. Da kyar ta daina kukan amma bata bar jikinsa ba shima bai takura mata ba ya yi wa motar key suka ci gaba da tafiya. Har suka je wajen babu wanda ya sake cewa komai, Abba ya yi parking yana kallonta ya ce“Nana taso” a sanyaye ta ɗago kanta wanda take jin yana wani irin sara mata saboda tsabar kukan da take. Ya sauka daga motar sannan ita ma ta sauko tana ƙarewa wajen kallo, Babban shagon furnitures wanda yana ɗaya daga cikin manyan shagunan furnitures a cikin garin Yola. Abba ya riƙe hannunta cikin nasa sannan suka nufi cikin store ɗin.
Kai tsaye second floor suka nufa, Nana ta dinga bin ko ina da kallo dan bata taɓa zuwa irin wajen sai da kayan furnitures ba, duk da yanda take jin babu daɗi hakan bai hanata sakin jikinta tana kallon komai ba, a wani waje mai kama da reception suka zauna Abba ya ɗauko wayarsa ya danna wata lamba sannan ya kau kunne, ita dai Nana ta dinga kallonsa ba tare da ta ce komai ba, after 2mins ya sauke wayar ya sakar mata murmushi ganin yanda take kallonsa. Dakyar ta iya mayar masa da murmushin sai kuma ta sauke kanta ƙasa tana jin wani irin abu ya tsaye mata a ƙirji. Suna nan zaune har bayan mintuna biyar sannan mutumin ya sakko daga sama ya ƙaraso wajen yana kallon Abba cike da girmamawa ya gaishe shi, Abba ya amsa sannan ya tashi yana rike da hannun Nana suka bi bayan mutumin. Can hawa na uku suka hau, wanda komai na wajen yafi kyau da tsada, Nana ta dinga kallon kayan furnitures ɗin masu matuƙar kyau. Ko ba'a faɗa maka ba ka san kuɗi ke magana a wannan wajen, Abba ya yi murmushi yana sakin hannunta ya ce“yanzu ki zaɓa wanda ki ke so anan”
Da sauri ta kalleshi. Ya gyaɗa mata kai, sai kawai ta shige jikinsa tana sakin marayan kuka, girgiza kai Abba ya yi ya ɗago kanta yana murmushi ya ce“ke ba zaki daina rigima ba ko?” hannunta ta sanya ta rufe fuskarta tana ɗan dariya ƙasa-ƙasa. Ya ɗan kalli wajen sai kuma ya ja hannunta ya ce“c'mon muje na tayaki zaɓa” jiki a sanyaye Nana ta bi bayansa, suka dinga kallon kayan tare yana nuna mata wanda suka yi kyau. Abba ya taɓota sanda idanunsa suka sauka kan wasu Fendi casa Italian furniture ta dinga kallonsu ba tare da ta ce komai ba, Abba ya ja kumatunta yana fadin“ko basu miki kyau ba mu sauya?” girgiza masa kai ta yi dan itama kayan sun burgeta. Ya kalli mutumin dake tsaye bayansu ya nuna masa kayan ya ce“wannan muke so” okay kawai ya ce sannan ya nuna musu inda zasu biya, Abba ya yi gaba tana biye dashi. Cashier ɗin ya kalli kayan da suka nuna sannan ya ɗan duba system kafin ya ce
“10.5m”
Okay kawai Abba ya ce sannan ya miƙa masa atm card ɗinsa, Nana ta dinga kallonsa baki buɗe dan gaba ɗaya ta rasa abin cewa. Sai da aka cire kuɗin sannan aka basu receipt sannan ya juyo ya kalleta ya ce“muje” muryarta a ƙarye ta ce
“Abbaaa.”
Yanda ta yi maganar a sanyaye kamar wani abin na damunta ya sa ya ce“mene ne?” kamar zata yi kuka ta ce“sun yi tsada fa” taɓe baki Abba ya yi sannan ya ce“Ko?” ya yi maganar yana yin gaba ba tare da ya jira amsarta ba. Da idanu kawai Nana ta bi shi sai kuma tabi bayansa ganin yana shirin tafiya ya barta. Har suka koma mota babu wanda ya ce wani abu, ita gaba ɗaya zuciyarta a dagule take, ta rasa wani irin abu ya kamata ta yi, farin ciki ko kuma baƙin ciki. Taya ya zata iya bijirewa umarnin Abba? Ta ya zata iya cewa ba zata auri Safwan ba? To amma idan ta yarda da auren Safwan mene ne makomarta a wajen Junaid da Zahra? Zasu fitar da hotunanta domin su shiga tsakaninta da iyayenta da kuma danginta ko kuwa zasu haƙura ne su daina mata barazanar?.
“Ki zauna anan zan amso invitation cards ɗin ku”