Sashe 17
Naanah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ta gyaɗa masa kai sannan ta kashe wayar, kifa kanta tayi jikin ƙarfe hawaye na zubowa kan fuskarta kamar an buɗe famfo, ji take kamar ta je ta fadawa Abbanta bata son Yaya Safwan sir Junaid take so. Amma ta san ko ta faɗa ba zai taɓa tasiri ba, sai dai ya haddasa gaba tsakaninta dashi, domin Abba na ɗaya daga cikin wanda suka riƙi wannan al'adar kamar addini. Ta jima a wajen kafin ta ɗago kanta jiki babu kwari ta koma gida, zaune ta sami Amma a parlon tana cin abinci, ta dinga kallonta sai kuma ta ce"ina ki ka je?"
Sai da taji zuciyarta ta buga, ta ɗan haɗa kalmomin bakinta da kyar ta ce"da....daman naje waje ne zan yi waya, kuma nan babu network"
"Dawa ki ke wayar?"
Amma ta yi tambayar tana kai spoon ɗin shinkafar bakinta, rasa abin cewa ta yi dan bata yi tsammanin zata mata tambayar ba, jin bata ce komai ba ya sanya Amma ta ce"baki ji me nace ba ne?"
"eh?"
Nana ta yi maganar tana kallonta, harararta ta yi kafin ta ce"kina tunanin banza da wofi baki ji me nace ba right?" ta sunkuyar da kanta bata ce komai ba, tsaki Amma ta yi ta ce"je ki ɗebi abinci ki ci my friend, and kada ki daina tunani ki bari hawan jini ya kamaki" sauke ɓoyyayiyar ajiyar zuciya ta yi sannan ta nufi kitchen ɗin da sauri tana godewa Allah a ranta.
****
Ummi ta dinga kallonsa ganin yanda yake maganar da zallar gaskiyarsa yasa ta ce"Sultan! Sultan! Sultan!" ɗago jajayen idanunsa ya yi ya kalleta murya a ciki ya ce"na'am Ummi"
"Sau nawa na kira ka?"
Kallonta ya yi sai kuma ya ɗauke kansa yana huci, kwafa ta yi sannan ta ce"kar ka jawo min magana, kar ka jawon abin da zai dameni, ni ban aikeka ba, mahaifinka shi ne babba a wajen zartar da wannan hukuncin, saboda haka dole ka yarda dashi. Kar ka je ka yi abin da zai zo ya ɓata zumunci"
Tashi tsaye ya yi yana kallonta muryarsa a dake ya ce"nifa ba ɗauko miki magana zan yi ba Ummi, ni babu abin da zan yi, kawai zan fadi gaskiyata ne, ni ba za'a min auran dole ba wallahi! Kamar yanda Yaya Abdusammad ya dage akan ba zai ba kuma a ka bar shi haka nima ba zan yarda ba wallahi, saboda wannan ba adalci bane, shi an bar shi ya auro wadda yake so sannan dan an zo kan mu a ce za'a ci gaba da auren zumunci, wallahi ba zamu yarda..."
Marin da Ummi ta sauke masa shi ne ya hana shi ƙarasa faɗar abin da ke bakinsa, ya dinga kallonta hannunsa dafe da kuncinsa, cikin tsananin ɓacin rai take kallonsa tana nuna shi da yatsa ta ce
"Wallahi idan na sake jin makamanciyar wannan maganar a bakinka sai na saɓa maka fiye da tunaninka! Dole ne ka yi biyayya ga manyanka! Da kai da Abdusammad ba abu ɗaya bane! Kuma ba zaku taɓa zama ɗaya ba, dan haka kai baka isa ka ce zaka ɓata abin da aka gida shekara da shekaru ba! Idan kuma har ka ce zaka yi hakan to sai dai ka nemi wata uwar ba dai ni ba!"
08106608363
Nanameera.*🌹 NAANAH 🌹*
Page 11...
Kallonta ya dinga yi ba tare da kiftawa ba, Ummi ta yi tsaki sannan ta juyar rai ɓace ta bar wajen, sauke idanunsa ƙasa ya yi yana ƙoƙarin mai da hawayensa, dakyar ya ja ƙafarsa ya bar wajen jiki a sanyaye. Abba ya dinga kallonsa yana jin jina kai har ya kai ƙarshen maganar sannan ya sauke numfashi ya ce"yanzu me ka ke nufi Abdusammad?" gyara zamansa ya yi kana ya ce"yauwa Abba, what i mean is kada a tilastawa yaran nan, a bari su zaɓi wanda suke ganin zasu iya rayuwa dashi. Saboda aure ba fa ƙaramar magana ba ce, rayuwa ce wadda ake tunanin a yi ta har abada, so idan har za'a ɗorasa a bisa son zuciya ina ganin za'a samu matsala ne babba ba ƙarama ba" Girgiza kai Abba ya yi yana ƙoƙarin tashi daga kan sofar ya ce"kana so ka ce a bar magana auren nan? Kada a musu aure ko me ka ke nufi?" da sauri ya ƙaraso gabansa ya ce"a'a Abba ba wai haka nake nufi ba, ina son dai a tambayi kowacce wanda take so a cikinsu, haka suma mazan a tambayesu"
"Akan me? A saboda mu bamu isa mu zaɓa musu mazajen aure ba?"
Abba ya yi maganar a ɗan fusace. Furzar da iska ya yi daga bakinsa sannan ya ce"a'a Abba, kun isa mana, amma kada a yi musu abin da zai ɓata farin cikinsu, ni nawa tunanin kenan"
"To an gode da shawara, amma ba za'a fasa wannan auren ba!"
Daga haka ya juya ya bar parlon kamar zai tashi sama, Girgiza kai Abdusammad ya yi yana tunanin ta inda zai ɓullowa al'amarin, yafi 3mins a tsaye kafin ya sauke numfashi ya fice daga parlon shima.
****
Hajiya ta dinga kallonta sai kuma ta ce"ban gane ba?" tura baki Nana ta yi ta ce"haka Mama ta ce wai Yaya Safwan zan aura, haka ne Hajiya?" Jinjina mata kai ta yi ba tare da ta yi magana ba, Nana ta ɗan kwaɓe fuska ta ce"amma Hajiya me ya sa sai shi zan aura? naga...."
"Bana son sake jin wannan maganar a bakinki kin ji Nana!"
Hajiya ta yi maganar fuska babu wata walwala, numfashi Nana ta sauke sannan ta gyaɗa mata kai. Ta ce"ki je kitchen wajen Rabi ki ce ta baki robar" Toh kawai ta ce sannan ta tashi jiki a sanyaye ta nufi kitchen ɗin, After 2mins ta fito hannunta riƙe da wata farar roba mai ɗauke da dambun nama. Ta dinga kallonsa kafin ta ƙaraso a sanyaye ta ce"Hajiya sai da safe"
"Allah ya tashe mu lafiya"
Hajiya ta bata amsa idanunta na kan Abdusammad, Amin ta ce sannan ta ɗan kalleshi ganin ba ita yake kallo ba ya sa a sanyaye ta ce"uncle sai da safe" Jinjina kansa ya yi ba tare da ya ce komai ba, ita ma kuma bata tsaya jiran amsar tasa ba ta juya ta fice daga parlon. Hajiya Babba ta ɗan yi murmushi mai kama da na takaici kafin ta ce"Abdusammad! Abdusammad! Abdusammad!"
"Na'am Hajiya"
Ya amsa mata still looking at her. Fuskarta babu alamun fara'a ko annuri ta ce"kana son ka ɓata min rai ne daga zuwanka? ko kuma kana son tarwatsan iyali daga dawowarka?"
Numfasawa ya yi kafin ya ce"Allah ya huci zuciyarki Hajiya, amma ba haka nake nufi ba, kawai dai..."
Dakatar dashi ta yi ta hanyar ɗaga masa hannu, ya dinga kallonta bai ce komai ba. Tashi ta yi tana kallonsa ta ce"kai ka yi abin da ka ke ganin shi ne dai dai, ka auri wadda ka ke ganin ita ce dai dai da kai, duk da baka shawarceni ba a matsayina na mahaifiyarka. Amma na yi haƙuri na kau da idona daga kan ka, ba dan ban ji zafin abin da ka yi min ba, ba dan ba'a dinga ƙananun maganganu a cikin gidan nan ba, ba dan zuciyata bata min zafi kullum ba, sai dan nayi hakuri kuma ina jin wata rana zan sauya wannan al'amarin. Saboda haka kada ka zo ka bata min rai da zan ji daman baka dawo ba dan Allah Abdusammad!"
Sunkuyar da kansa ya yi yana jin ransa a dagule dan ko kaɗan baya son ɓacin ranta, ta sauke numfashi sannan ta juya ta shige ciki abinta. Da idanu ya dinga bin ta har ya daina hangota, ya mike jiki a saluɓe ya fice daga parlon shima.
Koda ya shiga gida zaune ya tadda Zahra a parlon tana jiransa, sanye take da wata sleeping dress doguwar riga mara nauyi wadda ta tsaya mata iya gwuiwarta, ta yi parking ɗan gashinta da bashi da yawa a ƙasan ƙeyarta. Sai tashin ƙamshi take gwanin sha'awa, tana ganinsa ta tashi tana murmushi ta ce"sannu da zuwa" jinjina mata kai kawai ya yi sannan ya nufi hanyar upstairs, Zahra ta bishi da kallo ganin har ya haye sai kuma tabi bayansa. Yana shiga ɗakin ta shigo, ta saki handle ɗin ƙofar har sai da ya yi ƙara wadda ta sanya ya juyo ya ɗan kalleta sai kuma ya ɗauke idanunsa.
"Lafiya da Abu Noor?"
Bai juyo ba haka kuma bai bata amsa ba, ya zare rigar da ke jikinsa ya nufi toilet. Zama ta yi gefen gado tana tunanin wanda ya sake ɓata masa rai da daren nan, ta dinga jiransa har bayan 20mins sannan ya fito daga toilet ɗin sanye da bathrobe jikinsa sai ɗigar ruwa yake. Gaban dresser ya tsaya ya gyara kansa sannan ya ɗan shafa body lotion ɗin da yake sakawa ya feshe jikinsa da turare nan da nan ɗakin ya ɗauki wani ƙamshi na musamman. Press ya ƙarasa ya buɗe ya dauko pyjames maroon colour ya saka sannan ya juya yana shirin fita daga ɗakin, ganin haka ya sanya ta tashi tana kallonta muryarta na rawa ta ce
"Ina kuma zaka je? Idan wani abun aka yi maka ka sanar dani dan Allah"
Cak ya tsaya amma bai juyo ba, ta ƙarasa wajensa da sauri ta rungumeshi ta baya tana shessheƙar kuka, ji ya yi jikinsa ya yi sanyi, ya janyo hannunta ya dawo da ita gabansa yana kallonta ganin yanda take kuka yasa ya ɗan juya gajiyayyun idanunsa ya sauke a kanta, dakyar ya iya laɓɓansa da juna kafin ya a sanyaye ya furta
"And what is this?"
Shigewa jikinsa ta yi tana kukan a hankali, ya girgiza kansa sannan ya ɗago fuskarta yana murmushi ya ce"tafi ki kwanta" a shagwaɓe ta ce"a'a ka faɗa min abin da aka yi maka dan Allah" jan kumatunta ta yi yana kallon wani wajen ya ce"idan na faɗa miki akwai abin da zaki iya ne? Uhm.."
Yanda ya yi maganar ya sanya ta yi murmushi ta shiga jan cute beard ɗinsa sannan ta ce"eh mana, I'll, zan yi faɗa da duk wanda ya taɓa min mijina, I won't take it likely with that person"
Faɗaɗa fuskarsa ya yi yana sake janta jikinsa ya ce"ko?"