Sashe 74
Naanah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kamar zata yi kuka ta ce“to ba amarya ba ce ba ni? Kuma ai ana siyawa Amarya kaza. Kuma ni naga baka siya min ba” tsuke fuska ya yi ya gyara tsaiwarsa yana kallonta sosai ya ce“yaushe na fara wasa da ke Nana?” sunkuyar da kanta ta yi saboda kaifin da idanunsa suka mata, Ya ja dogon tsaki sannan ya nufi upstairs da sauri. Shiru Nana ta yi tana kallon ƙasa, ta maƙale hawayenta gudun kada Zahran ta gani ta nufi saman ita ma, Zahra kuwa tashi ta yi jiki a saluɓe tabi bayansu, kowa ɗakinsa ya shige daban. Nana na zuwa ta faɗa kan gado ta fara birgima tana kuka, To ina aka taɓa kai Amarya ba'a siya mata kaza ba? Daman haka ake auren?. Ta sake rushewa da wani sabon kukan, Ji tayi kamar ta tashi ta yi tafiyarta, sai dai sanin dare ya yi ya sanya ta fasa ta ɗauki aniyar gobe da sassafe zata yi wucewarta. Da wannan tunanin ta tashi ta zame kayan jikinta sannan ta nufi toilet ɗin da yake dakin, wanka ta yi sannan ta ɗauro alwala kamar yadda ta saba duk dare, tana fitowa ta nufi press ɗinta inda aka jera mata kayanta sabbi ta buɗe. Wata sleeping dress ta ɗauko mara nauyi ta saka sannan ta nufi kan gadon, ta kwanta ta ja lallausan duvet ɗin ta rufe gaba ɗaya jikinta. Gajiya da kuma yunwar da take ji su ne suka taimaka wajen hanata bacci, ta dinga juyi akan gadon tana riƙe da cikinta, can kuma ta miƙe kamar wadda aka zabura ta tashi ta nufi toilet. Ƙaƙarin amai ta dinga yi amma kasancewar babu komai a cikinta ya hana aman zuwa, ta gaji ta kuskure bakinta ta dawo ɗakin. A wahale ta koma ta kwanta, ta ci gaba da mata gungun ɗinta a wajen har bacci ɓarawo ya ɗauketa. Da asubah ya shigo ɗakin bayan ya dawo daga Masallaci, kwance ya hangeta ta dunƙule jikinta waje ɗaya. Ya girgiza kansa sannan ya ƙarasa ciki, ɗan dukanta ya yi da hannunsa yana faɗin
“Nana! Ke Nana!”
Dakyar ta buɗe idanunta, ta kasa tashi saboda ciwon da cikinta ke mata. Daga kwance ta dinga kallon sa tana murza idanunta, Ya kafeta da idanu ya ce“tashi ki yi sallah” ya juya ya fice daga ɗakin ba tare da ya sake cewa komai ba. Da idanu kawai Nana ta bi shi sai kuma ta rufe idanun, hawaye suka fara zirarowa ta gefen idanun. Ta daɗe a haka har sai da gari ya fara haske sannan ta yunƙura ta tashi, ta zura slippers ɗin dake ƙasan gadon sannan ta nufi toilet tana tafe kamar iska zai hureta. Wanka ta yi sannan ta ɗauro alwala ta fito tana gyara ɗaurin towel ɗin jikinta, a hankali ta ware idanunta lokaci ɗaya kuma ta saki wani ihu ta sanya hannayenta duk biyun ta rufe fuskarta. Da mamaki ya dinga kallonta can kuma ya miƙe ya karasa wajen ganin yanda take abu kamar wata zararriya, duk tunaninsa wani abun ta gani dan haka ya jawota jikinsa gaba ɗaya ya rungumeta. Ai kamar ya sake turata haka ta ci gaba da ihunta tana ƙoƙarin janye jikinta, kallonta ya yi jin towel ɗin dake jikinta na neman kwancewa, Ya sanya hannunsa na hagu ya riƙe shi gam kafin ya ce
“Ke lafiyarki? Mene ne?”
Janye jikinta ta yi tana ci gaba da kukanta, Ya kai hannu ya taɓa wuyanta yana cewa“ko baki da lafiya ne?”
“Ni ka fita uncle!”
Ta yi maganar cikin kuka. Da mamaki yake kallon ta sai kuma ya ce“me yasa?”
“to babu kyau ganin tsirarar mutum, kuma sai ka shigo ban saka kaya ba?” Cewar Nana ta sake ƙanƙame idanunta ita a dole ba zai ganta ba. Wani dogon tsaki ya ja, ya dinga kallon ta rai ɓace, to me take tunani? A ɗan fusace ya ce
“mene ne a tsirarar naki da har zan kalla?.”
Turo baki ta yi tana ɗan buɗe idanunta, ganin yanda ya haɗe ransa ya sanyata sakin idanun. Ta bar wajen da sauri, Press ta buɗe ta ɗauki Abaya sannan ta koma toilet ɗin. Takaici da baƙin ciki ne ya sanya shi fita daga dakin, a ransa yana jinjina haukanta.
Koda ta fito daga bayin samu ta yi baya nan, ta sauke ajiyar zuciya tana rike da veil ɗin Abayar. Can kuma wata zuciyar ta ce mata
“To wane bai san jikin ki ba? Bayan hotunan ki da kowa ya gama gani? Da gaske yake mene ne abun ɓoyewa a jikin ki?.”
Nana ta ja dogon numfashi lokaci ɗaya hawaye na kawowa cikin idanunta. Tabbas bai cancanci ta ɓoye jikinta ba, dan kowa ya gama gani. Ta koma gefen gado ta zauna ta haɗe kanta ta gwuiwa ta fashe da kuka. Ta jima sosai a wajen har sai da ta yi mai isarta sannan ta tashi, ta koma toilet ta wanke fuskarta sannan ta fito, veil ɗin rigar ta yafa akanta, ta sake shi loosely sannan ta fito daga ɗakin. Bata samu kowa a main parlon ba dan haka ta yi ficewarta ba tare da damuwa ba. Kai tsaye apartment ɗinsu ta nufa, tana zuwa ta tsaya a bakin ƙofar ta dinga knocking, sai dai har bayan mintuna goma babu alamar za'a zo a buɗe. Dan haka ta juya ta bar wajen tana yan matan hawayenta. Rasa inda zata je ta yi, gashi yunwa na neman illatata, dan haka kawai ta nufi apartment ɗin Hajiya Babba dan ta san nan ne kawai a buɗe. Bakinta ɗauke da sallama ta murɗa handle ɗin ƙofar, Hajiya Babba da ke zaune kan sofa ta amsa tana kallonta da mamaki. Jiki a sanyaye Nana ta ƙarasa ciki ta durƙusa har ƙasa ta gaisheta.
“Nana lafiya dai? Ina Abdusammad ɗin?”
Hajiya Babba ta yi tambayar tana kallon ta bayan ta zauna gefenta. Madadin ta bata amsa sai kawai ta fashe da kuka tana faɗawa jikinta, Hankalin Hajiya Babba ya tashi ta ɗagota tana faɗin
“mene ne? Me ya yi miki?”
Kasa magana ta yi saboda kukan da ya ci ƙarfinta. Dai-dai nan Atta ta fito daga kitchen hannunta riƙe da madaidaicin plate mai ɗauke da soyayyen dankalin turawa, Ta ƙaraso wajen da sauri tana faɗin
“wa nake gani kamar ƴar gidan Ahmadi?”
Gyada mata kai Hajiya Babba ta yi kafin ta ce“Eh ita ce Atta.”
“Subhannallahi, Ba dai yaron nan har ya aikaceta ba babu tausayi, mu sam lokacin mu ba haka ake ba wallahi tallahi, sai yarinya ta girma sannan. Amma saboda jaraba ta ya'yan yanzu da an kai musu yara sai su haike musu, wannan ai magunta ce fisabilillahi.”
Atta ƙare maganar cikin kunfar baki. Shiru Hajiya Babba ta yi dan ita ma abin da ta ya zo ranta kenan. Ta sake ɗago Nana da ke kuka kamar ranta zai fita ta ce“Ya isa haka Nana. Faɗa min me ya yi miki?”
“To me za ki tambayeta kuma fisabilillahi, bayan ga abu nan ƙiri-ƙiri?”
Atta ta jawo hannun Nana tana makon ta ta ce“Saboda Allah Hadiza faɗa min me ya yi miki? Ni wallahi yanzu sai na shirya naje na ci masa mutunci. Ina ganinsa kamar mai hankali ashe ba haka bane?”
Dakyar Nana ta kwace jikinta saboda yanda Attar ta cacumeta, Ta yi baya tana fadin
“Ni ki cikani jikin ki duk ƙashi!”
Ta yi maganar tana sake rushewa da wani sabon kukan. Mitsi-mitsi Atta ta yi da idanu kafin ta ce“Ji min ruɓaɓɓiyar yarinya! To a shekaruna idan ba'a samu ƙashi a jikina ba me za'a samu?”
Babu wanda ya tanka ta a cikin su, dan haka ta yi shiru tana kallon su. Hajiya Babba ta kalli Nana murya a sanyaye ta ce“faɗa min me ki kewa kuka?”
Nana ta fara murza idanunta tana ƙoƙarin tsagaitawa da kukan ta ce“Hajiya ko ba uncle bane. Tun jiya ban ci abinci ba! Kuma yunwa ta kusa kasheni” Da mamaki Hajiya Babba ta ce“babu abinci kuma? Baki ci abinci ba?” gyaɗa mata kai Nana ta yi tana kuka. Hajiya Babba ta girgiza kanta kafin ta kira wata maid, bayan ta zo ta ce ta kawo mata abinci. Ba'a fi 5mins ba ta dawo hannunta riƙe da tray, Ta ajiye gabansu sannan ta juya ta bar parlon. Nana ta zame ta sauka kasa ta ja tray ɗin, tea flask ɗin ta buɗe ta tsiyaya tea ɗin sannan ta saka sugar kaɗan ta fara sha. Dakyar take haɗiyewa yana ƙoƙarin dawo mata saboda yunwar data riga da ta gama cinyeta, ta ajiye mug ɗin sannan ta fara cin soyayyen Irish potato ɗin tana haɗawa da kwan. Tass ta cinye sannan ta miƙe tana gyatsa, Hajiya Babba da ke jan counter ɗin hannunta ta ce
“kin ƙoshi?”
Gyaɗa mata kai Nana ta yi, ta karasa kan doguwar sofa ta kwanta nan da nan bacci ya ɗauketa. Hajiya Babba ta dinga kallonta ganin yanda take ta kwaɓe fuska a cikin baccin. Kafin daga bisani ta ɗauke kanta tana murmushi.
****
Ringing ɗin wayar data ji ne ya sanyata fitowa daga parlon, ta kalli Haule dake kallon tv sai kuma ta kalli inda ta ajiye wayar tata. A ɗan fusace ta ce“ke baki ga ana kirana ba? Ba zaki iya zuwa ki faɗa min ba?” jiki a sanyaye Haule ta kalleta sai kuma ta ce“Allah shi baki haƙuri” ta yi maganar tana ɗauke kai, Kwafa Siyama ta yi sannan ta ƙarasa ta ɗauki wayarta ta koma kitchen ɗin. Ganin sunan Mommynta ya sanya ta ɗaga, Aunty Khadijah da ke zaune gefen gado ta ce
“Siyama ya gidan?”
Ɗan taɓe fuska ta yi kafin ta ce“Gashi nan dai. Amma kin san me Mom?” girgiza kai Aunty Khadijah ta yi ta ce“a'a sai kin faɗa”
“Ni fa wallahi ban ga kuɗin da ki ke magana ba. Safwan bashi da kuɗi kamar mijin Anty Zahra. Bana ganin zamu samu abin da muke so, and kuma kwanan nan gaba ɗaya bashi da lafiya, ko kusa dashi naje sai ya ce na tafi, ballantana na yi aiki da maganin da malamin ya bamu.” Shiru Anty Khadijah ta yi tana tunani, Siyama ta ci gaba da cewa