Sashe 109
Naanah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A sanyaye ta kalle shi, dan rabon da ya yi mata magana tun ranar da Noor zata mutu, Ta yi saurin gyaɗa masa kai tana tashi tsaye. Bai ce komai ba ya ja ya tsaya, ta gane abin da yake nufi dan haka ta nufi sama da sauri, After some minutes ta dawo sanye da hijabi har ƙasa, Ya nufi waje tana biye dashi. Wata black Lexus ɗinsa dake compound ɗin gidan ya shiga, Zahra ta buɗe passenger seat ɗin ta shiga a hankali. Sai da ya yi warming motar sannan ya bar gidan, Tun da suka fara tafiya babu wanda ya ce komai, Can dai ya yi breaking silence ɗin ta hanyar faɗin
“Can i ask you?”
Gyaɗa kanta ta yi kafin ta ce
“Eh doctor.”
Jinjina kansa ya yi sannan ya ce“Zahra faɗa min, ina miki wani abu wanda baki so?”
Da ɗan mamaki ta kalleshi can kuma ta ce“But doctor...”
Kallon ta ya yi wanda ya sanyata yin shiru, Ya ɗan yi murmushi kafin ya ce“Kawai tambaya nayi fa” A sanyaye ta girgiza kanta ta ce“A'a doctor, kana zaune dani saboda Allah, baka cutar dani, kai mutum ne wanda kowa yake so. Kana da kyan hali, kana da kawaici, Sannan kuma kana da ilimi. A duk zaman da muke tare baka taɓa cutar dani ba, Ina jin daɗin zama da kai, Hasalima wasu lokutan ni ce nake ɓata maka.” Zahra ta ƙare maganar tana murmushi, Sai da ya sha kwana sannan ya jinjina kansa ya ce
“Really?”
Ta sake gyaɗa kanta tana murmushi. Murmushin ne shi ma ya kwace masa, Ya gyaɗa kansa fuskarsa a sake ya ce“Kenan ban cutar dake? Kin tabbata?” langwaɓar da kai ta yi ta ce“Eh mana doctor.” Shiru Abdusammad ya yi kamar me tunani, Can kuma ya sake kallon ta ya ce“kin tabbatar da hakan Zahra?” Shiru Zahra ta yi jin abin da ya sake cewa. Ta tura baki tana kallon titi ta ce
“Ni ka bar wannan tambayar doctor”
Bai sake cewa komai ba ya ci gaba da tuƙinsa hankali kwance, Ta ɗan kalle shi ta gefen ido sai kuma ta ɗauke kanta. Sam bata san inda suke nufa ba, Dan hankalinta gaba ɗaya baya wajen, Tana can tunanin Noorie sai ji ta yi ya kira sunanta.
Ɗago kanta ta yi ta kalle shi, Fuskarsa a ɗan cure babu yabo babu fallasa, Ya ɗan numfasa cikin nutsuwar da ta gama ratsa shi ya fara cewa
“Kin faɗa da kan ki ban cutar da ke ba Zahra, Bana yi miki abin da baki so sai dai idan da rashin sani. Ina zaune da ke tsakani da Allah, ina zaune dake saboda ina son ki, saboda na yaba da hankalin ki, naji zaki iya zama uwar Yayana”
Zahra ta yi shiru tana tunani sa, ta girgiza kanta a sanyaye ta ce
“Doctor na sani, wallahi na sani.”
“But why? Akan me zaki kashe mahaifiyata? Akan mene ne Zahra? Me nayi miki.”
Girgiza kanta ta fara yi cikin tashin hankalin daya ziyarceta ta ce
“Wallahi! Wallahi! Wallahi ban yi niyyar kasheta ba! Wallahi doctor ban yi niyya ba, Bana nufin kowa naka da sharri, na rantse maka da Allah...!”
“Idan haka ne me yasa zaki saka mata guba? Akan mene? Kin jawo na rasa ƴata, na rasa Noor Zahra! Kin kasheta da hannun ki. Kin kashe ƴar da muka haifa, Yarinyar da nake so fiye da komai, Yarinyar da nayi burin ganin girmanta,Me yasa Zahra?”
Tuni hawaye ya fara zubowa kan fuskarta, Sai girgiza kai take tana kuka, Tama kasa magana saboda tashin hankali. Jin bata ce komai ya sanya shi jan numfashi yana ƙoƙarin saita nutsuwarsa ya ce
“Ba zan tambaye ki ba, Ba zan nemi naji dalili ba. Na haƙura, na yafe miki Zahra, Na yafe miki har gaban abada wallahi.”
Ita dai bata ce komai ba sai kukanta take ci gaba da yi, Ya zaro wata farar welfolded paper daga aljihunsa ya ɗora mata akan cinya, Zahra ta kalli takardar sai kuma ta kalle shi, Ji ta yi tana neman rasa nutsuwar, Ta girgiza kanta cikin wani irin kuka ta ce
“Na shiga ukuna, Dan girman Allah, dan Allah, Dan Annabi kar ka rabu dani. Na shiga uku Doctor, Wallahi ban yi niyyar cutar da Hajiya Babba ba, Ban san maganin yana kisa ba, Anty Khadijah ce ta bani wai zai saka ta dinga sona. Wallahi ban san na kisa bane...”
Ta ƙare maganar tana sakin wani raunataccen kuka, Girgiza kansa ya yi muryarsa a ɗan dausashe ya ce
“Ba komai Zahra, Duk abin da ki ka yi ba zan rike ki ba. Naji daɗi daya kasance Noor ta fara cin abincin kafin Hajiya Babba, Duk da naji ciwo, naji zafi, naji raɗaɗin rashinta. Amma da ace Hajiya Babba ta rasu gwara Nooriya, Domin ita ni kaɗai zan yi rashin ta, ni kaɗai na san zafinta, Ita kuma Hajiya Babba gaba ɗaya dangin mu ne zai yi rashi. Ko da gangan ki ka yi, ko kuma bada saninki ba, Na haƙura na yafe miki Zahra. Amma ba zan iya ci gaba da zama dake ba, Domin zan ta kallon ki da abun, sannan ba zan iya kyautata miki ba, Sannan bana son dangina su riƙe ki idan suka ji wannan labarin, Tun asali na aureki bada yardar su ba, dan haka duk abin da ya faru zasu dinga ɗora laifin akaina. Ki yi haƙuri amma ni Abdusammad Muhammad Shuwa na sakeki saki ɗaya, na sake ki saki biyu, na sake ki saki uku! A zaman da muka yi da ke, idan na cutar dake Allah ya saka miki, idan kuma ni ki ka cutar to na yafe miki har abada, Ina miki fatan Alkhairi a ragowar rayuwar ki Zahra!.”
08106608363
Nanameera.*Page 65*
Zahra ta dinga kallon sa hawaye sai biyo fuskarta yake, Ta girgiza kanta cikin tashin hankali ta ce
“Na shiga ukuna doctor, Dan Allah dan Annabi kada ka bar ni, Kar ka rabu dani. Wallahi ina sonka, Ina son ka sosai fiye da tunanin ka, Idan ka rabu dani ya zan yi?”
Kallon ta kawai Abdusammad ya yi, Shi kansa zuciyarsa a dagule take. Ya numfasa sannan ya ce“Ko da na so zama da ke to ba zai yiwu ba Zahra, dole ne sai mun rabu. Ba zan iya ci gaba da zama dake ba domin zan ta tunawa da abubuwa da dama, ke kan ki kin san ba zan iya ba. Kin kashe Noor da hannun ki, Ta ina ki ke tunanin zan ci gaba da zama da ke? Bayan haka da a ce ba Noor ce ta ci ba da Hajiya Babba ki ka kashe, Zahra ba zan iya ba!”
Ya ƙare maganar yana girgiza kansa, Bata sake cewa komai ba, ta kifa kanta akan cinyarta tana kuka kamar ranta zai fita. Above 5mins kafin ya sauke numfashi ya juya yana kallon titin Gibson's jalon wanda yake shiru babu hayaniya, Muryarsa a nutse ya ce
“Allah ya sani ban sake ki dan na tozarta ki ba, Babu yanda zan yi ni. Ki yi haƙuri”
Ɗago kanta ta yi tana kallon sa, Lokaci ɗaya ta shiga goge hawayenta. Cikin shessheƙar kuka ta ce“Na sani doctor, Ba komai Allah yasa haka ne mafi alkairi. Amma nima ka sani, ban zauna da kai da niyyar cutarwa ba, na soka domin Allah doctor, na yarda ƙaddara ce zata rabamu, Na gode doctor!...”
Ta yi shiru tana jan numfashi, Bai iya cewa komai ba, Dan a duk sanda damuwa ta yi masa yawa baya iya magana. Tsawon mintuna biyu kafin ta buɗe motar ta zura kafarta daya a waje, Juyowa ta yi tana kallon sa ganin har sannan idanun sa na kan titi. Ta sauke numfashi sai kuma ta fice daga motar ta rufe masa, Jiki a sanyaye ta juya ta fara tafiya hannun ta riƙe da wayarta da kuma divorced paper ɗinta. Sai da ta buɗe gate ɗin gidan ta shiga sannan ya juyo ya kalleta, Ta mayar da gate ɗin ta rufe. Zazzafan numfashi Abdusammad ya sauke sannan ya dauƙe idanun sa. Ya jima zaune cikin mota yana saƙa da warwara kafin daga bisani ya yiwa motar key ya yi reverse ya bar unguwar.
****
Amma ta dinga kallon ta ganin taƙi cin abincin tun ɗazu, Ta girgiza kanta a ɗan fusace ta ce“Wallahi Nana ba zan iya ba, Ba zaki tayar min da hankali ba. Akan me? Wannan damuwar ki ke zai saka wanda ya tafi ya dawo ne? Ba ki da tawakkali?”
Kallon ta kawai Nana ta yi da idanun ta wanda suke a kumbure, Amma ta tashi ta dawo gefenta ta janyo tray ɗin dake kan table ta ce
“Ki ci abinci ko kuma yanzu na kira Babanki.”
Ta ɗan kalli tray ɗin sai kuma ta sake langwabar da kanta kamar zata yi kuka ta ce“Amma ni bana jin yunwa fa”
Shiru Amma ta yi ta zuba mata idanu, Ganin haka ya sanya Nana tura baki kamar an mata dole ta ce
“To zan ci fa.”
Ita dai Amma bata sake cewa komai ba, Nana ta ta shige kitchen, After some minutes ta dawo hannun ta riƙe da mug. Ta dawo ta zauna sannan ta dauki tea flask ɗin ta tsiyaya shayin kadan, Sugar kawai ta saka sannan ta fara sha a hankali. Amma ta ajiye mata tray ɗin gefenta ta tashi ta shige ɗaki, Da idanu kawai Nana ta bita sai kuma ta sanya hannu ta fara cin wainar kwan, Ko loma uku bata yi ba ta cire hannunta. Shayin ma a wajen ta bar shi ta tashi ta nufi ɗakinta. Toilet ta shige ta fara amai, Sai da ta amayar da duk abin da ta ci sannan ta wanken bakinta ta fito tana sauke numfashi. Kwanciya ta yi gefen gado ta lumshe idanun ta, cikin yan mintuna bacci ya ɗauketa.