← Book details Naanah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 120 OF 125

Sashe 120

Naanah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Daga haka ya juya ya fice daga ɗakin kamar zai tashi sama. Sai da ta ga ya rufe kofar sannan ta kece da wani kukan baƙin ciki, Ta koma ta kwanta tana kuka kamar ranta zai fita. Abincin da bata ci ba kenan har bacci ɓarawo ya saceta, Cikin dare ta farka saboda ciwon da cikinta ke mata, Ta tashi zaune tana dafe da cikin nata. Ta jima zaune a wajen tana kuka kafin ta tashi ta shige toilet, Fitsari kawai ta yi ta dawo ta kwanta, After 5mins ta tashi da gudu ta koma toilet ɗin, Amai ta yi ta tsaya a wajen tana sauke numfashi. Sai da ta ɗan ji sauƙin cikin sannan ta fito daga toilet ɗin ta kwanta akan gadon, Ta jima kafin wani baccin ɗauketa. Da asuba ya shigo ɗakin yana sanye da jallabiya mai taushi hannunsa riƙe da counter da alama masallaci zai je, Kallon ta ya dinga yi ganin yanda ta cure jikinta waje guda, Daga jin yanayin yanda take numfashi ka san ba daɗi kwanciyar take ji ba. Ya ƙarasa ciki ya gyara mata kwanciyar sannan ya ja duvet ya rufeta, Ya ɗan yi jim yana kallon kyakkyawar fuskarta wadda ta kwaɓe ta kamar zata fashe da kuka, Girgiza kansa ya yi sannan ya juya ya fice daga ɗakin. Sai ƙarfe 8:00 na safe ta farka, Tana tashi ta shige toilet ta yi wanka, Ta fito ta shirya cikin wasu riga da wando marasa nauyi, Ta koma gefen gado ta zauna ta yi shiru tana tunanin abin da ya faru jiya. Kenan har yanzu yana sonta? Har yanzu bai rabu da ita ba? Har yake iya yi mata tsawa akanta. Shar haka taji hawaye na zubowa kan farar fuskarta, Babu abin da ya fado mata a rai sai Junaid, Allah sarki, Duk da ya aikata mata ba daidai ba amma ta san da shi ne ba zai taɓa yi mata haka ba. Domin shi ne wanda ya nuna yana sonta, Wannan kuwa kowa ya san auren alfarma ne a tsakanin su, Da wannan tunanin ta kifa kanta tsakanin cinyoyinta tana fashewa da wani sabon kukan. Sai da ta gaji dan kanta sannan ta tashi ta shige bayi, wanke Fuskarta ta yi ta fito ta zura hijabi kan kayan jikinta sannan ta ɗauki wayarta da jakar makarantar ta ta fice daga ɗakin.

Bata same shi ba ko a ƙasa duk da kasancewar ranar Sunday ne, Kawai ta samu driver ta ce ya kaita schl ɗin. Koda ya sauketa shiga ta yi, Babu wasu mutane sosai domin ba kowa ke da lecture Sunday ba, Suma wani lecturer ne ya kira su. Dan haka kai tsaye department ɗinsu ta nufa, Tana zuwa ta samu har an fara lecturen. Haka dai ta nemi waje ɗaya ta zauna tana saurara duk da ba fahimta take ba, Bayan sun gama tana shirin fitowa taga Amani. Kallon ta kawai ta yi sai kuma ta ɗan yi murmushi ta ce

“Ina Mu'ash?”

“Bata zo ba”

Amani ta bata amsa kai tsaye, Jinjina kai Nana ta yi sai kuma ta ɗauki jakarta tana ƙoƙarin ratayawa ta ce

“Zan tafi sai jibi.”

“Nana me ya faru ne? Naga duk kin yi wani iri, Me ya samu fuskar ki?”

Sai a sannan Nana ta kai hannunta kan fuskarta saitin daya mareta.

“Wa ya dake ki?”

Amani ta sake mata tambayar, Girgiza kanta ta yi hawaye na taruwa cikin idanun ta ta ce

“Babu kowa.”

Ɗan murmushi Amani ta yi sai kawai taja hannunta suka fice daga class ɗin. Can wajen wata coconut tree ta kai ta suka tsaya, Ta ɗan yi murmushi ta ce

“Nana idan baki faɗa mana abin da ya dame ki ba wa zaki faɗawa? Kin san dai baki da kowa a ƙasar nan idan ba mu ba ko? To akan me zaki ɓoye mana abin da ya dame ki”

Ai kamar jira Nana take ta fashe da kuka, Ta fara murza idanunta da hannunta na hagu, Amani ta ɗan yi shiru tana kallon ta can kuma ta riƙe hannunta ta ce

“Ki yi haƙuri ki daina kuka, Ki faɗa min abin da aka yi miki”

“Uncle ya tsaneni, Baya sona. Uncle bani yake so ba matarsa yake so, Nima bana son shi, Tafiya gidanmu zan yi, Ba zan koma gidan sa ba. Ƙasar mu zan tafi, Sai dai ya sakeni, Ba zan zauna dashi ba wallahi!”

Amani da bata gama fahimtar abin da ya faru ba ta ce

“Wai me ya yi miki? Me ya sake haɗa ki dashi? Shi ne ya mareki?”

Gyaɗa mata kai Nana ta yi cikin kuka ta ce

“Saboda na zagi tsohuwar matarsa shi ne ya ke min bala'i, Kuma ya mareni, ai baya sona. Ita yake so har yanzu, Nima ai gara na bar gidan kawai”

Girgiza kai Amani ta yi ta ce

“Akan me zaki bar gidan Nana? Gidan mijin ki ai, Kin san me ya sa yake miki haka?”

Shiru Nana ta yi lokaci ɗaya ta shiga girgiza kanta. Amani ta gyara tsaiwarta sannan ta ce

“Saboda wannan cikin ne! Shi ne abin da ya saka yake nuna baya sonki. Mazan yanzu haka suke, Zasu nuna suna sonki, Su dinga taraiyarki, Su saka ki farin ciki da nishaɗi, Amma daga sanda ya fahimci akwai ciki a jikin ki sai ya watsar. Sai ya daina ɗaukan al'amuran ki da girma, Ya mayar da ke kamar wata mara amfani, Sai ki yini bai shiga harkar ki ba. Wanda da a sanda ki ke lafiya ne yake morarki baya miki haka”

Shiru Nana ta yi tana nazarin kalaman Amani.

Amani ta sake cewa “Ke yanzu da haka yake miki? Sanda ya aure ki haka yake miki? Ko farkon zuwan ki ƙasar nan haka ya dinga miki?”

Girgiza kai Nana ta yi, Amani ta ɗora da faɗin

“To me ya sa yanzu ya sauya miki? Me yasa ya daina kulawa da ke? Me yasa yake iya dukan ki? Amsar guda ɗaya ce, Saboda yanda yana ganin ciki a jikin ki. Yana ganin kin gama masa amfani idan bana haihuwa ba, Wannan shi ne ya sanya sanda ya aure ki ya dinga yiwa Zahra haka ita ma. Ki nutsu ki fahimci komai Nana”

Kusan mutuwar tsaye Nana ta yi a wajen saboda mamaki, Tunanin bai taɓa kawo wa nan ba, Sai yanzu da Amani ke faɗa ta fara tabbatar da hakan. Da gaske sanda bata da ciki ba haka yake mata, Daga samun cikinta zuwa yanzu basa kwana biyu basu yi faɗa ba, Kusan kullum sai ya mata tsawa. Kenan wannan shi ne dalili? Amani ce ta katse mata tunanin da take ta hanyar faɗin

“Kin gane abin da nake nufi?”

Nana ta gyada mata kai hawaye na zubowa kan fuskarta. Jinjina kai Amani ta yi kafin ta ce

“Yanzu shawara ta rage naki, Idan har kina son zama cikin gidanki hankali kwance cike da soyyayar mijin ki to sai dai ki rabu da wannan cikin da ke jikin ki!”

Shiru Nana ta yi, Ta rasa wace makama zata kama, Ta yarda ta zubar da cikin ko kuwa ta bar shi? Idan ta bar shi haka zata ci gaba da zama gidan Uncle cikin baƙin ciki daga nan har ta haihu? Ta girgiza kanta a fili ta ce

“To ya zan yi na zubar?”

Murmushi Amani ta yi ta ce“Yauwa kin zaɓi abin da zai fissheki. Kina ji yanzu ki zo muje na sauke ki sai mu biya da pharmacy ɗin da muke siyan magani na karɓa miki tablet ɗin.”

Jiki a sanyaye Nana ta ce “To kuma zai zube ɗin?”

Wani kallon sheƙeke Amani ta yi mata sai kuma ta ce“a'a ƙarya zan miki!”

Daga haka ta yi gaba abin ta, Sauke numfashi Nana ta yi sannan tabi bayanta. Kamar yanda Amani ta faɗa haka ce ta faru, Ta barta a motar ta tsallaka ɗaya side ɗin inda babban Medcare pharmacy ɗin yake. Ta shiga bata jima ba ta dawo hannun ta riƙe da leda, Akan cinyar Nana ta ajiye ledar sannan ta yiwa motar key suka ci gaba da tafiya. Nana ta dinga kallon ledar ba tare da ta yi gigin taɓawa ba, A bakin mansion ɗin nasu ta yi parking sannan ta juyo tana kallon ta ta ce

“To gashi nan, Guda ɗaya kawai zaki sha, Kada ki sha sama da haka. Sannan ki bari sai baya nan, Kamar kin san ya kusa dawowa ko kuma zai fita sai ki sha, Ki yi komai a nutse, kar ki bari ya gani”

Ban da gyada kai babu abin da Nana ke yi, Ta sauke numfashi kafin a sanyaye ta ce

“To babu matsala dai ko? Idan na sha kuma wani abun ya sameni fa?”

Ɗan tsaki Amani ta yi ta ce

“Ke wai yaushe zaki fara fahimtar abubuwa ne? Cewa nayi fa ki sha idan ya kusa dawowa, Ko kuma ya kusa fita, Yanda ba zai yi nisa ba. Sai ki ce ko faɗuwa ki ka yi ko wani abun, Kada ki bar ya gani! Kada ki kuskura ki bari ya gani”

To kawai ta ce sannan ta ɗauki ledar ta mata sallama ta buɗe motar ta fita. Amani ta bita da idanu sai kuma ta girgiza kanta, Ita har cikin zuciyarta tausayi take bata. Sai da taga ta shiga gidan sannan taja motar ta ta yi gaba, Nana kuwa a compound ɗin farko ta tsaya ta zare maganin daga ledar ta yar a dustbin sannan ta saka maganin cikin ɗan ƙaramin aljihun jakarta sannan ta ci gaba da tafiya. A sanyaye ta buɗe ƙofar parlourn ta shiga, Zaune ta hange shi yana magana a system da alama vidcall yake yi, Ta ƙarasa ciki ba tare da ta ce komai ba. Tsayawa ta yi a bayansa dan ganin da wanda yake wayar, Sai dai fuskar wadda ta gani ya sanyata sunkuyar da kanta. Murmushi Zahra ta yi ta daga mata hannu ta ce

“Hi Nana!”

Sai a sannan Abdusammad ya juya yana kallon ta dan sam bai lura da shigowar tata ba, Bata ce komai ba ta juya ta nufi hanyar sama a sanyaye. Sai da ta bar wajen sannan Zahra ta ce

“Dan Allah doctor ka tayani bata hakuri, Ta daina jin haushina”

“Just leave her”
Chapter 120 · 0% Book details