← Book details Naanah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 125

Sashe 14

Naanah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Abincin kala-kala aka dinga jerawa kan carpet, dan ranar a wajen zasu ci lunch tare, Abba ne ya ce"Abdusammad ina iyalin naka?" dafa kansa ya yi cikin daddadar muryarsa ya ce"suna mota Abba" Girgiza kai Abba yayi ya ce"a kira su mu gaisa ko" okay ya ce sannan ya kalli Aliyu ya ce"Buddy pls" ya gane me yake nufi dan haka ya taɓe baki ya ce"ni ɗan aikenka ne?" langwaɓar da kai ya yi ya ce"yi haƙuri kaje mana, ka ga ni baƙo ne and baƙonka Annabin ka" taɓe baki Aliyu y yi sannan ya juya ya fita. Kowa ya dinga murmushi a wajen dan daman an san halin dramar su. Tashi ya yi Hajiya ta kalleshi ta ce"ina kuma zaka je?"

"Wanka zan yi Hajiya"

Harararsa ta yi ta ce"daga zuwanka Abdu?" komawa ya yi ya zauna yana faɗin"okay Hajja mai Makka da Madinah na zauna" murmushi ta yi ta ce"da ya fi maka dai"

After 2mins Aliyu ya dawo hannunsa ɗauke da wata ƙaramar baturiyar yarinya wadda ba zata shige 5yrs ba, sai murmushi take, sai kuma wata mata wadda ba zata shige 27yrs ba a bayansa, tana sanye da Abaya black colour, wadda ta haska farar fatarta. Ƙarasowa ciki ta yi ta dinga gaida kowa cike da fara'a, suma suka amsa sannan ta nemi gefen kujera ta zauna, Abba ne ya karbi yarinyar yana mata wasa sai dariya take, ganin kamar bata jin Hausa ya sanya ya ce"Abdusammad bata jin hausa ne?" girgiza kansa ya yi ya ce"tana ji amma kaɗan, Zahra nayi mata"

"Kai baka mata kenan?"

Ɗago kansa yayi ya kalleshi sai kuma ya ce"ina ruwanka dani? Kaji da kanka da rashin aurenka ma" tuntsirewa suka yi da dariya Aliyu ya riƙe baki sai kuma ya ce"oh gori ka ke min kenan?"

"Yeh!"

Cewar Abdusammad yana kafeshi da idanu, taɓe baki ya yi ya ce"to kaci kan ka, nima dai soon zan yi auren nan"

"Better" ya ce a takaice sai kuma ya mayar da kansa wajen Abba suna ci gaba da hira.

Da sallama suka shigo parlon kowannensu sanye da hijabi, aka amsa sannan suka ƙaraso ciki, cike da nutsuwa suka gaishe shi ya amsa yana cewa"Maimoon ko?" ya ƙare maganar yana nuna Maimoon da hannunsa, gyaɗa masa kai ta yi a nutse ta ce"Eh Uncle" jin jina kansa ya yi ya ce"ashe nagane ki" sai kuma ya nuna Hamida ya ce"Amrah right?" Girgiza kanta tayi ta ce"a'a Hamida, ga Amrah nan" ta nuna Amrah da ke gefenta kai a sunkuye, dafe kansa ya yi ya ce"ya aka yi ban gane ki ba Hamida, yarinya mai ƙoƙari" murmushi kowa ya yi sannan ya kalli Amrah ya ce"ita kuma wannan daman bata magana kurma ce" dariya suka yi ban da Amrah wadda jikinta ke rawa,ya ce"yara duk sun girma, sai aure ba" Dariya aka yi suka tashi kowacce ta koma kusa da mahaifiyarta ta zauna, maids suka fara serving kowa, koda aka zuba masa nasa ƙasa ya sakko ya zauna ya tankwashe ƙafafunsa sannan ya yi bismillah ya fara ci, tasowa yarinyar ta yi daga jikin Abba ta dawo wajensa, akan cinya ya ɗorata sannan ya fara bata abincin kamar yanda ya saba. Turo ƙofar ta yi ta shigo, sai dai ganin yanda aka cika parlon ya sanya ta tsaya tana kallon kowa ɗaya bayan ɗaya,

"Nana".

Da sauri ta kalli wajen sai kuma ta yi murmushi ta ƙarasa ta tsuguna gabanta ta ce"Aunty Zahra ina yini?" murmushi Zahra ta yi ta ce"ashe za ki gane ni, haka ki ka girma?" Murmushi Nana ta yi ta ce"eh mana, kin manta kin tura min pictures ɗinki" Zahra ta jinjina kai sai kuma ta ce"eh haka aka yi" tashi Nana ta yi ta ƙarasa gabansa ta tsuguna cikin sanyin murya ta ce"sannu da zuwa Uncle" ɗago kansa ya yi ya kalleta sai kuma ya haɗe rai, sunkuyar da kanta ta yi tana wasa da fingers ɗinta.

"Ina hijabin ki?"

Sai da gabanta ya faɗi jin yanda ya yi tambayar, bata ɗago kanta ba ta ce"yana gida" Abdusammad ya ce"tashi ki je ki dauko" jiki a sanyaye ta tashi ta bar parlon, Aliyu ya sauke numfashi ya ce"ga Sheikh ɗin gidan ya dawo, yara duk sai sun shiga nutsuwarsu"

Bai kalli Aliyu ba ballantana ya saka ran bashi amsa, ya ci gaba da cin abincinsa hankali kwance. Koda ya gama ci tashi ya yi bayan ya janye yarinyar da ke jikinsa yana cewa"Nur je ki wajen Ummi" gyaɗa kanta ta yi sannan ta koma jikin mahaifiyarta ta zauna, shi kuma ya kalli Hajiya ya ce"ina key ɗina Mama?" Kafin ta yi magana Safwan ya ce"an gyara komai Yaya, kuma a buɗe yake" ɗan kallonsa ya yi sai kuma ya ce"okay i see" daga haka ya nufi kofa ya fita daga parlon.

Ba'a fi 2mins ba ta dawo sanye da dogon hijabi, kalle-kalle ta dinga yi ganin bata ganshi ba ya sanya ta ce"ina uncle ɗin?" yanda ta yi maganar muryarta na rawa ya sanya mutanen wajen dariya, Zahra ta ce"yana apartment ɗinsa, ki je yanzu ya fita" toh kawai ta ce sannan ta juya ta fita da sauri. Ta fi 2mins a gaban kofar tana tunanin shiga ko ta haƙura, daga ƙarshe dai kawai ta tura kofar ta shiga bakinta ɗauke da sallama. Babu kowa a parlon sai tv dake faman aiki, ko ina neat sai tashin ƙamshi yake, tsayawa ta yi a tsakiyar parlon kamar zata yi kuka ta shiga faɗin

"Uncle! Uncle! Uncle"

Shiru babu amsa, ta sunkuyar da kanta hawaye na biyo fuskarta, tura baki ta yi sai kuma ta juya ta fito daga parlon. Tsaye ta sami Amrah tana zazzare idanu, ta dinga kallonta sai kuma ta ce"mene ya kawo ki nan?" sunkuyar da kai Amrah ta yi tana ƙoƙarin ɓoye hawayenta ta ce"kin gan shi?" girgiza kai Nana ta yi still looking at her ta ce"na kira shi bai amsa ba, maybe wani abun ya ke, zan je sai na dawo an jima" Amrah ta sauke ajiyar zuciya sai kuma ta ce"daman Abba yake kiran ki" daga haka ta juya, Nana ta dinga kallonta tana mamakin yanda take abu kamar mara lafiya, sai dai kuma tunawa da ita da abin da ke gabansu ya sanya ta sauke numfashi sannan tabu bayanta..

08106608363
Nanameera.*🌹 NAANAH 🌹*

Page 9...

Ƙarfe 4:15 na yamma ta fito daga ɗakin tana murza idanunta, Amma ta dinga kallonta sai kuma ta ce"sai yanzu ki ka tashi?" gyaɗa mata kai ta yi tana ƙoƙarin rufe bakinta saboda hammar da take yi, ƙarasowa parlon ta yi ta zauna gefen Amma murya a sanyaye ta ce"Amma wai Yaya Safwan zan aura?" Shiru Amma ta yi tana kallonta, Nana ta ɗora kanta gefen kafaɗarta sannan ta ci gaba da faɗin "Amma me ya sa sai shi? Ita Amrah Yaya Sultan zata aura, ita kuma Maimoon Yaya Aliyu, shi ne ni zan auri Yaya Safwan?" Har sannan Amma bata iya cewa komai ba, ba dan bata ji abin da ta ce ba, sai dan bata da abin fadar. Hawayen Nana suka dinga sauka kan kafaɗarta, wanda ya sanyata ɗagowa ta kalleta a nutse ta ce"to mene ne dan kin auri Safwan ɗin? Shi ma kamar sauran yake, yana da sauƙin kai ma fiye da na sauran" Tashi ta yi daga jikin Amma ta miƙe tana shirin barin wajen ta ce"ni bana sonsa" daga haka ta nufi ɗakinta. Da idanu kawai Amma ta bita sai kuma ta sauke numfashi, da tana da dama to da tabbas ba zata bari a aurar da Nana yanzu ba, amma sanin bata da wannan ikon ya sa ta kawar da tunanin daga cikin ranta, ta mai da Idanunta kan tv tana kalla duk da ba fahimtar abin da ake take ba. Tana nan zaune har bayan mintuna goma Nana ta sake fitowa daga dakin, wannan karon sanye take da Abaya baby pink ta yi rolling mayafin abayar akanta, Amma ta dinga kallonta ba tare da ta tambayeta inda zata ba, Nana ta ƙaraso gabanta murya a ɗan shaƙe ta ce"zan je wajen uncle" toh kawai ta iya ce mata, ta juya ta fice daga parlon.

Zaune ta hangeshi kan farar kujera a cikin flowers ɗin da ke garden, ta ɗan yi jim kafin ta ƙarasa wajen tana tafiya a hankali. Sultan na zaune yana danna waya ta ƙaraso gabansa, kujerar da ke gefen tasa ta ja ta zauna sannan ta ce"Yaya" yanda ta yi maganar a sanyaye ya sanya ya ɗago kansa, kallonta ya dinga yi ganin yanda fuskarta ta faɗa kamar ba ita ba, above 2mins kafin ya sauke numfashi ya ce"Nana ina zuwa?"

"Yaya Amrah zaka aura?"

Tambayar ta zo masa a bazata, dan haka ya gyaɗa mata kai kana ya ce"but why do you ask me?" Sunkuyar da kanta ta yi tana ƙoƙarin ɓoye hawayenta ta girgiza kanta. Sultan ya gyara zamansa yanda zai dinga kallonta sosai sannan ya ce"Nana"

"Na'am Yaya" ta amsa masa muryarta na rawa.

"Ɗago ki kalleni"

A sanyaye ta ɗago kanta ta kalleshi sai kuma ta sake sunkuyawa hawaye na zubowa kan kuncinta. Mamaki ne ya cika shi, ya dinga kallonta baki buɗe kafin ya yi ƙarfin halin cewa"kuka ki ke Nana? Mene ne ya sanya ki kuka?"

Girgiza masa kai ta yi tana goge hawayen da hannunta ta ce"babu komai" daga haka miƙe tana shirin barin wajen

"Kina sona ne Nana?"

Sultan ya yi maganar bayan ya miƙe tsayen shima. Wani irin dukan uku-uku ƙirjinta ya dinga yi, ta kasa magana haka kuma ta kasa barin wajen, takowa Sultan ya yi ya dawo gabanta yana kallonta ya ce"faɗa min kina sona ne? kin taɓa jin kina son na zama mijinki cikin estate ɗin nan? Or you daman u're just pretending all this time!"

Da sauri ta ɗago kanta ta kalleshi, ya gyaɗa mata kai fuskarsa babu yabo babu fallasa. Ganin bata ce komai ba ya sanya ya ɗan furzar da iska daga bakinsa kana ya ce"shikenan, ai yanzu ma komai ya ƙare, zan auri wadda ba ita ce zaɓina ba, zan auri wadda ban taɓa mata kallon daya shige na ƙanwa ba, zan auri wadda ba lallai bane nayi farin ciki iya tsawon rayuwata"
Chapter 14 · 0% Book details