Sashe 42
Naanah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Har bayan mintuna talatin da fara tafiyarsu babu wanda ya ce wa wani komai, Nana ta mai da kanta gefen titi tana kalle-kalle wanda take jin yana ɗan ɗebe mata kewa, she wish ace ba yau zasu koma gida ba, dan daga jiya zuwa yau ta ji wani abu yana ɗan ragar mata daga cikin damuwarta. Saɓanin kwanakin baya da kullum take yini babu walwala. Ringing ɗin wayarta ne ya dawo da ita daga duniyar data tafi, ta kalli wayar dake kan cinyarta sai kuma ta ɗauka, ganin wanda yake kiran ya ta matse gefen wayar ta mayar ta ajiye sannan ta ci gaba da kallon da take. Ko sakan biyu ba'a ayi ba aka sake kira, ta ɗan saci kallon Safwan dake tuƙinsa ba tare da yana lura da ita ba. Ta sake katse kiran tana tura baki a hankali, ko ajiye wayar bata yi ba ƙarar faɗowar saƙo ya shigo, ta buɗe wayar ganin a WhatsApp ne ya sanya ta shiga, numbern Junaid ta gani dan ta yi unblocking ɗinsa tun bayan daya nemi hakan, a hankali ta buɗe saƙon ganin kamar hotuna aka turo ya sanya ta danna downloading tana jin bugun zuciyarta na tsananta, kamar kiftawar idanu haka hotunan duka suka buɗe, ta yi saurin kifa wayarta bayan ta ga abin da ya turo. Dakyar ta iya mai da kanta gefen titi hawayen dake cikin kurmin idonta ya samu damar gangarowa kan fuskarta, ta ɗan ja numfashi ba tare da sauti ba tana kallon hotunan a cikin idanunta. Sabon sakon daya shigo ya sanya ta sake firgita, ta kasa ɗago wayar saboda fargabar abin da zata gani, sai dai sanin bata da wata mafita data shige ta buɗe saƙon ya sanya ta ɗago wayar, sakone ya rubutu kamar haka
_Ina sake tuna miki ne, idan har ki ka ɗauki maganata wasa to tabbas ranar Lahadi za'a wayi gari da maganar waɗanda hotunan naki a kowace kafa ta sada zumunta, sannan bugu da ƙari Abba zai yi farin cikin da bai taɓa yi ranar ba, domin ranar ta kasance daya daga cikin ranaku mafiya tsada a cikin rayuwarsa. Wato ranar auren yar sa! na san ba zaki so ya rasa wannan farin cikin ba, ko nace baƙin ciki mara misaaltuwa ya maye gurbinsa. Dan haka ki san duk yanda zaki yi a fasa daura miki aure da wannan mutumin, shawara nake baki._
Nana ta dinga kallon screen ɗin wayar tana jin wani irin abu nayi mata yawo tun daga tsakar kanta har zuwa ƙafafunta, gaba ɗaya jikinta ya yi wani irin saki, dakyar ta iya danne hoton da maganar ta yi deleting ɗin su daga kan wayarta. Kafin ta kashe wayar gaba ɗaya tana lumshe idanunta, hawaye suka dinga zuba daga cikinsu kamar an buɗe famfo.
Safwan dake lura da ita tun ɗazu ya ɗan taɓe baki dan duk tunaninsa maganar auren ce har yanzu bata haƙura ba. Ganin sun fara shigowa cikin gari ya sa ya yi gyaran murya ba tare da ya kalleta ba ya ce
“Ina son maganar da muka yi dake jiya ta zama sirri tsakanina da ke, koda wasa banson na ji ta a wani wajen, ka da ki kuskura ki faɗawa wani koda kuwa a cikin labari ne”
Ya ƙare maganar yana kallonta, Bata amsa mata ba, dan babu alamar ma tana sauraren abin da yake cewa, she's just busy crying. Dan haka a ɗan tsawace ya ce
“Ke Nana!”
Wannan karon ta ji shi sai dai nauyin da idanunsa suka mata shi ne ya hanata buɗe su, muryarta cikin wani irin sanyin da ya shige misali ta ce
“na'am”
“kin ji abin da na ce ko?”
Gyaɗa masa kai ta yi duk da bata jin ba, kuma bata da burin jin koma mene ya ce mata ɗin. Ya jinjina kansa ya ce“good” sannan ya ci gaba da tuƙinsa ba tare da ya sake cewa komai ba.
Har suka ƙaraso gida bata daina kuka ba, kuma ko sau ɗaya bai yi tunanin rarrashinta ba, a ranta ta dinga tunanin Yaya Sultan wanda ta tabbata da ace shi ne yaji tana kuka ba zai taɓa barinta ba, koda ace ya san dalilin kukan nata to sai ya tsaya ya sake jin ba'asi sannan kuma ya yi iya yin sa wajen ganin ya sanya ta yi shiru.
Har ya yi parking a compound ɗin Hajiya Babba bata sani ba, sai da ya ga da gaske bata san zo ɗin a sannan ya kai hannunsa na dama ya taba ta. Ta buɗe idanunta da kyar tana kallonsa, sosai ta bashi mamaki da bai yi tunanin kukan da take har ya kai yawan wannan ba, Babu yabo babu fallasa ya ce
“it will be better for you if you stop this nonsense, ki sauka ki tafi gida”
Bata ce komai ba ta ɗauki wayarta da ke kan cinyarta sannan ta sauka daga motar, kowa apartment ɗin Hajiya Babba ya nufa amma ita juyawa ta yi ta nufi nasu sashin dan bata jin zata iya magana da kowa. Babu kowa a parlonsu sai tv dake aiki ita ɗaya, ta ɗan kalli hanyar kitchen jin ƙamshi na tashi yasa ta tabbatar da Amma na kitchen dan haka kai tsaye daƙinta ta nufa, koda ta shiga zame doguwar rigar jikinta ta yi ta faɗa kan gado ta rufe jikinta gaba ɗaya sannan ta sake fashewa da wani irin kuka tana jan numfashi da kyar..
****
Around 9:30pm Zahra ke zaune gefen gadon tana shafa bayanta a hankali, sai da ta tabbatar da baccinta ya yi nisa sannan ta tashi ta rage gudun ac ta rufeta ruf da duvet sannan ta sauya mata hasken zuwa blue ta fice daga ɗakin. Sai da ta koma daƙinta ta fashe jikinta da turare sannan ta nufi ɗakinsa tana gyara zaman doguwar sleeping dress ɗin dake jikinta. A hankali ta tura ƙofar ɗakin bakinsa ɗauke da sallama, A zuciya ya amsa idanunsa maƙale da farin glasses wanda ya ƙara masa kyau, yana danna system da hannunsa na dama ɗayan hannun kuma ya riƙe mug ɗin coffee sai tiriri yake, yana sipping a hankali. Gefen gadon ta zauna tana kallonsa ba tare da ta ce komai ba, Jin har bayan mintuna biyar bata yi magana ba ya sanya ya ɗago kansa yana kallonta fuskarsa a sake ya ce“Da matsala dai?” girgiza kanta ta yi tana wasa da fingers ɗinta, ya ɗan yi jim kafin ya ce“to mene ne?” ɗan kallonsa ta yi ganin ya kafeta da manyan idanunsa yasa ta sake ƙasa da nata a sanyaye ta ce“daman ina son magana da kai ne” rufe system ɗin gabansa ya yi yana gyara zamansa ya ce“okay go ahead”
Zahra ta ɗan yi shiru tana tunanin ta in da zata fara can kuma ta ɗan numfasa cikin sassanyar murya mai cike da ladabi ta ce
“Dan Allah dan Annabi dan girman Allah Doctor kada ka auri Nana, ka da ka yarda da maganar Atta. Wallahi zan iya mutuwa idan ka aureta, ba zan jure ganin ku tare ba, Dan Allah kada ka bari maganganunta su yi tasiri akan ka. Ka rufa min asiri dan Allah...” ta ƙare maganar cike da damuwa mai tarin yawa.
Abdusammad ya dinga kallonta ba tare da ya ce komai ba, fuskarsa kuma sam babu alamun damuwa ko kuma mamaki. Jin shirun nasa ya yi yawa ya sa ta ɗago jajayen idanunta ta kalleshi sai kuma ta sake faɗin
“na sani ka aureni ne ba da soyyayar danginka ba, na sani daman dole wata rana zasu iya cewa ka ƙara aure, kuma wallahi ba zan taɓa ja da wannan ba, ba zan yi yunkurin hanaka ba. Amma dan Allah dan Annabi ka auri wata ba Nana ba! Ka samo mata wadda ban sani ba, dan girman Allah kada watarana ka ce zaka haɗani kishi da Nana, zan mutu ne Doctor.. wallahi mutuwa zan yi...”
Ta kasa ƙarasa maganar saboda wani irin kuka daya kwace mata. Furzar da iska kawai ya yi daga bakinsa still looking at her, Lokaci ɗaya ya saki wani yalwattacen murmushi yana ɗan ɗauke kansa zuwa gefe guda kafin ya yi gyaran murya cikin nutsuwar data gama ratsa shi ya ce
08106608363,
Nanameera.*🌹 NAANAH 🌹*
Arewabooks@Nanameera08
Wattpad@Nanameera08.
Page 27...
“Fateemarh kenan. Kina tunanin zan iya auren Nana? Ko da ace ya zama dole na ƙara aure. Kina tunanin zan iya zama da yarinyar da nake ma kallon ƴata? Yarinyar da ya ci ace na haifi kamarta, how?”
Ya dakata da maganar yana furzar da iska daga bakinsa. Gyara zamansa ya yi yana riƙo hannayenta duk biyun cikin nasa ya ci gaba da faɗin “Ba zan taɓa auren Nana ba, koda ace zan ƙara aure to ba zan aureta ba. Ballantana ma kawai kina son ɗaga hankalin ki ne akan abin da ki ke da tabbacin ba zai yiwu ba, ko kin manta nan da wani satin i yanzu Nana matar aure ce?”
Ya ƙare maganar yana kafeta da idanu, Zahra ta sunkuyar da kanta tana sauke ajiyar zuciya murya a sanyaye ta ce“ban manta ba, kawai dai na tsorata ne da kalaman Atta. Kai da kan ka kace ba'a tsallake umarninta idan har ta ce ayi abu to dole sai an yi shi, to kuma kana gani da kanta abin da ta ce. Wallahi ba zan taɓa hanaka ƙara aure ba, saboda na san ka yi min, ka aureni duk da kasan hakan ba abu ne wanda aka yarda dashi ba cikin danginka. Sannan kana shige min faɗa idan har wani ya yi yunkurin takani ko kuma aibatani. Kuma ka bani damar haifa maka ƴa wadda na san ba dan ka yarda dani ba, ba zaka taɓa yin hakan ba. Kaga kuwa dan yanzu ka ƙara aure ba zan ja da kai ba!” Ta ƙarasa maganar hawaye na zubowa kan fuskarta.