← Book details Naanah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 55 OF 125

Sashe 55

Naanah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya ƙare maganar yana jifa da hotunan. Ban da kallonsu babu abin da sauran ke yi, Maimoon kuwa sai ajiyar zuciya take saukewa ta ruƙube a jikin bene. Abba ne ya sunkuya ya ɗebi hotunan dan gabansu suka faɗo, Ya dinga buɗe su ɗaya bayan ɗaya. Baya ya yi ya faɗi ƙasa, jikinsa sai rawa yake, Abdusammad ya sunkuya da sauri yana kallonsa ganin kamar bata cikin hayyacinsa ya amshi hotunan. Waro idanunsa ya dinga yi akan ko wane daya daga cikin su, Lokaci ɗaya ya miƙe tsaye ya ƙarasa wajen Safwan ya shaƙeshi yana faɗin

“Tell me ina ka samu wannan? Wane ya baka? A ina ka samu Safwan?”

Ya ƙare maganar yana jijjigashi kamar zai tsinke masa jiki. Girgiza kai Safwan ya yi bai ce komai ba, Abdusammad ya hankadashi sannan ya koma in da Abba yake ya riƙe shi yana faɗin

“Abba kada wannan ya dameka kaji, nothing will happen”

Wani murmushi mai ciwo Abba ya yi sannan ya dafa Abdusammad ya miƙe, sai da ya kalli kowa na parlon da idanunsa wanda suka kusa rufewa sannan ya yi murmushi mai haɗe da hawaye. Ba ƙaramin mamaki da kuma tausayi ya bawa kowa ba, domin rabon da ya zubar da hawaye tun mutuwar late Muhammad Shuwa, dan haka ba kowane ya taɓa ganin hawayen nasa. Amma ce ta taso da sauri ta ƙaraso gabansu kamar zararriya ta ce

“mene ne? Me ya samu Nana?”

Ganin babu wanda ya ce mata uffan yasa ta dinga kallon kasa cikin sa'a kuwa idanunta ya sauka kan hotuna guda biyu, kusan yar tsere suka yi da Sultan sai dai kafin ya ɗauka hoton ta riga da ta ɗauka. Ta dinga kallonsu tana girgiza kanta bakinta na wata irin rawa ta ce

“a... A'a... Wannan ba Nana ba ce, ba Nanata bace..ba ita ba ce wallahi!”

Sai kuma ta zubar da hotunan ta koma inda Abba yake tsaye ta riƙe kwalar rigarsa cikin tashin hankali ta ce

“Ahmad ka faɗa min, ka faɗa min gaskiya, ai ba Nana ba ce ba ko? Ba ita ba ce ba ko! Ni nasan ba ita ba ce, wannan ba Nanata ba ce, ka sanar dani dan Allah”

Ta ƙare maganar tana rushewa da wani raunataccen kuka. Abba rasa abin yi ya yi sai kawai ya rungumeta a jikinsa yana sauke numfashi a hankali, murya can ƙasa ya ce

“Ki yi haƙuri Rabi'ah”

Da sauri ta ɗago kanta tana kallonsa sai kuma ta ce“Nana ce?”

Jin bai ce mata komai ba ya sanya ta sake sakin wani marayan kukan ta ce“ka faɗa min mana!”

A hankali ya shiga gyada mata kai, Amma ta dinga kallonsa kai kuma ta yi baya ta faɗi ƙasa Sumammiya. Cikin hanzari Mama dasu Maimoon suka yi kanta. Abba kuwa kasa koda motsi ya yi sai numfashi yake saukewa. Da hannu ya yiwa Safwan alamar ya zo, ya ƙaraso kansa a ƙasa dan kunyar haɗa idanu yake da Abban. Shafa kansa Abba ya yi muryarsa a kusan ƙarye ya ce

“Safwan ni na amince ka auri wadda ka ke so, ba kai ba bana fatan kowani daga cikinku ya auri Nana!”

Da sauri duk suka kalleshi, Papa ya miƙe idanunsa sun yi jajur shima. Zai yi magana Abba ya ɗaga masa hannu ya ce”a'a Yaya kada ku hana shi dan Allah, Ni ina neman wannan alfarmar a bar shi ya auri wadda yake so”

Rungume shi Safwan ya yi yana kuka, ya rasa farin ciki zai yi ko kuma baƙin ciki. Abba ya shafa kansa yana murmushin ƙarfin hali. Can ya ɗago kansa yana kallon Abba ya ce“Abba koda ba yar cikin gidan nan bace?”

Gyaɗa masa kai kawai Abba ya yi dan ya fara daina ganewa, Safwan ya yi murmushi mai haɗe da hawaye ya ce“to daman ƙanwar matar Yaya nake so”

Da mamaki Abdusammad ya dinga kallonsa, lokaci ɗaya kuma ya girgiza kansa ya ce“kai ka isa, ba zaka aureta ba wallahi, ba zaka auri wadda ba yar danginmu b!”

Rufe masa baki Abba ya yi ya ce“a'a Abdusammad ka yi kaffara, zai yi aurensa. Wannan alƙawarina ne, ku je ku gabatar da komai, a ɗaura auren kowace cikin farin ciki zan je na huta”

Kasa cewa komai suka yi, gaba ɗaya wajen tausayinsa suke, ko bai faɗa ba sun san ƙarfin hali kawai ya ke. Ya juya yana ƙoƙarin tafiya, sai dai sarawar da kansa ya yi masa ya sanya shi dakatawa, ya dafe kan yana kiran sunan Allah. Ji ya yi an riƙe shi ya ɗago jajayen idanunsa yaga Abdusammad ne, murya a sanyaye ya ce“bari na raka ka Abba” daga haka ya gyara riƙon da ya yi masa. Kasa cewa komai Abba ya yi har suka fice daga parlon.

Har ɗakinsa ya kai shi ya zaunar dashi kan gado sannan ya zare masa hular kansa ya ajiye gefe, Abba ya sauke nannauyar ajiyar zuciya sannan ya jingina da jikin gado, ya lumshe idanunsa lokaci ɗaya hawaye suka fara sintiri akan fuskarsa. Shiru Abdusammad ya yi yana kallonsa cike da tausayawa, can kuma ya tsuguna a gabansa ya riƙe hannunsa jiki a sanyaye ya ce

“please Abba, kada ka damu kan ka, ni nayi maka alƙawarin zan dawo da Nana, zata dawo cikin aminci”

Dakyar ya iya buɗe idanun nasa, dan da gaske jikinsa ya yi sanyi sosai, ya dafa kan Abdusammad yana murmushi mai haɗe da hawaye ya ce

“me yasa ta yi haka Abdul? Why? Bata san halin da zan shiga ba, yau da safe na tashi da farin ciki, irin farin cikin da baya misaltuwa. Naji ni cikin annashuwa da nutsuwar zuciya saboda ina tunanin zan aurar da tilon ƴata wadda Allah ya bani matsayin amana.” Abba ya yi shiru saboda kukan dake neman tawo masa, ya numfasa sannan ya ci gaba da fad'in “sai dai sam ban yi tunanin Nana zata tafi ba, ban yi tunanin zata bari na tozarta idon duniya ba. I feel ashamed Abdul...na tursasa yara dayawa sun yi auren dangi, domin samar da al'umma mai kyau, sai dai ƴata dana haifa ta guji hakan. Na gayyaci mutane domin su tayani farin ciki sai dai yanzu ban san da wane idanu zan kallesu na ce musu an fasa auren Nana ba, na kuma faɗa musu cewa Nana ta gudu ta barni..” ya dakata saboda tarin daya turnuƙeshi. Abdusammad ya riƙe shi sosai yana hawaye shima ya ce“a'a Abba, dan Allah kada wani abun ya sameka”

Murmushi kawai Abba ya yi yana kallon enlargement ɗin hoton Nana dake maƙale a jikin bangon ɗakinsa, lokacin bata fi 3yrs ba, tana tsaye hannunta riƙe da teddy bear ta kwaɓe fuska kamar mai shirin kuka. Wasu zafafan hawaye ne suka shiga sakkowa kan fuskarsa, Ya lumshe idanunsa sannan ya sake buɗe su ya ce

“Ashe bani da rabon aurar da ɗiyata, haka Allah ya ƙaddara min, shiyasa ya bani Nana ita kaɗai”

Da sauri Abdusammad ya girgiza kansa ya ce“a'a Abba ya zaka ce haka? Me zai hana ka aurar da Nana? Nace maka zan dawo da ita”

Girgiza kai Abba ya yi cikin kuka ya ce

“To ko ta dawo wane zai aureta Abdul? Nobody! Babu wanda zai auri Nana! Babu mai iya aurenta”

Yanda ya yi maganar a mugun sanyaye shi ne ya ƙara bawa Abdusammad tausayi, gaba ɗaya Abba ya yi loosing hope. Agogon hannunsa ya kalla sai kuma ya ce“kaje domin kai ne a bigirena, just go”

Dakyar Abdusammad ya miƙe yana sake kallon Abba. Ganin haka yasa Abba yin murmushi ya ce“kar ka damu I'll be fine. Just go”

Jiki a sanyaye ya juya ya fice daga ɗakin, Abba ya numfasa sannan ya kwanta a gefen gadon yana lumshe idanunsa.

A balcony ya tsaya ya goge hawayensa da hanky sannan ya nufi apartment ɗin Hajiya Babba kamar babu abin da ya faru. A zaune ya samu su Papa da angwayen dan haka ba'a tsaya sake ɓata lokaci ba aka gabatar da ɗaurin auren.

****
Tsaye suke jikin ƙarfen bene, Aliyu sai kallonsa yake ganin yanda ya yi shiru kamar me tunani. Ya numfasa sannan ya ce

“Buddy are you sure abin da ka yi shi ne daidai?”

Buɗe gajiyayyun idanunsa ya yi akan Aliyu sai kuma ya ɗauke kai yana kallon gefe, Aliyu zai sake magana Papa da Baba Lawan na Njomboli suka ƙaraso wajen, dafashi Baba ya yi cikin jin daɗi da farin ciki ya ce

“Allah ya yi maka albarka Abdusammad, ya sanya albarka cikin auren, tabbas abin da ka yi shi ne dai-dai. Kuma muna alfahari da kai”

Jinjina kansa ya yi jiki a sanyaye ya ce“Amin Baba. But ina jin kamar ban yi dai dai ba idan ya kasance ni ne na auri Nana, wallahi ban taɓa yi mata kallon wadda zan aura ba, ban taɓa kallonta matsayin mace bama. Kawai ganinta nake kamar ƴata, yanda zan yiwa Noor abu haka nake ganin zan yiwa Nana, ya zata ji idan aka ce mata ni ne wanda aka ɗaura mata aure dashi?”

Ya ƙare maganar da damuwa sosai akan fuskarsa
Dafashi Papa ya yi kafin ya ce“mun sani Abdusammad kuma abin da ka yi shi ne dai-dai. Ahmad ba zai manta da wannan abun ba, ka share masa hawayensa sannan ka fitar dashi kunyar jama'a. Gefe guda kuma ka wanke kanka akan aurenka na farko wanda ka yi bada yardar danginka ba. So you don't need to be worry kaji”

08106608363
Nanameera.*🌹 NAANAH 🌹*

This page na dedicated to u jama'ar Nanameera's forum.

Page 34...

Shiru Abdusammad ya yi yana kallon Papa. Ya ɗan bubbuga kafaɗarsa sannan ya juya suka bar wajen. Harɗe hannayensa ya yi a ƙirji yana jin wani irin abu cikin ransa, mamaki da damuwa sun yi masa yawa, idan ya tuna cewa yanzu Nana matsayin matarsa take amsawa sai yaji gabansa ya faɗi.

“Ya rabb!”

Ya furta yana furzar da zazzafan numfashi daga bakinsa. Dafashi Aliyu ya yi ganin yanda ya damu yasa ya ce“Buddy ka daina damuwa kaji dan Allah. Always Allah's plan is the best”

Kallonsa ya yi da gajiyayyun idanunsa ya ce“Buddy Nana fa. Nana fa”

“to mene a ciki?”
Chapter 55 · 0% Book details