← Book details Naanah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 48 OF 125

Sashe 48

Naanah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Zaune suka tadda Abba kan kujerar da ke ɗakin, yana waya da wasu abokansa da zasu zo daga Paris. Ganin hawaye a fuskar Nana ya sanya ya katse wayar ba tare da ya gama ba. Ya dinga kallonsu sai kuma ya ce

“lafiya dai?”

Ya yi tambayar yana miƙewa tsaye. Amma bata ce komai ba, sai sakin hannun Nana da ta yi. Ta ƙarasa gabansa a hankali tana kuka ƙasa-ƙasa, Ba ƙaramin rikicewa Abba ya yi ba, dan duk wani abu daya shafi Nana baya ɗaukansa da sauƙi. Ya riƙe hannayenta duk biyun muryarsa cike da damuwa ya ce

“Nana mene ne?”

Sunkuyar da kanta ta yi wasu zafafan hawaye suka shiga sakkowa kan fuskarta. Ta kasa cewa komai sai murɗa yatsun hannunta take, Abba ya yi shiru sai kuma ya kalli Amma ya ce“what's going on?” girgiza kai ta yi a sanyaye ta ce“wallahi nima ban sani ba. Ramlah ta zo ta ce min wai gata nan tana kuka, da naje shi ne ta ce na kawo ta wajenka”

Abba ya mai da idanunsa kan Nana wadda har sannan bata ce komai ba. Ya zaunar da ita sannan ya zauna gefenta yana kallonta sosai ya ce“Nana tell me meya faru? Why are you crying?”

Ɗago jajayen idanunta ta yi ta kalleshi, bakinta ya fara rawa kamar zata yi magana sai kuma ta sake sunkuyar da kanta tana sakin wani sabon kukan. Abba da ransa ya fara ɓaci ya ce

“Kin faɗa min mene ne ko sai na bugeki?”

A hankali ta sake ɗago kanta tana kallonsa, sai kuma ta ɗaga kanta ta kalli Amma dake tsaye kusa da su. Ganin duk ita suke kallo yasa ta saukar da idanunta ƙirjinta na wani irin bugawa da ƙarfi, ta buɗe bakinta da take jin kamar ba nata ba. In a very polite tongue ta ce

“Abba daman akwai abin da nake son faɗa maka, but...but I can't, saboda ban san ya zaku ɗauki al'amarin ba”

Abba ya yi shiru yana saurarenta. Jin babu wanda ya ce komai a cikinsu yasa ta ɗago kanta hawaye na biyo fuskarta ta ce

“wallahi bana son Yaya Safwan. Bana son aurensa, dan Allah dan Annabi Abba a fasa auren nan. Wallahi ba zan iya zama dashi ba, dan girman Allah kawai...”

Bata samu zarafin faɗin ƙarashen abin da ke bakinta ba, sakamakon zazzafan marin da Abba ya sauke mata akan both checks ɗinta. Ta sanya hannunta ta dafe kuncinta tana jin wata irin raɗaɗin azaba. Dakyar ta iya buɗe idanunta wanda take jin kamar sun fashe ta ɗago kanta. Tsaye taga Abba a gabanta yana wani irin huci kamar yunwataccen Zaki. Yanda yake kallonta zai tabbatar maka da tsananin ɓacin ransa da yake ciki, gumi sai tsatsafo masa yake duk da ac dake ɗakin.

Amma ta ƙaraso wajen da sauri ta jawo hannun Nana itama ta sauke mata wani zazzafan mari a kuncinta na dama, Nana ta rasa yanda zata yi saboda azabar data mata yawa. Cikin tsananin ɓacin rai Amma ke faɗin

“Wato duk irin abin da na faɗa miki baki ji ba kenan ko Nana? Duk nasihar da nayi miki ta tashi a banza kenan ko? Baki ji abubuwan da nace miki ba ko?”

Ban da girgiza kai babu abin da Nana ke yi dan gaba ɗaya magana ta gagareta. Ta zube a ƙasa ta riƙe ƙafafun Abba da duka hannayenta biyu cikin wani irin kuka mai tsuma zuciya ta fara magana

“Na sani Abba ban kyauta ba, ban kuma yi dai dai ba idan har naƙi bin umarninka a matsayinka na mahaifina. Ka cancanci nayi maka kowace irin alfarma Abba, amma wallahi ba zan iya wannan ba, ba zan iya auren Yaya Safwan ba. Zuciyata ba zata jure zama dashi ba, na so na danne na kuma yi haƙuri akan haka, amma ina gudun abin da hakan zai haifar daga baya. Dan haka dan girman Allah, dan soyyayar ka da Annabinsa. Ka raba auren nan dan Allah, kada ka bari na aure shi Abbana, ka rufa min asiri!”

Ta ƙare maganar tana sakin wani irin marayan kuka. Dakyar Abba ya janye ƙafafunsa daga gurin, ya shiga zagaye ɗakin ba tare da ya ce komai ba. Amma ta tsaya a wajen kamar statue, sai ta kalleshi sai kuma ta kalli Nana. Above 5mins kafin yaja ya tsaya a tsakiyar ɗakin hannayensa naɗe a ƙirjinsa yana kallonta. Idanunsa sun kaɗa sun yi jajur dasu, har wani ruwa-ruwa ne ya kwanta a cikinsu na zallar baƙin ciki. Ya furzar da zazzafan numfashi daga bakinsa sai kuma ya shiga girgiza kansa yana faɗin

“Wai Ƴata! Wai ƴar dana haifa ce zata faɗi irin wannan maganar. Ƴar da nake saka ran zata yimin biyayya koda ace bata son abu, Yar dana ɗauki dukkan yarda na ɗora mata ita ce take shirin watsa min ƙasa a idanu!. Yar da nake tunanin ba zata taɓa bani kunya ba, ita ce ke shirin tona min asiri a cikin dubban jama'a.” Ya tsaya da maganar yana sauke numfashi, Sai kuma ya sake mai da idanunsa kanta a zafafe ya ce

“Wallahi tallahi baki isa ba Nana! Ban haifi Yar da zata juyani ba. Duk abin da ki ke so zan iya miki shi, amma ba zan taɓa yarda ki zubar da mutuncin gidanmu ba! Baki isa ba Nana!”

Kasa ɗago kanta ta yi sai hawaye take dan yanzu ko sautin kukan nata ma ba'a ji. Amma ta yi shiru tana kallonsa duk da bata ji daɗin abin da Nana ta yi ba, hakan bai hanata jin tausayinta ba a matsayinta na mahaifiyarta. Sai dai ganin yanda ran Abba ya ɓaci ya hanata cewa komai. Da kansa ya tako har gabanta ya sanya hannunsa ya ɗagota yana kallonta ya ce

“Koda auren Safwan na nufin rasa rayuwarki wallahi Nana sai dai ki mutu. Na kuma yarda na rasa ki, akan ki zubar da martaba da kuma ƙimar da muka ɗauki shekaru masu yawa muna tattalinta. Dan haka ki shirya zama matar aure daga yau zuwa jibi.” yana gama faɗin hakan ya saketa ya juya ya fice daga ɗakin yana bugo ƙofar. Amma ta sulale a ƙasa tana jin ranta na mata wani irin suya, ita kuwa Nana kasa motsi ta yi sai numfarfashi take. Har bayan mintuna sha biyar suna zaune a wajen zuciyoyinsu babu daɗi, Nana ta yunƙura da kyar ta tashi ta fice daga ɗakin tana riƙe da kanta, Amma ta bita da idanu har ta fice. Lokaci ɗaya ta fashe da wani irin kuka, wanda rabonta da ta yi kuka tun rasuwar mahaifiyarta sai gashi yau tana sake kuka akan auren NAANAH..

****
Ƙarfe 9:30 na dare ta buɗe ɗakin ta shigo. Zaune ta hangeshi tsakiyar gado ya tankwashe ƙafafunsa yana sipping coffee a hankali, hannunsa ɗaya akan system yana operating ɗinta. Zahra ta dinga kallonsa can kuma ta sauke numfashi ta ƙaraso ciki, A gefen gadon ta zauna tana kallonsa har sannan ba tare da ta ce komai ba. Idanun da yaji suna yawo akan sa ya sanya shi ɗago kansa, suka yi ido biyu da Ita, a hankali ta sauke nata idanun. Ya dinga kallonta sai kuma ya rufe system ɗin ya sakko daga kan gadon, a gefen drawer ya ajiye system ɗin ya kuma ajiye mug ɗin hannunsa. Sannan y koma ya zauna yana kallonta yace

“Zahra”

Yanda ya yi maganar a sanyaye ya sanyata ɗago kanta, hawaye ya gani kan farar fuskarta. Ya yi shiru can kuma ya ce“zo mana” jiki a sanyaye ta tashi ta ƙarasa inda yake sannan ta zauna, ya jawo hannunta yana shafawa a hankali ya ce

“Mene ne?”

Muryarta na rawa ta ce“doctor da gaske aure zaka yi?”

Ta ƙare maganar tana ɗago idanunta wanda hawaye ke zuba daga cikinsu. Abdusammad bai iya ɓoye-ɓoye ba dan haka ya gyaɗa mata kai ba tare da ya ce komai ba. Ta sunkuyar da kanta tana kuka a hankali, girgiza kansa y yi sai kuma ya ɗago fuskarta da hannunsa na hagu yana kallonta ya ce

”but you promised cewa ba zaki tada hankalin ki ba right?”

Zahra ta gyaɗa kanta lokaci ɗaya ta shiga goge hawayen idanunta ta ce“i'll not. Allah ya bamu zaman lafiya”

Amin kawai ya ce sai kuma ya yi shiru yana nazarinta. Tabbas bata ji daɗi ba, kawai dai bata son ta nuna tashin hankalinta har ya ɓata masa rai, dan haka shima bai sake maganar ba suka shiga wata hirar ta daban.

Daren ranar babu wanda ya runtsa tsakanin Abba, Amma da kuma Nana. Kowa da abin da yake saƙawa a cikin ransa, Amma na tunanin yanda zata saka Abba ya yarda a fasa auren Nana, yayinda Abba ke tunanin yanda zai ɓoye al'amarin kada kowa ya samu labari. A ɓangaren Nana kuma ta kwana tana kukan rashin sanin abin yi, ya zata yi da Junaid da kuma Zahra? Junaid ya yi alkawarin idan har bai ji maganar fasa aurenta gobe ba zai turowa Abba hotunanta. Haka ma Zahra, dan haka abin duniya ya isheta ta kasa koda runtsawa sai juyi take akan gadonta, ana fara kiraye-kirayen sallar asuba ta mike daga kwancen, ta shiga toilet ta ɗauro alwala sannan ta fito ta fara gabatar da sallolin nafila har aka yi assalatu. Koda ta idar da sallah zama ta yi nan kan ladduma ta ci gaba da saƙa da warwara har gari ya fara haske. Ringing ɗin wayarta ne ya sanya ta tashi daga wajen, ta ƙarasa gaban mirror ta ɗauki wayarta, ganin kiran Junaid ya sanya gabanta ya yanke ya faɗi, hannunta na rawa ta ɗaga kiran ta kai kunne. Junaid na fitowa daga masallaci ya ce

“Ya dai Nana?”

Shiru ta yi tana tunanin ta hanyar da zata fara faɗa masa. Jin bata ce komai yasa ya sake cewa

“are you there?”

Ta gyaɗa kanta kamar yana gabanta. Sai kuma ta numfasa ta ce

“eh.”

“Ya ku ka yi dasu?”

Girgiza kanta ta yi ta ce

“basu yarda ba, Abbana ya ce dole sai na aure shi. Dan Allah dan Annabi sir ka yi haƙuri, ka barni na yi auren nan. Ni na haƙura da soyyayar, Allah ya baka wadda ta fini”

Junaid ya yi wani murmushi sai kuma ya ce
Chapter 48 · 0% Book details