← Book details Naanah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 59 OF 125

Sashe 59

Naanah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Ke daɗina da ke ba'a iya miki. Ina ƙoƙarin yin abin da zai taimakeki amma ke bakya gani, to sai me idan an yi mata asirin? Le dai ba burinki ta rabu da mijinki ba?”

Tashi itama Zahran ta yi tana kallonta ta girgiza kanta ta ce

“Ni ba ina nufin a cutar da ita bane. Kawai dai bana son ta zauna matsayin kishiyata, amma wallahi ba zan iya saka hannu cikin sake cutar da ita ba!”

Harararta ta yi ta ce“to ai sai ki yi ta yi, kina nan kuwa zata rabaki da gidan da ki ke taƙama dashi!”

Tura baki Zahra ta yi tana kallon wani wajen ta ce“ni dai babu ruwana!”

Aunty Khadijah bata sake saurarenta ba ta ƙarasa ta ɗauki jakarta inda ta ajiye ta yi waje fuuu. Sai da taga ta fita sannan ta koma ta zauna kan sofa ta fashe da kuka, ita sam bata da niyyar sake cutar da Nana. Amma ba zata iya zama da ita matsayin kishiya ba.

Tana nan zaune tana kuka aka buɗe parlon, ta ɗago kanta da sauri ganin wanda ya shigo. Sanye yake da kayansa na jiya sai dai babu babbar rigar, ta dinga kallonsa ganin yanda ya fice hayyacinsa. Kallo ɗaya ya yi mata ya nufi sama da sauri, ta bi shi da idanu sai kuma ta tashi tabi bayansa da sauri.

Tsaye ta same shi a tsakiyar ɗakinsa, ya zare rigar jikinsa sai fara singlet a jikinsa. A hankali ta saki ƙofar tana kallonsa, Ta ƙarasa gabansa muryarta a sanyaye ta ce

“Doctor”

Kallonta ya yi sai kuma ya ce“na'am”

Ƙoƙarin magana take amma ta kasa, sai rawa bakinta yake. Ya ɗan kalleta sai kuma ya ce

“I want to take shower”

Gyada masa kai ta yi hawaye na biyo kuncinta. Ya nufi toilet ba tare da ya sake kallonta ba, da idanu Zahra ta bi shi sai kuma ta zauna kan kujerar dake ɗakin, lokaci ɗaya ta haɗe kanta da gwuiwa ta fashe da kuka. Tana nan zaune har bayan mintuna ashirin ya fito daga toilet ɗin yana goge kansa da towel, Ya kalleta sau ɗaya sai kuma ya nufi wajen dresser tashi. Cikin yan mintuna ya shirya cikin wasu kananan kaya t-shirt fara da jeans blue colour. Ya gyara sumar kansa sai sheƙi take, turaren arabian oud ya fesa sannan ya dauki wayarsa yana shirin fita. Zahra na ganin haka ta mike da sauri bakinta na rawa ta ce

“Dd... Doctor!”

Cak ya tsaya lokaci ɗaya kuma ya juyo yana kallonta. Sunkuyar da kanta ta yi ganin yanda fuskarsa take babu alamar walwala. Ya gyara tsaiwarsa yana kallonta sosai ya ce

“Ina ji”

A sanyaye ta ce

“Daman i just want to ask you ne”

Gyaɗa mata kai ya yi ya ce

“uhm..”

Ta ɗan numfasa tana ƙoƙarin riƙe kukanta ta ce

“wai da gaske ka auri Nana?”

“Eh”

Ya bata amsa kai tsaye, Durƙushewa Zahra ta yi a wajen, ta haɗe hannayenta duk biyun alamar roƙo ta ce

“Dan Allah dan Annabi ka yi haƙuri. Kada ka aureta doctor, ka rufa min asiri, wallahi ba zan iya zama da Nana matsayin kishiya ba. Ba zan iya ba doctor, na san baka sonta! Na san dole aka maka, ba yin kanka bane!”

Ban da kallonta babu abin da Abdusammad ke yi, sam babu alamar damuwa akan fuskarsa. Ya yi mata alama data tashi, babu musu ta mike tana kuka har sannan. Furzar da numfashi ya yi kafin ya ce

“Ki yi haƙuri!”

Ya yi maganar yana juyawa, ganin ya fice daga ɗakin yasa Zahra sake fashewa da wani kukan, lokaci ɗaya kuma ta bi bayansa da gudu, a parlon ta same shi yana shirin fita. Cikin kuka ta ce

“Kana nufin zaka zauna da ita? Zaka haɗa zuri'a da ita? Yarinyar da aka tabbatar da bata da tarbiyya! Yarinyar da kowa yaga hotunanta da namiji? Yarinyar da ke bin maza!”

Ta yi shiru tana girgiza kanta, sai kuma ta tako har gabansa ganin bai ko motsa ba. Cikin kuka ta ce

“Kada ka zauna da ita doctor, na san baka sonta. Na san wallahi baka son Nana dole aka maka, dan girman Allah ka saketa! Ka saketa mu yi komawar mu US, kada ka ce zaka haɗa zuri'a da lalatacciyar yarinya ka...”

“Shut up!”

Ya daka mata wata razananniyar tsawa wadda ta sanyata firgita. Gaba ɗaya jijiyoyin kansa sun tashi, idanunsa sun kaɗa sun yi jajur sai huci yake, rai ɓace ya ce

“Kar na sake ji kin haɗata da wadannan munanan kalaman! Zan bata miki fiye da tunanin ki Zahra. And you know what? Babu wanda ya yi min dole sai na auri Nana, Ni ne na aureta saboda raɗin kaina, kuma kin san me yasa na aureta?”

Samun kanta ta yi da girgiza masa kai. Ya ƙara taku ɗaya gabanta wanda yasa suka yi kusa sosai har suka jin hucin numfashin juna ya ce

“Cause i love her! Na aureta ne saboda ina sonta! Ina son Naanah! Kuma ba zan taɓa sakinta ba! She's my wife!”

08106608363,
Nanameera.*🌹 NAANAH 🌹*

Arewabooks@Nanameera08
Wattpad@Nanameera08.

Page 36.

Ya yi maganar yana watsa mata wani irin kallo. Girgiza kai Zahra ta yi ta riƙe shi a kiɗime ta ce“A'a wallahi na san baka sonta. Kawai dai ka faɗa ne, baka sonta wallahi!” ta ƙare maganar tana fashewa da wani irin kuka. Shiru Abdusammad ya yi yana kallonta, can kuma ya janye hannunta daga jikinsa ya juya ya fice daga ɗakin zuciyarsa a dagule babu daɗi. Zahra ta durƙushe a wajen tana kuka kamar ranta zai fita, she just can't believe a ce doctor ya ce yana son Nana, how? Ta girgiza kanta tana tashi zaune ta ce“A'a impossible”Ta tashi da sauri ta haye sama.

Kai tsaye apartment ɗin Hajiya Babba ya nufa, ya murɗa handle ɗin bakinsa ɗauke da sallama, zaune ya same su suna tattauanawa. Ya ƙarasa ciki ya tsaya gefen kujera ba tare da ya ce komai ba. Papa ne ya ce

“Ya jikin Ahmad ɗin?”

Numfasawa ya yi kafin ya ce

“Da sauki Alhamdulillah, bacci ya daukesa ma"

Papa ya jinjina kansa sai kuma ya yi shiru. Atta ta ce ta girgiza kanta tana hawaye ta ce“oh ni Maryama, ko ina yarinyar nan ta shiga Allah masani”

Sultan ne ya yi saurin faɗin

“maybe ai tana wajen wanda aka hoton nasu tare”

Cikin kuka ta ce“to ina zamu san wane shi?”

“where are the pictures?”

Abdusammad ya yi maganar yana kallon Sultan dan shi ne ya ɗauke su. A sanyaye ya ce“suna ɗakina”

“Bring them”

Okay kawai ya ce sannan ya tashi ya fice daga parlon. Sai a sannan Hajiya Babba ta ce“Abdussamad a samu a yi reporting wajen yan sanda”

Okay kawai ya ce yana gyara tsaiwarsa. After some minutes Sultan ya dawo parlon hannunsa riƙe da envelope ɗin, ya miƙa masa ya karba yana faɗin

“Good job”

Murmushi kawai Sultan ya yi sannan ya koma ya zauna. Papa ya miƙe tsaye kana ya ce“bari naje na duba shi, we should talk later” okay kawai suka ce sannan ya fita daga parlon.

Abdusammad ya zauna idanunsa na kan Hajiya Babba ya ce“Hajiya”

“Na'am” ta amsa a sanyaye..

“Ina Safwan yake?”

Ya yi tambayar fuskarsa a ɗan haɗe.

Hajiya Babba ta kalli hanyar sama sai kuma ta ce“Da dai yana nan bai tafi ba, amma ban sani ba ko ya je gidansa wajen Haule. Tun da ita ɗayar yarinyar har yanzu basu kawota ba”

Miƙewa ya yi ya ce“okay bari naje sai an jima” daga haka ya fice daga ɗakin yana tafe cike da taƙama.

****
Papa ya yi shiru yana kallon Abba jiki a sanyaye. Can kuma ya girgiza kansa ya ce

“A'a Ahmad ba'a haka, yarinya ce ƙarama, akwai rashin hankali a tattare da ita. Bai kamata a ce ka ɗauki wannan mummunan hukuncin ba, beside ma yarinyar ta yi aure yanzu!”

Da sauri ya kalli Papa sai kuma ya ce

“Ta yi aure? Yaushe ta yi aure ban sani ba Papa? and wa ta aura?”

Murmusawa Papa ya yi sai kuma ya ce

“Wa ka ke tunanin zai share maka hawaye irin haka?. Abdusammad ne ya aureta, dashi aka daura mata aure”

Da wani irin mamaki Abba ke kallon Papa, sai kuma ya girgiza kansa ya ce

“Yaya ban da wasa, ka faɗa min da gaske Abdusammad ya aureta?”

Dafa shi Papa ya yi ya ce“Eh da gaske ne, kasan bama irin wannan wasan da kai ai”

Tashi Abba ya yi ba tare da ya ce masa komai ba ya zura slippers ɗin dake ƙasan gadon sannan ya yi waje da sauri, duk da yanda yake jin jikinsa babu daɗi.

Da idanu Papa ya bi shi sai kuma ya tashi ya biyo bayansa dan ganin inda zai je. A parlon suka ci karo dashi, Ya yi saurin riƙe kwalar rigarsa rai ɓace ya ce

“me yasa? Me yasa Abdul? Why? I said why!”

Ya ƙare maganar yana jijjigashi. Kallonsa kawai Abdusammad ke yi ba tare da ya san akan abin da yake magana ba, Amma da ke zaune ita da Aunty Ramlah suka miƙe tsaye. Ta ƙaraso wajen tana kallonsu, dai dai nan Papa ya fito daga ɗakin. Da sauri kuma ya ƙaraso gabansa yana ƙoƙarin janye hannunsa ya ce

“Subhanallahi Ahmad mene haka?”

Girgiza kai Abba ya yi yana sake matse kwalar rigarsa ya ce

“Ka faɗa min meyasa zaka yi haka? Me ya saka zaka aureta! Akan mene ne!”

Sai a sannan Abdusammad ya fuskanci inda ya dosa. Ya ɗan yi murmushi yana janye hannunsa ya ce“to mene ne Abba? Nana ce fa”

A tsawace Abba ya ce

“Nanan! Ita Nanan bana son ganinka da ita. Bana son kowace mu'amala ta haɗata da yan gidan nan, ta riga da ta bar cikin dangin nan, yanzu bata kasance daya daga cikin mu . Akan me zaka aureta Abdul? Ka san zafin da naji?”

Shiru ya yi yana kallonsa ganin da gaske yake faɗar maganganun, Ya riƙe hannunsa a sanyaye ya ce“Abba ka yi haƙuri mana”

“Ba zan yi ba!”

Ya ce a zafafe. Kallonsa suka dinga yi da mamaki, Amma da tuni hawaye ya wanke mata fuska ta ƙaraso wajen ta rike gefen rigarsa cikin kuka ta ce
Chapter 59 · 0% Book details