← Book details Naanah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 67 OF 125

Sashe 67

Naanah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Nana ta katseta da sauri. Kallonta kawai Zahra ta yi ta kasa cewa komai, Nana ta sauka daga kan gadon ta ɗauki Jersey veil ɗin dake kan gado ta ɗora kan riga da wando jikinta, kasancewar jeans ne a jikinta blue sai yar ƙaramar riga me bottles itama blue, ta gama yafa mayafin sannan ta ɗauki wayarta ta fice daga ɗakin ba tare da ta sake kallonta ba.

Da idanu kawai Zahra ta bita sai kuma ta sunkuyar da kanta, daman ta san ba lallai bane ta saurareta, sai dai ta yi hakan ne a bisa umarnin da Umma ta bata. Zaune ta samu Amma a parlon tana cin abincin rana, ta dinga kallonta sai kuma ta ce“har kun gama?” gyaɗa mata kai ta yi tana shirin fita waje ta ce“eh.”

“Nana!”

Cak ta tsaya jin yanda Ammar ta kira sunanta, ganin irin kallon da take mata ya sanya ta sunkuyar da kanta ƙasa.

“A haka zaki fita?”

Amma ta yi tambayar tana kafeta da idanu. Kallon jikinta ta yi ba ƙarya jeans ɗin ya matseta sosai, dan duk surar jikinta ta bayyana. Amma ta ajiye spoon ɗin hannunta still looking at her ta ce“bana son shashanci fa”

Sum-sum ta koma daƙinta, bata ko kalli Zahra dake zaune tana kuka ƙasa-ƙasa ba ta ƙarasa press ɗinta ta ɗauki wata After dress baƙa ta ɗora akai sannan ta fito parlon. Kallo Ɗaya Amma ta yi mata ta ɗauke kai, ta fice daga parlon da sauri kai tsaye kuma apartment ɗin Maimoon ta nufa.

Koda ta shiga bata sameta a parlon ba, ƙamshin girkin da taji ya sanya ta nufi kitchen ɗin, tsaye ta sameta tana juya stew, ta jingina da jikin cabinet tana murmushi ta ce

“Amaryar Yaya Aliyu”

Kallonta kawai Maimoon ta yi sai kuma ta ɗauke kai ta rufe tukunyar sannan ta dawo gabanta ta ce“uwar gida” daga haka ta fice daga kitchen ɗin. Bin bayanta Nana ta yi suka dawo parlon, ta zauna kan kujera ta ɗauki remote ta ƙaro gudun ac dan zafi take ji, Nana ta zauna gefenta ta ɗora kanta a cinyarta ta ce“ke yanzu dan Allah duk sanyin da ake bakya ji?” gyaɗa mata kai Maimoon ta yi. Nana ta taɓe baki ta tashi zaune kamar wadda aka tsikara ta ce tashi zaune tana kallonta ta ce“kin san me?” girgiza mata kai Maimoon ta yi, Nana ta hankaɗeta ta ce“ke ji banza. Ina miki magana kina wani shareni wai ke matar aure” murmushi kawai Maimoon ta yi ta ce“to ke me ce ce?” tuntsirewa da dariya Nana ta yi ta ce“matar gida mana. Wai abun mamaki duk kun yi aure” ta sake tuntsirewa da dariya. Kallonta kawai Maimoon ke yi ba tare da ta kanta ta ba. Nana ta ce“wai Zahra ce ta zo apartment ɗin mu yanzu wai na yafe mata” gyara zama Maimoon ta yi ta ce“sai ki ka ce mata me?” ɗan juya Idanunta ta yi kafin ta ce“na ce mata ai na yafe mata” wani mugun kallo Maimoon ta watsa mata ta ce“amma ke banza ce wlh” murmushi kawai Nana ta yi ta ce“to me zance mata? Ai idan ta yimin da kyau ta sani, idan kuma ta cutar da shima ta sani.”

Tashi tsaye Maimoon ta yi tana kallonta cike da masifa ta ce“Ada kenan da baki da damar ramawa, yanzu kuwa kina da damar da zaki rama ki nuna mata ke ba yarinyar da zata rainawa hankali ba ce.”

Kallonta kawai Nana ta dinga yi, Maimoon ta ci gaba da faɗin“koda wasa kada ki bari ta huta, ki nuna mata cewa ke ki ke da gida kuma ke ce yar uwarsa” Ita dai Nana kallonta kawai take dan ba fahimtar abin da take cewa ta yi ba. Ta taɓe baki ta ce“to wai akan wa zan rama?”

“Akan uncle Abdusammad mana!”

Shiru Nana ta yi sai kuma ta ce“to a matsayina nawa?”

Harararta Maimoon ta yi ta ce“a matsayinki na matarsa mana! Kuma kishiyarta.”

Nanameera
08106608363.*🌹 NAANAH 🌹*

Arewabooks@Nanameera08
Wattpad@Nanameera08.

Page 41.

Wani kallon sheƙeke Nana ta yi mata sai kuma ta ce“ke me ki ka ce?” sai a sannan Maimoon ta tuna abin da ta faɗa. Lokaci ɗaya ta sanya tafin hannunta na dama ta rufe bakinta a fili ta ce

“Ya ilahi”

Leƙa fuskarta Nana ta yi. Ta ɗago tana kallonta, da hannu ta yi mata alama da mene ne, ta girgiza kanta tana murmushi ta ce“ke babu komai. Zauna ki ji” taɓe baki Nana ta yi sai kuma ta koma ta zauna tana kallonta, Maimoon ta furzar da iska daga bakinta sannan ta zauna ita ma tana kallonta ta ce“kin je wajen Hamida kuwa?” girgiza mata kai ta yi ta ce“to kawai sai na dinga yi muku yawo a gida mazajenku na nan” tsaki Maimoon ta yi tana kai mata duka ta ce“kin ji banza. Dallah can ki je bata da lafiya”

Ƙasa-ƙasa Nana ta yi da murya, ta ɗan matso kusa da ita sosai ta kara hannunta a gefen kunnen Maimoon ta ce“ko dai itama irin abin da ya same ki ne ya sameta?” ta ɗago tana kallon fuskar Maimoon ɗin to see her reaction. Haɗe rai Maimoon ta yi ta turata tana cewa“ke daɗina dake hauka wallahi. Bata da lafiya ne kawai” kamar jira Nana take ta fara sheƙa dariya kamar zararriya, Maimoon ta dinga kallonta cike da takaici, ji ta yi kamar ta shaƙeta saboda haushi, dan gaba ɗaya cikin ya mayar da ita masifaffiyar ƙarfi da yaji. Sai da Nana ta yi mai isarta sannan ta tashi ta gyara zamanta tana kallon yanda Maimoon ɗin ta haɗe rai. Ta tsuke bakinta kamar gaske ta ce“Tam na daina muku dariya. Allah ya sauke ku lafiya, in sha Allah mace zaki haifa a saka mata sunana”

Banza ta yi mata, ta yi murmushi sai kuma ta dafata ta ce“to bana baki haƙuri ba?” madadin ta bata amsa sai kawai taga ta fashe da kuka. Nan da nan hankalin Nana ya tashi, ta dinga taɓa ta cike da damuwa ta ce

“mene ne? Ko baki da lafiya? Ina ne ke miki ciwo? Ko na kira miki Ummi?”

Shiru Maimoon ta yi mata, sai kukanta take.. Nana ta sake matsawa kusa da ita ta riƙe hannunta cikin nata a sanyaye ta ce“to bana ce ba zan ƙara ba? Wallahi ba zan sake miki dariya ba.”

Janye hannunta ta yi daga nata, ta shiga goge hawayenta cikin shessheƙar kuka ta ce“to nima ance miki son cikin nake? Gaba ɗaya tsoro nake ji. Wallahi bana so na haihu yanzu, shikenan kowa ya yi ta kallona” ta ƙare maganar tana sake rushewa da wani sabon kukan. Girgiza kai Nana ta yi tana kallonta cike da tausayawa ta ce“Allah sarki to ki yi haƙuri. Idan Yaya Aliyu ya shigo sai ki faɗa masa ke bakya son cikin nan a zubar” ko saurareta Maimoon bata yi ba ta ci gaba da kukanta a hankali.

****
Da daddare bayan sallar isha'i tana zaune kan cinyar Amma tana danna wayarta a hankali. Ita kuma Amma tana kallon dramar da ake a tv, kamar wadda aka tsikara haka ta tashi zaune ta juya tana kallonta sosai ta ce

“Amma”

Kallonta Amma ta yi kafin ta ce“na'am mene ne?”

Kamar ba zata yi magana ba sai kuma ta ce“Allah Maimoon tausayi take bani, ɗazu fa da naje sai kuka take.”

Da ɗan mamaki Amma ta kalleta ta ce“ita Maimoon ɗin? To meya ke damunta?”

Langwaɓar da kai ta yi ta ce“akan wannan cikin ne fa. Gaba ɗaya ta zama abar tausayi, ni kuwa nace ta cewa Yaya Aliyu yasa a zubar da cikin ko dan Allah?” ta ƙare maganar tana kallon Amma dan ta ji me zata ce. Wata uwar harara ta maka mata kafin ta ce“saboda ke ce gwana uwar iya ko? Ina ruwanki?” tura baki ta yi ta sunkuyar da kanta daman ƙaikaiyin bakinta yasa ta fadawa Ammar. Amma taja tsaki tana janyeta daga jikinta ta ce“ni tashi ki bani waje. Na sake jin irin wannan maganar a bakinki” tashi tayi ta ɗauki wayarta ta bar parlon jiki a saluɓe. Tana shiga daƙinta ta mayar da ƙofa ta rufe ta sake zumɓura baki a fili ta ce

“To daga na faɗa mata gaskiya?. Taɓ”

Ta ƙare maganar tana zame hular kanta, kyakkyawan gashinta wanda ya sha gyara ya sakko har gadon bayanta dan ba'a kitse yake ba. Ta ƙarasa wajen gado ta zauna tana sauke ajiyar zuciya.

****
Bakinsa ɗauke da sallama ya murɗa handle ɗin ƙofar parlon, Turus yayi ganinsu zaune dan bai yi tunanin kiran na meeting bane. Ganin yaja ya tsaya yasa Atta ta ce

“To kai kuma tun da ba soja bane ai ka ƙaraso ciki ko?”

Kallonta kawai ya yi sai kuma ya saki ƙofar ya ƙaraso ciki. Kujerar da Abba ke kai ya ƙarasa ya zauna sannan ya gaida Hajiya Babba da kuma Mama dan su ne yau bai gani ba. Bayan sun amsa Papa y yi gyaran murya kafin ya ce

“Ba wani abu ya saka muka taru anan ba sai don maganar zumuncinmu...”

Bayan sun gama tattaunawa Abdusammad ya tashi zai wuce dan Allah Allah yake ya bar parlon, Sai dai cikin rashin sa'a Hajiya Babba ta kira sunansa. A dole ya koma ya zauna yana kallonta fuskarsa babu annuri, Kallonta duk suka yi dan basu san me zata ce ba, ta gyara zamanta tana kallon Papa ta ce

“Kabeeru ai ina ga ba'a gama ba”

Da ɗan mamaki ya ce“To muna ji Hajiya”

Ta numfasa sannan ta ce“ba wani abun bane daman maganar aurensa ne. Ina ga ya kamata ace Nana ta tare a ɗakin mijinta tunda dai komai ya riga da ya saisaita”

Atta ta cafke maganar kamar daman jira take ta ce

“Ashe bani kaɗai nake wannan tunanin ba.. wallahi kullum dashi nake kwana dashi nake tashi, to yarinya sai zama take da aure aka. Ita ba'a danganata da ɗakin aurenta ba. Gashi sa'annin auren duk kusan Allah ya bada rabo, to dan Allah itama ba ƙara ta tafi nata ɗakin ba, ko mun sake samun jikoki?.”

Murmushi suka yi, Ban da Abdusammad wanda ya sake haɗe rai kamar yaga mala'ikan mutuwa. Hajiya Babba ta ce“In sha Allah Atta nan bada jimawa ba zata tare”
Chapter 67 · 0% Book details