← Book details Naanah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 125

Sashe 20

Naanah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan sallar isha'i Amma ta buɗe ɗakin ta shigo, tana kwance akan gadonta ta rufa da lallausan duvet, ta ƙaraso gabanta ta ajiye tray ɗin kan drawer sannan ta dafata a sanyaye ta ce"Nanata" shiru ta yi mata duk da taji abin da ta ce, Amma ta sake cewa"tashi kin ji, tashi" juyawa ta yi ta mai da kanta ɗaya side ɗin, Amma ta ɗan yi murmushi sannan ta yaye duvet ɗin ta leƙa fuskarta ta ce"taso mana yar autar Ammarta" sake dunƙule jikinta ta yi hawaye na sintiri kan kyakkyawar fuskarta. Amma ta janyo hannunta tana faɗin "taso mana" dakyar ta tashi zaune har sannan idanunta a rufe suke fuskarta ta yi jajur jikinta duk alamun jini ya kwanta, Amma ta dinga kallonta tana jin wani irin ɗaci a ranta, koda wasa bata san ganin abin da zai taɓa lafiyar tilon ƴar tata, shiyasa bata taɓa gwada dukanta komai zata yi sai dai ta mata faɗa. Ganin yanda take numfashi da kyar ya sanya ta ce"sannu, zo ki sha tea" girgiza kanta ta yi ba tare da ta ce komai ba, ta koma ta kwanta. Tashi Amma ta yi ta fito daga parlon, Abba na zaune da Abdusammad suna magana ta ƙaraso wajen, gaisawa suka yi dashi kafin ta maida idanunta kan Abba ta ce"Daman cewa nayi ko zaka je kaga jikin yarinyar, naji zazzaɓi sosai a jikinta"

Da sauri Abba ya ce"subhanallahi" daga haka ya miƙe, tashi shima Abdusammad ɗin ya yi yana faɗin "lafiya dai Abba?"

"Nana ce bata jin daɗi" ya yi maganar da damuwa akan fuskarsa. Girgiza kai Abdusammad ya yi ya ce"subhanallahi tana ina?" Daƙinta Abba ya nuna ya yi gaba sannan ya bi bayansa, Amma ta dinga kallonsu kafin ta bi bayansu itama. Ƙarasawa jikin gadon ya yi ya durƙusa ya taɓa jikinta kafin ya ce"Kee Nana!" da kyar ta buɗe idanunta dan da gaske zazzaɓi ne sosai ya rufeta, ya riƙe hannunta ta tashi zaune da kyar. Kallon jikinta ya dinga yi dan vest ce a jikinta, ya daga idanunsa ya kalli Abba da mamaki ya ce"wane ya daketa Abba?"

Murya a sanyaye Abba ya ce"ni ne" Abdusammad ya dinga kallonsa kafin ya ce"but why? me yasa zaka daketa Abba? she's too young fa" girgiza kai Abba ya yi ya ce"raina ne ya ɓaci Abdusammad, na kasa danne fushina"

"Kome ta maka bai kamata ka daketa ba Abba, duka baya gyara, yanzu kaga ya taɓa lafiyarta"

Shiru shi dai Abba ya yi dan bashi da abin cewa tun da ya san ya yi laifin. Abdusammad ya kalleta a nutse ya ce"sannu, zaki iya tafiya?" kamar jira take ta shiga yarfe hannu tana girgiza kanta, ya durƙusa daidai tsayinta ya ce"oyaa hau muje" bata yi musu ba ta hau faffaɗan bayan nasa, ta zura hannayenta wuyansa ta rike shi sosai. Tashi ya yi yana riƙe da ita a bayansa ya ce"da safe na dawo da ita" okay Abba ya ce sannan ya fita daga ɗakin, Kamar jira Nana take ta sake narkewa a bayansa tana sauke numfashi a hankali.

****
Junaid ya sauke wayar yana yin tsaki, saurayin dake zaune gefensa ya ce"what?" rai ɓace ya ce"bata ɗaga ba, wallahi ji nake kamar naje na ɗauketa daga wancan kurkukun gidan nasu, yarinya bata isa ta sake ba!" Taɓe baki Al-ameen ya yi ya ce"kai ma wallahi kana bada maza, sai ka ce ita kaɗai ce yarinya mace, ga yan mata nan sai wanda ka zaɓa, kai da ka yi zaman Lebanon ma har a faɗa maka ganin mata zafafa" Harararsa Junaid ya yi ya ce"ita fa ba irin waɗancan matan ba ce, wannan so nake na aureta, amma danginta sun ƙi yarda, su a dole sai dai ta auri ɗan uwanta" wani murmushin mugunta Al-ameen ya yi ya ce"then baka san yanda zaka sameta ba?" kamar ƙaramin yaro Junaid ya gyaɗa masa kai, ya ɗan cije baki sai kuma ya ce"bani kunnenka ka ji" babu musu ya saki steering motar ya miƙa masa kunnen, Al-ameen ya raɗa masa magana sai kuma ya ɗago yana kallonsa fuskarsa ɗauke da murmushi.

08106608363
Nanameera.*🌹 NAANAH 🌹*

Page 13...

Junaid ya dinga kallonsa da mamaki, Al-ameen ya ƙifta masa idanu yana faɗin"ya ka ji shawarar tawa?" Girgiza kansa ya yi yana jingina da kujerar motar ya ce"gaskiya i can't" haɗe rai ya yi sannan ya ce"but why?" Junaid ya ɗauke kansa yana kallon tsirarin motocin da ke titin kafin ya ce"saboda ina sonta! aurenta nake son yi" tsaki Al-ameen ya yi yana faɗin"ai sai ka yi ta fama kuwa" shi dai Junaid bai ko kalleshi ba ballantana ya bashi amsa, zuciyarsa da ƙwaƙwalwarsa suna can tunanin dalilin daya hana Nana ɗaga kiransa.

****
Zahra na zaune gefenta ya dawo ɗakin hannunsa riƙe da injection, Nana na ganin haka ta sake matsawa jikinta a hankali. Tsayawa ya yi ya haɗa allurar kafin ya kalleta yana faɗin"tashi na miki" kasa cewa komai ta yi ta miƙe a hankali, skirt ɗin jikinta ya janye ƙasa sannan ya yi bismillah ya kafa allurar, runtse idanunta ta yi saboda azaba ta dinga yarfe hannu, ya janye empty sringy ɗin daga bayanta ya ajiye gefen dresser. Komawa ta yi ta zauna kusa da Zahra ta ɗora kanta akan cinyata, zazzaɓi ne sosai a jikinta dan haka Zahra ta ɗora hannunta akan bayanta tana taɓata a hankali. Juyawa ya yi ya fice daga ɗakin not too long kuma ya dawo hannunsa riƙe da wayarsa, kallonsu ya yi sannan ya ce"kin ci abinci?" gyaɗa masa kai ta yi a hankali duk da bata ci abincin ba, ya ɗan yi shiru can kuma ya ce"to ki gyara kwanciyarki sai da safe" ya ƙare maganar idanunsa ƙur akanta. Da taimakon Zahra ta gyara kwanciyar sannan ta rufa mata blanket, ta dinga sauke numfashi a hankali har bacci ya dauketa, ajiyar zuciya ya sauke sannan ya juya ya bar ɗakin, ita ma ta tashi ta kashe hasken ɗakin sannan ta fita. Koda ta shiga ɗakinsa bata same shi ba dan haka ta tabbatar da yana gurin Noor dan duk dare sai ya shiga ya ganta kafin ya kwanta. Gefen gado ta zauna tana danna wayarta a hankali, ba'a fi 5mins ba ya buɗe ɗakin ya shigo bakinsa ɗauke da sallama. Amsawa ta yi sannan ta ci gaba da danna wayarta, shi ma bai bi ta kanta ba ya nufi toilet dan watsa ruwa. Gajiya ta yi da jiransa ta tashi ta fita daga ɗakin ta koma nata, bayan 30mins ta kashe wayar hannunta ta tashi ta koma ɗakin. Zaune ta same shi gefen gado yana sipping coffee a hankali, ta ƙarasa ta zauna gefensa ta yi shiru, sai da ya gama ya ajiye mug ɗin sannan ta ce"wai me ya sameta ne? Naga jikinta duk a fashe" girgiza kansa ya yi sannan ya ce"Wallahi wai Abba ne ya daketa saboda ta yi faɗa" ɗan zaro idanu ta yi sai kuma ta ce"faɗa kuma, ita dawa?" kamar ba zai magana ba sai kuma ya ce"wai da Amrah suka yi ɗan rigima sai ta mareta, shi ne shi kuma ya zaneta" Zahra ta langwabar da kai ta ce"Ayyah daman Nana bata son zaman lafiya tun tana ƙarama, amma nayi mamaki ma ganin tun da mu ka zo ba'a ce ta yi faɗa da kowa ba" murmushin da bai yi niyya bane ya kuɓuce masa, ya janye kafafunsa kafin ya ce"to ai an samu lafiya ne, shi ne yanzu take neman dawowa da halin nata" Zahra ta murmusa ta ce"shima Abba da ya yi haƙuri kwana nawa ne zata yi aurenta ta bar wajensa" Abdussamad ya dinga kallonta ba tare da ya amsa maganar tata ba. Ganin bai ce komai ba ya sanya ta ce"yauwa daman inason na tambayeka"

"Uhm ina ji" ya ce yana ƙoƙarin kwanciya, sunkuyar da kanta ta yi tana wasa da fingers dinta ta ce"dan Allah gobe ina son naje gurinsu Umma idan babu damuwa" jinjina kansa ya yi ya ce"daman jira nake naji zaki ce zaki ko sai na tuna miki, Allah ya kaimu lafiya" dariya ta yi ta ce"zan ce mana, kawai dai bari nayi mu ɗan kwana biyu tukun" sake jinjina kansa ya yi yana lumshe idanu dan ba ƙaramin bacci yake ji ba, ganin haka yasa ita ma ta haura kan gadon ta yi kwanciyarta.

Washegari da sassafe ta tashi ta je ɗakin da Nana ta kwana, sai dai bata sameta a ciki ba, dan babu ma alamar an kwanta ko ina tsaf yake. Tana ƙoƙarin juyawa suka kusa karo ya ɗan yi baya yana kallonta, fitowa ta yi tana cewa"wai ka ga na duba ban ga Nana ba a ciki"

"Bata ciki kuma?" Abdussamad ya tambaya da ɗan mamaki, gyaɗa masa kai ta yi ya ce"ko ta tafi ne?"

"Kuma sai ta tafi bata faɗa mana ba?" Zahra ta yi maganar a ɗan dame, jan kumatunta ya yi ya ce"ai da ke da Nanar ban san wanda ya fi wani son rigima ba, to mene zai hanata tafiya tun da ta san hanya abin ta?" Tana ƙoƙarin maganar suka ji an turo ƙofar, kamar haɗin baki suka kalli wajen a tare, tsaye take ita da Noor suna kallonsu, Zahra ta sauke ajiyar zuciya ta ƙarasa wajen da sauri tana faɗin"Nana na ɗauka tafiya ki ka yi ai?" girgiza kanta ta yi a sanyaye ta ce"ina kwana Aunty?" Murmushi ta yi ta ce"lafiya kalau ya jikin?"

"Da sauki" ta ce tana yin gaba, wajensa ta ƙarasa ta ɗan durƙusa cike da ladabi ta ce"ina kwana uncle?"

"Ya jikin?" ya ce yana zama kan sofa, bin bayansa ta yi tana faɗin"da sauki ya daina min zazzaɓin, sai jikina ne kawai yake ciwo" jinjina kansa ya yi ya janyo hannunta ya zaunar da ita gefensa a nutse ya ce"Nana me ya haɗa ki faɗa da Amrah?" sunkuyar da kanta tayi ba ta ce komai ba, ya juya yana kallonta sosai ya ce"baki ji bane?" Cikin shesshekar kuka ta ce"babu komai uncle kawai zagina ta yi fa, kuma ta mareni shi ne na rama"
Chapter 20 · 0% Book details