Sashe 29
Naanah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
****
Abdusammad ya dinga kallon Abba can kuma ya ce“to daman tana fita ba'a sani ba?” Girgiza kai Abba ya yi ya ce“nima ban sani ba wallahi, koma mene ne ai laifin uwarta ne da har zata bari ta fita bata sani ba, yarinya kamar Nana a ce ta kai har yanzu a waje, to ina ma ta sani ballantana taje?” Abba ya ƙare maganar yana sauke wani zazzafan numfashi, ko ba'a faɗa ba kasan ransa ya gama ɓaci, ɗan dafa shi Abdusammad ya yi ya ce“calm down dan Allah kada wani abun ya sameka, bari naje wajen Hajiya Babba ko taje can” saurin riƙe hannunsa Abba ya yi ya ce“a'a kar ka sanar mata, ban son hankalinta ya tashi, shiyasa ban bari an sanar da ita ba” shiru Abdusammad ya yi can kuma ya ce“alright ka koma gida, zan dawo da ita in sha Allah” jinjina masa kai kawai Abba ya yi sannan ya saki hannunsa ya nufi balcony ɗin gidansa, sai da yaga ya shige ciki sannan ya sauke numfashi ya juya shima ya bar wajen..
****
Zaune ya same su a parlon suna faman hira, yana shigowa kowacce ta yi shiru murya can ƙasa suka ce“sannu da zuwa Uncle” bai amsa ba, sai kallo daya dinga bin su dashi wanda ya sanya suka sunkuyar da kawunansu, harɗe hannayensa ya yi a ƙirji yana tawowa toward them ya ce“ina Nana take?”
Da sauri suka kalleshi sai kuma suka sake sunkuyar da kai, ya jinjina kansa sannan ya sake cewa“okay, ba zaku faɗi inda take ba ko? Then zan yi maganinku duka yanzun” ɗago kansu suka yi, kowacce ta dinga girgiza kanta dan ba ƙaramin tsoronsa suke ba, Maimoon da tafi kowa firgita ta ce“wallahi tallahi uncle ban sani ba, ni ban ma ganta ba yau, ban san ma bata gida ba” ta ƙare maganar tana girgiza hannunta, kallonta ya dinga yi rai a haɗe, lokaci ɗaya kuma ya mayar da idanunsa kan Hameeda, girgiza kanta tayi cikin sanyin muryarta ta ce“uncle ban ganta ba wallahi, rabon da naga Nana an fi kwana uku ma, bata fitowa yanzu” taɓe baki ya yi sannan ya kalli Amrah wadda taƙi ɗago kanta, ganin yanda take rawar jiki ya sanya ya daka mata tsawa wadda ta firgita su duka ya ce“ina Nana take?”
“wallahi ban sani ba, ban sani ba Uncle, bama magana da ita dan haka bata zuwa inda nake, ban san inda take ba wallahi” ta ƙare maganar tana fashewa da kuka, Numfasawa ya yi dan ya tabbatar basu san inda take ban, ya juya ya fice daga parlon ba tare da ya sake ce musu komai ba, dafe ƙirji Maimoon ta yi a fili ta ce“wallahi Allah ya isana ba zan yafewa Nana ba data sanya aka ɗaga min hankali” girgiza kai Hameeda ta yi ta ce“mene haka? Ki ka sani ko wani uzurin ne ya fitar da ita?”
“Na rantse da a ce na san inda ta tafi sai na faɗa masa, to dan dai kawai ban sani bane” Amrah ta yi maganar cikin ɓacin rai, harararta Hameeda ta yi ta ce“saboda ba zaki iya rufawa yar uwarki asiri ba?”
“ai ita ba wadda za'a rufawa asiri ba ce, ke kina ganin da a ce kece ba zata faɗa ba?” Hameeda ta gyaɗa kanta ta ce“eh wallahi, ni nasan da ni ce Nana ba zata taɓa faɗa ba, ke koma ta san yawo na tafi ba zata faɗa ba, saboda bata da baƙin hali” daga haka ta tashi ta fice daga parlon. Da harara Amrah ta bita kafin ta ce“ai daman ni ce mai baƙin hali, naji ɗin to, wallahi sai na faɗa?” Ita dai Maimoon shiru ta yi tana tunane-tunane cikin ranta.
****
Ƙarfe 7:45pm ya yi parking a bakin estate ɗin, ganin bata ma san sun zo ba ya sanya ya juyo ya ɗan kalleta murya a sanyaye ya ce”Nana mun zo fa” janye mayafin data rufe fuskarta ta yi, ta ɗan kalleshi da kumburarrun Idanunta sai kuma ta buɗe motar ta sauka ba tare da ta ce komai ba ta nufi gate ɗin estate ɗin jiki a sanyaye. Ajiyar zuciya Junaid ya sauke sannan ya juya ya bar wajen lokacin da yaga ta shiga, koda ta shiga ciki bata samu kowa ba, dan daman i wannan lokacin ba'a fiye samun jama'a ba kasancewar akwai sanyi a garin, kowa yana cikin gidansu, ta dinga tafiya kamar wadda aka cirewa laka har ta ƙaraso bakin balcony ɗinsu, banda faɗuwa babu abin da gabanta ke yi, tunanin ɗaya abinda zata ce dasu Amma idan ta shiga ciki, dan haka ta ɗan tsaya tana sauke numfashi da sauri da sauri.
“Nana!”
Sai da taji sautin zuciyarta ya ɗan buga saboda tsoron da taji, ta juyo a hankali idanunta ya sauka akan Maimoon da ke tsaye sanye da hijabi, kallonta ta dinga yi sai kuma ta ce“ina ki ka je Nana?” kasa bata amsa ta yi sai kawai ta faɗa jikinta ta rungumeta tana kuka a hankali, tsoro da fargaba ne suka ziyarci Maimoon, ta ɗago fuskarta tana tattaba jikinta ta ce“kina lafiya dai?”
“Tsoro nake ji Moon, tsoro nake ji wallahi!”
Ta yi maganar cikin kuka, kallonta Maimoon ta dinga yi sai kuma taja hannunta suka fara tafiya, ita dai Nana sai bin ta take da kallo ba tare da ta san inda suka nufa ba. A bakin apartment ɗin Hajiya Babba ta tsaya ta kalleta murya can ƙasa ta ce“Hajiya ce kawai bata san bakya nan ba, dan haka ki shiga ki salallaɓa ki shige ko ɗakinta ne ki kwanta, ki cire wannan rigar ta jikin ki sannan kada ki nuna ba'a nan ki ka yini ba, ki ce baki da lafiya ne, ni kuma zan je na karbo abinci a wajen Ummi idan na shigo zan zo na taso ki kin ji” gyaɗa kanta kawai ta dinga yi still crying ta ce“to idan kuma Hajiyar tana ɗakin fa?” sai da ta kalli compound ɗin ta tabbatar babu kowa sannan ta ce“tana parlon, yanzu zan shiga na sanya ta shiga kitchen sai ki shigo kin ji” to kawai ta ce sannan Maimoon ta nufi ƙofar parlon ta murɗa handle ɗin a hankali, Hajiya Babba na zaune kan sofa tana cin abinci a hankali, Maimoon ta ƙarasa tana murmushi ta ce“hajiya Babbarmu” kallonta kawai ta yi sai kuma ta girgiza kanta ta ce“kin zo ki hana ni cin abinci ko?” kitchen Maimoon ta nufa tana faɗin“ni na isa na hanaki cin abinci, kawai nama zan ɗauka” zumbur Hajiya ta tashi tsaye tana kallonta ta ce“kar ki taɓa min abu a kitchen kin ji ko” ko saurarenta Maimoon bata yi ba ta shige kitchen ɗin tana dariya, ganin haka ya sanya itama Hajiyan ta bita da ɗan saurinta tana faɗin “yau naga tsiya da wasali!” Nana data kasa kunne tana saurarensu ta tura ƙofar a hankali ta shiga, ganin babu kowa a parlon ya sanya ta cire takalman ƙafarta ta kwasa da gudu ta yi sama. Hajiya Babba ta kwace robar dambun naman tana faɗin “fita ki bani waje” kwaɓe fuska Maimoon ta yi ta ce“kai Hajiya duk kin fi son Nanar nan haba!” daga haka ta fito daga kitchen ɗin tana leƙan parlon, ko tsayawa ba ta yi ba ta nufi hanyar fita daga parlon ta fice abin ta, ta dinga kallon balcony ɗin ganin babu Nana ya sanya ta sauke ajiyar zuciya sannan ta nufi hanyar gidansu da sauri.
Tana hawa saman ta shige ɗaya daga cikin bedrooms ɗin saman wanda ta tabbatar ba anan take kwana ba, ta ajiye wayar gefen madubi sannan ta nufi toilet da sauri, wanke fuskarta ta fara yi sannan ta ɗauro alwala ta fito, ta sake naɗa mayafin akan ta sannan ta fara gabatar da sallolin da ake bin ta. Bayan ta idar da sallar ta tashi ta fice daga ɗakin a hankali ta shiga ɗakin Hajiya Babba ta buɗe press ɗinta, kasancewar tana ajiye kayanta a ɗakin ya sanya ta ɗauko wasu riga da wando na bacci ta mayar ta rufe sannan ta fice da sauri. Ɗakin ta koma ta cire Abayar jikinta ta shiga toilet ta watsa ruwa sannan ta fito ta sanya kayan, ta naɗe Abayar da mayafin ta tura ƙasan gadon sannan ta hau kan gadon ta kwanta har da jan duvet ta rufa..
Bata ƙarasa gida ba ta haɗu da Juwaira hannunta riƙe da warmer, kallonta ta yi sai kuma ta ce“Hajiya zaki kai wa?” gyaɗa mata kai ta yi, ta yi saurin karɓa tana faɗin “bari na kai mata” murmushi Juwaira ta yi dan daman ba son zuwa take ba ta ce“yauwa Yaya, nagode miki daman kallo nake” daga haka ta juya ta nufi hanyar gida, taɓe baki Maimoon ta yi sannan ita ma ta juyo ta nufo gidan Hajiya Babba. Koda ta dawo zaune ta sameta tana cin abincin har sannan ta ajiye warmer sannan ta ce“ba zaki jira a dinga kawo miki abinci ba sai ki dinga ci ko?” murmushi ta yi ta ce“to ai duk ina ci idan aka kawo min ɗin, yanzu wannan gobe da safe shi zanci”
“ɗumamen abinci zaki ci?” jinjina kai Hajiya ta yi ta ce“eh” Maimoon tana faɗin “tab ni ba zan iya ba” ganin ta nufi sama ya sanya ta ce“ina kuma zaki je?” zata bata amsa kenan sai ga Abba ya shigo shi da Abdusammad, Maimoon ta kallesu jiki a sanyaye ta ce“Abba an ganta?” girgiza mata kai ya yi yana ƙoƙarin zama kan sofa ya ce“a'a Maimunatu” kamar zata yi kuka ta ce“allah sarki, Allah yasa ba ɓata tayi ba” kallonsu Hajiya ta dinga yi sai kuma ta ce“wane ba'a gani ba?” furzar da numfashi ya yi daga bakinsa kafin ya ce“Nana ce!” da sauri ta miƙe tsaye tana kallonsa ta ce“Nana kuma? Yaushe? Kuma a ina?” Hajiya Babba ta jera masa tambayar da tashin hankali sosai akan fuskarta. Abdusammad ne ya ce“Ki zauna Hajiya sai a miki bayani” jiki a sanyaye ta koma ta zauna ta zuba musu idanu tana kallonsu.
Tana hawa saman ta buɗe ɗakin ta shiga, kwance ta hangeta dan haka ta ƙarasa ta taɓa ta ta ce“ke Nana tashi” buɗe idanunta ta yi sai kuma ta tashi zaune tana kallonta ta ce“mene ne?”