Sashe 26
Naanah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
“Nana ce fa, yar ƙanin babansu doctor, zama ki ganeta wadda nake zuwa da ita gida fa da, kawai dai ta girma ne” taɓe baki ta yi sai kuma ta ce“shi ne har take shigar miki ɗaki kanta tsaye?” ɗan juya idanu Zahra ta yi sai kuma ta ce“kai Aunty Khadijah Nana fa, ai Nana yar ɗakina ce tun ina amarya” jinjina kai Aunty Khadijah ta yi ta ce“eh i see” Zahra bata sake cewa komai ba ta koma kitchen ɗin, tsaye ta same su suna aiki suna hira, ta ƙarasa bayan Safeena tana duba carrots ɗin da take yankawa ta ce“wato bama aikin ku ke ba hirar ku kawai ku ke abin ku” Siyama da ke tsaye gaban tukunyar da aka ɗora ta ce“kai Aunty aikin fa muke, kawai hirar ce ta zo” taɓe baki ta yi ta ce“ku dai ku ka sani” daga haka ta juya ta fice.
****
Bayan sun gama cin abincin suka kwashe kaf kayan da suka ɓata suka koma kitchen suna wankewa, Zahra ta dinga kallon Aunty Khadijah jin abin da take faɗa, murmushi kawai ta yi ta ce“anan family ɗin? Ai ko abin da kamar wuya” ɗan haɗe rai ta yi ta ce“wuya kamar yaya? Kina cikin dangi sannan ki ce ba zaki samar mata wanda zata aura ba” girgiza kai Zahra tayi ta ce“a'a nifa ba wai ba zan samar mata bane, idan Siyama ta auri ɗaya daga cikin ya'yan gidan nan zan fi kowa murna dan nasan ta samu miji wanda kowace mace ke fatan samu, amma fa kin sani su basu auren bare, i junansu suke aure” wani kallon sheƙeke Aunty Khadijah ta yi mata sai kuma ta ce“eh mana ai shiyasa naga ke an auro ki, tun da kema yar dangin ce” kallonta Zahra ta dinga yi baki buɗe, can kuma ta ce“nifa Aunty ba maganar tashin hankali ba ce wannan ko kuma cin mutunci, na auri Doctor ne saboda Allah ya ƙaddara ni matarsa ce, babu kuma wanda ya isa ya goge wannan abun”
“Eh to yanda kema ki ka aure shi saboda Allah ya ƙaddara, haka ita ma zata auri ɗaya daga cikinsu, nifa tun da daman na shirya a gidan nan nakeson Siyama ta samu miji, dan haka aiki ya rage naki, ko dai ki taimaka mata wajen samun abin da muke so ko kuma ni nayi da kaina, ai kin san ba zai gagara ba, wato kina cikin daula da arziki shi ne baki son wasu su zo su ci to wallahi baki isa ba, Sai Siyama ta auri ɗan dangin nan!”
Tashi Zahra ta yi ta bar wajen ba tare da ta sake cewa komai ba, Aunty Khadijah ta bita da harara tana fadin “sai dai ki yi, amma wallahi babu wanda ya isa ya hanata! Idan bata auri ɗan dangin nan ba sai dai idan bana raye” .
****
Dafata Maimoon ta yi ganin yanda take hawaye yasa jikinta ya yi sanyi, ta ɗan numfashi kafin ta ce“ki yi haƙuri Nana, tun da har ki ka ce kin rabu dashi to kawai ki daina ɗaga wayarsa, ki yi blocking lambarsa ta inda ba zai sake samunki ba, ballantana kuma ya faɗa miki abin da zai karya miki zuciya” Girgiza kanta ta yi wasu hawayen na sake zubowa fuskarta ta ce“na kasa jurewa ne Maimoon, na kasa mantawa dashi, idan ya kirani ta zuciyata zafi take min, I feel like na koma na ci gaba da kula shi, amma da zarar na tuna da Abba sai naji na ƙara sarewa, shin ya zan yi ne ni? Me ya sa nake cikin ruɗani? Me ya kamata na kare? Soyyayata ko kuma iyayena?”
“iyayenki!”
Maimoon ta yi maganar muryarta a dake cike da kwarin gwuiwa, jin jina kai Nana ta yi ta sanya hannunta tana share hawayenta wasu na sake zubowa ta ce“alright, zan manta da sir Junaid, zan ci gaba da bawa zuciyata haƙuri har ta saba da rashin sa, amma wallahi wata tana zuciyata zata iya bugawa na mutu, zan iya mutuwa Maimoon” rungumeta Maimoon ta yi suka dinga rera kukan tare kamar waɗanda aka yiwa mutuwa.
****
Ƙarfe 5:34 na yamma suka fito daga gidan, sai da ta rako su har wajen motarsu sannan ta ce“to Aunty ku gaida gida, a gaida min da Umma da Abba” okay Aunty Khadijah ce, ta juya zata shiga motar sai kuma ta ce“au na manta, da kin kaimu wajen uwar mijin naki ai mun gaisa” to kawai Zahra ta ce duk da ba haka taso ba, ta ce“muje” daga nan suka nufi hanyar apartment ɗin Hajiya Babba. Bakinta ɗauke da sallama ta shiga sannan suka biyo bayanta, Hajiya Babba na zaune kan kujera hannunta riƙe da azkar tana dubawa, ta amsa sallamar tana ɗago kanta, har ƙasa Zahra ta durƙusa sannan ta ce“Hajiya ina yini?” fuskarta a sake ta ce“lafiya kalau Fatima” tashi ta yi tana kallon su ta ce“to ku gaisa” cikin girmamawa Aunty Khadijah ta gaisheta haka ma su Safeena da Siyama, Zahra ta ce“Yayata ce Hajiya shi ne na ce bari na kawota ku gaisa” jin jina kai Hajiya Babba ta yi ta ce“Oh Masha Allahu, y yaran?” ta yi maganar tana kallon Aunty Khadijah,
“Suna nan kalau Alhamdulillah” ta ce da murmushi a fuskarta, masha Allah kawai Hajiya ta ce sannan kowa ya yi shiru, Siyama ta dinga kallon parlon kamar idanunta zasu fito, After 2mins Zahra ta ce“to Hajiya zamu tafi” Allah ya tsare ta musu sannan ta sanya aka ɗauko musu turamen atampa vilisco Holland wadda kimaninta ya kai 240k, suka dinga godiya kafin suka bar gidan. Apartment ɗin su Zahra suka koma ta sake musu sallama sannan suka shiga mota ita kuma ta juya ta koma ciki.
Basu yi nisa a cikin estate ɗin ba, Siyama ta dinga kallonsa sai kuma ta taɓo Aunty Khadijah tana fadin
“Mom! Mom! Kin ga wannan” ta ƙare maganar tana nuna shi da hannunta, ɗan tsayawa ta yi da tuƙin ta dinga kallonsa ita ma, fitowarsa kenan daga motar ya dauko briefcase ɗinsa sannan ya nufi hanyar apartment ɗin Hajiya Babba, sai da ya shige ta gaban motar su sannan ta kalleta ta ce“ya yi miki ne?” gyaɗa kanta ta dinga yi tana murmushi ta ce“sosai ma Mom, kalleshi fa, ga kyau ga kuɗi kuma saurayi” Ɗan murmushi Aunty Khadijah ta yi ta ce“shikenan” Safeena dake baya ta ɗan yi murmushi sannan ta ce“Hajiya Aunty Khadijah to ya za'a yi ta auri wannan?” ta madubi ta kalleta ta ce“ki jira ki gani” Safeena ta yi murmushi ta ce“to shikenan” daga haka ta ja motar suka ci gaba da tafiya.
****
Bayan magrib Aunty Ramlah ta fito hannunta riƙe dana ... tana kallon Amma ta ce“to shikenan yanzu yaushe zata zo?” Amma ta miƙewa.. chocolate sannan ta ce“ko gobe ne, dan yanzu ma ban ganta bane da sai ku tafi tare”
“to goben sai ta zo, ina gida ai, idan ya so sai muje na rakata” okay Amma ta ce daidai lokacin da suka ƙaraso balcony suna hango Daddyn... da ya yi parking motarsa yana kallonsu ta ce“to ku gaida gida” zasu ji ta ce sannan ta juya ita kuma Amma ta koma gida. Bata fi 3mins da zama ba Nana ta shigo hannunta riƙe da bowl, Amma ta kalleta sai kuma ta ce“sai yanzu?” zama ta yi gefenta ta ajiye bowl ɗin farfesun kayan cikin ta ce“eh ina gidan su Maimoon ma fa”
“Zahran bata nan?”
Girgiza kai Nana ta yi ta ɗauki hanta ta kai bakinta sannan ta ce“tana nan, baƙi naga ta yi, wata mata kamar yar tiktok” Amma ta ɗan kalleta sai kuma ta ce“ita Zahran?” Nana ta gyaɗa kanta tana ci gaba da cin namanta, shiru Amma ta yi bata sake cewa komai ba, ta ci gaba da danna wayarta.
Da daddare tana kwance around 10:20pm wayarta ta fara ƙara, ta tashi zaune ta janyota ganin numbern Junaid ya sanya ta yi tsaki sannan ta mayar ta ajiye ta koma ta yi kwanciyarta, kiran ne ya sake shigowa ta yi banza har ya katse sannan ta lumshe idanunta, ba'a fi seconds biyu ba taji ƙarar message dan haka ta ɗauki wayar, buɗe message ɗin ta yi taga an rubuta
“Ki ɗaga wayar akwai abin da za'a faɗa miki”
Nana ta dinga kallon message ɗin fuskarta ɗauke da mamaki, abun mene ne zai faɗa mata? Kuma za'a faɗa mata? To wane kenan?. Bata gama wannan tunanin ba wani sabon kiran ya sake shigowa, ta ɗan sauke numfashi kafin ta ɗaga ta kai kunne, daga can ɓangaren aka ce
“Salamu alaikum”
Sai da gabanta ya faɗi jin ba muryar Junaid ba, murya a sanyaye ta ce
“wa'alaika assalam, sir?”
Ta yi maganar da sigar tambaya, girgiza kansa ya yi yana rike da hannun Junaid da ke kwance ya ce“bashi bane”
Da mamaki sosai ta ce“bashi bane? To wane ne? Ina yake?” ta jera masa tambayoyin hankali a ɗan tashe, ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce“ɗan uwansa ne, daman kira nayi na faɗa miki bashi da lafiya, yana kwance a asibiti, sai kiran sunanki yake shiyasa ma na ce bari na kira ki”
Dafe ƙirji Nana ta yi ta sauko daga kan gadon ba tare da ta sani ba, muryarta a raunace ta ce“innalil lahi wa ina ilayhi raji'un, me ya same shi?”
“har yanzu likita bai sanar damu ainihin abin da ya same shi ba, amma dai sun ce yana da bukatar kulawa” tuni hawaye suka fara zubowa kan fuskarta kamar an buɗe famfo, ta girgiza kanta cikin shessheƙar kuka ta ce“Allah sarki, Allah ya bashi lafiya, zan zo na duba shi da safe idan Allah ya kaimu” jinjina kai ya yi ya ce“to Allah ya kaimu” Amin ta ce sannan ya kashe wayar, ta silale ƙasan rug ta fashe da kuka, kenan bashi da lafiya saboda ya rasata? Me zai same shi?.
08106608363
Nanameera.*🌹 NAANAH 🌹*
Masu tambaya daga farko su yi following channel akwai acan dan Allah🙏
Page 17...