Sashe 15
Naanah Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Cikin shassheƙar kuka ta ce"a'a Yaya, ni ban taɓa jin sonka ba, amma naji babu daɗi da aka ce min Amrah zaka aura, ban sani ba ko hakan na nufin na soka, ko kuma kawai ina maka kallon yaya ne all the time, Yanzu ma da nake kuka ba wai ina yi bane saboda na rasa ka, a'a ina kuka ne saboda irin kaddara ɗaya ce take bibiyarmu, kamar yanda zaka auri wadda baka ra'ayinta haka nima zan auri wanda bana so, wanda ko a mafarki ban taɓa tunanin zai zama miji a gareni ba. Sai dai gara kai namiji ne, kana da damar auren wadda ka ke so koda bayan wannan auren, amma ni wannan auren tamkar ƙarshen labarina ne, irin karshe mara kyau da ba'a fatan samu!"
Daga haka ta yi gaba da sauri kamar zata faɗi ta bar wajen, Sultan ya dinga bin ta da kallo har ta ɓacewa ganinsa, ya runtse idanunsa yana jin zuciyarsa na masa wani irin suya da raɗaɗi, taya zai bar ta? Ta ya zai fara rayuwar aure da Amrah bayan Nana tana raye?
"Innalil lahi wa ina ilayhi raji'un"
Ya furta yana mai neman taimakon Allah akan masifar da take tunkarosa.
****
Yana zaune kan ɗaya daga cikin luxury sofa ɗin da suka zagaye parlon ta fito daga kitchen, kai tsaye wajensa ta ƙaraso tana tafiya kamar babu laka a jikinta ta zauna gefensa. A hankali ta ɗora kanta bisa ƙirjinsa tana lumshe idanu saboda ƙamshin turaren daya gama cika ta, sanye yake da wata farar riga armless wadda ta fito da kowace sura ta jikinsa, ƙaton tatu ɗin da ke damtsensa na hagu ya bayyana, hoton zaki aka zana a jiki, sai kuma maciji ya faso kansa, abun gwanin ban sha'awa, Ajiye wayar da ke hannunsa ya yi jin yanda take sake narkewa a jikinsa yasa ya ce"lafiya dai?" Ya ƙare maganar yana jan kumatunta, sake lumshe idanu ta yi a karo na biyu cikin wata sassanyar murya mai kashe zuciyar wanda ake yiwa ta ce"Yallaɓai nawa, Abu Noor ɗina, mijina abin alfaharina, Allah ya kula min da kai, ya kare ka sharrin maƙiya, ya raba ka da Hajiya lafiya" bai san sanda ya saki wani yalwattacen murmushi ba, ya ɗago fuskarta da hannunsa yana kallonta ya ce"Amin ya rabbi Zahra" daga haka ya ɗora bakinsa kan nata ya mata light kiss dai dai nan Nana ta turo ƙofar ta shigo, da sauri ta saki handle ɗin tana sauke idanunta ƙasa. Zahra ta tashi tana gyara zamanta a ɗan dabarbarce ta ce"un..Nana... Nana ke ce?"
"Ku yi hakuri ban san kuna nan ba na shigo"
Cewar Nana ta juya zata bar parlon,
"Kee zo nan!"
Sai da taji hantar cikinta ta kaɗa saboda yanda taji ya yi kiran nata, ta juyo a hankali ba tare da ta yarda ta kalleshi ba. Gyara zamansa ya yi kan kujerar ya kafeta da idanu, a hankali ta ƙaraso wajen ta tsuguna gabansa muryarta na rawa ta ce"ga...gani uncle"
Matsowa ya yi ya riƙe kunnenta da ke cikin mayafi fuskarsa a haɗe ya ce"baki iya sallama ba?" Girgiza kanta ta yi tana ƙoƙarin fashewa da kuka ta ce"nayi sallama wallahi, baku ji ni bane" Tashi Zahra ta yi tana kallon su ta ce"bari na ɗauko wayata" daga haka ta nufi hanyar upstairs a nutse, da idanu ya bita sai kuma ya sauke idanunsa kan Nana dake faman shessheƙar kuka ya ce"oh baki daina halin naki ba kenan ko?" shiru ta yi bata bashi amsa ba, ya saki kunnenta ya koma ya gyara zamansa.
Wayarsa ya ɗauka ya ci gaba da dannawa yayinda take tsugune har sannan kanta a ƙasa, after 5mins ya ajiye wayar ya ɗago ya ɗan kalleta, hannunsa ya miƙa mata ba tare da ya ce komai ba, ɗago kanta ta yi ta kalli hannun sai kuma ta ɗora nata akai ta miƙe tsaye, gefensa ya zaunar da ita kana ya ce"kin yimin shiru ko kuwa?"
Kamar ƙaramar yarinya haka ta dinga sauke ajiyar zuciya tana rage kukan nata, sai da ya ga tayi shiru gaba ɗaya sannan ya girgiza kansa ya ce"u will never change ko Nana?" sunkuyar da kanta ta yi tana wasa da fingers ɗinta, taɓe baki ya yi ya ce"kurma ki ka zama?" da sauri ta ɗago kanta sai kuma a sanyaye ta ce"Uncle sannu da zuwa"
Kallonta kawai ya yi sai kuma ya ɗauke kansa, ta ɗan yi murmushi sannan ta sake cewa"uncle ina tsarabata?"
"Daga zuwana ɗazu? To ban zo da ita ba" tura baki ta yi ta ce"ai nasan ka siyo mana ko Uncle, ka siya min da Abaya?" ɗauke kansa yayi yana murmushi ya ce"kin bada kudin ne?" girgiza kanta ta yi a sanyaye ta ce"to ai ni ka san banida kuɗi" yanda tayi maganar da iya gaskiyarta ya sanya shi dariyar da bai shirya ba, ya ce"to nima ban dashi ai"
Langwaɓar da kanta ta yi tana murmushi ta ce"kaii kana da kuɗi dayawa ma kuwa"
"Nace miki?" Ya tambayeta muryarsa a sake, girgiza kanta ta yi tana murmushi ta ce"ai kowa ya sani, ko a goggle aka yi searching AM Shuwa za'a ganka"
"Ko?"
Ya sake faɗa a takaice, gyada masa kai ta yi dai dai nan Zahra ta dawo parlon hannunta riƙe da wayarta. Kallonsu ta yi tana murmushi ta ce"amma dai yau Nana a nan zaki kwana ko?" Da sauri ta girgiza kanta, Zahra ta ce"haba dai, ba zaki zauna wajen Uncle ɗin naki ku yi hira ba? Ko yanzu kin girma?" Murmushi kawai Nana ta yi bata ce komai ba, tashi ya yi ba tare da ya sake bi ta kansu ba ya haye sama, Zahra ta zauna in da ya tashi tana kallon Nana ta ce"wai Nana naga kin girma" kwaɓe fuska ta yi kamar zata yi kuka ta ce"kaii Aunty Zahra, ni ɗin!"
Jinjina kai Zahra ta yi cikin zolaya ta ce"eh mana, gashi za'a miki aure, ai wadda ta girma ita ake yiwa aure" shiru Nana ta yi bata ce komai ba, lokaci ɗaya yana yinta ya sauya, daga na farin ciki zuwa na damuwa. Zahra ta lura da hakan dan haka ta riƙe hannunta cike da damuwa ta ce"mene ne? Ko dai u're not happy about it?" kasa ɓoye damuwarta ta yi duk yanda ta yi ƙoƙarin yin hakan, ta faɗa jikin Zahra tana fashewa da wani irin kuka mai ban tausayi. Hannunta duka biyun ta sanya ta rungumeta tana jin yanda take kukan kamar ranta zai fita, shafa bayanta ta dinga yi da hannu ɗaya tana cewa "yi hakuri Nana, faɗa min mene ne?" Cikin kuka ta ce"aunty bana son sa, ni bana son auren, bana so a yimin aure yanzu, tsoro nake ji Aunty.."
Ta ƙare maganar tana sake ƙanƙameta, sosai Zahra ta ji tausayinta, ta yi shiru na wasu mintuna kafin ta yi karfin halin cewa"haba Nana mene ne abin da ki ke tsoro ɗin? Ɗan uwanki zaki aura fa, mu ma ba duk haka muka yi auren ba, sanda na auri Uncle naki ban fi 18yrs ba, yanzu kusan shekaru tara kenan, ai a haka zaki saba, da an yi auren zaki daina jin tsoron kin ji" girgiza kanta ta dinga yi tana kuka ta ce"a'a Aunty ni bana so, karatu nake so nayi, bana son auren nan, mutuwa zan yi idan aka yimin wallahi!"
"Keee!"
Suka ji muryar Abdusammad a kansu, da sauri ta saketa jikinta na rawa, Zahra ta dinga kallonsa ganin yanda ya haɗe rai kamar bai taɓa dariya ba, idanunsa ƙur akan Nana wadda ta sunkuyar da kanta sai kuka take a hankali, bai ce komai ba ya durƙusa gabanta yana kallonta ya ce"why?" ɗago kanta ta yi kawai ta shige jikinsa shima tana sake sakin wani sabon kukan, kasa cewa komai ya yi yana jin yanda hawayenta duk ya jiƙa masa riga. Ganin taƙi daina kukan ya sanya ya zauna ta sake shigewa jikinta tana ci gaba da kukanta.
08106608363
Nanameera.*🌹 NAANAH🌹*
Page 10...
Sai da ta yi shiru dan kanta ta fara sauke ajiyar zuciya sannan ya ɗago kansa ya kalleta, ta rufe fuskarta a jikinsa dan haka ya sanya hannunsa na dama a hankali ya ɗago kanta, fuskarta a jiƙe da hawaye haɗi da majina sai sauke numfashi take, ya ɗan girgiza kansa kafin ya goge mata da gefen hannunsa yana cewa"ba zaki girma ba ko? komai kuka ki ke masa" tana jin sa amma bata buɗe ido ba ta ci gaba da shessheƙar kukanta a hankali. Tashi ya yi bayan ya janyeta daga jikinsa ya kalli Zahra dake zaune tun ɗazu tana kallonsu ya ce"zan je wajen Aliyu" to kawai ta ce a sanyaye. Ya mai da idanunsa kan Nana dake zaune a kujerar ya ce"taso mu tafi" bata yi masa musu ba ta tashi ta riƙe hannunta cikin nasa sannan suka bar parlon.