← Book details Naanah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 125

Sashe 32

Naanah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Can ɓangaren Aunty Khadijah ta kalli ƙawar tata mai suna Kaddu ta ce“kin ji baƙin halin ko? Kin dai ji abin da ta ce da kunnenki, ai wallahi ba zata taɓa yarda ta haɗa su ba! Wannan mai baƙin halin”

Kaddu take zaune ta hakimce akan kujera ta ce“na ji kuwa, amma ki kwantar da hankalin ki, wallahi sai ya auri Siyama, haba sai ka ce ba yar mu ba ce”

Aunty Khadijah ta dinga kallonta can kuma ta ce“to ai kin ga yaron ne kamar akwai tsari a jikinsa, ki ga fa duk irin aikin wannan malamin amma ya kasa tasiri akan sa” tsaki Kaddu ta yi tana watsa hannu ta ce“dallah bar maganar wannan malamin, wake ta irin waɗannan? Ai wannan daman ba aikin malami ba ne, ni na san inda zamu je wallahi ko a gobe ki ke son ya auri Siyama sai ya aureta, me kuma aka yi aka yi shi?”

Gyara zama Aunty Khadijah ta yi tana murmushi ta ce“ke ƙawata taɓani da alkhairi, wai da gaske ki ke dan Allah? Ina ne?” wani shu'umin murmushi ta yi kafin ta ce“ke dai ki bari zamu je ki gani da idon ki” Aunty Khadijah ta sauke ajiyar zuciya sai kuma ta ce“har naji sanyi a raina wallahi, kai wannan abu” Kaddu ta yi murmushi sai kuma suka ci gaba da wata hirar.

****
Ranar Saturday misalin ƙarfe 4:20 na yamma ta fito daga ɗakin tana gyara zaman jakar hannunta a kafaɗarta, Amma da ke ajiye drinks a freezer ta ɗan kalleta sai kuma ta ce“kin shirya?” gyaɗa mata kai ta yi bakinta ɗauke da murmushi ta ce“eh Amma, yanzu zan tafi” sai da ta rufe freezern sannan ta mai da Idanunta kanta sosai tana kallonta, wata doguwar rigar material up white ce a jikinta mai zanen flowers manya-manya, ɗinkin boubou wadda bata kama jikinta ba, sai ta yi rolling jersey veil baƙi, babu kwalliya a fuskarta amma ta yi tas da ita sai sheƙi take. Amma ta ce“driver ne zai kai ki?” jinjina kanta ta yi kafin ta ce“eh ai Maimoon ma ta ce zata je, wai perfume ɗinta ya ƙare” Toh kawai Amma ta ce sai kuma ta nufi hanyar daƙinta, da idanu Nana ta bita har ta shiga sannan ta ɗauke kanta, bayan minti biyu ta fito hannunta riƙe da Atm card ta tana miƙa mata, amsa Nana ta yi sai kuma ta ce“yauwa Ammata”

“sauran ki tsaya siyan banza da hofi” murmushi ta yi ta ce“ba zan siya ba, kawai dai chocolate zan ɗauka” ta ƙare maganar tana langwaɓar da kai, taɓe baki Amma ta yi ta ce“shige kuma kar ku daɗe” to kawai ta ce sannan ta waje da sauri.

Tana sauka daga balcony ta hango Maimoon tana tawowa, sanye take da Abaya Egyptian ruwan ƙasa, ta yi rolling mayafin akanta, ta ƙaraso gabanta tana murmushi wanda ke ƙara mata kyau,

“ai na ɗauka sai na yi jiranki”

Ta yi maganar tana kallon Nana, harararta Nana ta yi ta ce“a'a abin da ya fi jirana zaki yi, ni muje” murmushi kawai Maimoon ta yi sannan suka riƙe hannun juna gwanin sha'awa suka nufi parking lot ɗin gidan. Sun yi nisa Maimoon ta ɗan kalleta cike da zolaya ta ce“wai ina sir Junaid kuwa?” taɓe baki Nana tayi ta ce“ni na daina kula shi, kina ganin saboda shi rannan uncle ya dakeni” tuntsirewa da dariya Maimoon ta yi dai dai sanda motar ta yi kwana ta ce“au wai daman wajensa ki ka je?” kamar ba zata yi magana ba sai kuma ta ce“ba fa wajensa naje ba, bashi da lafiya ne sai abokinsa ya kirani ya faɗa min shi ne naje duba shi” Maimoon ta gyaɗa kanta kafin ta ce“kuma shi ne ki ka kai dare?” ɗan siririn tsaki ta yi ta ce“ke baccine ya kwashe ni, daren ranar ne ban yi bacci ba, kuma da wuri na tashi na fita shi ne da naje bacci ya ɗaukeni” Maimoon ta dinga dariya sai kuma ta ce“eh lallai Ashababba a asibitin ki ka hau bacci?” gyaɗa mata kai Nana ta yi, ta ci gaba da dariyarta, haɗe rai ta yi ta ce“ni ki daina min dariya ke kuma” kallonta ta yi sai kuma ta rufe bakinta da hannunta saboda wata dariyar da ta tawo mata. Nana ta harareta ta ce“banza kawai” ta ƙare maganar tana kallon titi. Har suka ƙarasa supermarket ɗin babu wanda ya sake cewa komai, bayan driver ya yi parking suka fito suka nufi cikin mall ɗin. Banda turaruka da maya-mayai babu wani abu mai amfani da suka siya, sai tarkacen kayan zaki chocolate da biscuits, sai ƙarfe 6:00 sannan suka fito daga cikin mall ɗin, kai tsaye kuma in da drivern su yake suka nufa, suna cikin tafiya kamar daga sama suka ji ya kira sunanta, Cak Nana ta tsaya amma bata juyo ba, ya ƙaraso gabanta hannayensa zube cikin aljihu, kallonsu ya dinga yi duka kafin ya yi murmushi yana kallon maimoon ya ce“hii Moon” ɗan durƙusawa ta yi ta ce”afternoon sir” ya jinjina kansa sannan ya mai da kallonsa ga Nana wadda ta yi shiru ya ce“Nana me nayi miki da zafi haka ki ka daina ɗaga kirana? Uhm, meyasa? Ko na yi wani laifi ne” ya ƙare maganar yana murmushi. Wata uwar harara ta watsa masa sannan ta ce“saboda banida buƙatar kiran naka, bana son kana kirana, dan Allah kar ka sake ƙoƙarin neman yin magana dani, ka barni na yiwa iyayena biyayya” ta ƙare maganar tana haɗe hannayenta waje guda alamar roƙo, da wani irin mamaki Junaid ya dinga kallonta, duk zatonsa wasa take dan haka yayi murmushi ya ce“haba Nanata, duk cikin fushin nan? Rannan Abba ya bugeki ne? Ki yi hakuri kin ji” wani irin kallo ta dinga masa sai kuma ta yi tsaki ta kama hannun Maimoon dake tsaye kamar an dasata ta ce“muje dan Allah” daga haka suka yi gaba, da sauri shima ya sake biyo su ya sha gabansu yana kallonta ya ce “wait Nana me ki ke nufi ne? Ban gane inda ki ka dosa ba? Wane ya sauya miki ra'ayi?” sakin hannun Maimoon ta yi a fusace ta ce“baka gane me nake nufi ba? Hala baka ji abin da na ce ba, to bari na maimaita maka, ni Nana na rabu da kai rabuwa ta har abada, ba dan na daina sonka ba sai dan ba zan iya bijirewa iyayena saboda kai ba! Dan haka kaje na nemi wata nima zan zauna da wanda Allah ya zaɓa min, Allah ya baka wadda ta fini”

Tamkar zararre haka Junaid ya dinga kallonta, nan da nan kammaninsa ya sauya, idanunsa suka circiko da hawaye ya shiga girgiza kansa yana faɗin“a'a Nana, wallahi ba ke ba ce, ba zaki taɓa yanke wannan hukuncin ba, ni na san ba haka bane, ƙarya ki ke Nana! Ƙarya ki ke ki ce zaki iya rabuwa dani! Wallahi ba zai taɓa yiwuwa ba!” shiru ya yi yana kallonta ganin yanda ta haɗe rai, ya mai da idanunsa kan Maimoon muryarsa na rawa ya ce“yauwa Maimuna ki faɗa mata ta daina cewa haka dan Allah, ki faɗa min wane ya sauyata? Me ya sa zata min haka?” kallonsa ta dinga yi cike da tausayawa, Nana ta ja tsaki sai kuma ta yi gaba fuuu ta bar wajen, da idanu ya bita sai kuma ya kalli Maimoon kafin ya yi magana ta ce“ka yi hakuri dan Allah, ka bar ta haka, tun da har ta haƙura mu ma haka muke fata, dan Allah kada ka sake nemanta koda a waya ne, ka manta da Naana!” ta ƙare maganar a sanyaye sai kuma ta ratsa ta gefensa ta yi gaba itama. Junaid ya juya yana kallonsu har suka shige mota suka bar wajen, ya durƙushe a wajen yana rike saitin zuciyarsa saboda wani irin bugawa da ta yi.

Basu daɗe da hawa babban titi ba Maimoon ta ɗan kalleta ganin yanda take sharar hawaye tun ɗazu ta ce“amma Nana me ya sa ki ka yi haka? Da gaske kin haƙura dashi? Ko kuma haushi ya baki?” kallonta ta yi sai kuma ta ɗauke kanta cikin shassheƙar kuka ta ce“wallahi na haƙura dashi, na haƙura da sir Junaid, zan zauna da Yaya Safwan koda hakan na nufin mutuwata, ba zan bawa Abba da Amma kunya ba, ba zan bari su yi dana sanin haihuwata ba, ba zan bar su ba!” ta ƙare maganar tana sakin wani marayan kuka, matsawa kusa da ita Maimoon ta yi ta dafata kamar jira take ta faɗa jikinta tana ci gaba da kuka, shafa bayanta ta dinga yi a hankali tana sauke numfashi.

Driver na ƙarasa parking suka buɗe motar suka fito, Maimoon ce ta ɗebo kayan nasu duka tana kallon Nana da ke goge hawayenta ta ce“kar ki bari a gane kin yi kuka dan Allah” gyaɗa mata kai ta yi har sannan bata bar sauke ajiyar zuciya ba, suka jera suka fara tafiya babu wanda ya ce komai. Siyama ta dinga kallonsu har suka matso dab da ita, Nana ta ɗan kalleta sai kuma ta ɗauke idanu dan ta ganeta, murmushi ta sakar musu bayan ta tsaya wanda suma ya sanya dole suka tsaya ta ce“sannunku” Maimoon ce kawai ta amsa dan ita Nana ko kallonta bata yi ba, bata damu da rashin amsawar ta ta ba ta ce“yauwa daman na zo wajen Aunty Zahra ne to amma ban ganta ba, shi ne nake tambaya ko kun san inda take” girgiza kai Maimoon ta yi ta ce“ayyah wallahi bamu sani ba, mu ma kin ga dawowar mu kenan” jinjina kai Siyama ta yi, suna shirin tafiya ta sake cewa“au afuwan dan Allah D
Safwan fa?”
Chapter 32 · 0% Book details