Sashe 37
Naanah Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Mutuwar tsaye Nana ta yi a wajen, ta kasa koda ɗaga ƙafarta ballantana ta yi ƙwaƙwaran motsi, above 5mins kafin ta sulale ƙasa a hankali ta zauna kan tiles lokaci ɗaya ta fashewa da wani irin raunataccen kuka na zallar baƙin ciki da damuwa, gani take kamar a mafarki abin da ke faruwa, kenan bayan Junaid yanzu har da Zahra cikin masu son treating ɗinta? Me ya sa Zahra zata mata haka? Me ya sa mutanen data fi yarda dasu sune suke son cutar da zuciyarta, sai kawai ta sake rushewa da wani sabon kukan tana kifa kanta akan cinyoyinta. Can ƙasa kuwa Zahra ce ta kalli Aunty Khadijah sai kuma ta yi murmushi ta ce“ai kar ki wani damu wallahi kamar an yi auren nan ne, Nana ba zata taɓa bijirewa abin da nace mata ba, ni na sani” Aunty Khadijah ta jinjina kanta kafin ta ce“na yarda dake Zahra amma duk da haka akwai buƙatar mu sake kama yaron hannu biyu, saboda kin ga shi ne wanda zai je ya gabatar da Siyama a wajen iyayen nasa”
“Ai Aunty kawai ki bar komai a hannuna, ni zan kira Safwan nan muyi magana dashi, ba dai yana son Siyama ba?” Zahra ta ƙare maganar cikin sigar tambaya, gyaɗa maya kai Aunty Khadijah ta yi ta ce“eh mana, har gida fa yake zuwa, ko jiya suna tare har wajen isha'i baki ga abun arzikin daya kawo mata ba”
Zahra ta sauke numfashi sai kuma ta ce“to indai haka ne kar ki wani damu, Safwan ba zai taɓa bamu matsala ba, kin san me?” girgiza kai Aunty Khadijah ta yi, Zahra ta gyara zamanta sannan ta ce“Ba Safwan ne zai rabu da Nana ba, a'a ita da kanta ce zata ce bata sonsa, idan har ta ce haka to a sannan ne za'a saka ya fito da zaɓinsa, kin ga sai ya nuna Siyama” Murmushin jin daɗi Aunty Khadijah ta yi ta ce“gaskiya kuwa kin kawo shawara mai kyau Zahra, shiyasa nake son ki ƴar ƙanwata” murmushin kawai ita ma Zahra ta yi tana shirin magana suka ji ƙarar taku wanda ya sanya suka kalli wajen a tare, Nana ta ce take sakkowa daga benan a hankali tamkar wadda aka zarewa laka, fuskarta ta yi caɓa-caɓa da hawaye, bata kalli inda suke ba ta nufi hanyar fita daga parlon, Zahra ta taɓe baki sai kuma ta mai da Idanunta kan Aunty Khadijah ta ce“kin ga abin da na faɗa miki ko? Ba zata iya ja dani ba yanzu” gyaɗa kai kawai Aunty Khadijah ta yi, ƙasan zuciyarta tana jin wani irin farin ciki mara misaaltuwa, koda wasa bata yi tunanin Zahra zata amince nan kusa ba, ta yi zaton duk maganganun da malamin nan yake faɗa mata karya ne sai gashi yanzu ta tabbatar da hakan da kanta.
Nana na sakkowa daga balcony ɗin gidan suka ci karo dashi, ta ɗan ja baya a hankali idanunta a lumshe dan bata san ma ya tawo ba, kallonta Abdusammad ya dinga yi ganin yanda fuskarta ta yi jajur ga alamar hawaye a tattare da ita, ta sunkuyar da kanta muryarta na rawa ta ce“uncle ina yini?” shiru ya yi bai amsa mata ba, ya gyara tsaiwarsa kafin ya ce“mene ne?” girgiza kanta ta yi kuka na ƙoƙarin kwace mata ta ce“babb...babu komai!” taɓe baki ya yi sai kuma ya ce“baki ji me nace ba?” kasa jurewa ta yi kawai ta faɗa ta jikinsa ta ƙanƙameshi tana sakin wani marayan kuka, Kallonta ya dinga yi da mamaki kafin a hankali ya sanya hannayensa duk biyun ya riƙeta sosai ta dinga rera kukanta kamar daman jira take a tambayeta, shiru ya yi mata ba tare da ya yi yunkurin hanata ba, Above 5mins kafin ta fara rage sautin kukan nata, ta dinga shessheƙar kuka tana sauke ajiyar zuciya, Sai a sannan ya ɗan kalleta dan gabaɗaya ta yi wata yar ƙarama a gabansa, a iya ƙirjinsa kanta ya tsaya, ya sanya tattausan hannunsa ya ɗago fuskarta wadda ta gama lalacewa da hawaye da majina, hannunsa na hagu ya zura cikin aljihun trouser jikinsa ya zaro wani hanky coffee sai ƙamshi yake, da kansa ya goge mata hawayen sannan ya ce“now tell me mene ne?” janye jikinta ta yi daga nasa tana shessheƙar kuka ta ce“babu komai” Abdusammad ya haɗe ransa kamar ba shi ba ya ce“yaushe na fara wasa dake Nana?” girgiza kanta ta yi a sanyaye ta ce“babu komai wallahi kawai tsoro nake ji”
“tsoron me?”
Ya ce yana kafeta da idanunsa masu kaifi. Bakinta na ɗan rawa ta ce“ba..bana son auren nan uncle, tsoro nake ji sosai” dariya ce ta kusa kufce masa, amma ya maze ya sanya hannunsa ɗaya ya ja kumatunta sannan ya ce“silly girl, saboda za'a miki auren ki ke kuka? Ba kin girma uhm?” ya kare maganar yana murmushi, tura baki ta yi ta ce“ni ban girma ba uncle, I'm still a baby” jinjina kansa ya yi ya ce“yeh! U're still a baby tun da har yanzu baki daina kukan banza ba, anyway zan faɗawa Safwan ya dinga siya maki chocolate kin ji, so don't worry aure ba abin tsoro bane, daɗi fa zaki ji”
Waro idanunta ta yi dan har ta manta da ƙalubalen dake gabanta cike da yarinta ta ce“daɗi kuma uncle? Bayan ni zan dinga girki, sannan ba zan dinga fitowa kullum ba, ba zan dinga zuwa wajen Ammana kullum ba, sannan malamin mu ya ce sai an yi aure ake haihuwa, zan samu baby”
Murmushi sosai Abdusammad ya yi dan sai yau ya sake tabbatar da yarinyar ta, ya ɗauke kansa yana kallon compound ɗin gidan mai cike da shuke-shuke sannan ya ce“and u want a baby ba?” gyaɗa masa kai ta yi tana murmushi ta ce“ina son Baby, tun da Amma bata haifa mani ba, ni zan haifa ai ko?” ta ƙare maganar tana kallonsa, gyaɗa mata kai ya yi yana ƙoƙarin barin wajen ya ce“toh tun da kina son Baby that's means kina son aure” girgiza kanta ta yi tana tura baki gaba ta ce“ni bana son aure, baby kawai nake so” daga haka ta yi gaba ta bar wajen, da idanu kawai ya bita sai kuma ya yi dariya a fili ya ce
“ƙuruci dangin hauka”
Daga haka ya ci gaba da tafiya shima. Bakinsa ɗauke da sallama ya shiga parlon, Zahra ta yi saurin miƙewa daga zaune da take tana ƙirƙiro murmushi ta ce“welcome back doctor” jinjina kansa kawai yayi sannan ya nufi upstairs, Aunty Khadijah ta bi shi da kallo dan daman can ba shiri suke ba har ya haye sama. Sai a sannan Zahra ta kalleta ta ce“aunty why baki masa magana ba?” harararta ta yi ta ce“dani dashi wa ya kamata ya fara yiwa wani magana? Ni fa sirikarsa ce” Zama Zahra ta yi sannan ta ce“but he's older than you, beside ma kowa a gidan nan ganin girmansa yake, kuma kema ya kamata ace yanzu kin ga girmansa kodan Siyama, saboda wallahi idan har ya ce a yi auren nan babu wanda ya isa ya hana, haka idan har ya ce baya so wallahi babu wanda ya isa ya yi shi” Aunty Khadijah ta jinjina kanta sai kuma ta ce“haka ne?” gyaɗa mata kai Zahra ta yi, Ta tashi tsaye tana faɗin “to idan haka ne shi ya kamata mu mallake ba Safwan ba, dashi ya kamata mu yi amfani ba Nana ba” da sauri itama Zahra ta mike sai kuma ta girgiza kanta ta ce“a'a Aunty koda wasa kada ki ce zaki yi haka, wallahi ba zai mallaku ba, saboda ba'a zaune yake ba, sannan koma zai mallaku mijina ne fa, uban Yayana kin san irin yanda nakeson Doctor? Kin san irin yanda na damu dashi? Wallahi a'a ba zai yiwu ba” tsaki Aunty Khadijah ta yi kafin ta ce“to sannu me miji, ni dai abin da zai fisshemu shi zan yi” Zahra ta ce“eh you can do whatever you want, amma ban da taɓa min mijina!”
Kallonta kawai Aunty Khadijah ta yi ganin yanda ta haɗe rai kamar ba ita ba, ta dafata tana murmushi ta ce“to Shikenan” ajiyar zuciya Zahra ta sauke sannan ta kalli upstairs tana faɗin“bari naje gurinsa na dawo” tana ƙoƙarin barin wajen Aunty Khadijah ta ce“a'a nima tafiya zan yi mayi waya kawai” juyowa Zahra ta yi kamar zata yi kuka ta ce“aunty ba zaki jira na sakko ba?” girgiza kai ta yi ta ce“a'a akwai wanda muka yi alƙawarin haɗuwa dashi, Gara naje kawai” numfasawa Zahra ta yi ta ce“okay to ki gaida su Umma”
“Zasu ji” ta ce tana ɗaukan mayafinta, sai da ta fita daga parlon sannan Zahra ta nufi sama da sauri.
A hankali ta murɗa handle ɗin ƙofar tana leƙen ɗakin, zaune yake gefen gado idanunsa zube kan system yana dannawa, ya rage kayan jikinsa daga shi sai wando 3-quater da kuma armless, farar fatarsa ta bayyana sai sheƙi take. Zahra ta ja ta tsaya tana ƙare masa kallo, sometimes tana tambayar kanta anya akwai mutum irin mijinta? babban mutum wanda ya san kansa, mai tarin dukiya da ilimi, mai kyau da nasaba, daɗin daɗawa hali nagari. Sai kawai ta lumshe idanunta a fili ta ce
“Alhamdulilah!”