← Book details Naanah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 84 OF 125

Sashe 84

Naanah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Me yasa zai yi haka? Mene yake damun Safwan? Ni gaba ɗaya na kasa gane kansa.”

Bai bashi amsa ba, dan idan har ransa na ɓace baya iya magana. Dan haka Aliyu ya yi shiru yana kallon sa, Above 5mins kafin ya sauke wani zazzafan numfashi ya kalleshi ya ce“Kai ta apartment ɗin Abba. Ina zuwa” bai tsaya jiran amsar Aliyun ba ya yi gaba abin sa. Da idanu duk suka bi shi , Haule ta ce“Hamma me ya faru?” yanda ta yi maganar a sanyaye ya bawa Aliyu tausayi, Shikenan ya mayar da yarinya ƙaramar bazawara?. Ya sauke numfashi sai kuma ya ce“Ba komai muje." Jiki a sanyaye tabi bayansa suka nufi apartment ɗin su Nanar.

****
Zahra ce tsaye gaban gadonta tana ƙoƙarin yafa mayafi akan atampar dake jikinta wayarta ta fara ƙara, Ɗauka ta yi ganin lambar Anty Khadijah ta ɗaga ta kai kunne kafin ta yi magana Anty Khadijah ta ce

“Zahra kin yi amfani da maganin kuwa?”

Dafe kai Zahra ta yi dan har ta manta ta ce“wayyo Anty wallahi har na manta. Bari na ɗauka na sha yanzu zan tawo gida ma”

Anty Khadijah ta ce“Okay ki yi maza ki sha sai ki tawo.” Ohk Zahra ta ce sannan ta kashe wayar, A jaka ta sakata sannan ta ɗauki maganin dake kan dresser ɗinta ta nufi parlour, Ruwan zafi ta ɗan zuba a cup sannan ta kwance maganin ta zuba, ta saka cokali ƙarami ta juya sannan ta kafa kai ra shanye tas. Bayan ta gama ta ɗauki ruwa ta sha sannan ta fita ta koma saman.

****
Nana na zaune kan cinyar Amma tana danna wayarta aka yi knocking ƙofar, Amma dake haɗa turaren wuta ta ce“Nana je ki ga wane” To kawai ta ce sannan ta sauka daga jikinta ta ɗauki hularta data faɗi ta saka sannan ta nufi ƙofar. Koda ta buɗe tsayawa ta yi tana kallon su, Aliyu ya ce“Nana zata zauna anan zuwa an jima.” Kallon Haule ta yi sai kuma ta ce“Tam Yaya.” Aliyu ya juya ya bar wajen, ta matsa daga jikin ƙofar sannan ta ce“Zo ki shige.” Babu musu Haule ta shigo parlourn a sanyaye. Amma ta dinga kallon ta kafin ta yi magana Nana ta ce “Yaya Aliyu ne ya ce ta zauna a nan zuwa dare.” Amma ta ce“Tom shigo ki zauna mana.”

“Ina yini?”

Haule ta yi maganar bayan ta durƙusa, Da murmushi Amma ta amsa sannan ta ce“Ya gidan?”

“Alhamdulillah.”

Cewar Haule, Amma ta ce ta zauna kan kujera sannan ta zauna ta sunkuyar da kanta. Itama Nana komawa ta yi ta zauna kusa da Amma ta ci gaba da game ɗin da take yi, Bayan Amma ta gama abin da take ta miƙe ta nufi kitchen. Ta dawo hannunta riƙe da plate mai ɗauke da drinks, table ta ja gaban Haule sannan ta ajiye mata ta ce

“Maza ki sha bari na kawo miki abinci.”

“Na gode Amma.”

Ta ce a sanyaye. Murmushi kawai Amma ta yi sannan ta koma kitchen ɗin, Nana ta tashi tabi bayanta. Tsaye ta sameta tana ƙoƙarin zubawa Haule abinci, Ta jingina da jikin cabinet sannan ta ce

“Amma nima zan sake cin abincin.”

Yanda ta yi maganar a shagwaɓe ya sanya Amma ta kalleta, Ta haɗe rai ta ce“Wanda ki ka bar min fa? Ko ba cewa ki ka yi kin ƙoshi ba.?”

Tura baki Nana ta yi kafin ta ce“To ai yanzu ya sake bani sha'awa.”

“To ba zaki ci ba!”

Amma ta yi maganar tana harararta. Zumɓura baki ta yi ta ƙarasa wajen freezer ta buɗe ta ɗauki coke sannan ta fice daga kitchen ɗin, Amma ta bita da kallo sai kuma ta girgiza kanta tana tsaki.

****
Bayan sallar isha'i suna zaune a babban parlourn Hajiya Babba. Papa ya numfasa kafin ya ce“To mene dalilin daya sanya ya yi haka? Akan me zai saketa? Me ta yi masa.?” Shiru parlourn ya ɗauka, Can dai Sultan ya ce“Nifa daman Papa ba tun yau ba na fuskanci sauyi daga gare shi. Safwan ya sauya kamar bashi ba, rabon da na gan shi har na manta.”

“Sauyi? Wane sauyi ne da har zai iya sakin yarinya ba tare da ta masa wani laifi ba? Kuma saki mafi wulaƙanci har saki uku. Wannan shi ne sauyin?”

Abba ne ya yi maganar a zafafe. Papa ya ce“Ya isa haka Ahmad, dole a bi komai a sannu. Yanzu dai idan ya dawo daga asibitin sai aji dalilinsa na yin haka.”

“Babu buƙatar jin dalilinsa, Tun da har ya riga da ya yanke hukunci to magana dashi bata da amfani. Ku bar shi, ku manta dashi kawai dan Allah...”

Hajiya Babba ta yi maganar cikin wata irin murya mai nuna asalin damuwar da take ciki. Abdusammad ya girgiza kansa zai yi magana ta ɗaga masa hannu. Miƙewa tsaye ta yi tana kallon sa ta ce

“Kar ka damu ƙaddarata ce a haka. Mahaifin ku ya tafi ya bar ni daku, Ya huta bai san abin da ke faruwa ba. Duk abin da Safwan ya yi kai ne ka bashi dama, A matsayinka na babba ka iya watsa mana ƙasa a ido, Ka auri wadda ka san ba yar danginka bace. Baka damu da wane hali zan shiga ba, Baka damu da kallon da za'a dinga yi min ba, Sannan kuma ka koyawa ƙaninka rashin yin biyayya a gare mu”

Dakatawa ta yi saboda hawayen dake zubowa daga cikin idanunta, Ta sanya hannunta ta goge kafin ta ci gaba da faɗin

“Ba komai. Na haƙura, kuma mun haƙura gaba ɗaya, daman duk abin da muke yi, muna yi ne saboda ku, saboda gobenku data ƴaƴa yanku, Amma tun da hakan bai zama abin da zai saka ku ga ƙimar mu ba. Babu komai, A yi lafiya!.”

Hajiya Babba na gama faɗin hakan ta nufi sama da sauri. Shiru parlourn ya ɗauka, kowa da abin da yake tunani. Abba ya kalli Abdusammad wanda ya sunkuyar da kansa ƙasa ba tare da ya ce komai ba, Dafashi Abba ya yi, ya ɗago runannun idanunsa ya kalli Abba. Girgiza masa kai Abba ya yi dan haka ya mai da kansa ƙasa, Allah ne kaɗai yasan yanayin da yake ciki a sannan. Shi kaɗai ya san abin da yake ji a cikin zuciyarsa, Bai taɓa tunanin Hajiya Babba zata zubar da hawaye akan su ba, Sai gashi duk haƙuri irin nata ta buɗi baki ta faɗi irin wannan maganganun.

Atta ce ta miƙe tsaye tana kallon su duka ta ce“Ai shikenan, Gobe idan Allah ya kai mu zamu koma gida nida ita.”

“Amma Atta da kin bar ta anan, Ai kin ga...”

Daga masa hannu ta yi, Fuskarta babu walwala ta ce“kada ka ƙarasa Ahmadi, Gobe da Haule zan tafi naje na bawa iyayenta haƙuri.”

Shiru ya yi bai sake cewa komai ba, Ta bar parlourn itama. Tashi ya yi ya ƙarasa inda Abdusammad yake tsaye ya ce“taso muje.”

Miƙewa ya yi suka bar parlour. Suna zuwa compound ɗin gidan Abba ya saki hannunsa sannan ya ce“Na san zaka ji babu daɗi. Kamar yanda mu ma muka ji babu daɗi, amma ka sani abin da ta faɗa gaskiya Abdusammad. Da baka auro wata ba Safwan ba zai taɓa wannan tunanin ba, A rayuwa shi Babba har kullum madubi ne, kuma abin koyon na ƙasa dashi. Kai ne babba kuma kai ka fara fito da wannan abun. Yanzu ka ga irin matsalar da muke gudu ko?”

Girgiza kansa ya yi hawaye na biyo kan fuskarsa ya ce“Na gani Abba. Yanzu ya zan yi? Hankalina a tashe yake, Ya za'a yi a ce Hajiya na zubar min da hawaye, ban san hakan me yake nufi ba. Abba idan har bata so wallahi zan iya rabuwa da Zahra, Domin samun farin cikinta.”

Wani murmushi irin na manya Abba ya yi, Ya dafashi sannan ya ce“Akan me zaka saketa? Kana ganin sakinta zai zama abin da zai sauƙaka wannan matsalar? Idan ka saketa ita laifin me ta yi maka? Kana ganin baka cuceta ba?.”

Shiru Abdusammad ya yi, Abba ya ce“Kawai ka ci gaba da addu'a kana neman yafiyar ubangiji, Amma maganar saki sam bata taso ba, kuma ba zan taɓa bari ka yi hakan ba.”

Ƙarasowar Papa ya dakatar da maganar tasu, Ya tsaya yana kallon Abba ya ce“Ahmad yarinyar nan ta zauna a wajenka, Saboda ba zai taɓa yiwuwa Atta ta tafi da ita ba. Gara ta zauna a nan muga abin da hali zai yi.”

Jinjina kai Abba ya yi kafin ya ce“Nima abin da nayi tunani kenan. Idan Allah ya kaimu gobe zan yi magana da Safwan”

“Ku bari zan masa magana yanzu.”

Abdusammad ya yi maganar jiki a sanyaye. Girgiza kai Papa ya yi ya ce“a'a wani ɓacin ran zaka janyo, ka je gida kawai." Dan murmushin ƙarfin hali ya yi ya ce“Babu abin da zai faru Papa, idan Allah ya kai mu gobe ma zan bar ƙasar.”

“Da wuri haka?”

Papa ya yi maganar da mamaki dan bai san da batun tafiyar ba, Gyaɗa masa kai Abdusammad ya yi sannan ya ce“Eh. Abubuwane suka fara yin yawa acan ɗin, so i have to go.”

Jinjina kai Papa ya yi kafin ya ce“Haka ne. To Allah ya yi jagora, amma bada sassafe ba dai?”

“Da wuri maybe ma around 7:00am mun tafi.”

Papa ya ɗan yi shiru can kuma ya ce“To Allah ya kaimu goben da lafiya.” da Amin ya amsa sannan ya juya zai bar wajen, kamar kuma wanda ya tuna wani abu sai ya dawo, Abba ya ce“lafiya dai?”

“Nana bata koma gida bane, naga kuma dare ya fara yi bari sai na bika mu tawo tare.”

Jinjina kai Abba ya yi kafin ya ce“Eh dan kusan ka san halinta yanzu sai ta ce tsoro take ji.”

Koda suka je a ƙofar apartment ɗin ya tsaya, Abba da ya shiga ya kira masa ita. Yana tsaye a ƙasan balcony ta fito hannunta riƙe da mayafinta tana ƙoƙarin yafawa akan doguwar rigar jikinta. Bayan ta ƙaraso waje ta kalleshi ta ce“uncle ni sai an jima zan dawo fa.” bai ce komai ba ya ja hannunta suka fara tafiya, Ko nisa basu yi ba ta tirje a wajen ya juyo yana kallonta da shanyayyun idanunsa. Ganin yanda take yarfe hannu yasa ya ce
Chapter 84 · 0% Book details