Sashe 117
Naanah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
****
Washegari da wuri Nana ta tashi don ranar zasu tafi, Ƙarfe 7:00 na safe ya shigo ɗakin yana sanye da riga da wando masu nauyi saboda sanyin da ake, Kallon ta ya dinga yi ganin yanda ta yi shiru ta zuba uban tagumi, Gabanta yar ƙaramar trolley ɗinta ce wadda ta gama haɗa komai nata. Ƙarasawa ya yi ya zauna kan drawer yana kallon ta ya ce
“Nana mene ne? Ko jikin ne?”
Kallon sa ta yi idanunta cike tab da hawaye, Muryarta a sanyaye ta ce
“Uncle ni ka bar ni anan dan Allah.”
Shiru ya yi yana kallon ta, Can kuma ya miƙe ya ce“Ba zan bari ba, Ki fito waje ina jiran ki” Daga haka ya dauki trolley din ya fice daga ɗakin. Da idanu ta bi shi, Hawayen da ke cikin idanun ta ya fara zubowa kan farar fuskarta, Ita ko kaɗan bata so ta bi shi, Saboda ta san zaman kadaice zata yi, Babu kowa ba kamar da ba da akwai Noor wadda suke hira tare, koma tana makaranta akwai Zahra duk da ba magana suke ba. Tana nan zaune har bayan mintuna sha biyar wayarta ta fara ringing, Ta kalli screen ɗin wayar ganin sunan uncle din ya sanya bata daga ba, Kawai ta tashi ta zura hijabin da ke gefenta sannan ta ɗauki wayar ta fice daga ɗakin.
A compound din Hajiya Babba ta same su, Kamar yanda suka saba tsayawa anan a duk sanda zai yi tafiya, Jiki a sanyaye ta ƙarasa wajen tana zuwa ta shige jikin Hajiya Babba, Rungumeta ta yi ta shafa kanta ta ce
“Allah ya tsare hanya kin ji”
Dakyar ta ce Amin saboda kukan da ke neman tawo mata. Ta janye jikinta ta ƙarasa wajen Abba, Rungume shi ta yi tana sakin kuka, Duk da sun gama sallama tun asuba, Ya ɗan yi murmushi duk da yanda shi ma yake jin babu daɗi tafiyar da zata yi ya ce
“Ba zaki daina rigima ba ko Nana?, Allah ya tsare hanya.”
“Abba dama na zauna anan...”
Ta yi maganar cikin kuka, Murmushi kawai Abba ya yi ya ɗago fuskarta ya fara goge mata hawayen sannan ya ce
“Ai darajar ko mace ƴa mace gidan mijinta Nana, Dan haka ni zan fi alfahari da ke idan kina daƙin mijin ki. Ki zauna lafiya kin ji”
Gyaɗa masa kai kawai ta yi, Ya ja kumatunta yana murmushi, Wajen Papa ta ƙarasa ta sake masa sallama, Sannan ta faɗa jikin Amma tana kuka kamar ranta zai fita. Ajiyar zuciya kawai Amma ta dinga saukewa, Dan ko kaɗan ba son tafiyar take ba, Dan babu yanda zata yi ne. Amma da anan za'a bar ta har ta haihu, Tausayinta kawai take ji, Nanar da bata iya kula da kanta yanda ya kamata ita ce zata kula da wani, Ta girgiza kanta jin yanda take ci gaba da kuka ta ce
“Ke ya isa mana, so ki ke a yi miki dariya?”
Girgiza kanta ta yi ba tare da ta ɗago kan ba, Amma ta ce“Ki zama yarinyar kirki Nana dan Allah, Ban da saka magana, Ban da rashin ji, Ki kula da kan ki da kuma lafiyar ki, Ban da neman magana.”
A sanyaye ta amsa da to sannan ta saketa, Ta ƙarasa wajen su Maimoon suka sake sallama sannan ta koma wajen Atta. Girgiza kanta ta yi ta ce
“A'a ba sai kin zo min ba, Kar ki shafa min ciki, Je ki kawai Allah ya sauke ki lafiya”
Ba Nana ce taji kunyar ba, Abdussamad ne da ke tsaye, Yaji kamar ya daskare a wajen saboda kunya, Musamman saboda su Abba da Papa da ke tsaye. Atta ta kalle shi ta ce
“Kai kuma kaji tsoron Allah, Ka dinga barin yar mutane tana hutawa. Yauwa, Dan bana son mugunta”
Wata uwar harara ya zabga mata sai kuma ya dauke kansa yana kwafa, Atta ta taɓe baki kafin ta ce
“Ohho! Kai ka ga zaka iya, Ni dai sai na faɗi gaskiya ko za'a kashe ni.”
Bai tanka ta ba, Aliyu sai murmushi yake, Nana ta sake musu sallama sannan ta buɗe motar ta shiga, Sai da ya sake yi musu sallama shi ma sannan ya shige motar, Driven yaja motar suka bar compound ɗin.
****
Wajejen ƙarfe 10:00 na safe ya shigo ɗakin, Har sannan tana kwance, Ya tsaya gaban gadon yana kallon ta ya ce
“Khadijah ba zaki tashi haka ba? Mutan gidan na ta jiran ki ki fito”
Dakyar Anty Khadijah ta kalle shi, Tsabar baƙin ciki kasa cewa komai ta yi, Ta tashi zaune ta nufi banɗaki kawai. Kallon ta ya dinga yi har ta shige, Bata jima ba ta fito ta dawo ta zauna gefen gadon
“Ki samu ki fito ku gaisa da kowa”
Toh kawai ta ce sannan ta juya masa baya, Shi ma bai sake cewa komai ya fice daga ɗakin. Sai kusan ƙarfe 12:00 na rana sannan ta fito daga ɗakin, Ta shirya cikin wata atampa glitter sai sheƙi take, Ta nufi cikin gidan dan ta jiyo hayaniyar jama'a, Abin da ta gani ne ya sanyata makalewa jikin bango, Gaba ɗaya matan gidan suna tsaye cirko-cirko suna kallo, Haka ma ya'yan gidan da basu tafi Makaranta ba, Malam Garba ne riƙe da ƙatuwar dorina sai dukan wata mata yake, Ita kuma sai tsala ihu take tana birgima a cikin ƙasar wajen. Ta dinga kallon sauran matan biyu da ke tsaye kamar gumaka, Babu wanda ya yi tunanin zuwa ya hana shi abin da yake. Sai da ya gaji dan kansa sannan ya hankaɗata da ƙafa, Ya juyo yana kallon sauran yana haki ya ce
“Cikin ku wata ta sake irin abin da ta yi, Wallahi sai kin raina kan ki a gidan nan! Ni ba zaka kawon wannan iskancin na ɗauka ba!”
Ya ƙare maganar yana haki... Babu wadda ta iya motsi a cikin su, Sai muzurai suke, Ya kalli Anty Khadijah da ta yi sak a fusace ya ce
“Ke ma dallah shige mu je an fasa gaisawar!”
Kallon sa ta dinga yi, Can kuma ta juya ta bar tsakar gidan. Zaune ta same shi a ɗakin ta sai haki yake saukewa, Ta ƙarasa gefen gado ta zauna ta zuba uban tagumi.
“Na shiga uku ni Khadijah, wace irin rayuwa na jawowa kaina?”
Wani ɓangare na zuciyarta ya yi mata tambayar. Rufe idanun ta ta yi tana sauke wani irin numfashi, Babu wanda ya fado mata a rai sai tsohon mijinta mahaifin Siyama. Mutun mai kirki da sanin ya kamata, Mutum mai addini da son ƴan uwansa. Amma sai da ta raba shi da kowa, Ta mallake shi daga ita sai ƴar ta. Runtse idanunta ta yi tana tuno wasu shuɗaɗɗun abubuwa da suka shige, Tana sake jin ina ma ace mafarki take ba gaskiya bane.
****
It's been a while da komawar su New York, Kusan kullum tana kwance bata da lafiya, Koda ace lafiyar kalau ma to ba lallai bane ya gane dan ba zata fito ko parlour ta zauna ba. Ko kaɗan kuma basa wani shiri dashi saboda gaddamar ta, Kullum sai sun yi faɗa akan cin abinci, Ita ta ce ba zata ci ba saboda amai shi kuma ya rantse sai taci, Daga ƙarshe idan ta ci ta amayar sai bacci ya dauketa. Ranar wata Monday ta gama shirinta ta safe tsaf dan ranar ta tashi da sauki, Abdussamad ya shigo ɗakin da niyyar duba jikinta, Ya sameta tsaye tana shafa lip balm a bakinta. Ta ɗan rame kaɗan idanunta sun firfito saboda rashin cin abincin da take, Ya dinga kallon ta da mamaki kafin ya ƙaraso gaban mirror ɗin ya harɗe hannayensa a ƙirji yana kallon ta ya ce
“Madam ina zuwa?”
Kallon sa ta yi, Sai kuma ta tura baki ta ce
“Makaranta zan je, Ni na gaji da zaman gidan nan...”
Ta ƙare maganar kamar zata yi kuka, Sosai ta bashi dariya, Ya jinjina kansa ya ce
“Wato kin gaji da zaman gida ko? To zaki bini asibiti?”
Maƙale kafaɗa ta yi ta ce“Ni school zan tafi”
Matsowa kusa da ita ya yi, Ya riƙe hannayen ta duk biyun cikin nasa ya ce
“Ban son yawo fa Nana, ki yi zaman ki a gida mana”
Rau-Rau ta yi da idanu tana shirin kuka ta ce
“Dan Allah uncle ni zan je a haka. Ai na samu sauki fa”
Shiru ya yi yana kallon ta, Ta shige jikinsa a shagwabe ta ce
“Kaji uncle ɗinaa!”
Numfasawa ya yi sai kuma ya ɗago fuskarta ya ce
“But sai kin min alƙawari”
“Alƙawarin me?”
Ta ce da sauri.
“Idan kin dawo ba zaki wahalar dani ba zaki ci abinci!”
Kwabe fuska ta yi ta ce
“To ba cikin ne yake hanani cin abinci ba! Nima ina so naci fa, Kuma nagaji ma..”
Ta ƙare maganar tana turo baki gaba, Murmushi kawai ya yi sai kuma ya yi mata light kiss a baki ya ce
“Alright muje nayi dropping ɗin ki”
Cike da murna ta ce to sannan ta ɗauki jakarta suka fice daga ɗakin.
A compound din makarantar ya yi parking, Ta ɗauki jakarta da ledar chocolate din daya siya mata a hanya ta ce
“Uncle zaka zo ka ɗauke ni?”
Gyaɗa mata kai ya yi ya ce
“Karfe nawa zaku gama lecture din?”
“3pm”
Ta ce tana kallon sa, Shiru ya yi sai kuma ya ce“Okay idan zan zo I'll call you”
“Ai zaka zo ma..”
Ta ce a shagwaɓe, Murmushi kawai ya yi ya ce“To naji, A yi karatu dayawa” Toh kawai ta ce sannan ta buɗe motar ta sauka, Ta daga masa hannu sannan ta nufi department ɗin su.
Karfe 1:30 na rana suka je cafeteria, Ita da wasu kawayenta Mu'ash da Amani, Kasancewar ranar Surry bata zo ba. Suka yi order abinci aka kawo musu, Nana ko loma uku bata yi ta fara amai, Har abin da taci da safe sai da ta amayar dashi, Su suka taimaka mata ta gyara jikinta sannan suka bar wajen. A kasan wani garden suka zaune, Amani ta dinga kallon ta ganin yanda ta jingina da jikin kujera ta yi shiru, Gaba ɗaya ta zama kamar ba ita ba. Taɓe baki ta yi ta ce