← Book details Naanah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 125

Sashe 40

Naanah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Atta ta dinga kallon Nana da bayyanin mamaki kafin ta ce“iko sai mai sama! Yanzu wannan yar jaririyar ce ta girma haka, yarinyar wajen Ahmadu dai?” gyaɗa mata kai Abdusammad ya yi ta sake jinjina kanta sannan ta kalleta ta ce“ke zo nan” dakyar ta iya miƙewa tsaye dan zazzaɓi ne a jikinta ta ƙarasa gaban Atta sannan ta tsuguna. Taɓa ta ta yi tana ɗago fuskarta sosai ta ce“gata kuma kamarta ɗaya da babanta” murmushi kawai Abdusammad ya yi ya ce“eh suna kama da Abba” sakinta ta yi tana cewa“amma girmanta ya bani mamaki, rabon dana ganta tun sanda naje Jimeta kafin mutuwar Yaya” Abdusammad ya ce“ai kin daɗe rabon ki da Jimeta gaskiya” sake kallon Nana ta yi ta ce

“To ai kuwa ka samu mata, wannan zankaɗeɗiyar yarinyar ba'a bari ta auri wani ba, daga ganinta za'a yi mace! Dan haka na maka mata ta biyu!”

08106608363
Nanameera.*🌹 NAANAH 🌹*

Arewabooks@Nanameera08
Wattpad@Nanameera08.

Page 25...

Kallonta ya dinga yi, sai kuma ya ɗan haɗe ransa yana kallon Nana ya ce“ke tashi ki tafi” kafin ta yi magana Atta ta yi saurin faɗin “a'a ba zata tafi ba wallahi, ban gama ganin jikata ba” ɗauke kansa ya yi bai sake magana ba, Atta ta tashi ta shige kitchen ɗinta. Bata jima ba ta fito hannunta da wani madaidaicin bowl mai tsafta, ta miƙa masa tana cewa“gashi nan na dama maka” amsa bowl ɗin ya yi yana murmushi idanunsa zube kan tsaftacciyar damammiyar furar wadda aka zubawa zuma akai, Nana ta ɗan leƙa bowl ɗin tana murmushi, ganin bai ce komai ba yasa Atta ta ce“idan ka gama sai kaje sashen Baba ka kwana” toh kawai ya ce yana ɗaukan ludayin da ke ciki furar ya fara juyawa a hankali.

Atta ta ja hannun Noor ta ce“muje ciki yar nan” daga haka ta fice daga parlon gaba ɗaya, Bismillah ya yi sannan ya kai ludayin furar bakinsa, daɗi da garɗin nonon ya sanya shi lumshe idanu. Nana da ke kallonsa ta lashe baki kamar ita ce ke shan furar, ganin yana ta shan furarsa ba tare da ya kalleta ba ya sanya ta tashi ta zauna gefensa tana murmushi ta ce

“uncle”

Yanda ta yi maganar a ɗan shagwaɓe ya sanya ya ɗago kansa ya kalleta, washe masa baki ta yi ta ce“nima zan sha furar” sai da ya ajiye ludayin cikin furar sannan ya ce“mene?” yanda ya yi maganar babu alamun wasa a tattare dashi ya sanya ta ɗan kama kanta. Murya a shagwaɓe kuma ta ce“to ni ba zan sha ba?” dungure mata kai ya yi ya ce“ni abokin wasanki ne? Tashi anan” rau-rau ta yi da idanu kamar za ta yi kuka, ya taɓe baki sai kuma ya ci gaba da shan furarsa. Tana nan zaune har ya kusa shanyewa ta ɗan leƙa bowl ɗin taga sauran kaɗan sai kawai ta fashe da kuka tana murza idanunta, ɗago gajiyayyun idanunsa ya yi ya ɗan kalleta sai kuma ya ce“mene kuma?”

“Sai ka shanye baka bani ba”

Ta yi maganar cikin kuka, girgiza kansa ya yi sannan ya ɗebo furar ya kai mata ludayin baki, kallonsa kawai ta yi sai kuma ta kalli ludayin. A hankali ta buɗe bakinta ya zuba mata furar, lumshe idanunta ta yi tana tauna furar, ya kalleta yana murmushi sai kuma ya dungure mata kai ya ce“kwaɗayayyiya kawai” turo bakinta ta yi a hankali ta ce“ni ɗin uncle” sai da ya sake kai furar bakinsa sannan ya ce“eh ɗin ke” daga haka ya ɗebo ya kai mata baki, haka suka dinga shan furar tare har suka shanye, ya miƙa mata bowl ɗin yana gyatsa a fili ya ce

“Alhamdulillah”

Sannan ya miƙe yana kallonta ya ce“tashi ki tafi wajen su Maimoon” Toh kawai ta ce sannan ita ma ta miƙe ta fara kai bowl ɗin kitchen sannan suka fito a tare. Kalle-kalle ta dinga yi a babban tsakar gidan, ganin yanda mutane ke ta shige da fice yasa ta rasa in da zata yi, ganin yana shirin barin wajen yasa ta ɗan ƙara sauri har ta cimmasa sannan ta ce“uncle to ina zan je?” juyowa ya yi yana kallonta fuskarsa a haɗe ya ce“Nana ba zaki kyaleni na huta ba kenan?” sunkuyar da kanta ta yi tana wasa da fingers ɗinta, ya ɗan kalli tsakar gidan sai kuma ya ja hannunta suka bar wajen.

****
Washegari da sassafe suka yi wanka suka shirya dan zuwa gaisar da sauran dangi da yan uwa, Nana na ƙoƙarin rufe ƙaramar trolley ɗin Maimoon bayan ta ɗauki mayafin Zahra ta shigo ɗakin, Kallo ɗaya ta yi mata ta ɗauke kanta, lokaci ɗaya ƙirjinta ya dinga wani irin bugu. Zahra ta zauna gefen gadon tana kallonta fuska a sake ta ce“Nana!” ɗago fuskarta ta yi ta ɗan kalleta a sanyaye ta ce

“Na'am”

Sai kuma ta mayar da kanta kan abin da take, Murmushi ta yi ta ce“ya muke ciki ne da ke akan maganar mu?” ɗago jajayen idanunta ta yi ta kalleta amma bata ce komai ba. Zahra ta girgiza kanta ta ce“naga kina shirin kuka? Mene ne abun kuka anan?”

“Dan Allah dan annabi aunty ki yi hakuri, dan girman Allah...” ta ƙarasa maganar cikin shessheƙar kuka, haɗe rai Zahra ta yi ta mike tana kallonta ta ce“da kin yi min wani abu ne Nana? Ni na ce ba zan haƙura ba? Ai bani za ki bawa haƙuri ba, zuciyarki ita zaki bawa haƙuri akan Safwan, ki san yanda zaki yi ki ce baki sonsa”

Cikin kuka Nana ta ce“wallahi ba zan iya ba Aunty, ke da kanki ki ka ce kada nayi abin da zai ɓata sunan Abbana, to idan har zan ce ba zan auri Yaya Safwan dai dai yake da ɓata sunansa ai”

“To ki ɓata ɗin. Sai me dan kin ɓata sunansa Nana?. Look ni bai dameni ba ko ki ɓata sunansa ko kar ki ɓata, kawai abin da na sani shi ne ki fasa aurensa!”

Zahra ta yi maganar cikin ɓacin rai. Ganin bata ce komai ya sanya ta yi kwafa ta sake cewa“kuma ki sani idan har baki yi abin da nace ba nan da kwana uku wallahi tallahi sai na tona miki asiri Nana! Sai na tabbatar da hotunan ki sun shiga in da bakya tsammani”

Cikin kuka ta rarrafa gabanta ta rike ƙafafunta ta ce“dan Allah Aunty kada kimin haka, dan girman Allah ki rufa min asiri, wallahi idan Abbana ya gani zai iya mutuwa” hankaɗeta Zahra ta yi tana mata wani shegen kallo ta ce“to sai me. Idan ya mutu ni ce na mutu? Ai gara ma ya mutu domin yana ɗaya daga cikin waɗanda suke haddasa wannan fitinar ta auren zumunci, wallahi Nana kin ji har na rantse idan har baki yi abin da nace ba sai na bata miki”

Ta janye jikinta ta fice daga ɗakin fuuu.. Ban da kuka babu abin da Nana take, ta dafe saitin zuciyarta dake mata wani irin zafi. Sannan ta tashi ta koma gefen gadon ta zauna tana ci gaba da rera kukanta.

Ƙarfe 1:20 na rana Maimoon ta shigo ɗakin hannunta riƙe da ƙaramin kofi, sai da ta zauna gefen gadon sannan ta taɓa Nana tana cewa“ke Nana! Ke!” a hankali ta buɗe idanunta wanda suka kumbura saboda kukan da taci, ta tashi zaune tana kallon Maimoon fuskarta a haɗe ta ce“mene ne?”

“kina ta faman bacci tun ɗazu har mun je gidajen wasu”

Taɓe baki Nana ta yi sai kuma ta ce“to ni daman bana son naje ko ina ai” Maimoon ta tashi tana harararta ta ce“to kar ki so kuma ki je Atta na kiranki” sauka tayi daga kan gadon tana gyara zaman hular kanta ta nufi toilet, da idanu kawai Maimoon ta bita sai kuma ta tashi ta fice daga ɗakin.

Ƙarfe 2:30 na rana suka haɗu dukkansu a parlon Atta, sai hira ake gwanin ban sha'awa, Atta ta kalli su Maimoon ganin babu Nana a ciki ya sanya ta ce“wai ina yarinyar nan naga tun da safe ban ganta ba”

Maimoon na kokarin magana Nana ta yi sallama ta shigo dakin, Atta ta washe baki tana cewa “yauwa yarinyar kirki shigo kin ji” jiki a sanyaye Nana ta ƙarasa inda take zaune ta zauna gefenta, Atta ta riƙe hannunta ta ce“baki da lafiya ne?” girgiza mata kai ta yi a sanyaye ta ce“a'a lafiyata kalau” jinjina kai Atta ta yi sannan ta ci gaba da musu hira tana basu tarihin rayuwarsu a da, Nana ta ɗan zame jikinta ta ɗora kanta bisa cinyar Atta tana lumshe ido. Suna nan zaune har aka fara kiraye-kirayen sallar la'asar sannan mazan suka tashi dan tafiya masallaci, Matan kuma ta ce su shiga cikin ɗakinta su yi sallar acan, Zahra ta miƙe ganin Abdusammad yana ƙoƙarin fita, Da idanu Atta ta dinga binta ganin tana shirin bin bayansa yasa ta ce

“Ke ina zuwa ne?”

Cak Zahra ta tsaya kafin ta juyo a hankali tana kallon Atta data tsareta da idanu..

“Naga kina wani kokarin bin sa lafiyarki dai?”

Murya a sanyaye ta ce“a'a Hajiya daman zan masa magana ne”

Cike da faɗa Atta ta ce“lalashewa ta same ki ƴar nan, sabidda baki da kunya irin ta fulani yasa zaki iya bin miji a gabana? To mu ba haka muke ba.Sam wannan ba ɗabi'ar mu ba ce, kuma ba zamu lamunci wannan abun ba!”

Ita dai Zahra shiru ta yi tana kallon Atta, ganin bata sake cewa komai ba ya sa ta koma ta zauna dan ita tana fashin sallah. A hankali Atta ta tashi Nana da bacci ya fara ɗauketa ta ce“tashi muje ki yi sallah” to kawai ta ce a sanyaye sannan ta tashi tana murza idanunta ta nufi cikin ɗakin Atta. Sai da taga Nana ta bar wajen Sannan ta kalli Zahra da tayi shiru ta ce“kin ga wannan yarinyar. Ita ce wadda mijinki zai aura nan kusa, dan ba zai yiwu ya zauna da ke ɗaya bare ba! Dole ya auri jininsa”
Chapter 40 · 0% Book details