Sashe 57
Naanah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ta ƙare maganar tana durƙushewa a gabansa. Safwan ya runtse idanu yana jin wani irin zafi a zuciyarsa, da gaske bai kyauta mata ba, da gaske ya yaudareta. Yanzu kowa laifinta yake gani, ya cutar da rayuwarta. A ina zai ga Nana ya nemi gafararta? Me ya sa bai tambayi inda zata je ba?.
Sakinsa Maimoon ta yi ta ɗauki mayafinta wanda ya faɗi ta juya zata bar wajen, da sauri ya sake biyota yana cewa
“Kin san inda Nana ta tafi?”
Kamar ba zata kulashi ba sai kuma ta juyo tana kallonsa ta ce“mene ne abun da ya shafeka da inda ta tafi? ko zaka bita can ne ka dawo da ita domin kowa ya tsaneta?” girgiza kansa ya yi a sanyaye ya ce“a'a zan bata haƙuri ne”
Da wani mamaki Maimoon ta dinga kallonsa, can kuma ta girgiza kanta ta ce“haƙuri? haƙuri zaka bata saboda ka cuceta? to wallahi koda na san inda Nana take ba zan taɓa faɗa ba! Ba zan bari kowa ya sani ba!”
Daga haka ta juya ta bar wajen a fusace kamar zata tashi sama. Safwan ya bita da kallo zuciyarsa cike da damuwa.
****
Around 5:00 na yamma ta fito daga kitchen ɗin hannunta riƙe da wata ƙatuwar warmer, ta ajiye akan table sannan ta ɗauki mayafinta da ke kan sofa ta yafa, sai baza ƙamshi take. Ta ɗauki warmer ta fito daga apartment ɗin kai tsaye kuma apartment ɗin Hajiya Babba ta nufa.
Zaune ta samu mutane ana ta hira, Hajiya Babba na zaune kan sofa two seater ita da Atta. Jiki a sanyaye ta ƙarasa ciki dan sam bata ji daɗin ganin Attan ba, ɗaya bayan ɗaya ta dinga gaisar da mutanen parlon, suka amsa cikin fara'a sannan ta tsuguna gaban Hajiya Babba ta gaisheta itama. Fuska a sake ta amsa mata, ta kalli Atta ta gaisheta. Ciki-ciki ta amsa tana ɗauke kai, Zahra bata damu ba dan daman ta san haka zata yi ta mai da kallonta ga Hajiya Babba ta ce“hajiya daman abinci na kawo miki” ta tura mata warmer. Murmushi Hajiya Babba ta yi ta ce“tom nagode Fatima” Zahra ta murmusa sannan ta mike tana shirin fita. Ɗaya daga cikin matan da ke zaune ta kalleta sai kuma ta kalli Hajiya Babba ta ce
“au wannan ce matar tasa ta farko?”
Kafin Hajiya Babba ta yi magana Atta ta yi saurin faɗin “ita ce. Yaje ya auro bare, to da Allah yasa yanzu ya wanke kansa ya auri yar danginsa. Abun nan ya min daɗi, daman can ni ina nake son ya aura wallahi, sai dai aka fi ƙarfina ashe dai rabonsa ce. Yarinya yar dangi ga kyau ga diri” Atta ta ƙare maganar rai a sake. Murmushi duka suka yi banda Hajiya Babba, Zahra ma na tsaye dan ta kasa tafiya, Ɗaya bafulatanar ta ce
“oh naganeta, yarinyar ita ce wadda suka zo ruga tare ko? Ai daman aradu sun dace da juna. Ni na ɗauka ma a sannan ɗin matarsa ce”
Atta ta girgiza kanta ta ce“a'a sannan bai aureta ba, ai ni gara da Allah yasa aka yi haka ma. Dan da ya auri Haule gara Nanar”
Wani irin abu ne ya zo ya tokarewa Zahra a ƙirji, ta juyo tana kallon Atta a firgice. Kasa ɓoye tashin hankalinta ta yi bakinta na rawa ta ce
“Hajiya... Atta me ki ka ce?”
Tsuke fuska Atta ta yi ta ce“cewa nayi gara daya auri Nanar!”
A mugun firgice ta dawo gaban Atta, ta zube tana kallonta bakinta na rawa ta ce
“Babba...ban gane ba, wa ya aura? wa Doctor ya aura Atta?”
“Naanah mana!”
08106608363
Nanameera.*🌹 NAANAH 🌹*
Arewaboooks@Nanameera08
Wattpad@Nanameera08.
Assalamu alaikum jama'a, ina son nayi amfani da wannan damar na sanar daku cewa duk wanda ya ga wannan littafin na NAANAH ba'a channel ɗina ba, sannan ba forwarding aka yi daga channel ba to ba nawa bane, saboda an fara ɗora wasu links wanda basu dace ba akan page ɗin book ɗin, so kada aga wani abu wanda bai dace ba a yi tunanin daga gareni ne. Ban sani ba, kuma banida hannu a ciki, a channel ɗina kawai nake posting littafin nan, sai dai nayi sharing ɗinsa daga can.Nagode 🙏.
Page 35...
Atta ta bata amsa kai tsaye. Wani irin zaman yan bori Zahra ta yi a wajen, ta dinga kallonta hankali tashe, nan take hawaye suka fara zubar shar daga cikin idanunta. Sam ta kasa gane abin da Atta ke nufi, ta kasa gazgata maganarta. Dan haka ta rarrafa gaban Hajiya Babba ta dafata cikin wani irin yanayi wanda yafi kama dana tashin hankali ta ce
“Hajiya bangane me Atta ta ce ba. Wa Doctor ya aura?”
Dafata Hajiya Babba ta yi babu yabo babu fallasa ta ce“Naanah ya aura, ɗiyar Ahmad.”
Wani irin abu ne ya zo ya tokarewa Zahra a ƙirji, ta kasa koda haɗiyar yawu sai kallon Hajiya Babba take. Can kuma ta sake cewa“Hajiya daman ba Haule zai aura ba? Daman Naanah zai aura?”
Girgiza kai Hajiya Babba ta yi kafin ta ce“Eh Haule zai aura. Amma saboda matsalar da aka samu ya sanya ya fasa auren Haule, aka maye gurbinta da Naana. Ita kuma Haule ta auri Safwan da kuma ƙanwarki!”
Shiru Zahra ta yi tana tunani, gaba ɗaya sai taji kamar mafarki take wanda zata farka taga babu abin da ya faru. Ta dinga sauke numfashi da sauri da sauri hawaye na biyo kuncinta, ganin yanda jikinta ya yi sanyi ya sanya Hajiya Babba cewa“tashi ki je. Idan ya dawo sai ya miki bayani yanda zaki fahimta” kasa cewa komai ta yi, ta miƙe da kyar tana dafe kanta saboda sara matan da ya yi, a daddafe kuma ta fice daga parlon. Atta ta bita da harara sannan ta ce“ai daman ni na san ba son auren zata yi ba! Kuma babu yanda ta iya wallahi. Idan bata yi wasa ba ma sai ya saketa” kallonta kawai Hajiya Babba ta yi ba tare da ta ce komai ba. Ta sauke numfashi a sanyaye ta ce
“Allah ya kyauta”
****
Zahra na komawa apartment ɗinta ta haye sama da sauri, daƙinta ta shiga ta rufe ƙofar sannan ta fara dialing numbern Aunty Khadijah hannunta na rawa. Ringing ɗaya ta ɗauka, kafin ta yi magana Zahra ta yi saurin cewa
“nashiga uku aunty, na shiga ukuna!”
Da mamaki Aunty Khadijah ta ce
“Lafiya dai Zahra?”
Cikin kuka Zahra ta ce“ya aureta! Wallahi ya aureta Aunty. Ya zan yi da raina? Taya zan jure ganin Nana matsayin matar mijina? Nana fa aunty!”
Aunty Khadijah da bata gane inda zancen ya dosa ba ta ce
“kin ga Zahra nutsu ki min bayani. Wace ya aura? Kuma wane ki ke magana akai?”
Girgiza kai Zahra ta dinga yi cikin tashin hankali ta ce
“Nanah mana! Doctor ya auri Nana, ashe da ita aka ɗaura masa aure ɗazu.”
A firgice Aunty Khadijah ta tashi daga zaunen da take ta ce
“what?!”
Zahra ta gyaɗa mata kai kamar tana gabanta. Cikin shessheƙar kuka ta ce
“Eh Aunty. Wallahi ita aka aura masa, yanzu Nana ce kishiyata, wayyo Allah na zuciyata aunty, wallahi ba zan iya ba. Mutuwa zan yi Aunty”
Ta ƙare maganar tana fashewa da wani raunataccen kuka.
Shiru Aunty Khadijah ta yi tana ayyana irin abin da zasu yi, jin yanda Zahra ke kuka kamar ranta zai fita yasa ta yi ƙasa da murya ta ce
“Ya isa haka Zahra. Zaki iya fitowa yanzu?”
Girgiza kanta ta yi ta ce“a'a ba zan iya ba wallahi”
Aunty Khadijah ta sauke numfashi sannan ta ce
“tom shikenan. Ki bari gobe da safe zan zo sai mu san yanda zamu yi Kinji, ki daina kukan”
Shiru Zahra ta yi tana shessheƙar kukanta. Aunty Khadijah ta sake ƙasa da murya cikin sigar rarrashi ta ce
“ki yi haƙuri kin ji. Ki ɗauka kamar ba'a miki kishiya ba, in dai ina da rai ba zan bari yarinyar nan ta tare ba”
Zahra ta gyaɗa kanta a sanyaye ta ce“tam Aunty.”
Jin ta kwantar da hankalinta ya sa ta sake cewa“to ki daina kukan, ki share hawayenki”
To kawai Zahra ta ce sannan suka yi sallama. Ta wurgar da wayar tsakiyar gado sannan ta durƙushe a wajen tana fashewa da wani sabon kukan, idan ta tuna yanzu ita da Nana suna ɗaya suke amsawa sai taji zuciyarta ta tsinke.
****
Tsaye suke a ward ɗin asibitin kowa ya yi jigum-jigum, Sultan ne ya fito hannunsa riƙe da wata takarda ya ƙaraso wajen, da sauri Abdusammad ya ƙarasa wajensa ya amshi takardar without say anything. Warware ya yi ya karanceta tas sai kuma ya ɗago kansa cike da damuwa ya ce
“Ya jikin nasa to?”
Numfasawa Sultan ya yi kafin ya ce“da sauƙi za'a ce. But har yanzu bai farfaɗo ba”
Miƙa masa takardar ya yi sai kuma ya nufi ɗakin da aka kwantar da Abban.
Kwance ya sameshi idanunsa a rufe yana sauke numfashi a hankali da taimakon na'urar da aka saka masa. Abdusammad ya riƙe hannunsa na dama yana jin zuciyarsa sam babu daɗi. Abba na ɗaya daga cikin mutanen da ya fi ƙauna a duniya, idan ka cire Hajiya Babba babu wanda ya kewa kallon mahaifi sama da Abba, he's not just his father but a friend. Yanda suke zama su yi hira da Abba koda Hajiya Babba baya yi, dan haka ganinsa cikin wannan halin babu abin da yake face tada masa hankali. Idan kuma ya tuna Nana ce sanadiyyar wannan abun sai yaji zuciyarsa ta sake ɓaci, sai yaji dama ya bar nan yaje ya dawo da ita gida ya nuna mata kuskuren abin da tayi. Furzar da zazzafan numfashi ya yi daga bakinsa still looking at Abba's face.
Ƙarar na'urar da yaji ce ta sanya shi gyara tsaiwarsa, ya dinga kallon Abba wanda yake ƙoƙarin buɗe idanunsa. Da sauri ya zauna a gefen shi har sannan yana riƙe da hannunsa ya ce
“Abba!”
A hankali Abba ya buɗe idanunsa wanda suka yi jajur dasu, ya kalli Abdusammad sai kuma ya sake rufesu. Jiki a sanyaye Abdusammad ya ce
“Abba ka yi haƙuri dan Allah, kar ka damu kan ka kaji”
Shiru Abba ya yi kamar ba zai magana ba can kuma ya ce.
“Abdul”
“Na'am Abba”