Sashe 100
Naanah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
****
Zahra na zaune kan kujera a parlornta wayarta dake hannunta ta fara ringing, Ta ɗaga tana murmushi ta ce“Hello Anty” Anty Khadijah dake jan numfashi kamar wadda ke kuka ta ce“Zahra kina ji?” Gyara zamanta ta yi jin muryar tata ta ce“Anty lafiya dai? Me ya same ki?”
“Zahra bana son auren Malam Garban nan, wallahi bana so. Gashi ɗazu sun zo sun kawo kuɗin aure nan da 2 weeks za'a ɗaura auren...”
Tashi tsaye Zahra ta yi tana girgiza kanta ta ce
“Haba dai Anty. Wallahi ba zaki auri wannan mutumin ba! Ya ma za'a yi ki aure shi? Idan ma wani asirin ya yi miki sai dai ya faɗa kansa wallahi Anty. amma ke dai kin fi ƙarfin aurensa”
Cikin kuka Anty Khadijah ta ce“nima na san da haka Zahra. Wallahi ni ba sa'ar aurensa ba ce, akan mene ma zan aure shi?”
Zahra ta yi shiru tana jin zuciyarta a dagule, Anty Khadijah ta ja numfashi ta ce“kina ji? Amma kina shan maganin nan?” Girgiza kai Xahra ta yi a sanyaye ta ce“Wallahi a'a Anty, kwana biyu kin ga ban sha ba. Ni mantawa ma nake dashi” Anty Khadijah ta yi shiru can kuma ta ce“To ki ɗauko ki shanye yanzu, saboda bana son ya kai wani satin zai lalace." To kawai Zahra ta ce sannan suka ci gaba da tattauna maganar auren...
Sai bayan sallar magriba sannan ya shigo gidan, Kai tsaye ɗakin Nana ya nufa dan ranar kwanan Zahra ne. Ya sameta zaune ƙasan gado tana danna wayarta bayan ta idar da sallah, Ƙarasawa ciki ya yi ya ajiye ledar dake hannunsa ya zauna gefen gadon yana kallon ta fuskarsa a sake ya ce
“Hey baby.”
Ɗago kanta ta yi ta kalle shi, Ya sakar mata murmushi yana miƙa mata hannu. Tura baki ta yi ta tashi ta koma can ƙarshen gado ta zauna, Murmushi ya yi sannan ya juya inda take yana kallon ta, Fuskarta a haɗe babu alamar wasa. Ya hau tsakiyar gadon ya zauna kusa da ita yana jan kumatunta ya ce
“Wa ya taɓa min ƴar rigimata?”
Janye hannunsa ta yi tana tura baki, Ya sake kai hannunsa zai taɓa ta. Tsam ta tashi daga wajen ta koma wani ta zauna tana kallon sa, Ya girgiza kansa ya sake bin ta, Ƙoƙarin sauka take daga kan gadon ya jawota jikinsa. Tura shi ta fara yi kamar zata yi kuka ta ce
“Ni Allah uncle bana so. Ni ka bari”
Sake matseta ya yi a jikinsa yana kallon ta ya ce“Ni zaki dinga sharewa?” Ɗauke kanta ta yi tana kallon wani wajen, Ya yi kwafa kafin ya janyo fuskarta ya ce
“Idan ki ka sake ɗaukewa sai na baki mamaki.”
Ganin babu alamar wasa akan fuskarsa ya sanya ta fasa ɗaukewa, ta sunkuyar da kanta nan take hawaye suka fara zubowa kan fuskarta. Waro idanunsa ya yi yana kallonta kafin ya ce
“me kuma nayi miki?”
Cikin kuka ta ce“Ni bana so, bana so kana taɓani wallahi. Ka daina!”
Kallon ta kawai yake. Can kuma ya yi murmushi ya ce“Yanzu warning ki ke min or what Nana?” tura baki ta yi tana ƙoƙarin kwace kanta. Ya sake matseta yana kallonta ya ce“ai sai kin amsa min yarinya.” marairaice fuska ta yi ta ce
“uncleee!”
“Auntyyyy..!”
Ya ce yana kwaikwayon muryarta. Tuntsirewa Nana ta yi da dariya tana kallon sa, Shima dariyar yake. Ta duke shi a ƙirji ta ce“ni ka daina kwaikwayon magana ta Allah!”
Gyaɗa mata kai ya yi ya ce“To na bari Aunty.”
“Ni bana sooo!”
Ta ce a shagwaɓe.
Murmushi kawai ya yi yana ɗora kansa a wuyanta ya ce“Zo ki ci abinci.”
Turo baki ta yi kafin ta ce“ni bana ci” Bai ce komai ba ya janyeta daga jikinsa ya sauka daga kan gadon, Ledar daya shigo da ita ya ɗauko ya miƙo mata. Ta karɓa tana kallon sa, sai kuma ta buɗe, washe baki ta yi ta ɗago kanta tana kallon sa ta ce
“Laaa kaza?”
Gyaɗa mata kai ya yi ya ce“Eh bashin kazar ki ce.”
Turo baki ta yi ta tura masa ledar ta ce“bana ci”
“A kan me?”
Ta koma ta kwanta ta ce“kawai bana ci.”
Murmushi ya yi ya sanya hannunsa ya jawota, Ya ɗago kanta ya ce“Ko dai ki ci ko kuma...”
“Zan ci wallahi!”
Ta katse shi da sauri. Ta ɗauki ledar kazar ta buɗe ta fara ci tana taunawa a hankali, Ɗago kanta ta yi taga yana kallonta. Ta dauko tsoka ɗaya ta miƙa masa tana tauna ta bakinta ta ce
“Cii”
Yanda ta yi maganar ne ya bashi dariya, Ya ja kumatunta ya ce“Am full” bata sake cewa komai ba ta kai naman bakinta tana rausaya kai. Tashi ya yi yana kallonta ya ce“sai da safe.”
To kawai ta ce a sanyaye, Ya juya ya fice daga ɗakin. Sai a sannan ta ture ledar gabanta ta kifa kanta akan cinyoyinta ta fashe da kuka tana birgima a wajen. Haka ta gaji da kukan ta haƙura ta tashi ta shige bayi ta wanko bakinta sannan ta yi wanka ta fito, Wasu riga da wando masu sulɓi ta ɗauka ta saka sannan ta yi kwanciyarta. Ta dade tana juye-juye kafin bacci ya ɗauketa, Abdusammad koda ya fita ɗakin Zahra ya shiga ya ce mata yana apartment ɗinsa. Amma har wajen ƙarfe 12 na daren bata zo ba dan haka ya yi kwanciyarsa. Washegari ma bai zauna a gidan ba saboda aiki da ya ya masa yawa, Zahra kuwa ko inda yake bata je ba. Ko Noor bata kai school ba tayi kwanciyarta a ɗaki doing nothing. Nana na zaune akan sofa wajejen ƙarfe 7:00 na dare, wayarta ta fara ringing, numbern Abba ta gani, Ta ɗaga ta kai kunne tana murmushi.
“Happy birthday daughter!”
Cewar Abba muryarsa cike da farin ciki. Tuntsirewa da dariya Nana ta yi dan ita har ta manta ma, Can kuma ta tsuke fuska ta ce
“Abba yau birthday ɗina babu celebration”
Murmushi ya yi ya ce“Uncle ɗin ki bai miki ba?” taɓe baki ta yi ta ce“uncle ɗin bai ma sani ba.”
“Haba?”
Abba ya yi maganar yana murmushi, Sake tura baki ta yi ta ce“Abba ina birthday gift ɗina?”
Abba ya ce“To yanzu Nana ta ina zan baki birthday gift? But tell me what do you want, Sai na siya miki duk randa ki ka zo na baki.” Ɗan juya Idanunta ta yi kamar mai tunani ta ce“Yauwa Abba ina son ka siya min teddies da kuma sabon system!" Girgiza kai Abba ya yi yana murmushi ya ce“Nana kenan, you will never change. To naji” Dariya sosai ta yi ta ce“Yauwa Abbana thank you, Allah ya ƙara maka arziki, Ya baka lafiya ingantacciya!” Lumshe idanunsa ya yi yana jin zuciyarsa wasai babu damuwa ya ce
“Amin ya rabbil alameen Nana Khadijah, Allah ya miki albarka ya zaunar min da ke lafiya, Ya kaɗe sharri daga cikin aurenku. Ya baki ya'ya na gari”
Sunkuyar da kanta ta yi tana murmushi ta ce“Abba idan na haihu sai na bar muku ɗan ko?” Dariya ta bashi, Ya ce“Zaki bar min ɗan?” Ta gyaɗa kanta ta ce“Eh Abbana! Sai na bar muku kai da Amma.” Murmushi sosai ya yi ya ce“To Allah ya baki ya'yan Nana” Ta yi murmushi ta ce“Amin Abbana” Sun daɗe suna hira kafin ya kashe wayar. Ta sauke numfashi jin ana kiran sallah ta tashi ta shige bedroom ɗinta, Alwala ta yi ta gabatar da sallah sannan ta yi kwanciyarta dan ba yunwa take ji ba. Tana jin convey ɗinsa, Amma bai shigo gidan ba har sai da aka idar da sallahr Isha'i. Tana kwance tana kallon wata Chinese drama ya shigo dakin, Ta amsa sallamar ciki-ciki. Zama ya yi gefen gadon yana kallon ta ganin ko ɗago kanta bata yi ba, Ya ɗan yi murmushi ya ja yatsun ƙafarta ya ce
“Heyyy”
Ɗago kanta ta yi ta kalle shi sai kuma ta tura baki, Ya girgiza kansa ya ce”wato ke kullum baki so a zauna lafiya ko? Haka ake yiwa miji aka ce miki?”
Ɗauke kanta ta yi tana zumɓura baki gaba. Ya taso ya dawo kusa da ita ya janye system ɗin ya rufe yana kallon ta ya ce“faɗa min yau kuma mene ne? Wa ya taɓan ƴan matana?” Janye hannunta ta yi ta ce“Ni bana so..”
Haɗe rai ya yi babu alamar wasa ya ce“baki son me?” ta kalle shi amma bata ce komai ba. Tashi ya yi yana faɗin “tun da baki da abin cewa sai da safe.” Ganin da gaske tafiya zai yi ya sakata tashi tsayen itama, Ta kira sunansa cikin shessheƙar kuka, Juyowa ya yi yana kallonta da mamaki ganin hawaye akan fuskarta. Ya dawo ya riƙe hannunta ya ce
“Mene ne?"
Fashewa ta yi da kuka ta shige jikinsa tana cewa“Ba kai ne ba, baka san yau birthday ɗina ba? Kuma Abba ya ce kai ne zaka min birthday cake...”
Ta ƙare maganar tana sakin wani sabon kukan, Wani lafiyayyen murmushi ne ya kwace masa, Ya dafa bayanta yana ƙoƙarin saita kansa kafin ya ɗago fuskarsa a haɗe ya ce
“Ni bani da abin yi zan tsaya wasa? Sakeni ni” Ya janyeta daga jikinsa, Bai tsaya jiran abin da zata ce ba ya juya ya yi ficewarsa. Nana ta bi shi da kallo sai kuma ta koma gefen gado ta zauna tana fashewa da wani irin kuka..
Koda yaje dakin Zahra zaune ya sameta tana waya, Ya tsaya har ta gama kafin ya ce“Madam kwana biyu abun ne ya motsa?” Girgiza kanta ta yi a sanyaye ta ce“Ba komai fa doctor” Ya yi shiru yana kallon ta can kuma ya sauke numfashi ya ce“Alright bari naje ina zuwa.” To kawai ta ce ya juya ya fice, Ta bi shi da kallo sai kuma ta taɓe baki.
Nana na kwance gefen gado Around 9pm taji ana knocking ƙofar, Ta goge hawayen dake kan fuskarta sannan ta sauka daga gadon. Koda ta buɗe ƙofar Maid ta gani tsaye, Ta sunkuya ta gaisheta kafin ta ce“Madam ana kiran ki” Nana ta ɗan kalleta da kumburarrun Idanunta ta ce“ina?”
“Downstairs”