← Book details Naanah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 125

Sashe 23

Naanah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

****
Junaid ya girgiza kansa idanunsa zube kan wayar hannunsa ya ce“ni fa ba zan yi ba, kai wai kana ma da hankali ne? Ce maka nayi fa ina son na aureta, idan ba zaka iya bani shawarar arziki ba ka rabu dani dan Allah” ya ƙare maganar yana ɗago kansa, Taɓe baki Al-ameen ya yi sai kuma ya ce“Baba ka ji fa, ana bashi shawara yana gwale mutane, to kaje ka ci gaba da bin ta tana jan ka a ƙasa” ya yi maganar cikin ɓacin rai, Harararsa Junaid ya yi ya ce“eh naji mene ne dan ta jani a ƙasa? Ai daman ita mace an santa da haka, kuma kaf cikinku babu wanda yake dating yar babban gida irin yanda nake, sai dai idan baƙin ciki ku ke min”

“kai ka isa mu maka baƙin ciki akan waccan kwailar yarinyar? Mu da muke da mata waɗanda suka san kansu” cewar Habib a ɗan zafafe. Kallonsu ya yi sai kuma ya taɓe baki ya ci gaba da danna wayarsa ba tare da ya sake bi ta kansu ba.

****

“Sultan! Sultan! Sultan...”

“na'am Ummi”

Ya amsa mata yana kokarin tashi zaune, kallonsa ta dinga yi daga tsayen da take kafin ta ce“mene haka? Kwanciyar me ka ke a ɗaki har wannan lokacin?” Ummi ta yi tambayar tana kallon fuskarsa wadda ta rame sosai, girgiza kansa ya yi ya ce“babu komai Ummi, kawai ina ɗan ciwon kai ne shi ne ya hana ni tashi, amma yanzu zan tashi”

“ciwon kai ne ya hana ka tashi daga kwance har la'asar ko? Sultan ko dai kana son ka zaja min masifar da ba zan iya da ita bane? Akan maganar aure ka bi ka ɗaga hankalinka, ita matar mutum ai ƙabarinsa mene ne abun wannan damuwar?”

Lumshe shanyayyun idanunsa ya yi kafin ya ce“na haƙura fa Ummi, na bar wa Allah komai, idan Nana ce Alkhairina Allah ya sani kuma zai bar min ita a duk yanda take, amma idan ba ita ba ce ba na san ba zan sameta ba, so ki bar damun kan ki” ya ƙare maganar a sanyaye, girgiza kai Ummi ta yi sannan ta zauna gefen gadon ta dafa kafaɗar sa cike da kulawa irin ta uwa ta ce

“na sani akwai ciwo ka rabu da wanda ka ke so, na sani kana son Nana, ita kuma tana sonka, amma ka sani baka isa ka bawa kan ka abin da Allah bai baka ba, idan ba ita Allah ya ƙaddara maka ba, ba zaka taɓa samunta ba, sai dai ka yi ta damun kan ka kana shiga wani hali, mata su aka sani da irin wannan ba maza ba, ka zama mai ɗaukan ƙaddara a duk yanda ta zo maka, ka daina wannan ƙuncin da damuwar. Ka fawallawa Allah komai dan Allah Sultan”

Faɗawa jikinta ya yi yana sakin wani marayan kuka mai ban tausayi, kuka yake ko ya samu sauƙin abin da yake ji a zuciyarsa, ya sani ba lallai bane ya samu Nana tun da aka yi haka, amma zuciyarsa ta kasa haƙura ta daina tunaninta. Ummi ta shiga shafa kansa a hankali tana jin babu daɗi a ranta, tabbas da tana da dama da sai ta bawa Sultan matar da yake so, sai dai ko kaɗan bata da wannan damar, ba zata iya cewa koda ƙala ba akan maganar auren, dan haka dole ta ci gaba da rarrashinsa da kuma yi masa addu'a har ya manta da Nana.

****
Around 5:20 na yamma ta sakko ƙasan hannunta riƙe da wayar Zahra, babu kowa a parlon dan haka ta yi waje da sauri kafin wani ya zo. Tafiya ta dinga yi tana waiwaye har ta fice daga gidan, ta tsaya a jikin gate ta fara dialing numbern tasa, sai dai kafin ta kai ga kira taji ana yin horn daga gefenta na dama, dan haka ta juya tana kallon wanda yake horn ɗin, kamar yanda ta zata haka ce ta faru, Junaid ne zaune gaban motar hannunsa maƙale kan steering motar yana kallonta, ta sauke numfashi sannan ta ƙarasa wajen. Buɗe motar ta yi ta shiga tana kallonsa, ya dinga kallonta shima yana murmushi, sunkuyar da kanta ta yi tana wasa da fingers ɗinta ta ce

“ina yini?”

Yanda ta yi maganar ya sanya shi murmushin da bai yi niyya ba, ta ɗago ta kalleshi sai kuma ta sake sunkuyar da kanta tana murmushin itama.

“kin yi kyau abin ki”

Ya yi maganar cikin nishadi, ɗago kanta ta yi ta kalleshi ta ce“kai ma haka sir, ka yi kyau kamar ango”

“ango ranar bikinsa ko?”

Gyaɗa masa kai ta yi ya ce“to yaushe ne bikin namu?” ɗan zaro idanu ta yi sai kuma ta ɗauke kanta bata ce komai ba, ya dinga kallonta can kuma ya ce“kin san me yasa na zo wajenki?” Girgiza kanta ta yi ya ce“daman ina son na sake tambayar ki ne akan maganar aurenku, shin da gaske nan da 6weeks ɗin ne?”

She just nodded her head fuskarta babu walwala, ya sauke numfashi sannan ya ce”and har yanzu Abbanki bai karbeni ba?”

Kamar zata yi kuka ta ce

“ban fa faɗawa Abba komai ba, da Amma kawai muka yi maganar saboda nasan ta fi shi sauƙin kai, but unfortunately sai naga ita ma bata yarda ba, ta ce idan na yiwa Abba maganar sai ta ɓata min rai, and nima na san koda na yi masa ba zan taɓa samun abin da nake so ba, ba zasu barni ba, in dai ina cikin estate ɗin M-Shuwa ba zan taɓa kasancewa da kai ba, sai dai...”

Ta ɗan yi shiru tana kallonsa idanunta cike taf da hawaye

“Sai dai me?”

Junaid ya yi maganar yana ci gaba da kallon kyakkyawar fuskarta. Furzar da numfashi ta yi sannan ta ce

“Sai dai idan barin gidan zan yi, sai dai idan na bika mu gudu, sai muje wani wajen muyi aure”

Da wani irin matsanancin mamaki Junaid ke kallonta, ya girgiza kansa kafin ya ce

“mu gudu kuma Nana? Kin san me ki ke faɗa kuwa?”

Jinjina masa kai ta yi hawaye na zubowa kan fuskarta ta ce

“eh mu gudu, ka gudu dani dan Allah, muje mu yi aurenmu muyi rayuwarmu mu kaɗai”

08106608363
Nanameera.*🌹 NAANAH 🌹*

Page 15...

Junaid ya dinga kallonta baki buɗe, ta goge hawayenta tana fadin“saboda idan har ina cikin gidan to sai dai mu haƙura da juna, amma idan muka yi aure basu sani ba, koda na dawo zasu haƙura kuma...”

“Nana!”

Ya daka mata tsawa wadda ta sanya ta yi shiru, cikin ɓacin rai ya ce“baki san me ki ke faɗa ba! Baki da hankali ne shiyasa, har yau yarinta ke damunki, kin san irin yanda iyayenki ke son ki da har zaki yi yunƙurin rabuwa dasu? Kin san halin da zasu shiga? Do you have any idea about how much they care about you? Kin san irin soyyayar dake tsakanin iyaye da ɗan su kuwa? Kin bani mamaki. Ko zan rasa ki ba zan taɓa yarda da wannan gurguwar shawarar taki ba, ba zan taɓa aminta da ita ba! Ki sake magana!”

Kallonsa ta dinga yi hawaye na zirarowa kan kuncinta sai kuma ta ce“Ai shikenan tun da ka ce haka, daman ba sona ka ke ba, a baki ka ke faɗar son amma babu shi cikin zuciyarka, har ka ke iƙirarin ka rasani, to kaje ɗin, nima na rabu da kai, ba zan sake kula ka ba! Ba zan sake kiran ka a waya ba! Ba zan kuma ba wallahi!” ta ƙare maganar tana fashewa da wani raunataccen kuka dake ƙaryata kalaman bakinta, ta buɗe motar a fusace ta fita. Junaid ya dinga kallonta har ta buɗe gate ɗin gidan ta shige, ya sauke numfashi yana jin babu daɗi a cikin ransa ganin yanda ta yi fushi. Sanin saurin fushinta da kuma saurin saukarta ya sanya bai damu ba ya yiwa motar key ya juya ya yi reverse ya bar unguwar.

Wata irin faduwar gaba ce ta risketa saboda ido biyu da suka yi da Zahra tana tsaye ta naɗe hannayenta a ƙirji, ta dinga kallonta ba tare da ta ce komai ba. Sunkuyar da kai Nana ta yi tana goge hawayenta da gefen mayafinta, Zahra ta fizgi hannunta ta fara janta. Bin ta Nana ta dinga yi tana jin zuciyarta na wani irin bugawa, tsoro da fargabar abin da Zahra zata ce mata suka shigeta. A gaban wasu fararen kujeru ta tsaya, ta dangwarar da ita akan ɗaya sannan ta zauna a wadda take facing ɗinta.

Ganin irin kallon tuhumar da take mata ya sanya jikin Nana ya sake sanyi, ta ɗago kanta cikin shassheƙar kuka ta ce

“wallahi Aunty...”

Dakatar da ita ta yi ta hanyar ɗaga mata hannu, ta yi shiru a dole ba dan ta fadi abin da ta yi niyya ba. Shiru wajen ya ɗauka na wasu mintuna kafin Zahra ta buɗi baki cikin kakkausar murya ta ce

“Nana wane wannan? A ina ki ka san shi? Mene ne alaƙar da ke tsakaninki dashi? And why you dey called him here!”

Zahra ta jera mata tambayoyin tana kafeta da idanu, shiru Nana ta yi tana matsar kwalla, hakan kuma ya ɓatawa Zahra rai matuƙa dan haka a fusace ta ce

“okay kar ki yi magana, wallahi idan baki faɗa min wane shi ba sai na faɗawa uncle ɗin ki, idan ya so ya sanar da Abba!”

Da sauri ta ɗago kanta, ta dinga girgiza kan tana hawaye a kiɗime kuma ta ce“a'a aunty zan faɗa miki, dan Allah kar ki faɗawa Abbana!”

Haɗe rai Zahra ta yi ta ce“oya faɗa min wane ne shi?”

Sai da goge hawayen dake kan fuskarta sannan ta buɗe bakinta a hankali ta fara faɗin
Chapter 23 · 0% Book details