Sashe 116
Naanah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ya faɗa yana sake miƙo mata tuwon, Ganin irin yanda ya haɗe ransa ya sanyata buɗe bakin nata, Ya saka mata tuwon yana harararta. Saurin toshe bakinta ta yi, Ta tashi da niyyar barin wajen ta ji ya rike ta, Girgiza masa kai ta dinga yi bakinta a rufe. Yaƙi barinta ta tashi, kuka ta saka tana ƙoƙarin kwace jikinta, Ya matseta a jikinsa ba tare da ya ce komai ba. Bata san sanda ta zare hannun nata daga kan bakin ba sai ganin amai tayi na zuba. Ta dinga kwarara amai tana riƙe da cikinta. Ban da kallon ta babu abin da Abdussamad ke yi, Gaba ɗaya ta wanke shi da amai, Ya kasa cewa komai, Ganin yanda ta galabaita sosai ya sanya shi jawota jikinsa, Kamar jira take ta ɗora kanta akan kirjinsa tana sakin wani irin wahalallen numfashi. Sai da yaga ta ɗan nutsu sannan ya tashi da ita a jikinsa suka nufi toilet, Wanka ta sake yi shi kuma ya gyara in da ta ɓata ya sauya bedsheet. Bayan ya gama ya fice daga ɗakin ya koma nasa, wankan shi ma ya yi sannan ya shirya cikin kayan bacci, Koda ya dawo ɗakin kwance ya sameta kan sofa tana daure da towel da alama tun da ta fito daga wankan take kwance a wajen, Ƙarasawa ya yi ya taba jikinta, Zafi yaji sosai. Ya girgiza kansa sannan ya ƙarasa press ɗin ta ya buɗe, Wata riga mai saukin nauyi ya dauko mata, Ya dawo ya taimaka mata ta saka sannan suka fice daga ɗakin. Ɗakin sa ya mai da ita, Ta kwanta akan royal bed ɗin sa ta lumshe idanu, Gaba ɗaya jikinta ciwo yake mata. Ga wani irin ciwo da mararta ke yi, Injection ya haɗo ya dawo ya zauna gefenta, Saurin tashi zaune ta yi duk da yanda take jin jikinta muryarta na rawa ta ce
“Uncle wa zaka yi wa allurar?”
Yana ƙoƙarin ɗaukan sringy ɗin ya ce
“Kaina zan wa”
Yana gama faɗin hakan ya jawota jikinsa, Kuka ta fara yi ta rike shi tana cewa
“Dan Allah uncle kada ka min allura, Wallahi bana so zafi fa”
Shafa dogon gashin kanta ya yi yana murmushi ya ce
“To shikenan zo ki kwanta”
“Ka fasa yi min?”
Ta tambaya tana hawaye. Bai ce komai ba ya yi kwanciyar sa, Ta ɗan yi jim tana kallon sa kafin ta kwanta a kusa dashi ita ma, Kasancewar a gajiye take yasa nan da nan bacci ya dauketa, Saukar numfashin ta da yaji ya sanya shi ɗaga kansa ya kalleta. Sai kuma ya tashi zaune ya dauko allurar, A hankali ya janye rigar jikinta ya sai ta allurar ya yi bismillah sannan ya yi mata, wata irin zabura ta yi ta tashi zaune, Ta dinga kallon sa sai kuma ta fashe da kuka. Murmushi ya yi ya jawota jikinsa ya rungumeta yana bubbuga bayanta ya ce
“Ya isa haka! Ya isa”
Cikin kuka ta ce
“Sai da nace bana so ka yi min, Wayyo Abbana zafi zai kasheni!”
Ta ƙare maganar tana sakin wani sabon kukan, Murmushi kawai ya dinga yi dan ya san halin rakinta. Ya kwanta har sannan tana jikinsa, A kunnenta ya raɗa mata wata magana, Ta daga idanunta ta kalle shi sai kuma ta sake ɓoye fuskarta a jikinsa, Shafa bayanta yayi a sanyaye ya ce
“Agreed?”
Makale masa kafaɗa ta yi tana ci gaba da kukanta, Ya girgiza kansa yana murmushi bai ce komai ba.
****
Washegari ta kasance ranar Lahadi, Bayan sallar azahar aka daura auren Anty Khadijah da Malam Garba. Gidan a cike yake da jama'a, Yawancin yan uwa da abokan arziki sun hallarci bikin, Musamman daya kasance an dade ba'a yi taro a gidan ba, Sai shige da fice ake, Ana shewa. Kowa na murna da Anty Khadijah ta samu miji, Ana ganin zata daina abubuwan da take ta zauna a ɗakin mijinta. Har mai dj aka ɗauko da Yamma ya zo compound ɗin gidan aka tashe, Amarya sai rawa take tana murna abin ta. Su Amal na tayata, Dan Siyama bata zo ba kasancewar tana takaba, Duk wannan bidirin da ake babu Zahra a ciki, tana sama a ɗakinta ta kulle, Yini ta yi zuciya babu daɗi, Gaba ɗaya mijinta ne ke faɗo mata, Sai kuma Noor, Shikenan babu wanda zata sake gani cikin su, Musamman Noor din, Kuma Anty Khadijah sai murnarta take zata tafi nata ɗakin mijin bayan ita ta rabata da nata. Wannan abun ya sanya Zahra yini tana kuka, Daga karshe ta kwanta, Sai dai sam baccin ya gagara zuwa, Data rufe idanun ta Abdussamad take gani. Haka ta dinga zama a ɗakin har bayan sallar magriba, Koda aka zo aka kirata su yi sallama da amarya ƙin fitowa ta yi, ta ce Allah ya bata zaman lafiya. Umma bata tilasta ta ba ta ce a rabu da ita, Anty Khadijah da abun ya ɓata mata rai ta nufi saman ba tare da an lura ba. Murɗa handle din ƙofar ta yi ta shiga, Ta samu Zahra na zaune kan dadduma tana jan carbi. Harararta ta dinga yi kafin daga bisani ta ce
“Wato Zahra baƙin ciki ki ke min da auren da nayi ko? Shi ne yasa ba zaki iya fitowa mu yi sallama ba ko? To ni gashi na zo. Allah ya bamu alkhairi, zan tafi ɗakin mijina. Kin san dama ita rayuwa juyi-juyi ce, Yau gareka gobe ga waninka, Da kece mai aure ni kuma bazawara, Sai gashi yau na zama mai aure ke kuma kin zama bazawara. To Ubangiji ya kawo miji a kusa, Na tafi!”
Anty Khadijah na gama faɗin haka ta juya ta fice daga ɗakin ba tare da ta jira jin amsar da Zahran zata bata ba. Ita ko Zahra kada koda motsi ta yi, Sai hawaye dake zubowa daga cikin idanun ta kamar an bude famfo. Tabbas ta yi wawta, Kuma ta yi nadama, Ta yi nadamar yarda da maganganun Anty Khadijah, Gashi yanzu ta cuceta. Ta bar ta a ruwa, Ta ɗora fuskarta a gefen gado tana fashewa da wani kuka mai sauti.
Daren ranar Malam Garba ya zo ya tafi da Anty Khadijah, Dan cewa ya yi baya son rakiyar amaryar nan, Suma basu takura kansu ba, aka bar shi ya tafi tare da ita. Gidan dai da suka saba zuwa da Kaddu nan ne gidan da zata zauna, Anty Khadijah ta dinga kallon soran gidan ganin ya tsaya anan yana buɗe wani daki dake wajen, Kamar ta yi masa magana sai kuma ta kasa, Ya buɗe ɗakin suka shiga. Da mamaki ta dinga kallon ɗakin, Ganin duk kayanta anan aka zuba su, Ɗakin yana da ɗan girma dan haka aka saka furniture da kuma kujeru guda biyu, Sai gas ɗin ta a gefe, Sauran kayan kuma aka bar su a corridor ɗin ɗakin. Dakyar ta nemi waje ta zauna dan gaba ɗaya jikinta a sanyaye yake, Ba haka suka yi dashi ba, Cewa ya yi akwai dakuna guda biyu a cikin gidan na tsohuwar matarsa ta uku da ya saka sai ta zauna a can. Dan haka koda aka zo jere har dashi aka jera kayan, Su kuma da suka koma babu wanda ya ce mata ga yanda gidan yake.
“Kin yi shiru Khadijah”
Maganar ta dawo da ita daga duniyar tunanin data tafi, Kallon sa ta yi ta ce
“Afwan ban ji bane.”
Murmushi Malam Garba ya yi ya ce
“A'a ba komai ai, cewa nayi ki tashi ki yi sallah”
To kawai ta ce sannan ta miƙe, Kalle-Kallen ɗakin ta dinga yi sai kuma ta ce
“Babu banɗaki ne?”
Girgiza mata kai ya yi yana nuna mata wata yar siririyar ƙofa wadda ta sha tsatsa ya ce
“Ga shi can akwai mana. Ai banɗakin ki da ban babu ruwan ki da sabgar matan gidan” Jinjina kanta tayi sannan ta ajiye mayafinta a gefen kujera ta nufi banɗakin, Ɗan karami ne sosai, Amma a wanke yake sai kamshin hypo ne ke tashi, Dakyar ta iya yin alwalar a ciki ta fito tana yarfe hannu. Sallah suka yi tare sannan ya janyo ledar kazar daya shigo da ita, Ita dai tun da ta ci sau daya bata sake ci ba saboda gaba ɗaya jikinta a sanyaye yake. Ta rasa wane irin hali take ciki, Farin auren Garba, Ko kuma dana sani. Ta rasa dalilin daya sanya ta yarda da auren ma,
“Khadijah lafiya dai?”
Ta tsinkayi muryarsa yana tambayrta. Bata ce komai ba ta tashi ta ƙarasa gaban wardrobe ɗin ta ta buɗe, Wata sabuwar rigar bacci ta dauka, Ya ce zai je cikin gidan ya dawo ta ce to sannan ya fita. Kafin ya dawo har ta gama shirin kwanciya ta zauna gefen gado ta zuba uban tagumi, Washe baki ya dinga yi yana dariya ya ce
“Kin ga yanda ki ka yi kyau kuwa?”
Da kyar ta ƙirƙiro murmushi ta yi masa ta ce
“Na gode sosai.”
Ya girgiza kansa ya ce “Ai babu godiya tsakanin mu Khadijah.”
Ita dai bata sake cewa komai ba, Taga ya nufi banɗaki. Jiki a sanyaye ta kwanta gefen gadon ta rufe idanun ta, Sam zuciyarta ta kasa nutsuwa, Gani take kamar a mafarki. Bayan ya gama shirin kwanciyar sa ya hauro kan gadon, Ta dinga kallon sa ganin yanda yake murmushi, Ita bata taɓa ganin muninsa ba ma irin ranar, tamkar wani naman daji haka take ganin fuskarsa. Babu yanda ta iya dashi haka ta yarda suka kwanta tare, Sai dai abin da Anty Khadijah ta fuskanta shi ne ya ƙara tayar mata da hankali, Bata taɓa sanin akwai irin wannan tashin hankalin ba. Ta inda Allah ya haramta ta nan ya dinga nemanta, Tun tana dauriya har sai da ta sume ba tare da ta san ta yi hakan ba. Shi kuwa ko a jikinsa dan ba yau ya fara hakan ba, Hasalima wannan shi ne tsarin gidan sa!.