Sashe 63
Naanah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Girgiza kai Safwan ya yi kafin ya ce“ban sani ba wallahi, kawai zuwa ta yi ta kirani da daddare ta bani. Ban san wanda ya bata su ba”
Jinjina kai kawai ya yi sannan ya dafa kafaɗarsa ya ce“okay thank you.”
Daga haka ya janyeshi gefe ya fice daga ɗakin, da idanu Safwan ya bi shi sai kuma ya sulale a ƙasa ya fashe da kuka kamar ƙaramin yaro. Yana sauka parlon ya ga ta fito daga kitchen, ganin yana shirin fita ya sanya ta ce“Yaya na ɗora maka abinci ba dai tafiya zaka yi ba?” kallo ɗaya ya yi mata, wanda ya sanyata sunkuyar da kai. Kamar ba zai magana ba sai kuma ya ce
“No need thanks”
Daga haka ya fice daga parlon kamar zai tashi sama. Tafiya ya dinga yi baya ko kallon gabansa, Allah Allah yake ya isa Apartment ɗin su yaje ya samu Zahra.
****
Sultan road, Kano state.
A tsakiyar compound ɗin gidan motar ta yi parking, Drivern ya buɗe ya fito sannan ya zagayo ya buɗe masa. A hankali ya zuro ƙafafunsa waje, yana ƙarewa gidan nasa kallo. Khadijah ta fito da wani irin gudu tana zuwa ta shige jikinsa tana ƙanƙameshi ta ce
“welcome back Dadyyyy!”
Rungumeta ya yi yana murmushi ya ce“Thank you Mimina”
Ta sake zagaye hannayenta a bayansa a shagwaɓe ta ce“Daddy shi ne baka dawo da wuri ba ko?”
Ɗago fuskarta ya yi da hannunsa na dama yana kallonta ya ce“abubuwane suka riƙe ni, kin je Yolan?” girgiza masa kai ta yi kafin ta ce“ai baka dawo ba shiyasa ban je ba. Nanar ma kuma tana nan”
Da ɗan mamaki ya ce“really?”
Ta gyaɗa masa kai dai-dai sanda Mami ta ƙaraso wajen ta kalleshi tana murmushi ta ce“sannu da zuwa Daddy” murmushin shima ya mayar mata kafin ya ce“Yauwa ya gidan?”
“Alhamdulillah ya hanya?" Ta sake tambayarsa. Amsa mata ya yi sai kuma ya mayar da kansa ga Khadijah ya ce“ina ji fasa bikin aka yi data zo?” kafin ta yi magana Mami ta ce“daga zuwanka zata isheka da magana anan, ku shiga ciki mana” tura baki Khadijah ta yi ta ce“to Mami yaushe rabon dana ganshi.”
“Muje ciki sai ki bani labarin” Daddy ya yi maganar yana riƙe da hannunta, to kawai ta ce sannan suka nufi cikin gidan.
Nana na zaune a parlon ta yi shiru idanunta zube akan tv duk da ba fahimtar abin da ake yi take ba suka shigo, ta tashi da sauri tana gyara mayafin rigar jikinta. Sai da ya zauna kan sofa sannan ta masa sannu da zuwa, ya amsa da murmushi a fuskarsa kafin ya ce
“Nana yaushe rabon dana ganki?”
Murmushi ta yi tana sunkuyar da kanta. Ya kalli Khadijah ya ce“zo ki ci gaba da bani labarin” kallon Nana ta yi dake tsaye sai kuma ta zauna gefensa ta ce“tam Daddy” Nana ta dinga kallonsu tana tuna sanda take zama da Abba haka tana masa hira a duk sanda ya yi tafiya ya dawo. Ganin kuka na son kwace mata ya sanya ta yi excusing kanta ta bar parlon da sauri. Mami ta bita da idanu cike da tausayinta sai kuma ta kalleshi ta ce“da dai ka fara cin abinci sai ta baka labarin tunda yana da tsayi” Girgiza kansa ya yi yana murmushi ya ce“ai bana jin yunwa, na sauka a Abuja” to kawai Mami ta ce dan ta san babu abin da zai hana bada labarin kuma. Khadijah ta gyara zamanta ta fara bashi labarin duk abin da ya faru in details, tun daga farko har ƙarshe. Sosai Daddy ya yi mamaki, sannan kuma yaji tausayinta. Ya sauke numfashi yana ganin yanda Khadijah ke hawaye, da kansa ya goge mata hawayen sannan ya ce
“Ya isa haka. In sha Allah komai zai zo da sauƙi Mimi”
Cikin kuka ta ce“Daddy tausayin Nana nake..gaba ɗaya kamar ba ita ba, ko hira bama yi, kullum sai dai ta yi ta kuka. Kuma ta ce tana son ganin Abbanta da Ammarta, amma tana tsoron ta koma gidan Yaya Safwan da Aunty Zahra su nunawa kowa hotunanta.”
Girgiza kai Daddy ya yi ya ce“zata koma in sha Allah, babu abin da zai faru. Kira min ita” to kawai ta ce sannan ta ta miƙe tana shirin barin wajen shima ya tashi ya ce“ko barta. An jima sai muyi magana, let me take a bath” tom kawai ta ce sannan ta nufi saman da sauri. Ya sauke numfashi yana kallon Mami ya ce
“But why baki kirani kin faɗa min ba Amina?”
“Abun ne babu dadin ji. Shi yasa na kasa kiranka wallahi” girgiza kai Daddy ya yi ya ce“a'a wannan ba hujja bace, yanzu duk inda iyayenta suke suna can suna nemanta. Kuma hankalinsu ba zai taɓa kwanciya ba, sannan kuma Allah kaɗai ya san baƙin cikin da suka shiga na guduwarta. Sam bai kamata abar wannan maganar haka ba” shiru Mami ta yi dan ita ta rasa abin cewa, tabbas ta san iyayenta ba zasu ji daɗi ba, to amma da ace sun ga abin da zai ɗaga musu hankali na har ƙarshen rayuwa gara ace iya wannan suka gani. Daddy bai sake cewa komai ba ya nufi hanyar upstairs.
Khadijah na shiga ɗakin ta samu Nana zaune gefen gado ta haɗe kai da gwuiwa sai kuka take a hankali. Jiki a sanyaye ta ƙarasa gabanta ta dafata sannan ta ce“Nana ki daina kuka” kasa ɗago kanta ta yi Khadijah ta zauna gefenta ta jawota jikinta tana kukan itama ta ce“koda da ƙaddararsa a rayuwa, ki ɗauka wannan ita ce ƙaddararki. Kuma komai ya yi farko zai yi ƙarshe, nan bada jimawa ba in sha Allah komai zai shige kamar ba'a yi ba. Dan Allah ki daina kukan nan” Cikin shassheƙar kuka Nana ta ce
“Na sani Mimi. Amma ya zan yi? Zuciyata zafi take min kullum, na kasa yarda da cewa ni ce na zama haka. Na kasa yarda cewa ni ce na bar gidanmu saboda tsoron tonan asiri. Na kasa yarda cewa sir Junaid ya cutar dani, mutumin dana bawa yarda fiye da kowa. Mutumin da nake masa kallon wanda zai zama garkuwata, mutumin dana so nayi rayuwar aure dashi...” taja numfashi ta sauke sannan ta ci gaba da faɗin
“Ya cutar dani Mimi. Ya ruguzamin farin cikina, koda ace babu wanda ya san da wannan maganar a gidanmu da wane ido zan dinga kallon Yaya Safwan? Kullum zai yi tunanin ni ba mutuniyar kirki bace. Wallahi da zuciya ɗaya naje duba shi, ban yi tunanin zai iya aikata haka gareni ba!”
Khadijah ta sake ƙanƙameta tana kuka, ta kasa magana saboda tausayin Nana daya cikata, can dai da kyar ta ce“na sani Nana. Na san ba zaki taɓa aikata irin haka da gangan ba, kuma suma yan gidanku zasu san haka, sai dai kin yi kuskure tun farko, ba'a taɓa bawa namiji yarda, bai kamata ace kin je duba shi dan an ce miki bashi da lafiya ba, wannan ba daidai bane. Koda kuma ya kama dole sai kinje sai ki tafi da wani, amma kin fita ba tare da kowa ya sani ba, sannan kuma kin dawo kin musu ƙarya, iya wannan ya isa Allah ya jarrabeki Nana.”
Lumshe idanu Nana ta yi, hawaye na zubowa kan fuskarta ta ce“sai yanzu nagane hakan, sai yanzu nagane bai kamata na yarda da namiji ba matuƙar ba muharramina ba, ina jin kamar mutuwa zan yi wlh Mimi. Idan na tuna abin da ya yi min sai naji bana son ci gaba da rayuwa, ina ma na mutu na huta kawai...” ta sake fashewa da wani raunataccen kuka. Shiru Khadijah ta yi tana kukan ita ma, after some minutes ta ɗagota tana goge mata hawayen fuskarta ta ce
“Kina ji ki daina kukan, kada ciwonki ya tashi. Bari naje na dawo” gyaɗa mata kai kawai Nana tayi, ta tashi ta fice daga ɗakin da sauri, ita kuma Nana ta kwanta kan gadon a hankali tana lumshe idanunta..
****
A fusace ya tura ƙofar parlon ya shiga, babu kowa a ciki sai tv dake aiki. Ya haura sama kai tsaye ya shige ɗakinta, tsaye ya sameta jikin mirror tana shafa mai, Ya saki handle ɗin kofar da ƙarfi wanda ya sanyata juyowa ta kalleshi.
“Doctor”
Ta ce a sanyaye, ganin yanda yake kallonta ya sanya ta sunkuyar da kanta. Haka kawai taji gabanta na faduwa, ya ƙaraso tsakiyar ɗakin yana ci gaba da kallonta cikin wata murya mai nuna zallar ɓacin ran da yake ciki ya fara cewa
“ashe daman zaki iya haka Zahra? Ashe zaki iya cutar da Nana ban sani ba?”
Da sauri ta ɗago kanta, lokaci ɗaya kuma ta shiga girgiza masa kai da hannayenta ta ce
“wallahi a'a ba zan iya ba doctor, ba zan iya ba, Nana kamar...”
Tsawa ya daka mata wadda ta tilasta ta yin shiru, Ya ɗan kalli gefensa na dama zuciyarsa cikeda tarin ƙunci da bakin ciki, sai kuma ya sake takowa har gabanta yana kallonta cikin ido ya ce“bana son na sake jin wata magana daga bakinki. Kin bani mamaki, koda wasa ban taɓa tunanin zaki iya aikata haka ba Zahra! Ban yi tunani ba, yanda yarinyar ta ɗaukeki tamkar ƴar uwarta wadda take iya fadawa sirrinta ashe ke ba haka ki ka ɗauketa ba. Har zaki iya fitar da hotunan da ki ka san zasu iya lalata mata rayuwa su ɓata mata suna a idon kowa, kin ji kunya!”
Zahra kasa cewa komai ta yi sai kuka da take kamar ranta zai fita, ta durƙushe a ƙasa tana wani irin kuka mai kunji ta ce
“na tuba doctor, wallahi na tuba ba zan sake ba. Ni kaina banso na fitar da hotunan nan ba, domin kamar amana ne Nana ta bani saboda ta yarda dani. Tana ganin ba zan taba faɗawa kowa ba, sai dai...” ta yi shiru saboda kukan daya ci ƙarfinta.
“Sai dai me?”
Ya daka mata wata irin tsawa wadda ta sanyata gigita. Girgiza kanta ta yi still crying ta ce
“Idan ban yi haka ba Siyama ba zata samu Safwan ba, ba zai aureta ba! Shiyasa nayi haka saboda na dakatar da aurensu.”