Sashe 94
Naanah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ya daka mata tsawa. Sosai ta firgita amma hakan bai sa taje inda yake ba, Ta fara tafiya hankali da niyyar fita daga dakin, Cikin yan sakanni ya tashi ya fizgota ta faɗa jikinsa. Kokawar kwace kanta ta dinga yi, sai dai sam ta kasa, saboda ba ƙarfinsu ɗaya ba. Ya matseta a ƙirjinsa yana watsa mata wani irin kallo ya ce
“Kin nutsu ko sai na sake marin ki?”
Ci gaba ta yi da kokawarta tana kuka kamar ranta zai fita, Komawa ya yi ya zauna har sannan bai saketa ba. Ya sanya hannunsa ya rufe mata baki sannan ya ce
“Ki nutsu ki faɗa min me ya faru. Me ta yi miki? Akan me ki ka zageta...”
Ya saki bakinta yana janyeta daga jikinsa, Tashi tsaye ta yi tana kallon sa cike da masifa ta ce
“Bazan nutsun ba, kuma ba zan faɗa maka ba ɗin! ai sanda ka mareni baka tambayi me ya faru ba. Ko ce maka aka yi banida hankali? To wallahi ba zan yarda ba, kuma sai na tafi gidanmu. Wallahi sai na faɗawa Abbana!...”.
Ta ƙare maganar tana sakin wani sabon kukan, da mamaki ya dinga kallonta dan tun da yake da ita bata taɓa faɗa masa magana irin haka ba. Ya miƙe tsaye yana kallonta ya ce
“Ni? Ni ki ke cewa ba zaki nutsu ba? Ni ki ke yiwa ihu aka?”
Ɗora hannayenta ta yi akan ƙugunta tana kallon sa idanunta babu alamar shakka ko tsoro ta ce
“Eh kai ɗin!”
Wani irin gudu ta saka ganin ya yo inda take, ta shige banɗaki ta murɗa key ɗin ta bar shi a jiki. Tsayawa ya yi a wajen yana kallon ƙofar toilet ɗin, Ya daɗe tsaye a wajen sai kuma ya juya ya fice daga ɗakin. Sai da ta tabbatar da ya tafi sannan ta buɗe ƙofar, Ta fito da gudu ta rufe ƙofar ɗakin ta saka key ta bar shi a jiki, sannan ta koma ta zauna gefen gadon ta kifa kanta akan cinyoyinta ta fashe da wani sabon kukan.
Washegari da safe ta shirya cikin wasu riga da wando na jeans da t-shirt, ta ɗaura after dress akai ta ɗauki jakarta ta fito. A parlour ta same su suna breakfast, Ko kallon inda suke bata yi ba ta nufi ƙofar fita daga parlon, Zahra ta bita da kallo sai kuma ta taɓe baki. Tashi ya yi yana shirin barin wajen, Ta ajiye pork ɗin hannunta ta ce“A'a ina zaka je?” bai bata amsa ba ya juya yabi bayan Nanar, Zahra ta bisu da kallo sai kuma ta ɗauke kanta. Can ya hangota tana tafiya toward direction ɗin fita daga first gate ɗin, Yabi bayanta da sauri har ya kamota, Janyo hannunta ya yi yana kallonta fuska babu walwala ya ce
“Ina zaki je?”
Kallon sa ta yi, sai kuma ta janye hannunta daga nasa ta ce“makaranta.” daga haka ta juya ta ci gaba da tafiya. Abdusammad ya dinga kallonta cike da mamaki, can dai ya sake bin bayanta ta fizgota wannan karon babu alamar wasa ya ce
“Daman haka ki ke tafiya makarantar? Kin fi abinci?"
Tuni hawaye ya fara wanke fuskarta, Ta fizge hannunta ta ce“Ni bana so abincin naku. Ba zan ci ba, kuma bana son a kai ni makarantar, bana buƙatar taimakonka, ka rabu dani!”
Ta ƙare maganar a fusace. Kasa cewa komai ya yi, ganin tana sake shirin barin wajen ya fizgota ta faɗa jikinsa, kuka ta saka tana dukansa. Ya matseta a jikinsa yana kallon ta ya ce
“Ni ki ke yiwa rashin kunya ko? Zan yi maganin ki.”
Daga haka ya fara tafiya da ita har suka fita daga gate ɗin, Kafin ya ƙarasa wajen parking space ɗin guards dake zazzaune suka taso suka nufo wajen, Ya miƙa ma drivern hannu ba tare da ya ce komai ba. Ya gane mai yake nufi dan haka ya miƙa masa key ɗin, Ya ƙarasa gaban wata Rolls-Royce fara ƙal ya danna key ɗin nan take ta yi ƙara. Passenger seat ya buɗe ya zurata sannan ya mayar ya rufe, Ya zagaya ɗaya side ya buɗe ya shiga. Sai da ya yi warming motar sannan ya yi reverse ya fice daga gidan.
Har suka kusa zuwa Columbia babu wanda ya ce komai a cikinsu, Barin ma Nana data juya kanta gefe ɗaya tana kallon titi. Dan tun bayar wayar da suka yi da Anty Ramlah ta faɗa mata yanda zata yi bata sake ɗaga hankalinta ba. A gefen titi ya yi parking sannan ya sauka daga motar, ita dai inda yake bata kalla ba ballantana ta yi masa magana. After 10mins ya dawo hannunsa rike da leda, Ya ɗora mata kan cinyarta sannan ya yi wa motar key suka ci gaba da tafiya. Har suka ƙarasa makarantar Columbia ɗin, A parking space yayi parking, Ta buɗe motar tana ƙoƙarin fita taji ya ce
“Make sure kin ci abinci, and when zaku tashi?”
Bata kalleshi ba tana ƙoƙarin ɗaukan jakarta ta ce“2:00pm.” ta ce tana sauka daga motar, Da idanu kawai ya bita sai kuma ya girgiza kansa yana murmushi. Ita baya yarda ba fushi take yi, Sai da yaga ta nufi department ɗinsu sannan ya juya ya bar school ɗin. Nana na shiga class ta samu ƙawarta Surry wadda ita ma yar Nigeria ce take zaune da mijinta a new York ɗin, Ɗaga mata hannu ta yi Nana ta ɗan yi murmushi sannan ta ƙarasa inda take. Zama ta yi gefenta, Surry ta janye glasses ɗin dake idanunta, Fara ce tas kuma kyakkyawa ta sakar mata murmushi ta ce
“Yau baki makara ba Nana? Ko Uncle ne ya kawo ki?”
Ta yi tambayar cike da zolaya, dan kusan kullum tana bata labarin uncle yafi sau 20. Nana ta gyaɗa mata kai fuskarta babu walwala ta ce“Eh, na tashi da wuri ne yau.” Surry ta yi shiru tana nazartar yanayinta, can kuma ta ce“what's wrong Nana?” Bata ji abin da ta ce ba, saboda tunanin data fara. Surry ta taɓata ta ce
“Nana...”
Kallon ta ta yi tana murmushi, Surry ta sake cewa“meke damunki?” Girgiza mata kai Nana ta yi tana ƙoƙarin kawar da zancen ta ce“ba komai fa. Kawai bana jin daɗi ne, Dr Makh bai shigo ba?” Surry ta taɓe baki ta ce
“Ina tambayar ki wani abun kina faɗan wani abun, Ƙarya ne ki ce babu abin da ke damunki Nana. Ba haka ki ka saba zuwa makaranta ba, and what's wrong with ur face? Wane ya mareki” sai a sannan Nana ta kai hannunta kan kuncinta, bata yi tunanin tabon bai baje ba dan bata kalli madubi ba ta fito. Surry ta kamo hannunta ta ce“Tell me meke damunki?” Sake girgiza kai Nana ta yi dan ko kaɗan bata son ta fitar da sirrinta, Ta buɗe jakarta ta ɗauko water bottle dinta ta buɗe ta sha ruwan sannan ta ce
“Babu komai fa, kawai mun ɗan samu saɓani ne da kishiyata.”
“Shi ne ta mareki?”
Surry ta yi tambayar tana kallon ta, girgiza kai Nana ta yi, lokaci ɗaya hawaye ya fara zubowa kan fuskarta, cike da ƙunci da baƙin ciki ta ce
“Uncle ne ya mareni...”
Ta ƙare maganar kuka na kwace mata. Surry ta kalli ɗaiɗaikun student ɗin dake shigowa da basu shige mutun uku ba, sai ta matso kusa da ita sosai ta rike hannunta dake kan fuskarta ta ce
“Saboda ita ya mareki? Me ki ka mata?”
Girgiza kai Nana ta yi tana kuka ta ce
“Ita ta fara zagina, ita ce ta fara tsokanata. amma kuma ita bai daketa ba, ni kaɗai ya daka, wallahi bana son auren nan, bana son zaman nan, gidanmu zan tafi. Ni ba zan koma ba!”
Surry ta ɗan girgiza kanta tana kallon ta cike da tausayawa, zata bawa Nana kusan 3yrs dan ta fita wayo sosai duk da girmansu ɗaya. Ta sanya hannunta ta fara goge mata hawayen kafin ta ce
“Idan ki ka bar gidan sai ki je ina?”
Nana ta buɗe jakarta ta zaro passport ɗinta har da visanta ta ce“Gida zan tafi. Ba zan zauna ba, ni bana son auren, bana son uncle.”
Surry ta yi shiru can kuma ta ce“Idan ki ka tafi kin bar mata gidan kenan? Kin yarda ta ci nasara ta koreki? Unbelievable, Ba haka ya kamata ki yi ba. Dole ki zauna a gidan dole ki nuna mata kece amarya kuma mijinta na sonki, Wallahi Nana uncle ɗin nan yana son ki, kuma kema kina sonsa. Kawai kuna wahalar da kan ku ne, Ki bari a tashi zan faɗa miki duk yanda zaki yi, da kansa zai dawo ya baki haƙuri.”
Nana ta sake goge hawayenta sannan ta ce“Baya sona wallahi, uncle baya sona. Alfarma ya yimin nida iyayena ya aureni, ba dan yana sona ba. Kin taɓa ganin amaryar da mijinta bai damu da ita ba? Ko sanda aka kaini gidansa babu ruwansa dani, baya kwana a ɗakina, a haka har kwanana ya ƙare. Kuma koda muka zo nan bai taɓa kwana a ɗakina ba, sai dai duk ranar da nake da girki naje ɗakinsa na kwanta, ita kuma duk ranar kwananta har daƙinta zai bita. Gaba ɗaya baya sona, idan nayi waya da sisters ɗina suna bani labarin yanda suke zaune da sauran yayyenmu, kowacce mijinta na sonta kuma yana kulawa da ita, duk da ba auren soyayya bane. amma ni a nan....”
Ta yi shiru saboda kukan da yaci ƙarfinta, Surayyah da taji tausayinta ya rufeta ta jawota jikinta, Nana ta ci gaba da kuka kamar ranta zai fita.
****
Nigeria.
Aunty Khadijah ce zaune bayan ta idar da sallar magriba, wayarta dake kan gado ta fara ringing, zare hijabin ta yi sannan ta hau kan gadon ta janyo wayar. Sabuwar lamba ta gani, dan haka ta ɗaga ta ce
“Assalamu alaikum.”
Daha ɗaya ɓangaren ya gyara tsaiwarsa ya ce
“wa'aiki assalam da Khadijah, kina lafiya.” sosai ta ɗau muryarsa, amma madadin ta fusata sai ta samu kanta da yin murmushi ta ce
“Ina nan kalau Alhamdulillah.”
Ya jinjina kai sannan ya ce
“Daman ina ƙofar gidanku ne, nazo mu ɗan zanta.”