← Book details Naanah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 85 OF 125

Sashe 85

Naanah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“What?”

“ƙafan uncle, zafi take min. Wallahi ba zan iya tafiyar ba”

Da buɗe idanunsa ya yi kamar ba zai magana sai kuma ya ce“To sai ki yi ya ya?”

“Ka goyani.”

Ta ce a shagwaɓe. Harararta ya yi ya ce“Abokin wasanki ne ni?. C'mon my friend!”

Madadin ta tawo sai kawai ya ga ta nemi waje ta zauna, ta harɗe ƙafafunta ta fara kuka a ƙarfi. Baki buɗe yake kallonta, ganin tana son tara masa jama'a ya sanya ya ɗan durƙusa dai dai tsayinta ya ce“Tashi muje mana, zan siya miki abin daɗi.”

Maƙale kafaɗa ta yi kafin ta ce“a'a ni sai ka goyani...” Ya jima yana kallonta ganin yanda ta yi da fuska kamar jaririya, agogon hannunsa ya kalla ganin dare ya fara yi ya sanya ya ɗan yi tsaki. Sannan ya juya mata baya ba tare da ya ce komai ba, Jin ta yi shiru ya sanya ya ce

“Kin hau ko sai nayi tafiyata?.”

Da sauri ta mike ta tattare rigarta ta hau bayan nasa, Ya mike tsaye yana rike da ita. Hannayenta ta sanya ta zagaye wuyansa, Ta ɗora kanta akan faffaɗan bayansa tana dariya. Yana jin ta amma bai ce mata komai ba, Sun yi nisa sosai ta ɗan leƙo fuskarsa ta ce

“Uncle.”

“Uhm” ya ce yana ci gaba da tafiyarsa.

“To da kana goya Anty Zahra?”

Shiru ya yi yana tunanin dalilin tambayar, Can kuma ya girgiza kansa ya ce“A'a.” dariya ta sake yi ta koma ta yi lamo a bayansa sannan ta ce“yauwa Uncle ɗina, ai ni kaɗai ka ke so ko?” shiru ya yi mata gudun ya bata amsa ya zama fitina. Bata damu da rashin amsawar da ya yi ba ta ce

“Ita kuwa Maimoon Yaya Aliyu baya goyata. Kuma ma ita cikine da ita” ta ƙare maganar tana tuntsirewa da dariya, Duk yanda yake jin ransa a dagule bai san sanda ya yi murmushi ba. Ya girgiza kansa bai ce komai ba. Suna zuwa bakin ƙofar ya ce“sauka!” ta sake ƙanƙameshi a shagwaɓe ta ce“ni sai ka kai ni sama.” girgiza kansa ya yi ya ce“sauka na ce!” Ta sake maƙale kafaɗa tana kwanciya a bayansa. Wata azabbabiyar tsawar daya daka mata ce ta sanya ta sauka daga bayan ba shiri. Ta nufi cikin gidan da gudu tana kuka, Tsaki ya yi sannan ya shiga parlon. Zahra na zaune akan sofa ita da Noor, Ta yi masa sannu da zuwa ya amsa sannan ya ƙarasa ya ɗauki Noor ya ɗorata a cinya, Kama gemunsa ta yi wanda ya zame mata dabi'a ta ce

“Abbie gobe zamu tafi?”

Jan kumatunta ya yi ya ce“Yeh!”

Ta yi dariya har sai beauty point ɗinta suka loma sannan ta ce“yauwa Abbiena ɗan albarka. Daman ina son naje naga su Abeeha” Murmushi shima ya yi ya ce“tom zaki gansu nan kusa. Muje ki kwanta kin ga da wuri zamu tafi ko?” gyaɗa masa kai ta yi ya miƙe da ita a hannunsa suka nufi sama, Zahra ta bi su da kallo.

Nana na shiga daƙinta ta faɗa kan gado ta fashe da kuka har sannan jikinta bai daina rawa ba, Ba'a taɓa yi mata tsawar data gigitata irin wannan ba. Ta dunƙule waje ɗaya tana ci gaba da kukanta a haka har bacci ya ɗauketa.

Around 10:20 na dare aka fara knocking ƙofar, Da mamaki ya dinga kallon ƙofar sai kuma ya janye laptop ɗin dake gabansa ya miƙe ya nufi ƙofar ya buɗe. Tsaye ya gan shi a wajen, Bai ce komai ba ya matsa daga wajen ƙofar. Safwan ya sauke numfashi sannan ya shigo ciki, komawa Abdusammad ya yi ya zauna kan kujera yana jiran ya ji abin da zai ce. Jiki a sanyaye Safwan ya zauna kujerar dake kusa da ta sa, Ya sunkuyar da kansa. Sun ɗauki mintuna a haka kafin Abdusammad ya ce

“Idan baka da abin faɗa zan tashi.”

Sauke numfashi Safwan ya yi kafin ya ce

“Na san na aikata ba dai-dai ba Yaya. Amma ina da hujjata ta yin haka, kuma Hujjar ta kai na aikata haka. Domin abin da nayi shi ne dai-dai, Na san babu wanda zai fahimceni a cikin su, amma ina da tabbacin kai zaka fahimta shiyasa na zo wajenka Yaya.”

Safwan ya yi shiru yana kallon Abdusammad, Da ɗan mamaki Abdusammad ya ce

“Hujja! Safwan mene hujjarka? Akan me zaka sake ta? Me ta yi maka? Ka san halin daka saka mutanen gida?. Ka san me Hajiya ta ce akan haka? Akan me zaka yi abu babu neman shawara?”

Tuni hawaye suka fara wanke masa fuska, Ya tashi ya dawo kujerar da Abdusammad yake ya tsuguna a wajen, ya ɗora hannayensa akan cinyarsa cikin kuka ya ce

“Yaya bani da wata mafitar ne. Ba zai yiwu na ci gaba da zama da Haule ba, Yaya ina da cuta mai karya garkuwar jiki wato HIV! Ta ya zan iya zama da ita a haka?”

Abdusammad bai san sanda ya ture shi daga jikinsa ya miƙe tsaye ba. Fuskarsa ɗauke da mabayyanin tashin hankali ya ce

“What! Me ka ce Safwan? Hiv kamar ya ya? Yaushe kuma a ina ka samu cutar!?.”

Abdusammad ya jera masa tambayoyin yana tsare shi da idanu. Jan numfashi Safwan ya yi kafin ya ce

“A sanda na auri Siyama. Ita ce wadda take ɗauke da cutar ta shafa min ba tare da ita ma ta san tana da ita ba. Ita kuma Haule bata da ita, saboda na kira likita ya gwada ya tabbatar min da bata da cutar, shiyasa na saketa saboda kada na cuceta!”

Ya ƙare maganar tana fashewa da wani raunataccen kuka. Durƙusawa Abdusammad ya yi ya ɗago shi yana kallon sa ya ce“Ita Siyaman take da Hiv? How? A ina ta samu?”

Girgiza kai Safwan ya yi kafin ya ce

“Nima bana ce ba Yaya. Amma kawai abin da na sani ban samu Siyama a matsayin budurwa ba, Wannan ke nuni da cewa a wani wajen ta shafa itama. Saboda haka idan har ina son na zauna lafiya dole na rabu da Haule, bana son na cutar da ita, bana son na shafa mata. Wallahi shiyasa na saketa ba dan wani abu ba Yaya!”

Girgiza kai Abdusammad ya yi cike da mamaki da kuma tashin hankali ya ce“to ta ya ita Haule bata shafi cutar ba? Ko kana son ka ce bata da iddarka?” Girgiza kai Safwan ya yi still crying ya ce

“A'a tana da ita. Saboda Haule ce ta fara tarewa kafin Siyama, Bayan Siyama ta zo sai naji bana son mu'amala da Haule, bana son ta zo inda nake. Wannan dalilin ya sanya na ƙaurace mata, Sai daga baya kuma na gano ina da wannan cutar shi ne ya sake sakawa na bar ta din. Na san zaka fahimceni Yaya, wallahi tallahi bani da niyyar cutar da rayuwar Haule, kuma bani da niyyar bijirewa gidanmu, na ɗauki wannan ɗin a matsayin Ƙaddara! Wadda ba zan iya guje mata ba.”

Rungumeshi Abdusammad ya yi yana shafa kansa, Safwan ya sake fashewa da wani matsananci kuka. Shi kansa Abdusammad ɗin kukan yake, saboda Safwan na ɗaya daga cikin abin da yafi soyuwa a gare shi. Yana son sa tun yana ƙarami, ƙaunar da yake masa ya sanya ya mayar dashi ɗan ɗakinsa, musamman daya kasance suna kama da juna. Koda wasa bai son yaji an ce wani abun ya sameshi yanzu zaka ga hankalinsa ya tashi, A yanzu kuwa sai yaji kamar shi ne ƙaddarar ta faɗawa. Sun daɗe a haka kafin daga bisani Abdusammad ya ɗago shi ya shiga goge masa hawayen fuskarsa ya ce

“Shikenan na gane, kuma na fahimceka Safwan. Kada ka damu komai zai zo da sauki, zan saka a ɗoraka akan magani sai ka dinga zuwa US check up. Saboda haka ka kwantar da hankalinka, and zan faɗa musu yanda zasu fahimta. Duk da gobe da wuri zan tafi, bayan sallahr asubah zamu yi magana dasu, Kada ka damu kaji. Abin da ka yi shi ne dai-dai, Allah ya baka da lafiya”

Sake rungume shi Safwan ya yi kafin ya ce“Amin Yaya. Nagode sosai, dan Allah ka ce duk su yafe min, ji nake kamar mutuwa zan yi Yaya”

Girgiza kai Abdusammad ya yi yana shafa bayansa ya ce“In ji wane? Ka taɓa jin cuta ta kashe mutum? Sai dai kwanansa ya ƙare. Saboda haka bana son na sake jin makamanciyar wannan maganar a bakin ka kaji!”

Gyaɗa masa kai ya yi, Ya yi shiru suna sauke numfashi.

Daren ranar kasa baccin kirki Abdusammad ya yi, gaba ɗaya ji ya yi duniyar tayi masa babu daɗi. Dan haka ya dauro alwala ya fara sallar nafila har aka fara kiran sallar asuba. Bayan sun fito daga masallaci ya sanya suka tsaya, Ya kuma yi musu bayani yanda zasu fahimta. Sosai jikin su ya yi sanyi Abba ya ce

“Abin da ya yi shi ne dai-dai. Allah ya gajarta walaha, In sha Allah zamu yi magana da Hajiya Babba gobe.” Jinjina kai Abdusammad ya yi sai kuma ya ce“Yauwa Abba, ni ka ga da wuri zan tafi. Amma in sha Allah nan bada jimawa ba zan zo” A haka suka rabu kowa ya yi hanyar gidansa jiki a sanyaye. Yana komawa ya nufi ɗakin Nana, Koda ya shiga zaune ya hangeta jikin gado sanye da hijabi. Ya ƙarasa ciki ya zauna gefen gadon yana kallon ta, Bayan ta abin da take ta tashi ta naɗe laddumar sannan ta nufi can ƙarshen gadon ta zauna jiki a sanyaye ta ce

“Ina kwana?.”

Shiru ya yi bai amsa ba, Ta sunkuyar da kanta tana wasa da fingers ɗinta. Ya dade yana kallonta kafin ya ce“zo nan.”

Komawa kusa da shi ta yi ta zauna kanta a ƙasa. Ya ɗan yi murmushi ganin yanda ta nutsu kamar ba ita ya ce

“mene ne? Haushina ki ke ji?”

Girgiza masa kai ta yi, Ya jawota jikinsa ya ce

“Shikenan ba zan ƙara ba. Kin ji Nanata”
Chapter 85 · 0% Book details