← Book details Naanah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 123 OF 125

Sashe 123

Naanah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Kin ji na yi miki magana akan ki daina abin da ki ke? Kin ji nace Nana bari? Ai bana so ki bari. So nake ki ci gaba, Ki ci gaba da duk abin da ki ke, Ba dai burin ki hankalina kada ya kwanta ba? Ba dai burin ki ki dinga sakani damuwa ba? To ki je ki ci gaba. Zan auro wadda zata dinga jin maganata, Ta kuma dinga girmamani. Ki je ki yi abin da ki ke ganin ya dace da rayuwarki!”

Haba ai ji ta yi kamar ta faɗi ta mutu saboda baƙin ciki, Ta saki wata irin ƙara tana ƙoƙarin yin baya, Cikin zafin nama ya tarota gudun kada ta faɗa kansa, Ya jawota jikinsa jin ta daina numfashi. Kumatunta ya dinga taɓawa yana cewa

“Ke Nana! Nana! Open ur eyes. Nana! Mamanaa. Mamanaa! Open ur eyes kin ji, Da wasa nake miki, I'm just kidding, Ba zan auro wata ba, Stay still kin ji.”

Ko kaɗan Nana bata jin abin da yake cewa dan tuni ta sume a wajen, Ya kwantar da ita ya tashi cikin tashin hankali ya fice daga ɗakin, Da sauri ya dawo hannunsa riƙe da gorar ruwa mai sanyi, Ya buɗe ya yayyafa mata. Wata irin ajiyar zuciya ta sauke tana wani irin numfarfashi, Ya ajiye ruwan a ƙasa ya hau kan gadon ya ɗauketa ya riƙeta a jikinsa. Ganin tana ƙoƙarin tashi ya sanya ya sake riƙeta ya ce

“Stay still kin ji, Da wasa nake miki. Babu abin da zai sa na sake aure”

Fashewa ta yi da wani raunataccen kuka,Ta ɓoye fuskarta a jikinsa cikin kuka take fadin

“Dan Allah uncle kada ka sake auren wata, mutuwa zan yi wallahi. Ka bari uncle ka ji,ba zan sake ba, ba zan kuma yi ba!”

Gyaɗa mata kai ya dinga yi dan tausayi ta bashi, Ya shafa kanta ya ce

“shikenan na haƙura Nana. Dama tuni na haƙura, baki ga ban miki faɗa ba? Na haƙura kinji. But ki saka a ran ki uncle ba zai taɓa kin ki ba, Ina son ki Nana! Ina son ki tun kina tsummanki, Ina son ki tun ranar da Amma ta haifeki, Da a lokacin na samu dama tuni zan aure ki Nana, Kawai nayi shiru ne saboda kada a ga son zuciyata. Na rayu da soyyarki Nana, a rashin ki na auri Zahra, kullum da tunanin ki nake kwana nake tashi, Aliyu ne kaɗai ya san abin da ke zuciyata, Shiyasa sanda na samu labarin aure ku na je Nigeria da tunanin yanda zan yi na mallake ki. Da yake Allah ya hukunta ina da rabon auren ki sai ya kawo wancan hatsaniyar, amma har na fitar da rai Nana. To ya za'a yi na ce bana son ki kuma? Ya za'a yi na ce haka Nana? Nafi kowa son ki, ko Abba sai da ya gane haka. Ina son ki sosai Nana, Sannan cikin da ke jikin ki babu abin da ya kara min illa ƙaunar ki, Ban taɓa son abu kamar yanda nake son ki ba Nana. Komai naki burgeni yake, Shirmenki, Wasan ki, Shagwaɓar ki, Tsiwar ki da kuma kukan ki. Ina son komai naki Nana, Ina son ki , Uncle na son ki! Uncle na son ki sosai Nana.”

Ji ta yi kamar zuciyarta zata fito, ta rasa wane irin hali take ciki, Farin ciki ko kuwa baƙin ciki, Ta kasa magana sai kuka da take kamar ranta zai fita. Ɗago fuskarta ya yi yana goge mata hawayen ya ce

“Ki yarda da uncle Nana, Duk abin da nake miki ba wai ina yi bane dan na cutar da ke. A'a ina yi ne saboda naga kin zama mutum, Idan da ta ni ne babu ruwana, Zan zauna da ke da halin ki wallahi. Amma jama'a nake ji Nana, Ina son ki zama mutum ki shiryu ki daina wasu abubuwan, Na yarda ki dinga yiwa uncle. Amma da zarar kin fita ki zama babbar mace, Matar minister of health Doctor Abdusammad M Shuwa, ki zama yarinyar kirki Nana.”

Gyaɗa masa kai kawai ta dinga yi tana shessheƙa kuka, Ya ɗan yi murmushi ya ja kumatunta ya ce

“My cry cry baby, Mamana sarkin kuka”

Hannunta ta saka ta rufe fuskarta, Ya ɗauke kansa yana dariya. Sun ɗauki mintuna a haka kafin ta ce

“Uncle”..

“Na'am Anty...”

Ya faɗa a sigar da ta yi maganar, Tura baki ta yi ta ce

“To nima ai ina son ka fa. Kuma ma shiyasa na ce bana son Yaya Sultan fa, Har muka yi faɗa da Amrah da ta ce tana sonka. Ai nima ina son ka, Shiyasa nake zuwa Apartment ɗin ku na zauna saboda na ganka. Kuma shi ne kai baka sona, kafi son Anty Zahr...”

Caraf ya kame bakin maganar da nasa, Ya fara kissing ɗinta cikin salo mai rikita wanda ake yi wa, Tuni suka fara hargitsa nutsuwar kansu. Muryarsa na rawa ya ce

“Nana i love you, I love you so much. I can't do without you, Please Nana kada ki bar ni, Ki so uncle ɗin ki. Ki yi min wannan alfarmar, Kada ki bar ni Mamana!”

Cikin kuka ita ma ta ce

“Toh uncle, Nima ina son ka ai, Kuma ina sonka sosai. Ina son komai naka uncle, Nafi sonka wallahi, Nafi Hajiya Babba son ka, Nafi Yaya Aliyu da Abba son ka. Ni kaɗai nake son ka Uncle ɗina!.”

Ta ƙare maganar tana sakin wani marayan kuka mara sauti, Bai ce komai ba ya mai da bakinsa cikin nata yana kissing ɗinta as if his life depends on it. A daren ranar sun yi kamar su cinye junansu saboda ƙauna, Duk wani sirri da ke ɓoye sai da suka faɗawa junansu, Daga ƙarshe ta shige jikinsa tana sakin wata irin ajiyar zuciya mai nuna kwanciyar hankalin da take ciki.

****
Ranar wata talata suna zaune cikin ɗakin Siyama na kallon Anty Khadijah da ke faman kuka, Umma da ke zaune kan farar kujera ta roba sai jan carbin hannunta take ta girgiza kanta ta ce

“Khadijah ba zaki daina kukan nan ba? Ba zaki fawallawa Allah komai ba?”

Anty Khadijah ta girgiza kanta tana hawaye ta ce

“Umma na kasa, Zuciyata zafi take min, Umma ya zan yi da hakkin mutane? Ya zan yi Umma? Da wane ido zan dubi ubangijina? Na rasa wane irin tunani ma zan yi. Na cutar da ƴar uwata ta jini, Na rabata da gidan mijinta da kuma ƴarta saboda son zuciya irin tawa, Na cutar da ƴar dana haifa da kaina na kai ta inda aka lalata rayuwarta, wace irin uwa ce ni Umma? Wace irin zuciya gareni!”

Ta ƙare maganar tana sakin wani sabon kukan. Gaba ɗaya kuka suke, Zahra, Siyama, Safeena da kuma Amal. Umma ma daurewa kawai take saboda ƙarfin zuciya irin nata, Ta girgiza kanta zuciyarta cike da tausayin ƴar tata ta ce

“Ki gode Allah da ubangiji ya baki ikon ganin kuskuren da ki ke aikatawa, Ya kuma hukunta ki tun a duniya. Tabbas kina da rabon rabauta ne, Ba dan haka ba babu yanda za'a yi ki gane laifukan da ki ke aikatawar, Sai lokaci ya ƙure miki, A sanda babu damar da zaki gyara kuskuren. Amma a yanzu kina da wannan damar, Kuma kin nemi yafiyarta ta yafe miki, Allah ba zai kama ki da haƙƙinta ba, Ki ci gaba da istigfari na sauran laifukan da ki ka yi, Ba'a yanke tsammani da rahamar ubangiji, Allah mai yafiya ne. Kuma idan ya yafe baya kallon bawansa da abun, Mutum shi ne wanda yake cewa ya yafe kuma ya ci gaba da kallon ka da abun, Shi ko ubangiji idan ya yafe ya yafu. Ki ci gaba da tsarkake zuciyar ki, Ki kuma yi tuba na zahiri, Kada ki bari sheɗan ya sake cin galaba akan ki”

Sosai jikin kowa ya yi sanyi, Anty Khadijah ta amsa da to tana ci gaba da kukanta. Washegarin ranar aka sallameta daga asibitin, Duk da bata takawa sai dai a wheelchair, Koda suka dawo gida Siyama ce ke zama a daƙinta. Itama gaba ɗaya ta sukurkurce kamar ba ita ba, Ta yi baƙi ta rame, Ko ba'a faɗa ba an san ciwo ne yake ɗawainiya da ita. Duk da bata wasa da karbo magani, Cikin satin basu sami zama ba, Domin a cikin sa ne aka ɗaura auren Zahra da Bashir, Da kuma Safeena da Kamal. Kasancewar auren zumunci ne duk ya sanya ba'a yi wani taro ba, Zahra da kanta ta kira Abdusammad ta faɗa masa zata yi aure, Sosai ya yi mata murna. Ya kira Umma ya yi mata murna ita ma, Sannan ya tura 5m account ɗin Zahran ya ce ta bawa Umma, Godiya sosai suka yi masa, Aka sha shagalin biki kowace aka sadata da ɗakin mijinta, Gidan ya rage daga Anty Khadijah, Siyama sai Umma, Dan Amal ta koma makaranta. Kusan kullum haka zaka gansu a zaune sun zuba uban tagumi, Basu da aiki sai tunane-tunanen rayuwa, Umma ce ke kwantar musu da hankali wani lokacin, Tana faɗa musu komai me wucewa ne. Ranar da aka zo aka faɗawa Anty Khadijah Kaddu ta haukace kwana ta yi tana kuka, Sai a sannan ta sake gane girman laifin da suka yiwa Allah, Kaddu ta bata tausayi ba kaɗan ba, Duk da itama abar a tausayawan ce amma gara ita da hankalinta. Nakasa kawai ta samu, kuma tana ƙoƙarin mai da kanta mutuniyar kirki, Ana idar da sallahr asuba Umma ta shigo ɗakin tana kallon ta, Zaune take kan dadduma sai kuka take bayan ta idar da sallahr. Umma ta ƙarasa ta zauna gefen ta tana kallon ta ta ce

“Ki daina wannan kukan Khadijah, Ki mai da duk al'amuranki ga Allah, Ubangiji na son ki da rahama, Ki manta da abin da ya wuce.”

Cikin kuka ta ce

“Umma wani iri nake ji, Da Allah yaso da yanzu ina tare da Kaddu mun haukace ko? Na shiga ukuna, Umma dama na mutu, Dan Allah ki yafe min duk abin da nayi miki. Ki yafe min Umma”

Ta ƙare maganar tana ɗora kanta kan cinyar Umman, Girgiza kai Umma ta yi ta ɗora hannunta akan ta ta ce
Chapter 123 · 0% Book details