← Book details Naanah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 125

Sashe 39

Naanah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Nana tun da nake ban taɓa miki kallon wadda watarana zan iya aura ba, na yi tunanin za ki ci gaba da kasancewa ɗaya daga cikin ƙannena, sai dai babu wanda ya san abin da zai faru gaba, ban yi tunanin irin wannan lokacin zai zo ba, da har za'a haɗani aure dake, duk da yarintar ki.” ya ɗan numfasa sannan ya ci gaba da faɗin “sai dai a wannan yan kwanakin ina ganin komai kamar mafarki, tamkar ba gaskiya ba, har yanzu zuciyata ta kasa yarda cewa kece wadda zan aura, ta kasa aminta da hakan, gani nake kamar za'a fasa auren nan.” ya ƙare maganar yana kallonta to see her reactions. Nana da ke kallonsa tun ɗazu ta ɗan janye idanunta tana kallon fararen kyawawan faratanta muryarta a sanyaye kamar koda yaushe cikin kwanakin nan ta ce

“nima haka Yaya, kullum gani nake kamar ba gaske ba, ji nake kamar za'a ce an fasa aurena da kai, but u no what?”

Ta yi maganar tana kallonsa, girgiza kansa ya yi yana ɗan ƙara gudun da yake, ta sauke numfashi sannan ta ce“i wish a ce an fasa ɗin, cause am not ready to get married, ban shirya zama matar gida ba, I'm too young to carry that burden..” ta yi shiru jin kuka na neman kwace mata, Safwan ya dinga kallonta fuskarsa ɗauke da wani irin yanayi mai wuyar fassaruwa, ya kasa tantance abin da yake ji game da ita a wannan lokacin, tausayi ne? Ko kuwa soyyaya ce?. Ya sauke nannauyar ajiyar zuciya yana ɗan faɗaɗa fuskarsa ya ce“kamar dai ni Nana, sai dai ni ba wai ina son a fasa aurena bane, a'a ina son nayi aure da wata ne bake ba?”

Da sauri ta kalleshi fuskarta ɗauke da mamaki gami da farin ciki, ta ɗan girgiza kanta ta ce“da gaske Yaya? Baka sona? Baka son ka aureni? Are ur sure?”

Girgiza kai Safwan ya yi yana kallon titi ya ce“that was not what i meant, ba wai bana sonki bane Nana, ina sonki, akan me zan ce bana son ki? Look at you, babu namijin da zai ce baya son yarinyar kamar ki, ga kyau ga hankali sannan ga nutsuwa, kina da qualities daya kamata ace an so ki saboda su, dan haka ba wai bana son ki bane, a'a kawai dai akwai wadda zuciyata ke ƙauna, wanda a yan kwanakin nan nake jin idan bada ita ba bazan iya rayuwa ba, ko bacci nake sai na farka na yi tunaninta, idan dare ya yi burina gari ya waye naje na ganta. And you know what?”

Ta girgiza kanta tana sake gyara zamanta, numfasawa ya yi ya ce“duk wannan son da nake mata bai kai rabin wanda take min ba, tana sona fiye da yanda nake sonta, but unfortunately we two can't be together!” ya ƙare maganar jiki a sanyaye babu wani kwari.

Girgiza kanta ta yi a hankali tana kwaɓe fuskarta kafin ta ce“ayyah Yaya sorry kaji, to mene ya hanaka ka faɗawa kowa ita ka ke so?” ɗan murmushin ya yi ya ce“idan na faɗa ma ba zai wani amfani ba, babu wanda zai ɗauka maganata serious balle har a dubata, kawai na yanke shawara araina ne” Nana ta dinga kallonsa sai kuma ta ce“mene shawarar?”

“Idan na aureki daga baya saina aureta as a second wife” ya yi maganar da zallar gaskiyarsa dan shi sam ƙarya bata daga cikin layinsa.

Kallonsa kawai Nana ta dinga yi lokaci ɗaya jikinta ya yi sanyi, ta koma ta jingina da bayan kujerar ta yi shiru tana tunani. Safwan ya ɗan kalleta sai kuma ya ci gaba da tuƙinsa jin bata ce komai ba.

Njomboli, Yola South.
Karfe 7:10 na magriba motocinsu suka fara parking a ƙofar babban gidan, ɗaya bayan ɗaya kowa ya fara fitowa suna sauke ajiyar zuciya wasu na hira ƙasa-ƙasa, Nana ta dinga kallon ƙaton gidan wanda ya kasance shine kaɗai kerarren gida kaf Njomboli da kallo, Babban gida ne wanda aka ƙawata shi tamkar a cikin gari yake, kasancewarsa shi ne asalin gidan su Late Alhaji Muhammad Shuwa, kuma nan ne inda sauran danginsu suke, Mutanen gidan suka firfito fuskarsu ɗauke da farin ciki mara misaaltuwa suna musu sannu da zuwa, kafin daga bisani suka musu jagora har cikin gidan.

A ɗakin Baba Atta suka sauka, wadda ta kasance yar uwa ga late Muhammad Shuwa wadda suke uba ɗaya, tsohuwa ce sosai amma Allah ya mata kyan jiki dan ba zaka taɓa cewa ta yi shekarunta ba idan tana wasu al'amuran, gaba ɗaya a ɗakin suka zauna dan ba ƙarami bane, ta dinga kallon su fuskarta ɗauke da fara'a cikin gurɓatacciyar hausarta ta ce

“Sannunku da zuwa, sannu sannu!”

Wasu a ciki ne suka amsa, wasu kuma suka yi shiru dan duk a gajiye suke, Abdusammad ne ya tashi ya koma kusa da ita dan daman tafi saninsa a cikinsu kasancewar babba kuma da yana zuwar musu sosai sanda yana ƙarami, Ya ja kumatunta yana murmushi cikin harshen fulde ya ce

“Yar tsohuwa mai ran ƙarfe”

Doke hannunsa ta yi tana Harararsa ita ma cikin harshen da ya yi mata magana ta ce“rabu dani kai, ai nayi fushi da kai” murmushin da yake ƙara masa kyau ya yi kafin ya ce“fushi kuma ki rufa min asiri Atta, idan ki ka yi fushi dani ina na kama? Har yarinyata fa na kawo miki”

Washe bakinta wanda haƙora suka fara zubewa daga ciki ta yi ta ce“haba da gaske oh ni Atta ahe zan ga jikata?” dariya ya yi yana kiran Noor da ke hannun Zahra ya ce“gata nan kamar ku ɗaya da ita” ya ƙare maganar yana miƙa mata hannun Noor, riƙeta ta yi tana murmushi ta ce“masha Allahu wannan yarinyar ba da kai take kama ba kuwa?” Girgiza kansa ya yi ya ce“a'a ki kalleta da kyau ko sai na saka an miki tabarau?” duka ta kai masa tana cewa“kaji min ɗa? Idanuna sun fi naka kwari bari kaji” Sai da ta ɗora Noor kan cinyarta sannan ta ce“wai ina ma matar taka?” da hannu ya nuna mata Zahra dake zaune opposite ɗin su ta sunkuyar da kanta. Atta ta kalleta sai kuma ta kalli su Nana da ke zaune a ƙasa ta ce

“Oh lalashewa ta sameka Arɗo”

Da ɗan mamaki ya ce“lalacewa kuma Atta?”

Gyaɗa masa kai ta yi sannan ta sake kallon Zahra tana taɓe baki ta ce“saboda baka jin magana, ka je ka haɗu da arnakun banza ya sanya ka auri wadda ba jininka ba, ko kunyar Ubangiji baka ji, to wallahi da sake sam ba zan yarda ba, sai ka auri jininka wallahi, dan Yaya ba zai taɓa alfari da kai ba idan ka mutu akan wannan turbar”

Ta ƙare maganar tana lakuce masa hanci, murmushi kawai ya yi yana satar kallon Zahra wadda ta sunkuyar da kanta ya ce“haba Atta, mene ne haka? Daga zuwanmu sai ki fara faɗa?” wani kallon tara saura kwata ta masa sannan da ƙarfi ta ce

“Kaltume! Salame!”

Shigowa suka yi a tare suna faɗin “gamu Atta” kallonsu ta yi sai kuma ta kalli su Nana ta ce“a kai su ɗaki su huta sai a kawo musu abinci”

“Ni dai fura nake so Atta”

Abdusammad ya ce da sauri, murmushi ta yi ta ce“to jikin Ahmadu ai daman nasani shiyasa tun da Kabiru ya ce min kuna hanya na sa aka tatso nono” jinjina kansa ya yi ya ce“Allah Atta? To nima na zo miki da tsaraba” washe baki ta yi ta ce“me ka kawon?” maƙe kafaɗa ya yi kamar ƙaramin yaro ya ce“sai kin fara bani fura sannan zan baki nima” taɓe baki ta yi ta ce“to ai sai ka yi ta yi” ta mai da Idanunta kan su Salame da suke tsaye har sannan ta ce“wai baku ji bane ku ke kallona kamar wasu gumakan farko?” ta ƙare maganar a ɗan fusace, murmushi kawai Abdusammad ke yi dan daman ya san halin jarabarta. Jiki na rawa suka kalli su Maimoon cikin gurɓatacciyar hausar su suka ce“mu je kun ji”

Ɗaya bayan ɗaya suka miƙe ban da Nana data ko motsi bata yi ba, Atta ta kalli Aliyu wanda tun shigowarsa bai ce komai ba ta ce“wannan ba Ali bane?” a sanyaye Aliyu ya ce“ni ne Atta” harararsa ta yi ta ce“aa to kaje da mugun halin ka, tashi ku je a buɗe muku sabon sashin can na yan jimeta” to kawai ya ce dan shi ba wani hira suke da ita saboda jarabarta ya kalli su Sultan ya ce“mu je ko” okay kawai suka ce sannan suka tashi suma suka fice, wajen ya rage daga Abdusammad sai Zahra da kuma Nana, wani kallo Atta ta yiwa Zahra sannan ta ce“ke ba zaki tashi bane?” jiki a sanyaye Zahra ta mike ta fice daga ɗakin dan ita bata taɓa haɗuwa da Atta ba tun da ta auri Abdusammad, duk yanda yake bata labarinta yau ta tabbatar da tafi gaban nan, ta mai da idanunta kansa dan sam bata lura da Nana ba ta ce“daman na ajiye maka gilishi so nake su hita na sa a ɗauko maka” murmushi kawai ya yi sannan ya ce“yauwa shiyasa nake sonki ai”

“bari kaji amma wallahi sai ka sake aure dan ba zaka zauna da jinin da ba naka ba, idan mata sun ƙare a jimeta sai ka ɗauki ɗaya anan ka shige da ita”

Kallonta kawai Abdusammad ya yi sai dai ban tanka ta ba, dan yana sake magana zata iya rantsewa, Kaltume ce ta dawo ɗakin tana kallonta cike da girmamawa ta ce“Atta ita wannan ba tafiya zata yi bane?” ta ƙare maganar tana nuna Nana dan tun ɗazu take jiran taga ta fito kuma ta ji shiru. Mitsi-mitsi Atta ta yi da idanu tana kallon Nana ta ce“wace wannan?”

Abdusammad ne ya juya yana kallonta ganin yanda ta sunkuyar da kanta, babu yabo babu fallasa ya ce“Nana” a hankali ta ɗago kanta ta kalleshi da kumburarrun Idanunta wanda hawaye ya cika su,Baki buɗe Atta ke kallonsu sai kuma ta ce“wace Nana?”

“Nana da ki ka sani ya gidan Abba”
Chapter 39 · 0% Book details