Sashe 93
Naanah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Jiki a sanyaye ta ɗauki wayarta tabi bayansa, Nana ta kasa ko da kallonsu saboda idanunta da suka ƙi buɗuwa. Sai da suka fita sannan ta zube a wajen ta saki wani marayan kuka, ban da raɗaɗi da azaba babu abin da fuskarta ke yi, ta daɗe a wajen tana dafe da kuncinta kafin ta tashi ta haye sama da gudu. Tana shiga daƙinta ta faɗa kan gado ta ci gaba da kuka kamar ƙaramar yarinya, Koda wasa bata yi tunanin zai mareta ba, bayan kuma ba laifinta bane..ita ta fara zaginta, Ta dunƙule jikinta waje ɗaya tana sake fashewa da wani sabon kukan, da gaske baya sonta, da gaske Zahra yake so. Nana ta ci gaba da kukanta tana dana sanin yarda da auren, dama bata dawo ba sanda ta garin gidansu Khadijah, dama ba gidan taje ba duniya ta shiga. Da babu wanda ya ganta, ta ci gaba da kukanta kamar ranta za fita. Tafi awa kwance a wajen kafin ta tashi ta zura slippers ɗinta ta shige toilet. A gaban madubi ta tsaya tana kallon fuskarta, gaba ɗaya shatin hannunsa ne akan fuskarta, Sai jini a gefen bakinta. Cikin kuka ta kunna sink ɗin ta tara hannunta ta ɗebi ruwan ta wanke bakinta sannan ta wanke fuskarta. Bayan ta gama ta fito ta koma ta kwanta tana kuka a hankali.
****
Anty Khadijah ce zaune kan sofa tana kallon Kaddu, Can ta ce“to ya za'a yi yanzu?" Kaddu ta ce“wallahi kin ga naje na karbo miki wannan maganin ma, wai ki saka ki a tea ki sha. Kina nan zaki gan shi ya zo har gidan nan” Anty Khadijah ta yi shiru kallonta kafin ta ce“to Zahra fa? Na yi magana da ita ta ce min wai tana shan maganin, to amma har yanzu ban ji ya saketa ba!” Kaddu ta yi murmushi ta ce“me ki ke ci na baka na zuba? Ai tunda aka ce miki zai saketa wallahi sai ya saketan. Kin manta yanda aka yi lokacin auren Siyama? Ai indai malam Garba ya faɗi abu to kamar ya faru ne.” Anty Khadijah ta ce“To shikenan, bani nasha yanzu ma.” Kaddu ta buɗe jakarta ta zaro ƙullin maganin ta miƙa mata. Tashi Anty Khadijah ta yi ta shige kitchen, Kaddu ta bita da kallo har ta fito hannunta riƙe da mug, a gabanta ta kwance maganin ta juye shi tas a ciki sannan ta saka spoon ta juya ta kafa kai ta shanye. Kaddu na murmushi ta ce“inda biyan buƙata?”
“Rai ba'a bakin komai yake ba!”
Anty Khadijah ta bata amsa, suka tuntsire da dariya a tare suna tafa hannu.
****
Siyama ta shigo ɗakin tana kallon sa, ajiye ledar hannunta ta yi ta ce“ko na kira maka Sultan ne?” Safwan dake kwance yana rawar sanyi ya girgiza mata kai, Ta zauna gefen gadon ta ce“to tashi ka sha maganin.” murya can ƙasa ya ce“Bani wayata”
Siyama ta juya ta ɗauko wayar dake kan drawer ta miƙa masa. Dakyar ya tashi zaune ya jingina da jikin gadon, Ya yi dialing numbernsa, sai da ta kusa katsewa sannan ya ɗaga. Abdusammad da ke zaune kan kujera ya ce
“Safwan ya jikin?”
Madadin ya bashi amsa sai kawai ya fashe da kuka kamar ƙaramin yaro. Abdusammad ya tashi tsaye hankali a tashe ya ce
“mene ne? Me ya faru?”
“Yayaaa...”
Ya kira sunansa cikin kuka.
“Na'am Safwan.”
Ya amsa a sanyaye, Safwan ya ja numfashi ya sauke ba tare da ya yi magana ba. Abdusammad ya sake cewa“ina jin ka, me ya faru?”
“Yaya mutuwa zan yi. Wallahi mutuwa zan yi, dan Allah ka zo kaji"
Girgiza kai Abdusammad ya yi sanin halin rakinsa ya ce“Ban son raki fa. Wane ya ce maka cuta mutuwa ce? Ka nutsu, zan saka a shirya maka Flight, zuwa next week sai ka tawo”
Safwan ya ja numfashi sannan ya ce
“Allah Yaya mutuwa zan yi, ka zo kafin na mutu.”
Tsaki Abdusammad yayi ya ce
“ranka zai ɓaci Safwan, kai ƙaramin yaro ne?”
Murmushin ƙarfin hali Safwan ya yi ya ce
“to shikenan Yaya.”
“kana shan maganin dai yanda ya kamata right?”
Safwan ya gyaɗa masa kai kamar yana gabansa sannan ya ce
“Eh ina sha.”
Abdusammad ya jinjina kansa ya ce
“ka ci gaba da sha to, idan na koma gida zamu yi waya." To kawai Safwan ya ce sannan ya kashe wayar, Siyama ta dinga kallon sa sai kuma ta yi murmushi ta ce
“Ji yanda ka ke kwaɓe fuska”
Harararta ya yi ya ce“dan baki san ciwon da nake ji ba” yanda ya yi maganar ya sanyata dariya, Ta ce“ka ganka kuwa?” Ya dauke kansa yana sakin ajiyar zuciya.
08106608363
Nanameera.
*🌹 NAANAH 🌹*
Arewabooks@Nanameera08
Wattpad@Nanameera08.
Page 56.
****
Basu dawo gidan ba sai wajen 8:00 na dare, Ya miƙa mata Noor dake bacci ya ce“Kai ta ɗaki ina zuwa.” Karɓarta Zahra ta yi tana murmushi ta ce“ina zaka je?”
“fita zan yi.”
Ya yi maganar yana juyawa. Zahra ta kalli security ɗin da ya shigo da kayayyakin da suka siyo, Ya ajiye a parlourn sannan ya fita. Sama ta nufa tana rike da Noor, Ta kwantar da ita akan gadonta sannan ta zare mayafin jikinta ta nufi toilet, Bayan ta fito ta zauna gefen gado dan already sun yi sallah a masallaci. Numbern Anty Khadijah ta yi dialing bayan ta ɗaga ta ce
“Anty Ya gida?”
Anty Khadijah dake kwance kan gadonta ta yunƙura ta tashi zaune tana cewa
“Zahra muna nan kalau”
Zahra ta jinjina kanta tana murmushi ta ce
“Anty daman kiran ki nayi na faɗa miki wallahi maganin da ki ka bani yana aiki. Yau dana sake sha da safe kin ga ɗazu a gabana ya mareta har sau biyu, kuma yanzu ma da muka dawo ko nemanta bai yi ba.” Anty Khadijah ta yi murmushi ta ce“to bana faɗa miki ba daman? Yanzu zaki ga ko kwana daƙinta ba zai dinga yi ba, ballantana ki ji ance tana da ciki.” Zahra ta ɗan yi dariya ta ce
“to ai Anty babu abin da ya taɓa shiga tsakaninsu fa, shi har yanzu baya yi mata kallon matarsa.” Anty Khadijah ta yi shiru kamar mai nazari can kuma ta ce
“amma kina ganin haka babu matsala Zahra?”
Zahra ta ɗan girgiza kai ta ce“eh babu matsala mana Anty, kin ga ai bani da damuwar ko ta samu ciki ko wani abu. A haka har ta gaji ta saka ya saketa”
Anty Khadijah ta sauke numfashi ta ce“haka ne kuma. To Allah ya sake rufa asiri”
Zahra ta yi murmushin jin daɗi ta ce“amin Antyna. Ki gaida su Umma”
“Ba zaki kirata ba?”
Girgiza kai Zahra ta yi ta ce“kin san halin faɗanta. Yanzu idan nayi kiranta ba zata bari mu yi hira ba zata fara min wa'azi kawai na kirata gobe.”
“Oh ku dare ne ko? To Allah ya kai mu” da Amin ta amsa sannan ta kashe wayar, Zahra ta ajiye wayar gefenta ta yi shiru tana tunani, ita kaɗai kuma ta fara murmushi saboda tunawa da abin da Abdusammad ɗin ya yiwa Nana.
****
Nana na zaune gefen gado Around 9pm taji an fara knocking ƙofar, Ta ɗaga kumburarrun Idanunta ta kalli ƙofar sai kuma ta sauke kanta. Tana jin sa har ya gaji ya bar jikin ƙofar, Ta koma ta kwanta ta fashe da wani sabon kukan, yini ta yi tana kuka. Takaici ya hanata yin shiru, Ta jima a haka kafin ta tashi ta shiga banɗaki, ta wanko fuskarta ta dawo ta zauna gefen gadon ta zuba uban tagumi. Abdusammad kuwa yana barin jikin ƙofar ɗakin Zahra ya nufa, Ya sameta zaune ta sauya kaya zuwa na bacci da alama wanka ta yi, tana ganinsa ta fara murmushi. Babu yabo babu fallasa ya ce
“Zahra mene ya haɗa ki da Nana ɗazu?”
Da ɗan mamaki take kallon sa, Ya ɗaga mata gira ya ce“Eh. Mene ya yi causing faɗan naku?”
Zahra ta ɗan juya Idanunta kafin ta ce“amma kusan a gabanka aka yi komai doctor, babu abin da nayi mata. Kawai daga muna magana akan fitar shi ne fa ta fara zagina, kuma ai ba yau suka fara min irin haka ba. Duk ƙannenka sun raina ni"
“Kina nufin baki ce mata wani abu mara daɗi ba?”
Ya yi tambayar yana kallonta. Zahra ta girgiza kanta ta ce“babu abin da na ce mata, yama za'a yi na tsaya ina faɗa da Nana?”
Numfasawa ya yi ya girgiza kansa ya ce“To bana son kina biye mata, ke da kan ki kin san yarinya ce. Kuma kin san halinta ba tun yau ba, Nana ba son zaman lafiya take ba, dan haka duk abin da zata yi kada ki sake biye mata.”
Rau-rau ta yi da idanu kamar zata yi kuka ta ce“kenan goyan bayanta ka ke?”
Wani irin kallo ya watsa mata wanda ya sanyata sunkuyar da kanta. Ya tako har gabanta yana kallonta fuska a ɗaure ya ce
“Babu wadda nake goyan baya a cikin ku. Ku duka matana ne, kuma duk wadda ta yi ba dai-dai ba zan mata magana. So behave ur self”
Zahra ta yi shiru har sannan bata ɗago kanta ba, Ya juya ya fice daga daƙin. Taɓe baki ta yi sannan ta yi kwanciyarta.
Koda ya fita ɗakinsa ya shiga, Ya duba keys ɗin ɗakunan ya zari guda ɗaya. Yana zuwa ya saka key ɗin ya murɗa, cikin sa'a kuwa yaji ya buɗe dan ba'a jiki ta bar keyn ɗin ba, Sam Nana bata ji alamun buɗe ƙofar ba saboda kukan da take. Sai mutum ta gani a gaban gadon, Ta yi saurin tashi zaune, ta koma can ƙarshen gadon ta dunƙule jikinta waje ɗaya. Kallon ta ya dinga yi sai kuma ya zauna gefen gadon, murya a sanyaye ya ce
“Ke zo nan..”
Sake matse jikinta ta yi tana kuka a hankali, Ya sake kiran sunanta ta yi masa banza. Ganin yana nufota ya sanya ta sauka ta ɗaya side ɗin gadon. Ya dinga kallonta lokaci ɗaya ya haɗe ransa ya ce
“Baki ji me nace bane? Zo nan!”