← Book details Naanah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 125

Sashe 30

Naanah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“yanzu zan sauka nace na gan ki, gasu Abba nan a ƙasa” jinjina kanta ta yi sai kuma ta ce“zazzaɓi nake ji Maimoon” hannunta ta kai wuyanta ta ji zafi sosai ta ce“sannu daman baki da lafiya?” lumshe idanu ta yi ta buɗe sannan ta ce“a'a yanzu kawai naji zazzaɓin” sannu kawai ta ce sannan ta mike ta ce“bari naje kar ace a na daɗe” daga haka ta fice daga ɗakin. Da gudu ta sakko ƙasa tana fadin “Abba! Abba! Abba!” tsaye ta same shi yana kallonta ya ce“lafiya dai Maimuna?” sama ta dinga nuna masa da hannunta kafin ta ce“Nana! Nana tana sama daman” da wani irin mamaki suka dinga kallonta, Abba ya yi gaba ya haura saman da sauri, ɗakin Hajiya ya buɗe yaga bata ciki, ya sake buɗe ɗayan, turus ya yi a wajen yana kallonta ganin yanda ta juya baya, a sanyaye kuma yace

“Nana!”

Da sauri ta juyo ta kalleshi, ya ƙarasa ciki yana kallonta ya ce“yaushe ki ka zo nan? Me yasa baki je gida ba?” muryarta a sanyaye ta ce“Abba banida lafiya, tun safe nake nan kuma na kasa tashi” ta ƙare maganar hawaye na zubowa kan fuskarta, Hannunsa ya kai wuyanta ya ji zafi sosai ya janye hannun dai dai sanda Hajiya Babba da Abdusammad suka shigo ya riƙe hannunta ya ce“sannu to, taso” miƙewa ta yi ta jingina da jikinsa tana lumshe idanu, Hajiya ce ta ƙaraso gabanta ta riƙeta tana faɗin “ke daman kina nan? Me ya sa baki sakko ba? Baki da lafiya?”

“wai ashe bata da lafiya ne, ta zo ta kwanta kuma bata tashi ba, bari muje a dubata” Hajiya Babba ta ce“koda naji, sannu kin ji takwara” gyaɗa mata kai kawai Nana tayi, Abdusammad dake tsaye jikin ƙofa ya harɗe hannayensa a ƙirji ya ce“kawai bari na tafi da ita Abba sai na dubata zuwa an jima na dawo da ita” Girgiza kai Abba ya yi ya ce“a'a Abdusammad, ka gaji dayawa tun ɗazu ka ke wahala kawai na kira likita a waje ya dubata” murmushi ya yi ya ce“babu komai Abba” daga haka ya ƙaraso wajen, hannunta ya riƙe suka fito daga ɗakin, Maimoon ta sauke ɓoyyayiyar ajiyar zuciya tana dafe ƙirji. Sai da suka fito Abba ya nufi apartment ɗinsa dan sanar da Amma sannan ya saki hannunta ya ce“muje ko” babu musu ta fara tafiya a hankali har suka ƙarasa gidansa, A parlon suka sami Zahra da Noor tana ganinsu ta miƙe tsaye tana faɗin “Alhamdulilah, a ina aka ganta? Nana ina ki ka je?” kafin ta yi magana ya riga ta ya ce“wai tana kwance ɗakin Hajiya ne tun safe bata da lafiya” girgiza kai Zahra ta yi ta ce“ayyah sorry kin yi, sannu Nana” gyada mata kai kawai ta yi, bai sake cewa komai ba ya ja hannunta suka bar wajen.

Ɗakinsa suka shiga, ya mayar da ƙofar ya rufe da key sannan ya jingina da jikin ƙofar yana kallon bayanta ya ce“keee!” a ɗan tsorace ta juyo saboda yanda taji ya kira sunan nata, ya dinga kallonta sai kuma ya ƙaraso wajen yana tafiya cike da izza, in a very calm voice ya ce“ina ki ka je?” da ɗan mamaki ta dinga kallonsa, ya yinda ƙirjinta ke wani irin bugu na tsananin tsoro da fargaba, cikin rawar murya ta ce “Bab..bba..babu inda naje, ina Apartment ɗin Hajiya tun safe kuma...”

Cak maganar ta tsaya saboda zazzafan marin daya sauke mata a fuska, ta runtse idanunta tana jin kamar idanunta sun makance, nan da nan fuskarta ta yi wani irin jaa, cikin zafin nama ya fizgota ta faɗo jikinsa, ya sanya hannunsa na dama ya riƙe gashin kanta da kyau cikin tsananin ɓacin rai da kakkausar murya ya ce“ina ki ka je nace!?”

Azaba da tashin hankali su ne suka hanata bashi amsa, ya hankaɗata ta tafi ta faɗi kan tiles, ta saƙi ƙara saboda azabar data mata yawa, belt ɗin da ke ajiye gefen drawer ya ɗauko ya shiga naɗeshi a hannunsa yana kallonta ya ce“sai kin faɗa min in da ki ka je tabbas!”

08106608363
Nanameera.*🌹 NAANAH 🌹*

Follow my account,
Arewabooks@Nanameera08
Wattpad@Nanameera08.

Page 19...

Ganin da gaske dukanta yake shirin yi ya sanya ta buɗe baki cikin shessheƙar kuka ta ce“dan Allah uncle ka yi hakuri, wallahi babu inda naje” ko rufe baki bata yi ba taji saukar belt a bayanta, ta dafa wajen tana wani ƙandarewa cikin tsananin azaba, ya durƙusa dai dai tsayinta ya riƙe kanta yana kallonta yana huci ya ce“ina ki ka je? And wane wanda ya sauke ki” kasa basu amsa ta yi sai jan numfashi take tana dafe ƙirji, ya saketa sannan ya yi kwafa, wurgi ya yi da belt ɗin sannan ya ce“bari naje na kira Abban sai ki fadi in da ki ka je a gabansa” daga haka ya juya zai bar ɗakin, cikin zafin nama ta tashi da gudu ta ƙarasa inda yake ta riƙe ƙafafunsa tana kuka ta ce“dan Allah uncle kada ka faɗa masa, wallahi dukana zai yi, dan Allah ka yi haƙuri” cak ya tsaya amma bai juyo ba, ta ɗora fuskarta jikin ƙafarsa ta dinga rera wani irin marayan kuka.

Juyowa ya yi ya kama hannunta har gaban gado sannan ya zaunar da ita ya ɗan durƙusa dai dai fuskarta ya ce“shikenan ba zan faɗa masa ba, faɗa min ina ki ka je? Me ya sa ki ka yi ƙarya? Yaushe ki ka koyi ƙarya Nana?” yanda ya yi tambayar ya sanya jikinta ya sake sanyi, ta sunkuyar da kanta bakinta na rawa ta ce“dan Allah ka yi haƙuri, wallahi gidan su ƙawata naje, kuma na san idan na faɗawa Amma ba zata bar ni ba shiyasa...”

Kasa ci gabawa ta yi ganin irin kallon da yake mata, ko bai faɗa ba ta san ya gane ƙarya take faɗa masa, dan haka ta cigaba da hawayenta. Numfasawa ya yi kafin ya tallafi fuskarta da hannunsa ya ce“ba zaki daina min ƙarya ba ko? Ni ki ke tunanin za ki yiwa ƙarya ban gane ba Nana? Kina cikin hankalinki kuwa?”

Girgiza kanta ta dinga yi sai kuma ta sanya hannunta na hagu ta goge hawayen sannan ta ce“ka yi haƙuri” sakinta ya yi ya koma gefenta ya zauna sannan ya ce“tell me ina ki ka je?”

Shiru ta yi tana tunanin abin da zata ce masa wanda zai yarda da ita, dan ko karen hauka ne ya cijeta ba zata taɓa faɗa masa gaskiya ba, dan haka ta shiga tunanin irin ƙaryar da zata masa. Gyaran muryar da ya yi ne ya dawo da ita daga tunanin da take, without looking at her ya ce“ina jin ki” wasa ta fara yi da fingers ɗinta cikin shessheƙar kuka ta ce“makarantar mu naje” kallonta kawai ya yi da neman ƙarin bayani, dan haka ta ci gaba da faɗin

“Daman ƙawata ce ta ce min an fara bada admission a Aun University, to shi ne nace zan je na tambaya yanda ake yi, kuma nasan idan na faɗawa Amma ba zata barni ba, cewa zasu yi ba zamu ci gaba da karatu ba, shiyasa..” ta ƙasa ƙarasa maganar saboda kukan daya tawo mata, kallonta kawai yake ba tare da ya ce komai ba, ganin ya yi shiru ya sanya ta ɗago ta ɗan kalleshi sai kuma ta sake sauke idanun ƙirjinta na bugawa da sauri.

“To me ya sa ki ka kai dare? Sannan wane wanda ya ajiye ki a bakin gate?”

Kamar daga sama haka taji tambayar tasa, ta ɗan yi shiru kafin ta ce“da naje ne aka ce sai na jira saboda basa nan, shi ne na dinga jira har yamma sannan aka ce min ba zasu zo ba ranar, to bayan na fito kuma babu kudi a hannuna sai nafara tawowa a ƙafa sai bayan magrib sannan na haɗu da wannan mutumin yaga ina kuka shi ne ya ce mene ne na faɗa masa shi ne ya ce bari ya kawo ni gida”

Ta ƙare maganar cikin sanyin murya tana mai fatan samun yardarsa. Jinjina kansa ya yi sannan ya ce“saboda haka yasa ki ka yanke shawarar ki yi ƙarya a gida? Bayan kin ɗagawa kowa hankali? Kin san me kuwa babu inda ban saka an duba ba amma ba'a same ki ba, amma kina tunanin zan yarda dan ance kina ɗakin Hajiya” ya ɗan yi murmushi sannan ya ci gaba da faɗin “kina tunanin har kin yi girman da zaki dinga yin ƙarya ko? Har kin san mene rayuwa ko?” girgiza hannunta tayi ta ce“a'a wallahi uncle, ka yi hakuri ba zan sake ba dan Allah” tashi ya yi yana furzar da numfashi kafin ya ce“duk ranar da ki ka sake fita ba'a sani ba sai ran ki ya ɓaci fiye da tunanin ki Nana, I'll show you the other side of me, so take care” daga haka ya nufi hanyar waje da sauri, da idanu ta bishi har ya rufe ƙofar sannan ta sauke ajiyar zuciya tana dafe ƙirji, muryarta na rawa ta ce

“Allah astagfirullah, Allah ka yafe min”

Sai kuma ta kai hannunta kan fuskarta, wani irin raɗaɗi taji wanda ya sanya ta runtse ido a fili ta ce“wayyo” sannan ta tashi da sauri ta ƙarasa jikin madubi, kallon gefen fuskar ta ta dinga yi ganin yanda ya yi jajur dashi ya ɗan kumbura, ta tura baki sai kuma ta ce“kuma sai ya dakeni” ta ƙare maganar a shagwaɓe, buɗe dakin aka yi ya shigo ta juya da sauri ta kalleshi sai kuma ta sunkuyar da kanta, taɓe baki ya yi sai kuma ya ce“zo ki tafi” kamar zata yi kuka ta ce“uncle kaga fuskata” ta yi maganar tana nuna masa gefen daya maretan, haɗe rai ya yi ya ce“to sai aka yi Ya ya?”
Chapter 30 · 0% Book details