Sashe 62
Naanah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
“wallahi ban sani ba. Ban ma san bata gida ba, ni tun ranar data kirani na ƙarshe ana i gobe ɗaurin auren ban sake magana da ita. Wane ya saceta? Dan na san Nana ba zata taɓa guduwa da kanta ba”
Junaid ya yi maganar yana kallonsa hankalina tashe. Zura hannayensa ya yi cikin aljihun trousern dake jikinsa kafin ya ce
“ta bar gida tun ranar ɗaurin aurenta da safe, kuma babu wanda ya san inda ta tafi. She's afraid akan zaka fitar da hotunanta”
Girgiza kai Junaid ya yi yana jin wani matsanancin tausayinta ya ce“Allah sarki Nana, yarinya ce ƙarama. Ba komai take iya ɗauka ba, but wait ya aka yi ka san da maganar hotunan nan? Na tabbata Nana ba zata faɗawa kowa ba” Abdusammad ya ce“me ka ke nufi ba kai ne wanda ka bawa Safwan hotunan ba?” da mamaki Junaid ya ce“ban san shi ba, kuma ban bawa kowa ba. Ban da Nana babu wanda ya san da maganar hotunan nan, taya aka yi suka je hannun wani?”
Sai a sannan tunanin Abdusammad ya kawo wajen, a ina Safwan ya samu hotunan Nana? Wane ya bashi?. Ya girgiza kansa sai kuma ya kalli guards ɗin dake tsaye ya ce“ku ci gaba da tsare shi.” cike da girmamawa suka amsa sannan ya juya ya bar ɗakin, Junaid ya bishi da idanu..
****
A hankali ta murɗa handle ɗin ƙofar bakinta dauke da sallama. Zaune ta hangeshi kan kujera yana operating system ɗin dake gabansa, ta sauke numfashi sai kuma ta ƙarasa ciki a hankali. A kan table ɗin dake gabansa ta ajiye mug ɗin sannan ta zauna gefensa. Ya ɗan kalleta sai kuma ya mayar da kansa ga system ɗin ba tare da ya ce komai ba. Itama Amma shiru ta yi ta sake zuba uban tagumi dan yanzu shi ne kaɗai abin da take yi, Abba ya kai hannunsa ya ɗauka tea ɗin ya fara sipping a hankali yana kallon abin da yake. Sai da kusan mintuna biyar suna shuɗe kafin ta sauke numfashi ta gyara zamanta tana kallonsa sosai ta ce“yallabai”
Juyo da idanunsa kanta ya yi yana kallonta ya ce“lafiya dai?” gyaɗa masa kai ta yi sai kuma ta ce“lafiya. Daman ina son nayi maka magana ne akan Nana naga...”
Dakatar da ita Abba ya yi ta hanyar ɗaga mata hannu, lokaci ɗaya ya haɗe ransa kamar wanda ta yiwa zancen mutuwa. Ya kuma ce“idan wannan maganar ce kar ki yimin dan Allah”
Amma ta dinga kallonsa jiki a sanyaye lokaci ɗaya hawaye ya cika kurmin idonta ta ce“to idan ban maka ba wa zan yiwa? Kana ganin fa kusan wata daya babu Nana babu labarinta. Ko gidajen rediyo da aka kai report da station ba'a samu wani magana ba. To kuma ka ce ba zan maka maganarta ba?”
“To mene ne nawa da zaki yi min magana akanta? Kin ji na ce kina son na ganta? Kin ji nace ina son ta dawo?. To bari kiji ni babu a akan maganarta, sannan I'm warning you karki sake min maganarta! Kar ki sake Rabi'ah”
Abba ya yi maganar rai ɓace, ya tashi ya rufe system ɗin gabansa ya fice daga ɗakin ya barta zaune. Amana binsa kawai ta yi da kallo sai kuma ta fashe da wani irin kuka, kenan ba zai nemo mata yarta ba? Babu wanda ya damu da ɓatan Nanar?. Ta sake rushewa da wani sabon kukan tana dunƙule jikinta waje ɗaya.
****
A compound ɗinsu Aliyu motar ta yi parking, ya buɗe back seat ya fito yana karewa compound ɗin kallo kafin ya furzar da numfashi ya nufi cikin gidan. Maimoon na zaune a parlon hannunta riƙe da wayarta ya shigo, tana ganinsa ta miƙe tsaye a ɗan firgice ta ce
“Welcome uncle”
Ganin yanda ransa yake a haɗe babu alamar wasa ya sanya ta sunkuyar da kanta. Ya shigo tsakiyar parlon yana kallonta har sannan, zama ya yi kan sofa ya ce“zauna magana zamu yi” kallonsa ta yi da mamaki ganin yanda ya yi maganar ba'a sigar faɗa ba, dan haka ta koma ta zauna tana kallonsa har sannan. A nutse ya ce
“Maimuna”
Ta kalleshi sai kuma ta sunkuyar da kanta a sanyaye ta ce “na'am uncle”
“zan tambayeki kuma ki tabbata kin sanar dani gaskiya. Kar ki ɓoye min koda abu guda ɗaya da ki ka sani”
Gyaɗa masa kai ta yi sai kuma ta ɗago fuskarta da hawaye ya fara zuba ta ce“tam uncle, zan faɗa maka duk abin da na sani wallahi”
Jinjina kansa ya yi kafin ya ce“mene ne abin da yasa Nana ta bar gidan nan? Who forced her? Wane yake treating ɗinta da hotunan, nd wane ya san da maganar hotunan har ta fita ta je wajen Safwan?”
Wata irin faduwar gaba ce ta ziyarceta. Ta haɗiye yawu da kyar sai kuma ta ce“uncle nima ban san wanda ke treating ɗinta ba, kawai dai na san Nana ta bar gidan nan a saboda tilastawar da Yaya Safwan ya yi mata. I was there da safen ya zo ya nuna mata hotunan ya ce idan har ta yarda aka ɗaura aurensu to sai ya fitar dasu kowa ya gani. Idan kuma ta bar gidan nan to ba zai faɗawa kowa ba, ya ce ta tafi idan aka gama maganar daurin auren sai ta dawo. Shi ne ta ce to saboda tsoron kada a fitar da hotunan da kuma barazanar da Junaid ke mata, yasa ta haƙura ta tafi duk da bata so, ta tafi ba tare da mun tambayeta inda zata je ba, wallahi uncle kullum da Nana nake kwana da ita nake tashi. Na kasa daina tunaninta, ko wane hali take?...”
Ta fashe da kuka tana girgiza kanta. Shiru ya yi yana saurarenta can kuma ya sauke numfashi ya ce“it's alright. Kenan baki san wanda ya fitar da hotunan ba?” shiru Maimoon ta yi tana tunanin abin da faɗar gaskiyar tata zai haifar, what idan ya saki Zahra saboda haka? Ko kuma hakan yasa kowa ya tsaneta?. Ta girgiza kanta tana fatan kada gaskiyar ta bayyana, kallonta ya dinga yi sai kuma ya ce
“ya dai? Kin san wanda yake treating ɗinta da hotunan?”
Girgiza masa kai ta yi har sannan tana hawaye ta ce“ban sani ba uncle, kawai a wajen Junaid na san su” Abdusammad bai sake cewa komai ya miƙe ya fice daga parlon. Ta bishi da kallo sai kuma ta silale ƙasa ta fashe da wani sabon kukan tana jin tausayin Nana. Ko'ina take?.
****
Yana fita kai tsaye apartment ɗin Safwan ya nufa, ya ɗan tsaya a bakin ƙofar dan bai taɓa zuwa ba tun da ya tare, can kuma ya murɗa handle ɗin ƙofar bakinsa ɗauke da sallama. Haule ce kawai a parlon ta zuba uban tagumi dan bata ma san ya shigo ba, ya kalleta sai kuma ya sake sallama. Sai a sannan ta ɗago ta kalleshi lokaci ɗaya ta mike tsaye jikinta na ɗan rawa ta ce
“in...ina yini?”
Amsawa ya yi kafin ya ce
“Safwan fa?”
Haule ta sake sunkuyar da kanta ta ce“yana sama”
Kallon hanyar saman ya yi sai kuma ya sake kallonta ya ce“ok kira min shi”
“ai bahida lafiya. Ko tashi ma baya yi”
Ta yi maganar a sanyaye. Shiru Abdusammad ya yi can kuma ya nufi saman da sauri, ɗakin daya tabbatar shi ne nasa ya buɗe, Kwance ya hangeshi kan gadon ya lulluɓe jikinsa da ƙaton duvet. Siyama na zaune gefensa taci uban kwalliya sai kallonsa take, tana jin an buɗe kofar ta ɗago a fusace dan ta yi tunanin Haule ce. Sai dai ganin Abdusammad ya sanyata miƙewa a sanyaye ta ce
“Barka da zuwa Yaya”
Jinjina kansa kawai ya yi dan bai zo dan su gaisa ba, ganin idanunsa na kan Safwan ya sanya ta fice daga ɗakin ta basu waje. Ya karasa gabansa cikin takunsa na isa da taƙama. Ya harɗe hannayensa a ƙirji yana kallonsa ya ce
“Safwan”
A sanyaya janye duvet ɗin daga kansa. Ya kalleshi sai kuma ya tashi zaune da kyar yana cije baki, Abdusammad ya dinga kallonsa ganin yanda ya rame ya lalace. Safwan ya ɗan yi murmushi wanda yafi kama da na ƙarfin hali sannan ya ce
“Yaya sannu da zuwa”
“Yauwa”
Ya amsa a takaice. Shiru ɗakin da ɗauka na wasu mintuna kafin ya numfasa yana kallonsa ya ce
“Nazo ne na tambayeka abu, kuma bana son ka ɓoye min komai daga ciki. Idan ka kuskura ka faɗa min abin da ba shi ba wallahi sai ranka ya ɓaci!”
Jin yanda ya yi maganar in a serious tone ya sanya Safwan kallonsa, bashi yake kallo ba, dan haka ya sunkuyar da kansa a sanyaye ya ce
“in sha Allah Yaya zan faɗa maka gaskiya”
“A ina ka samu hotunan Nana? Wane ya baka?”
Da wani irin mamaki Safwan ke kallonsaz lokaci ɗaya kuma ya yi kasa da kansa ya ce
“but Yaya...”
Ɗaga masa hannu Abdusammad ya yi sai kuma ya gyara tsaiwarsa yana kallonsa rai a haɗe ya ce“i'm just asking you, wane ya baka?”
Shiru Safwan ya yi yana tunanin abin yi, an ya ya ce Zahra ce? me hakan zai haifar? To amma idan har fadar na nufin dawowar Nana dole ya sanar dashi gaskiya. Dan haka ya numfasa ya ɗago yana kallonsa a sanyaye ya ce
“i'm sorry to say Yaya, Zahra ce ta bani!”
08106608363
Nanameera.*🌹 NAANAH 🌹*
Arewabooks@Nanameera08
Wattpad@Nanameera08.
Page 38.
Da wani irin mabayyanin mamaki Abdusammad ke kallonsa, Ya girgiza kansa kafin ya ce“me kace Safwan?” Safwan kasa haɗa idanu ya yi dashi, muryarsa na rawa ya ce“Zahra ce ta bani Yaya” kusan mutuwar tsaye Abdusammad ya yi a wajen, tuni idanunsa suka kaɗa suka yi jajur, jijiyoyin kansa suka fito sosai. Ganin yanayin da yake ciki ya sanya Safwan tashi tsaye yana kallonsa ya ce
“Kayi haƙuri Yaya. Wallahi ban yi niyyar faɗa ba, ban so kowa yaji maganar nan ba. Sai dai son da nakewa Siyama shi ne ya sakani aikata hakan” ya ƙare maganar yana share hawayen dake zubo masa. Furzar da iska ya yi daga bakinsa kafin ya dafashi a hankali ya ce“ita Zahra wane ya bata?”