← Book details Naanah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 125

Sashe 31

Naanah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“zafi yake min” ta ce a shagwaɓe, kamar ba zai magana ba sai kuma ya yi alamar ta zo da hannunsa, ta ƙarasa a hankali ta sunkuyar da kanta, tallafo fuskarta ya yi da hannunsa ya dinga kallon wajen ganin yanda ya yi jajur, hannunsa ya kai ya matsa gurin, ai ko kamar jira take ta fashe da kuka tana yarfe a hannu, haɗe rai ya yi yana kallonta ya ce“Quiet” shiru ta yi tana hawaye, ya ja hannunta suka fita daga ɗakin. A parlon ya samu Zahra zaune tana jiransu, ta miƙe ganin sun ƙaraso ta ce“sannu Nana ya jikin?” a sanyaye ta ce“da sauƙi Aunty Zahra” daga haka ya nufi hanyar waje da sauri.

Har Apartment ɗin su ya rakata sai da ta kai balcony sannan ya ce“kin ji abin da nace miki ko?” gyaɗa masa kai ta yi a hankali, ya juya ya bar wajen sannan ita ma ta juya, tan ƙoƙarin knocking ƙofar parlon taji an ce

“Nana”

A hankali ta juyo tana kallonsa sai kuma ta ce“Yaya Sultan” Ƙarasowa wajen ya yi yana tafe a hankali hannunsa zube cikin aljihun trouser ɗin da ke jikinsa, ya tsaya a jikin balcony ɗin yana kallonta ya ce“daga ina ki ke?” kamar mara son magana ta ce“daga wajen uncle nake, shi ne ya rakoni yanzu” Sultan ya bi inda ta kalla ɗin dan har sannan ana gano Abdusammad ɗin, sai kuma ya mai da idanunsa kanta ya ce“yanzu kin zama yar gidan uncle ko?” ɗan murmushi ta yi ta ce“a'a fa yau a gidan Hajiya Babba na yini da daddare naje wajensa” jin jina kai ya yi sai kuma ya ce“nagane, to je ki gida dare ya yi” Toh kawai ta ce sannan ta murɗa handle ɗin ƙofar ta shige ciki. Sultan ya ɗan jima a wajen yana tunani kafin daga bisani ya juya ya ci gaba da tafiya, koda ta shiga parlon bata sami kowa ba dan haka ta nufi daƙinta kai tsaye, bata fi 2mins da shiga ba Amma ta buɗe ɗakin ta shigo tana kallonta a fusace ta ce“ wani sabon rashin hankalin ki ka fito dashi na fita baki sanar ba? Dan baki da lafiya shi ne yake nufin ki je ki yini a can? Ba zaki iya dawowa gida ba? Kin fi so ki ɗaga min hankali ki hanani sukunin rayuwa?”

Shiru Nana ta yi tana sauraren faɗan Amman dan daman ta san sai ta yi mata, ganin yanda ta yi tsaye bata ce komai a ya sake fusatata dan haka ta ce“wato ga mahaukaciya na magana ko? Shi yasa kina ji ki ka min banza!” girgiza kanta ta yi a sanyaye ta ce“dan Allah Amma ki yi haƙuri, ba zan sake ba”

“Ai daman kin iya bada haƙuri, tun da kina da baki, to ki ci gaba kar ki fasa ja min magana Nana! Ki ci gaba idan ma so ki ke jinina ya hau saboda ke ɗaya to ki yi, kar ki fasa!” ta juya ta fice daga ɗakin tana buga ƙofa, ita dai Nana da idanu kawai ta bita sai kuma ta ƙarasa gefen gadonta ta zauna tana sauke numfashi.

Around 9pm ta fito daga ɗakin dalilin wata irin matsananciyar yunwa da taji, dan kwara kwata yau bata ci abinci ba, ta ƙarasa parlon tana kallon Amma da ke zaune tana kallon wani Film da ake haskawa a Arewa24, zama ta yi gefenta ta jingina kanta da jikinta kamar zata yi kuka ta ce“Amma yunwa nake ji, yau ban ci abinci ba” zafin da taji a jikinta shi ne ya sanya ta ɗago tana kallonta, sai kuma ta kai hannunta wuyanta tana faɗin “zazzaɓi ki ke?” gyada mata kai kawai ta yi, Amma ta ce“kin sha magani?” a sanyaye ta ce“eh uncle ya bani” tashi kawai Amma ta yi ta nufi kitchen da sauri, ita kuma ta kwanta akan kujerar tana lumshe idanunta. After 5mins ta dawo hannunta riƙe da plate mai ɗauke da farar shinkafa da miya wadda taji naman kasuwa, ta ajiye akan table ɗin sai kuma ta ƙarasa wajen freezer ta dauko mata ruwan roba da lemo ta ajiye suma sannan ta kalleta ganin yanda ta rufe idanunta ta ce“tashi ki ci abincin” a hankali ta buɗe idanun nata sai kuma ta tashi zaune ta jingina da fuskar kujerar tana sauke numfashi. Amma ta zauna gefenta sannan ta miƙa mata plate ɗin abincin ta ce“ci” kamar zata yi kuka ta ce“Amma ki bani a baki ba zan iya ci ba” kallonta kawai Amma ta yi sai kuma ta ɗauki spoon ta ɗiba abincin ta kai bakinta, buɗe bakin ta yi Amma ta yi mata bismillah sannan ta fara bata, ta dinga lumshe idanunta saboda daɗin da shinkafar ta yi mata. Sai da ta cinye tas sannan ta ɗauki ruwan tasha, Amma ta kalleta ta ce“ko na da ɗa miki?” girgiza kanta ta yi ta ce“na ƙoshi, bacci nake ji” ta yi maganar kamar za ta yi kuka, jinjina kai Amma ta yi ta ce“to tashi ki ke ki kwanta” gyaɗa kanta kawai ta yi sannan ta tashi ta bar wajen, koda ta shiga ɗakin kan gado kawai ta faɗa ta yi kwanciyarta dan a gajiye take sosai dan haka yasa nan da nan bacci ya ɗauketa.

****
Washegari around 6:00 na yamma Zahra ta sakko ƙasan hannunta riƙe da wata babbar leda tana kallon Siyama ta ce”gashi ki kai mata, ki ce size ɗin idan bai mata ba sai ta bayar a rage” to kawai Siyama ta ce sannan ta karɓi ledar ta ce“na tafi”

“ki gaida gida, ki cewa Umma wai Noor ta ce zata zo ta mata kwana biyu kafin mu shige” murmushi Siyama ta yi ta ce“to shikenan ko da mun tafi tare ai” Girgiza kai Zahra ta yi ta ce“a'a dai ki fara sanar da ita” to ta ce sannan ta nufi hanyar fita daga parlon ita kuma Zahra ta zauna kan sofa tana jawo wayarta.

Tafiya ta dinga yi cikin estate ɗin tana kalle-kalle, ko ina gwanin ban sha'awa, in dai maganar kyau da tsari ne to M-Shuwa Estate na kan gaba, ta lumshe idanunta a fili ta ce“nan bada jimawa ba nima zan shigo cikin wannan duniyar, ya ilahi can't wait” ta ƙare maganar tana wani irin murmushi. Tun daga nesa take kallonsa cike da farin ciki, murya can ƙasa ta ce“yauwa daman an ce zan gan ka” daga haka ta ci gaba da tafiyar ta tana kallon wani wajen daban, ganin sun kusa dab da dab ya sanya ta ɗan matsa gefe ta yanda zasu haɗu, sai da taga ɗan taƙin da ke tsakanin su bai fi ta mutum ɗaya ba sannan ta gurɗe hills ɗin ƙafafunta da gangan ai kuwa ta faɗi ƙasa tare da ledar kayan. Da sauri Safwan ya kalli wajen jin faduwar abu, ganin mace ce ya sanya ya ƙarasa da sauri yana kallonta cikin sanyin muryarsa ya ce“subhanallahi sannu” ɗagowa ta yi tana masa wani irin kallon ƙurilla kafin ta ce“yauwa thanks” daga haka ta shiga kwashe abayoyin da suka faɗo, tsugunawa ya yi ya tayata kwashewa ya zuba cikin ledar ba tare da ya kalleta ba ya ce“ki dinga tafiya a hankali” jinjina kanta ta yi fuskarta ɗauke da murmushi ta ce“tom in sha Allah nagode sosai” daga haka ta miƙe tana kaɗe jikinta, jinjina kansa ya yi sannan ya yi gaba abin sa. Ta dinga bin bayansa da kallo tana jin wani irin sanyi a ranta sai kuma ta yi murmushi a fili ta ce

“wow wannan shi ne haɗuwar” ta yi dariya mara sauti sannan ta zaro wayarta daga jaka, numbern Mom ɗinta ta yi dialing dan ba zata iya jira sai ta koma gida ba, ringing ɗaya ta ɗauka daga ɓangarenta ta ce“Siyama ba zaki dawo ba ne jiran ki fa nake masu kayan sun zo” murmushi ta yi ta ce“Mom Albishirinki?” Aunty Khadijah ta ce“goro mene ne?”

“Na haɗu dashi”

Da sauri ta tashi daga zaunen da take ta ce“haba da sauri haka? Daman malam ya ce zaku haɗu, yanzu ya ku ka yi?” Siyama ta lumshe idanunta kafin ta ce“ya tafi ma, yanzu nima zan dawo, sai mu san me zamu yi nan gaba” Aunty Khadijah ta jin jina kanta ta ce“haka ne kuma ki yi sauri ki dawo ina jiran ki, bari na kira Baturiya na sanar mata, daman na san aikin wannan malamin ba dai kyau ba” toh kawai Siyama ta ce sannan ta kashe wayar ta numfasa sannan ta ci gaba da tafiya..

08106608363
Nanameera.*🌹 NAANAH🌹*

Follow my account,
Arewabooks@Nanameera08
Wattpad@Nanameera08.

Page 20...

Bayan kwana biyu wajejen ƙarfe 9:00 na safe Zahra ta fito daga ɗakinta hannunta riƙe da waya, sai da ta rufe ƙofar sannan ta kai wayar kunne cikin sanyin murya ta ce“dan girman Allah Aunty ki rufa min asiri, so ki ke aurena ya mutu ne?” daga ɗaya ɓangaren Aunty Khadijah da ke zaune kusa da wata ƙawarta ta ce“kamarya aurenki ya mutu? Saboda kin ce wa mijin ki ga yarinya a bawa ƙaninsa sai aurenki ya mutu?” Zahra ta girgiza kanta kamar zata yi kuka ta ce“baki gane ba, wai ya za'a yi na cewa Doctor ga mata ya bawa Safwan? Bayan nasan basa haka, kuma ma bama wannan ba Safwan fa an riga da an yi maganar aurensa, yanzu ma maganar da nake miki sauran sati uku bikin wallahi tallahi, to kin ga idan na bijiro da wannan maganar ai kamar ban yi daidai ba” taɓe baki Aunty Khadijah ta yi a ɗan fusace ta ce“kin ga shikenan bana buƙatar taimakonki zan yi da kaina, kuma idan ma baƙin ciki ki ke kada Siyama ta shigo ta ci irin arzikin da ki ke ci to wallahi sai dai ki mutu”

Zahra ta buɗe bakinta tana jin jin karfin hali irin na Aunty Khadijahn, jin bata sake magana ba yasa ta ɗan kwantar da murya ta ce“ni fa Aunty ba haka nake nufi ba, kin ga...”

Tsaki ta yi sai kuma ta kashe wayarta, Zahra ta mai da wayar hannunta ta dinga kallon screen ɗin da mamaki, can kuma ta numfasa sannan ta koma ciki.
Chapter 31 · 0% Book details