Sashe 54
Naanah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Maimoon ta yi maganar kanta a ƙasa, Papa ya ɗan numfasa sai kuma ya kalli Abba ya ce“kira Rabi'ah ta tawo da Nana nan” ok kawai Abba ya ce sannan ya zaro wayarsa a aljihu ya yi dialing numbern Amma, ringing ɗaya ta ɗauka dan wayar na hannunta, Abba ya ce
“Ki zo da Nana apartment ɗin Hajiya yanzu”
“Dama bata tafi ba?”
Amma ta tambaya da mamaki, Eh kawai Abba yace sannan ya katse kiran, Amma ta tashi ta nufi daƙinta. Sai dai me koda ta buɗe babu Nana babu alamarta, ta girgiza kai sannan ta buɗe ɗakin Nanar, ga mamakinta sai ta tarar nan ma bata nan. Amma ta dawo parlon tana kallon Aunty Safiya ta ce“Aunty Nana bata fita ba kuwa?”
“Nana gaskiya bata fita ba, na dai ga ta shiga daƙinta ɗazu”
Amma ta ɗan ja siririn tsaki sai kuma ta koma ɗakin, ganin bata ciki yasa ta nufi toilet tana cewa“Nana ke Nana” jin bata amsa ba yasa ta ce“yi sauri Abbanki na jiranki” daga haka ta koma gefen gado ta tsaya, tana nan tsaye har bayan mintuna biyar kiran Abba ya sake shigowa wayarta, ta daga ya ce
“jiranki fa muke”
Amma ta ce
“ban ganta a ɗakin bane, I thought tana toilet kuma naji shiru”
Rai ɓace Abba ya ce“to ba zaki duba ba?” Amma ta ce to sannan ta kashe wayar, toilet ɗin taje ta murɗa sai ta ga wayam babu alamar mutum. Ta juyo tana faɗin
“To gidan ubanwa ta shiga so take ya yi ta...”
Maganar ta tsaya cak saboda takardar data gani akan gado iska sai kaɗata take, ta ɗan ware idanunta tana mamakin abin da ya kawo takardar, sai kuma ta ƙarasa a hankali ta ɗauka tana ƙarasa wareta. Amma ta buɗe idanunta sosai tana karanta rubutun dake jikin takardar kamar haka;
_Abba, Amma dan Allah ku yi haƙuri, ba zan iya ci gaba da ɓata muku rai ba, ba zan bari kuji mummunan labari akaina ba, nasan ba zaku jure ba. Ina fatan koda kun ga abin da za'a nuna muku ya kasance bana wajen, Ban tafi dan son raina ba, a'a na tafi ne dan babu yanda zan yi, ba zan iya jure ganin halin da zaku shiga ba. Dan Allah dan Annabi ku yafemin, wallahi ko me za'a nuna muku ba haka abun yake ba, idan Allah ya so watarana zan muku bayanin komai, idan kuma ban sake ganinku ba, ina roƙon ku daku manta dani. Ku manta da kun haifi ƴa kamata, ku manta dana rayu tare daku. Dan Allah ku manta da NAANAH!_
08106608363
Nanameera. *🌹 NAANAH 🌹*
Arewabooks@Nanameera08
Wattpad@Nanameera08
Page 33...
Amma ta dinga kallon takardar cikin tashin hankali, ilahirin jikinta rawa yake. Ta girgiza kanta sai kuma ta fice daga ɗakin da gudu. Kai tsaye apartment ɗin Hajiya Babba ta nufa tana tafe kamar zararriya, gaba ɗaya bata cikin hankalinta. Koda ta tura ƙofar tsaye ta samesu sun yi jigum-jigum da alama zuwan Nanan suke jira. Ta ƙarasa ciki kai tsaye kuma wajen Abba ta nufa tana faɗin
“Kaga! Kalli kaga”
Ta ƙare maganar tana miƙa masa takardar hannunta, Abba ya dinga kallonta da mamaki sai kuma ya karɓi takardar ya buɗe. Sai da ya sake kallon Amma da ke tsaye tana girgiza kanta sannan ya mai da idanunsa kan takardar ya fara karantawa.
Wata irin zufa ce ta dinga keto masa tun daga tsakiyar kansa, Ya kasa cewa komai hannunsa sai rawa yake, ganin haka yasa Abdusammad ya ƙaraso gabansa ya zare takardar ba tare da y ce komai ba. A fili kuma ya karanceta tas, ban da salati da sallalami babu abin da ke tashi a parlon, Su Hamida kuwa sai kuka suke kamar ransu zai fita. Atta ma ta ɗora hannu aka cikin tashin hankali ta ce
“*** wace irin masifa ce wannan? Ina yarinyar nan ta shiga? Mun lalashe”
Ta ƙare maganar tana sakin kuka. Sultan kuwa girgiza kansa kawai yake yana tunanin abin da yasa Nana ta yanke wannan ɗanyen hukuncin. To mene ne abun da take magana akai? wane zai fadi wani abu akanta. Lokaci ɗaya ya mai da idanunsa ka Safwan wanda babu alamar fargaba ko tashin hankali a tare dashi. Ya girgiza kansa yana tabbatar da cewa tabbas akwai abin da ya haɗata da Safwan ɗin.
Abba da ƙafafunsa suka fara gagarar ɗaukansa ya yi baya kamar zai faɗi, Abdusammad ya tare shi da sauri yana fadin
“Abba stay still pls”
Riƙe hannunsa Abba ya yi yana jinjina masa kai. Gaba ɗaya jikinsa ya yi sanyi, idanunsa sun kaɗa sun yi jajur, amma babu alamar tashin hankali a tare dashi a zahirance. Hajiya Babba da tun ɗazu bata ce komai ba ta numfasa sannan ta kalli Abba ta ce
“Aje a gabatar da ɗaurin auren, babu abin da zai hana Safwan auren Nana!”
Kusan a tare duk suka kalleta, Safwan ya girgiza kansa lokaci ɗaya hawaye ya kawo cikin idanunsa ya ƙarasa gabanta ya tsuguna murya a tausashe ya ce
“Dan Allah dan Annabi Hajiya kada amin dole, wallahi ba zan iya auren Nana ba! Ba zan iya ba, dan girman Allah a bar wannan maganar!”
Ya ƙare maganar yana haɗe hannayensa alamar roƙo. Ɗauke kai Hajiya Babba ta yi kamar bata ji abin da ya ce ba, dan haka yaja jikinsa da rarrafe ya ƙarasa inda Abba yake tsaye, ya dafa ƙafafunsa cikin kuka ya ce
“Abba na san kana da fahimta, na san kai ubane. Kuma zaka fahimci abin da nake nufi, wallahi tallahi ba zan iya auren Nana ba, kuma bani da burin sanar da ku wani abu game da haka. Dan haka dan Allah dan Annabi abar maganar aurena da ita”
“Kai ka isa, wallahi sai ka aureta! Kuma ita ma duk inda ta shiga sai ta fito! Dole ne a ɗaura wannan auren!”
Abdusammad ya yi maganar yana fincikoshi. Safwan ya dinga kallonsa hawaye na zubowa daga kan fuskarsa, ganin yanda ran Abdusammad ɗin ya ɓaci yasa ya ce
“A''a Yaya kada mu fara haka da kai, kada mu yi dan Allah. Ina jin maganarka, ina ganin girmanka. Ba zan so na ɓata maka rai ba, dan haka dan Allah ku fahimceni”
Wani irin kallon ka zama mahaukaci Abdusammad ya dinga yi masa can kuma ya sake shi ya girgiza kansa ya ce“ko kaɗan ban yi tunanin irin wannan daga wajenka ba Safwan. Wallahi ban taɓa tunanin zaka zo da irin wannan maganar ba, ka bani kunya! Ka bani kunya Safwan!”
Ya ƙare maganar a tsawace.
Shiru parlon ya ɗauka kowa da abin da yake saƙawa a cikin ransa, Amma ta yi zaman dirshan gefen Hajiya Babba sai kuka take kamar ranta zai fita, tunaninta shi ne ina Nanarta ta shiga? Me ya sa ta tafi ta bar su?.
Papa ne ya numfasa sannan ya tako daga inda yake ya zo gaban Safwan, ya sanya hannunsa na dama ya dafashi murya a ɗan cunkushe ya ce
“Safwan meyasa ba zaka iya auren Nana ba? Na san dole kana da hujjarka ta yin haka. Idan har ka faɗa mana hujjar kuma muka duba muka da abin da ka faɗa kana da gaskiya ba za'a maka dole ba, domin tun da har ka furta ba zaka aureta ba koda an yi auren ba za'a samu zaman lafiya ba”
Safwan ya dinga kallonsa fuskarsa caɓa da caɓa da hawaye kamar karamin yaro. Ya janye hannun Papa daga jikinsa sannan ya yi taku biyu gabansa ya ja ya tsaya, muryarsa a sanyaye ya ce
“Papa ba zan auri Nana ba, akwai wadda nake son na aura, kuma yau nake son a ɗaura mana auren da ita.”
Da wani irin mamaki suka dinga kallonsa. Sultan ya girgiza kansa a fili ya ce“daman na san wannan ne shirin ka, amma baka da hankali Safwan!” ya yi maganar rai ɓace. Papa ne ya ɗaga masa hannu sannan ya mai da idanunsa kan Safwan ya ce“ina jin ka, idan har ka faɗi hujjar da ta dace na yarda zaka auri wadda ka ke so”
Da sauri ya juyo ya kalleshi. Papa ya gyaɗa masa kai alamar tabbatarwa. Shiru Safwan ya yi yana tunanin mafita, can kuma ya nufi hanyar upstairs, da gudu Maimoon ta tashi ta ƙarasa inda yake ta rike babbar rigarsa ta baya tana kuka. Lamarin da ya sanya hankalin kowa ya koma kansu, Safwan ya juyo yana kallonta da mamaki, ta sake ruƙunƙumshe tana kuka ta ce
“A'a Yaya, dan girman Allah kada ka yi haka. Kada ka yi haka kaji”
Sosai jikin Safwan ya yi sanyi, ya janyeta daga jikinsa hawaye na biyo kan fuskarsa. Kuka take sosai gaba ɗaya ta birkice kanta, Ya yi shiru yana tunani sai kuma ya fara ƙoƙarin sakkowa daga saman. Maimoon ta sauke ajiyar zuciya sannan ta biyo bayansa tana kuka a hankali. Ganin yanda kowa ke kallonsa yasa ya sunkuyar da kansa yana kallon Papa ya ce
“I'm sorry Papa”
Murmushin takaici Papa ya yi kafin ya ce“sorry? Sorry for what Safwan?”
Kasa cewa komai ya yi, lokaci ɗaya ya shiga lalubar aljihunsa, cikin yan sakanni ya zaro envelope ɗin. Ban da kallonsa babu abin da ake a ɗakin, ita kuwa Maimoon mutuwar tsaye ta yi dan ko kukan ta gagara yi, ta tabbata asirin Nana ya gama tonuwa.
Papa ya dinga kallon envelope ɗin da Safwan ya bashi ba tare da ya ce komai ba. Safwan ya goge hawayen fuskarsa sannan ya ce
“wannan dalilin ya sanya ba zan iya auren Nana ba! Kuma na san idan ku ka gani zaku tabbatar da gaskiyata”
Daga haka ya sake sunkuyar da kansa. A hankali Papa ya buɗe envelope ɗin ya zaro hotunan gaba ɗaya, Sai dai abin da idanunsa suka gane masa sune suka sanya shi cikin wani hali na kiɗima da tashin hankali. Ya yi baya kamar zai faɗi Hamid ya tare shi yana amsar hotunan, ɗaya bayan ɗaya ya dinga buɗe su zufa na keto masa. Papa kuwa zaman daɓaro ya yi kan sofa ya tallafi fuskarta da duka hannayensa biyu, ban da innalil lahi babu abin da yake maimaitawa cikin ransa.
Sultan ne ya ƙarasa wajen Hamid ya fizge hotunan yana buɗe su, ya kasa ɓoye tashin hankalinsa a fili ya shiga furta
“Innalil lahi wa ina ilayhi raji'una, Ya subhanallahi!”