Sashe 88
Naanah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
“Kalleni! Ni Khadijah nafi ƙarfin ka ce zaka aureni wallahi! Ban da ma ƙaddara ta kawoni wajenka kai baka isa ko ganina ka yi ba. To idan ka aureni sai ka ajiye ni a ina? A wannan kejin gidan naka? Dame zaka ciyar dani? Ko kana son kace min da wannan banzar lalatacciyar sana'ar taka? To ka kama kanka tun wuri. Na rantse makamanciyar wannan maganar na sake ji a bakinka sai na saka an ɓatar min da kai. Baka san hau ɗina bane...”
Taja wani dogon tsaki ta sunkuya ta dauki jakarta ta zura takalmanta ta bar soron a fusace. Malam Garba ya bita da idanu sai kuma ya girgiza kansa ya koma ya zauna yana sauke nunfashi.... Kasa haƙuri ta yi taje gida, Ta gangara gefen titi tayi parking ta zaro wayarta daga jaka ta hau kiran Kaddu. Sai dai har kiran ya katse bata ɗaga ba, Anty Khadijah taja wani dogon tsaki sannan ta yi wurgi da wayarta ta ci gaba da driving ɗin, Lokaci zuwa lokaci take yin kwafa ko kuma ta girgiza kanta, har wani cije baki take na zallar masifar dake cinta.
****
Amma ta dinga kallon ta ganin yanda take kukan har sannan, Ta ajiye mug ɗin a gefen drawer sannan ta hawo kan gadon. A hankali ta dafa kafaɗarta cikin son kwantar mata da hankali ta ce
“Ya isa haka Haule, Ki yi haƙuri ki yarda da ƙaddara. Haka Allah ya yi aurenku ba zai daɗe ba, ki daina damun kanki kin ji.”
Gyaɗa mata kai Haule ta yi bayan ta goge hawayenta, Amma ta yi shiru tana kallon yarinyar cike da tausayawa, Dole taji babu daɗi dan mutuwar aure ba ƙaramin abu bane. Ko faɗa kuke idan ku ka rabu sai kun ji a jikin ku, ballantana kuma ana zaune lafiya babu wani tashin hankali a ce miki an sake ki.
“Tashi ki je ki wanke fuskarki ki zo ga tea na kawo miki.”
Amma ta yi maganar a sanyaye. Toh kawai Haule ta ce duk da bata jin zata iya shan tea ɗin amma ta sauka daga kan gadon ta nufi hanyar banɗakin jiki a sanyaye, Wanke fuskarta ta yi ta fito ta ɗan ja ta tsaya a jikin ƙofar ta riƙe kanta. Amma dake lura da ita ta ce
“Lafiya?”
Girgiza mata kai ta yi, sannan ta fara tafiya hannunta dafe da kanta. Idanunta ne suka fara lumshewa, ta riƙe kanta da hannu bibbiyu saboda wata irin sarawa, Ganin haka ya sanya Amma tasowa sai dai kafin ta iso gabanta tuni Haule ta faɗi ƙasa a sume. Cikin tashin hankali Amma ta durƙusa a gabanta, Ta ɗagota tana kiran sunanta, lura da bata cikin hayyacinta ya sanya Amma tashi ta fice daga ɗakin da sauri.
****
Upper East side,
New York.
A hankali ya fara buɗe idanunsa, Ya kalli Nana wadda ta riƙe shi sosai fuskarta a kwaɓe kamar mai shirin yin kuka, Hannunsa ya sanya ya janyeta daga jikinsa sannan ya tashi zaune yana kallon agogon dake maƙale a ɗakin, Ƙarfe 1:20 na rana. Dan haka ya zame duvet ɗin daga jikinsa ya sauka daga kan gadon, bedroom slippers ɗin dake ƙasan gadon ya zura a ƙafafunsa sannan ya nufi toilet. Bayan kusan mintuna talatin ya fito yana tsane kansa da towel, Yayinda jikinsa ke ɗigar ruwa, Gaban mirror ɗin sa ya ƙarasa, Ya saka dryer ya busar da kansa sannan ya shafa mai, Bayan ya gama ya gyara kansa ya feshe jikinsa da turaren Arabian oud mai daɗin ƙamshi. Ya ƙarasa gaban katon press ɗin dake gefen mirror ya buɗe, kayane a jere a ciki, kowane abu an ajiye shi a mazauninsa. Wasu t-shirt da 3-quater ya dauƙo, Ya warware su daga jakarsu sannan ya saka. Rigar fara ce tas sai ƙaton hoton mage a jiki kamar ya yi magana, Wando kuma blue colour ne mai aljihu dayawa. Wata p-cap ya dauko white ya ɗora akansa, gashin kansa ya sauka a gefe da gefe na kafaɗunsa. Ya ɗan kalli kansa a jikin madubi yana suɗe lips ɗinsa yana kuma taunesu a lokaci ɗaya. Ta jikin madubin ya hangota sai wargaza gashin kanta take, Ya sauke numfashi kafin ya juya yana kallon ta. Ita ma kallon nasa take da lumsassun Idanunta, Ya ƙarasa wajen cikin takunsa na isa da tagama. Wayarsa ya ɗauka akan drawer ya ɗan danna ganin har sannan tana zaune yasa ya ce
“Idan na fita ba zan dawo ba sai dare.”
Miƙewa tsaye ta yi tana kallon sa, sai a sannan ta tuna da ƙofar key gareta. Ta nufi toilet da sauri gudun kada ya tafi ya barta. Sabon brush ta ɗauka ta wanke bakinta sannan ta wanke fuskarta ta goge da towel sannan ta fito. Bata gan shi a ɗakin ba, Taji gabanta ya yi wani irin faɗuwa. Kamar mara gaskiya haka ta fara leƙa kowace kusurwa ta ɗakin tana cewa
“Uncle... Uncle... Uncle!”
Wani zaburraren ihu ta saka jin an riƙeta, Ya yi baya yana murmushi ya ce“Matsoraciya kawai.” marairaice fuska ta yi kamar zata yi kuka ta ce“Uncle ka bani tsoro wallahi.” Bai ce mata komai ba sai murmushi da yake a hankali, Dimple ɗinsa na lotsawa kamar ka yi ajiya a wajen. shagala ta yi da kallon sa, ganin yanda asalin kyawunsa ya bayyana. Ya ja hancinta ya ce
“Bar kallona yarinya.”
Ji ta yi kamar ta nutse saboda kunya, Ta yi gaba ba tare da ta ce komai ba ta fice daga bedroom ɗin. Girgiza kansa ya yi sannan yabi bayanta shima, Tana tsaye ya saka password ɗin ya buɗe ƙofar sannan suka fito. Kai tsaye kuma downstairs suka nufa, Xahra dake zaune akan sofa ita da Noor ta dinga kallon su da ɗan mamaki dan bata san sanda Nanar ta je apartment ɗinsa ba. Ita kuwa Nana hannunta ta zura a tsakanin nasa, ta riƙe shi gam kamar wadda taga abun tsoro. Zahra ta ɗauke kanta tana ci gaba da nunawa Noor videon da suke gani. Yarinyar na ganinsa ta taso da gudu ta rungumeshi ya sunkuya ya ɗauketa ya ɗorata a kafaɗarsa yana murmushi ya ce
“Yarinya kin dawo gida ko?”
“Abbie gobe zan ci gaba da zuwa school?”
Ta yi maganar tana ƙoƙarin jan gashin kansa. Gyaɗa mata kai ya yi kafin ya ce
“Yeh! Idan naci abinci sai ki zo muje a siya miki kayan tafiya school ko?”
Sake ƙanƙameshi ta yi tana dariya ta ce
“Yeeee Abbie i love u so much!”
Ya ja kumatunta yana dariya ya ce“love you too my baby girl.” Ya ƙarasa kan sofa ya zauna yana kallon Zahra ya ce
“Madam ki shirya idan na gama cin abinci zamu fita.”
“Okay doctor.”
Ta ce a sanyaye sannan ta tashi ta bar wajen, Nana ta bita da kallo sai kuma ta taɓe baki na zauna can nesa dasu tana kallon su ganin yake ta yiwa Noor ɗin wasa ita kuma tana dariya. After some minutes aka fara shigo da abinci, Cikin ƙankanin lokaci aka cika tsakiyar parlourn da nau'in abinci kala-kala, Dan shi ya ce masu ba zai ci a dining ba. Nana ta dinga kallon su har suka gama suka bar wajen, Ita dai bata motsa daga inda take ba ballantana taje inda abincin yake. Ya sauke Noor daga jikinsa sannan ya zamo ƙasa ya zauna dan ba ƙaramar yunwa yake ji ba. Kallon abincin ya yi sai kuma ya kalli Nana dake zaune kan kujera ya ce
“Zo ki ban abinci.”
Da ɗan mamaki ta dinga kallon sa, kamar wadda ta tuna wani abu kuma sai ta taso ta ƙaraso wajen, Da kansa ya dinga nuna mata yanda zata yi har ta gama haɗa masa ta miƙa masa. Ganin tana shirin tashi yasa ya ce
“Ke ba zaki ci abincin ba?”
Girgiza kanta ta yi kafin ta ce“Ni na ƙoshi.”
“Ko?”
Ya yi maganar yana watsa mata wani kallo wanda ya sanyata shiga taitayinta. Kasa motsi ta yi, Ya ɗauki mug ɗin coffee ɗin ya kai bakinsa bayan ya yi bismillah. After ya cire daga bakinsa ya miƙo mata, Ta dinga kallon sa sai kuma ta saka hannu zata karba, Ya doke hannun yana sake matsowa dashi wajen bakinta. Jiki a sanyaye Nana ta buɗe bakinta ya bata coffee ɗin, Ta ɗan lumshe idanu saboda zaƙin da taji. Haka ya dinga shan coffee ɗin yana bata yana haɗawa da hamburger, Sai da yaji ya ƙoshi sannan ya zare hannunsa yana kallon ta ya ce
“Kin ƙoshi?”
Saurin gyaɗa masa kai ta yi dan daman tun ɗazu take jiran taji ya ce mata hakan. Ya zabga mata harara ya ce“to sai kin cinye wannan raguwar” Ya nuna mata ragowar wadda ke plate ɗin wadda tafi rabin guda. Marairaice fuska ta yi tana tura ragowar ta bakinta ta ce
“wallahi uncle na ƙoshi, zan yi amai.”
“To ki yi ɗin.”
Ya faɗa in i don't care manner ɗin nan. Ganin ya ƙara dauƙowa yana nufo bakinta ya sanyata fashewa da kuka, Ta rufe bakinta tana girgiza masa kai. Kallon ta ya dinga yi can kuma ya mayar ya ajiye rai a haɗe ya ce
“Tashi ki bani waje.”
Kamar jira take ta tashi da gudu ta bar parlourn ta nufi benanta. Ya bita da kallo sai kuma ya girgiza kansa, A parlour ta fadi tana sauke numfashi, Ta dafe cikinta wanda take jin ya yi mata wani irin nauyi. Ita bata saba cin abinci dayawa haka ba, Duk haɗamarta abinci kaɗan ke isarta, Ta jingina da gefen kujera tana sauke numfashi.
Wajejen ƙarfe 3:00 na rana ya turo ƙofar ɗakin, Kwance ya hangeta cikin bargo ta lulluɓa har kanta, Ya harɗe hannayensa a ƙirji yana kallonta ya ce
“Nana!”
“Na'am...”
Ta amsa muryarta na rawa. Sam bai fahimta ba dan ya yi zaton bacci ne akanta, Dan haka ya ce
“Taso muje unguwa.”
Girgiza kanta tayi tana daga kwancen da take ta ce“Ni bana so.”
Shiru ya yi yana kallonta, Ya ɗaga kafaɗarsa sannan ya juya ya fice daga ɗakin, Ta sake juyi ta koma can ƙarshen gadon tana runtse idanunta. Tsaye ya samu Zahra a parlourn tana gyarawa Noor bottle ɗin rigar sanyin dake jikinta, Ya ƙarasa ya ɗauketa yana faɗin
“Ya kamata mu yi sauri, cause naga garin da hadari sosai.”