← Book details Naanah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 125

Sashe 5

Naanah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ko minti biyu basu yi a ɗakin Papa ba suka fito, Maimoon ta tsaya tana kallonta ta ce"wai wane turaren ki ka je ɗiba?" ɗaga kafada ta yi ta ce"ni ina ma na sani, kawai naji yana da ƙamshi, sai na ɗiba"

"To ina yake?"

A sanyaye ta ce"ya fadi ya fashe" taɓe baki Maimoon ta yi ta ce"asara". Nana ta ce"wai kuma a haka Hameeda take cewa tana sonsa? Wannan ai sai ya kasheta da masifa barin ita da bata iya ramawa ba" harararta Maimoon ta yi ta ce"ki bari aji wannan maganar a bakin ki wallahi babu ruwana yawwa" tura baki ta yi tana yin gaba da ƙarfi ta ce"to aji ɗin mana, sai me?" Daga haka ta sauka daga stairs ɗin, Maimoon ta girgiza kai sannan tabi bayanta.

****
Mama ta dinga kallonta da mamaki kafin ta ce"mene ne haka Hameeda? Meke damunki?" sunkuyar da kanta ta yi a sanyaye ta ce"babu komai Mama" rai ɓace Mama ta ce"ni ki ke cewa babu komai ko? Ni zaki kalla ki cewa babu komai!"

Sallamar da aka yi ya sanya ta yi shiru, ya dinga kallonsu kafin ya ƙarasa gabanta. Ya kalli Hameeda dake zaune kan kujera kanta a ƙasa sai kuma ya kalli Mama dake tsaye ya ce"lafiya dai Mama?"

"Ina fa lafiya Safwan, wai ni Hameeda ke kalla ta cewa lafiyarta kalao bayan tun da rana nagane akwai abin da ke damunta, amma ta faɗa min taƙi"

Safwan ya kalleta a sanyaye ya ce"Hameeda ke dawa?" Tashi tsaye ta yi muryarta na rawa ta ce"babu komai fa Yaya, kawai ina missing Aun ne shiyasa" daga haka tabi ta gefensu ta nufi ɗakinta. Da mamaki duk suka bita da kallo, ya sauke numfashi ya ce"Allah ya kyauta" Amin kawai Mama ta ce, ya miƙa mata ledojin hannunsa ya ce"Abbansu Hamid ya ce na kawo miki" okay kawai ta ce sannan ya juya ya fita. Koda ta shiga ɗaki kwanciya ta yi ta ci gaba da rera kukanta kamar wadda aka yiwa albishir da mutuwa, ita kanta bata san dalilin kukan nata ba, a haka har bacci ɓarawo ya saceta.

2weeks later.
7:30 na safe

Amma ta turo ƙofar ɗakin ta shigo hannunta riƙe da mug, kwance ta sami Nana kamar yanda ta barta. Ta ƙarasa ta ajiye mug ɗin akan drawer sannan ta hau gadon, yaye duvet ɗin data lulluɓa ta yi, idanunta a rufe yake sai rawar sanyi take ga kuma gumi daya cika fuskarta. Amma ta riƙe hannunta ta ce"tashi ki ɗan sha tea ɗin kafin Abbanki ya fito ya kai ki asibiti" dakyar Amma ta taimaka mata ta tashi zaune ta jingina da jikin gadon tana hawaye, sauka tayi ta ɗauko mug ɗin ta dawo ta miƙa mata. Hannunta na rawa ta karɓa ta kai baki, ko kwata bata sha ba ta miƙawa Amma tana girgiza kai.

"Kin shanye zai taimaka miki"

Muryarta na fita da kyar ta ce"Amma ba zan iya ba" daga haka ta sake komawa ta kwanta ta ci gaba da birgima akan gadon. Kallonta kawai Amma ta dinga yi cike da tausayawa dan tasan azabar irin wannan ciwon, ta tashi ta fice daga ɗakin da sauri. Tana ƙoƙarin shiga ɗakin ya fito, sanye yake da wata shadda sky blue, daka gansa kasan kuɗi ya zauna.

"Daman kiran ka zan yi"

Amma ta yi maganar da damuwa a fuskarta. Abba ya ce"ya jikin nata?" Girgiza kanta ta yi ta ce"da sauƙi za'a ce, kaje ka kaita asibitin dan Allah" okay kawai ya ce sannan ya nufi ɗakin nata da kansa. A durƙushe ya sameta ya ƙarasa ya tsaya yana kallonta ya ce"Daughterna" ɗago kanta ta yi ta kalleshi kawai sai ta fashe da kuka, da kansa ya kamo hannunta ya sakko da ita, ya taɓa jikinta. Zafi sosai yaji ya janye hannunsa ya jingina da jikinsa yana cewa"Ya jikin naki?" kasa magana ta yi sai kuka da take faman yi, girgiza kansa ya yi daidai lokacin da Amma ta shigo ya kalleta ya ce"ɗauko mata riga" okay kawai ta ce sannan ta ƙarasa press ɗinta. Abaya ta ɗauko da veil ta miƙo masa, da kansa ya sanya mata sannan yaja hannunta suka fita daga cikin ɗakin.

Suna fitowa daga gidan motarsa na yin parking a compound ɗin, Abba ya dinga kallon motar har ya fito daga ciki, sanye yake da ƙananun kaya daga ganinsa kasan shirin fita ya yi. Ya dinga kallonsu har ya ƙaraso wajen ya ɗan risina ya ce"Good morning Abba" fuska a sake Abba ya ce"Morning Sultan, ka tashi lpy?"

"Alhamdulillah"

Ganin irin yanda take kwance a jikinsa ya sanya ya ce"Abba lafiya dai?" Girgiza kai Abba ya yi ya ce"wallahi Sultan wai bata da lafiya, cramps ke damunta tun cikin dare, kuma kasan yanda take yi, so shine zan kai ta asibiti" Sultan ya ɗan girgiza kansa ya ce"Ayyah subhanallahi, to ko zan tafi da ita asibitin ne Abba? Kai sai ka huta kaga" Abba ya yi murmushi sannan ya ce"Da naji daɗi wallahi dan daman ina da appointment da Ig kawai dai zan kai ta ne" Sultan ya ce"kawai ka je Abba, bari mu tafi tare" okay ya ce sannan ya ɗagota daga jikinsa. Kuka ta saka muryarta bata fita ta ce"a'a Abba ni ba zan bi Yaya ba" cikin rarrashi ya ce"sorry daughter ki bishi kin ji, idan nagama da wuri zan zo" kuka ta dinga yi ba tare da ta yi magana ba. Shi dai Sultan ya tsaya yana kallonta.

Abba da kansa ya kai ta motar ya kwantar da ita sannan ya rufe ƙofar yana faɗin"take care son" Sultan ya yi murmushi ya ce"in sha Allah Abba" daga haka ya shige motar ya juya ya bar compound ɗin. Sai da suka fita daga estate ɗin gaba ɗaya sannan ya yi parking, ya juyo yana kallonta fuskarsa a haɗe kamar bai taɓa dariya ba ya ce"

08106608363
Nanameera.*🌹 NAANAH 🌹*

Masu nema daga farko su yi following WhatsApp channel nawa

https://whatsapp.com/channel/0029Vb250h2HVvTaF6S0UP3L

Page 4...

"Malama rufe min baki, sai shegen son jiki ki ka ajiye, ki tashi zaune tun kafin ranki ya ɓaci" Nana ta dinga kallonsa hawaye na biyo kan fuskarta, daman tasan haka zai yi mata idan sun rabu da Abba. Kwafa ya yi ganin bata tashin ba ya juya ya ci gaba da driving ɗinsa. A babban parking space ɗin specialist hospital yola ya yi parking motar, ya sauka ba tare da ya kalleta ba. Sai da ya fito sannan ya buɗe back seat ɗin ya dinga kallonta, kwance take kamar matacciya sai sauke numfashi take. Ya gyara tsaiwarsa sannan ya ce"sakko" shiru ta yi masa ba dan bata ji maganar tasa ba, sai dan ba zata iya bashi amsa ba. Ya ɗan haɗe rai ya ce"ina magana da gunki ne Nana?" sai a sannan ta ɗago kanta, tana kallonsa da idanunta wanda suka kumbura ta ce"wallahi Yaya ba zan iya tafiya ba" ta yi maganar da iya gaskiyarta, baki buɗe Sultan ke kallonta sai kuma ya ce"to yanzu ya ki ke son nayi miki?" madadin ta bashi amsa kawai sai ta sake fashewa da wani sabon kukan, tana dafe mararta. Ganin da gaske take ya sanya ya zura kansa cikin motar ya jawo hannunta. Ya fito da ita daga motar, ganin ta yi baya zata faɗi ya sanya ya jawota jikinsa ya riƙeta sosai. Ƙoƙarin rufe motar ya yi idanunsa ya sauka akan kujerar ganin yanda gaba ɗaya ta ɓaci da stain, ya girgiza kansa sai kuma ya mai da idanunsa kanta, ya rufe motar sannan ya janyeta daga jikinsa ya jingina da motar gudun kada ta ɓata masa jiki. Idanunta a rufe yake tana sauke numfashi dakyar ko ba'a faɗa maka ba kasan ba ƙaramar wahala take sha ba. Sosai ta bashi tausayi dan hakan ya kwantar da muryarsa cikin sanyi ya ce" ki daure ki taka kinji, kin ga jikinki ya ɓaci da sai na ɗaukeki" shiru tayi har sannan bata daina hawaye ba, ya sake cewa "Nana"

Gyaɗa masa kai kawai ta yi sannan ta buɗe idanun nata, hannunta ya riƙe suka fara tafiya a hankali har suka shiga cikin reception na asibitin. Gaisheda shi nurses suka fara yi, ya dinga amsawa cike da fara'a. Wata nurse ya samu ya ce ta raka Nana ɗaki yana zuwa, ta riƙe hannunta sannan ya nufi hanyar office ɗinsa.

****
Ƙarfe 8:20am Aliyu ya shigo parlon, zaune ya samesu suna breakfast, ya ƙarasa yaja kujera ya zauna idanunsa zube kan Hajiya Babba ya ce"ina kwana Hajiya?" Da murmushi a fuskarta ta ce"lafiya kalau Aliyu ka tashi lafiya?"

"Alhamdulillah" ya ce a takaice.

"Good morning Yaya"

"Good morning Bro"

Suka gaida shi a tare, ɗago kansa ya yi ya kallesu. Hameed ne da Safwan, ya ɗan yi murmushi sannan ya ce"morning ya kuke?"

"Alhamdulillah" Cewar Hameed yana miƙewa. Kallonsa duk suka yi kafin Aliyu ya ce"ina kuma zaka je?" Hameed ya ce"wallahi Bro I have alot to do ne a office, shiyasa nake sauri na tafi" jinjina kai Aliyu y yi sannan ya ce"Alright a dawo lafiya" Amin ya ce sannan ya mai da idanunsa kan Hajiya ya ce"Sai na dawo Hajiya"

"Allah ya bada abin da ake nema"

Ya amsa da murmushi sannan ya dafa Safwan ya ce"Barrister sai na dawo" harararsa Safwan ya yi sannan ya ce"Judge a dawo lafiya" dariya suka yi duka sannan ya juya ya bar wajen. Aliyu ya bishi da kallo har ya fita sannan ya ce"sometimes idan Hameed na yin abubuwa sai naga kamar Buddy wallahi" Safwan ya ajiye spoon ɗin hannunsa yana cewa"wallahi nima haka Yaya, irin halayensu ɗaya, kawai dai Yaya ya ɗan fisa rashin son hayaniya" Aliyu ya ce"Eh shi ne kawai abin da ya raba su, shi Buddy baya wasa, shi kuma Hameed yana son wasa" Safwan ya ɗan yi shiru sai kuma ya ce"Wai yaushe zai dawo Yaya? Wallahi we miss him alot" Ɗan murmushi Aliyu ya yi sannan ya ce"to sai dai ka tambayeshi dan ni ban sani ba" Safwan ya tashi yana cewa"Ni babu ruwana" dariya kawai Aliyu ya yi, Hajiya da ke cin abincinta tun ɗazu ta ce"zai maka faɗa ne dan ka tambayeshi?"

Safwan ya ce"Hajiya kin fa san halin kayanki, yanzu sai ya ciremin supsidy"
Chapter 5 · 0% Book details