← Book details Naanah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 125 OF 125

Sashe 125

Naanah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shi dai Abdusammad Ban da murmushi babu abin da yake, Dan tun da aka sanar dashi haihuwar bakinsa ya zaga rufuwa, Nana ta ɗaga kai ta kalleshi, Ya daɗa wani irin girma, Kwarjini da kuma haiba. Ya ƙara zama babban mutum kana ganinsa ka san kwanciyar hankali da jin daɗi sun zauna. Ya ƙarasa kan kujera ya zauna idanunsa zube kan yaran da ke hannun Mama, Ɗaya bayan ɗaya ya gaishe su, Suka amsa sannan suka yi masa Barka. Mama da kanta ta tashi ta miƙa masa yaran duk biyun, ya amsa ya riƙe a hannunsa yana murmushi, Bai san kalar farin cikin da yake ciki ba shi kansa. Ji yake kamar ya tashi ya taka rawa da ya'yansa, Allah mai kyauta da ya ɗauke masa ɗaya sai ya bashi biyu a tare, Sun daɗe a hannunsa kafin su Aliyu suka shigo, Nan fa aka zauna ana faman hira da shafta. Duk wannan abun da ake babu bakin Nana a ciki, Hawaye taf cikin idanunta, Bata yi tunanin zai kasa yi mata magana ba, Daga ƙarshe ta tashi ta haye sama jiki a sanyaye. Hajiya Babba na lura dasu, amma bata ce komai ba. Sai da aka fara kiran sallar la'asar sannan suka tashi suka fita, Bai sake dawowa gidan ba sai bayan sallar isha'i, Hajiya Babba kawai ya iske a parlourn Kowa ya tafi gida, Ya zauna suna magana can dai ta ce

“Abdusammad mene haka? Me ke damun ka? Me yarinyar nan ta yi maka? Koma me ya haɗaku bai ci ka haƙura ba yanzu? Tun ka zo baka kalleta ba, Ballantana ka ce mata ya ta sauka ko ya jikinta, wace irin rayuwa ce wannan?”

Shiru ya yi yana sauraren Hajiya Babba, Ta dinga yi masa faɗa ta inda take shiga ba ta nan take fita ba. Dakyar ya samu ta yi shiru bayan ta ce ya je ya ganta, Shi dai bai ce komai ya tashi ya nufi saman. Tana zaune gefen gado ta zuba uban tagumi, Yaran na kwance tsakiyar gadon suna bacci, Bakinsa ɗauke da sallama ya shigo. Ta ɗaga kai ta kalle shi dan bata yi tunanin zai zo ɗin ba, Ƙarasawa ciki ya yi ya zauna gefen gadon yana kallon yaran, Can dai ya kalleta ya ce

“Ya jikin naki?”

Madadin ta bashi amsa sai kawai ta fashe da kukan dake cin ta tun ɗazu, Ya yi shiru yana saurarenta, Can dai ya tashi ya koma daf da ita ya kamo hannunta ya ce

“Ke tambayar ki nayi ya jikin ba ba cewa nayi ki isheni da kuka ba, Ke baki san kin girma ba yanzu? Baki gan ki da ya'ya ba!”

Kukanta ta ci gaba da yi, Ya rungumeta yana murmushi ya ce

“Thank you kin ji. Allah ya yi miki albarka Mamana, Kin sakani farin ciki, naji kamar na yi kuka Nana. Thank you kin ji, Allah ya albarkaci rayuwar ki data ya'yanmu, Ya sa nan gaba ki haifa min yan uku”

Ya ƙare maganar yana jan hancinta, Tura baki ta yi ta maƙale a jikinsa cikin kuka ta ce

“Uncle zafi kamar zan mutu. Bana so na sake haihuwa”

Shafa kanta ya yi ya ce“Sorry kin ji, ai next tare zamu raba zafin, yanzu ma dan kin gujeni ne.”

Bata ce komai ba sai shigewa jikinsa data sake yi, Tana jin wata irin nutsuwa ta musamman na saukar mata, Wadda take da nasaba da kewar mijin nata da ta yi. Sati ya zagayo aka yi gagarumin suna mai ban mamaki, Ko sunan su Maimoon da aka haɗe bai kai shi haɗuwa ba. Iyaka kuɗi Abdusammad ya ɓarnatar da dukiya, Komai na wajen bana masu ƙananan ƙarfi bane, Tun daga kan mai jegon da shigarta da kuma ya'yan, Kafin azo ga uban Ya'yan. Ɗaiɗaiku ne basu zo ba a dangi, haka ma abokansa da ke America duk sun zo, Har da su Zahra sai da suka zo sunan, Khadijah ma sun zo ita da Mami. Yara suka ci sunan Amma da Atta, Ake ce musu Habibti da Noor. Hotuna kuwa wanda aka manta ne kawai ba'a ɗauka ba, Duk irin rashin son mutane na Abdusammad haka ya saki jikinsa aka dinga ɗaukan hotuna, Ana ɗaukan su wani hoto shi da Nana Aliyu ya yi dariya ya ce

“Wai wannan ai kai ne Abul banin ɗin (Baban ya'ya mata)”

Murmushi kawai Abdusammad ya yi ya ce

“Faɗi ka ƙara.”

Kyaututtuka kuwa ba'a maganar su, Nana ta samu abubuwa masu tarin yawa na kayan barka, Abdusammad kuwa takardun Company ya danƙa mata a matsayin kyautarsa, aka saka ihu a wajen ana tafi. Sai dare sannan kowa ya watse ya tafi gida, Suma suka koma ciki dan huce gajiya.

****
Five years later(5).

Saukar su kenan daga jirgin, Tana rike trolley ɗinta ɗayan hannun kuma ta riƙe wata yarinya, Shima tafiya yake rike da hannun ɗaya yarinyar suka nufi inda driver ya zo ɗaukan su, Suna ƙoƙarin shiga mota taji an kira sunanta, Ba ita kaɗai ba har Abdusammad sai da ya juya dan ganin wanda ke kiran sunan matar tasa, Junaid ne a tsaye yana murmushi. Nana ta dinga kallon sa sai kuma ta ɗan saki fuskarta, Ƙarasowa gabansu ya yi suka gaisa da Abdusammad cikin fara'a, Ya durƙusa daidai tsayin Habibti dake rike da hannun Abdusammad, kyakkyawar baturiyar yarinya sai kallon rashin sani take masa, Ya miƙa mata hannu ya ce

“Hi”

Cikin siririyar muryarta irin ta yara ta ce

“Hello.”

Ya yi murmushi sannan ya miƙawa Noor ma, Kamar su ɗaya da juna, Idan har ba wani sanin su ka yi ba to zai maka wahala ka tantance su. Sai da Junaid ya gama yi masu wasa sannan ya mike tsaye yana kallon Abdusammad ya ce

“Yara sun girma Sir, Allah ya raya.”

Murmushi Abdusammad ya yi ya ce“Amin ya rabbi thank you.”

Sai a sannan ya kalli Nana ya ce

“Nana Allah ya raya”

Da Amin kawai ta amsa dan ta san Abdusammad ba son yaga tana hira da maza yake ba. Shi ma Junaid bai damu ba ya yi musu sallama ya juya ya bar wajen, Sai a sannan ta sauke idanunta ƙasa tana jin babu daɗi a ƙasan ranta wanda bata san dalilin sa ba. Mota suka shige kai tsaye kuma estate ɗin su suka nufa, Tun daga bakin estate ɗin zaka gane arziki ya ci uban na da, Domin gaba ɗaya an sauya mata fasali zuwa na wannan zamanin. Wani kallon sai ka shiga ciki, Apartment ɗin Hajiya Babba suka nufa dan anan ne ake taron kasancewar lokacin ƙaramar sallah ne ana taron family, Suna shigowa aka fara murna. Nana ta ƙarasa ta rungume Abbanta da gudu, Girgiza kai Abba ya yi ya ce

“Na ga ranar da zaki girma Nana”

Murmushi ta yi sannan ta koma ta rungume Ammarta, Amma ta ce

“Ni wallahi ba zaki ƙarashe ni ba, Ji yanda ki ka zama wata ƙatuwa kin fini” tura baki ta yi tana kallon jikinta. Da gaske ta zama babbar mace, Hamshaƙiya mai faɗa aji a gidan mijinta, Kai daka ganta kaga wadda ke hutawa. Ɗaya bayan ɗaya ta gai da mutanen parlour kafin ta ƙarasa ta faɗa jikin Hajiya Babba, Murmushi kawai Hajiya Babba ta yi ta ce

“Takwarata.”

A shagwaɓe ta ce

“Hajiyar mu mai Makkah da Madina”

Murmushi duka aka yi, Nana ta juya ta kalli Atta wadda ke tabar baki, Tashi ta yi tana zuwa ta rungumeta tana murmushi ta ce

“Attar mu, Har yanzu ba zaki mutu ba wai?”

Turata Atta ta yi tana mele baki ta ce

“Ki gani akan ki, In sha Allah ba zan mutu yanzu ba.”

Ban da dariya babu abin da jama'ar parlourn ke yi, Nana ta koma cikin sauran yan uwanta su Hajiya Maimunatu wanda aka girma, Sun wani nutsu kamar manyan gaske su basu yarda ba sun ajiye iyali dan Maimoon da Amrah Ƴaƴansu biyu, Hamida kuma nada ciki. Sai Haule wadda aka aurawa Saddiq ita ma ta ɗan ƙaramin goyo. Hajiya Babba ta dinga kallon su ɗaya bayan ɗaya can kawai ta fara murmushi mai haɗe da hawaye, Tashi Abdusammad ya yi ya koma kusa da ita ya zauna ya ce

“Hajiya lafiya?”

“Farin ciki nake Arɗo, Allah ya cika min burina, Wasiyyar mahaifin ku bata tafi a banza ba, Allah na gode maka, Allah ya yi muku albarka, Ya baku ikon ci gaba da tafiya akan wannan turbar ta zumunci, Ya ƙara muku arziki da wadatar zuci, Allah ya jiƙan magabantan mu, Ya sa sun huta. Mu kuma ya bamu ikon ci gaba da imani.”

Da Amin kowa ya amsa, Sannan aka ci gaba da hira. Da gudu Ikram ta shigo ta ƙaraso wajen Nana tana kuka ta ce

“Ammi kin ga Noor ko? Sai dukana take”

Girgiza kai Nana ta yi ta kwala wa Noor kira, Shigowa ta yi ta tsaya tana kallon su, Yanayin yanda ta yi kamar Nana na ƙarama, Nana ta haɗe rai ta ce

“Ban hana ki rashin ji ba? Ban ce ki daina dukan mutane ba?”

Tura baki yarinyar ta yi sai kawai ta saka kuka ta fadi a wajen tana birgima, Papa da ke kallon su tun ɗazu ya ce

“Allah mai iko, Dama duk abin da ka yi sai an yi maka. Yau ga Nana ta haifo mai irin halinta, To idan yar Nana taji magana a ina ta samu?”

“A wajen Babanta mana!”

Abdusammad ya amsa yana murmushi, Tuntsirewa da dariya aka yi duka Nana ta tura baki ta ce

“Ai shikenan!.”

*Alhamdulillah! Alhamdulillah! Alhamdulillah. Anan zan ɗiga aya cikin wannan littafi mai taken NAANAH, Ina rokon Allah abin da na rubuta na daidai Allah yasa a ɗauka ayi amfani dashi, wanda kuma nayi kuskure Allah ya gyara mana baki ɗaya. I'm really really appreciate it, Na gode da ƙauna da kuma soyyayar da ku ka nunawa wannan littafi, Allah ya bar mu tare. Ku kasance dani Ameenatou I Ibrahim(Nanameera) Cikin Wani sabon littafin dan ganin abin da zan kawo muku. Tabbas ba zan baku kunya ba🥺🥰, Nanameera heart you guys❤️.*

© Nanameera.
Rate me
Chapter 125 · 0% Book details