Sashe 4
Naanah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Turus ta yi tana kallonsa, zaune yake kan sofa idanunsa zube akan tv, daga bayansa zaka gane babban mutum ne mai ƙiba, da sauri ta ƙarasa gabansa, ta zauna kusa da shi ta ɗora kanta a gefen kafaɗarsa. Ɗago kansa ya yi ya kalleta yana murmushi, Kyakkyawan bafulatani ne mai matuƙar kama da ita, ya shafa kanta cike da nutsuwa ya ce "Khadijatou" madadin ta amsa masa kawai sai ta fashe da kuka tana sake rikeshi, Ya girgiza kansa fuskarsa a sake ya ce"rigimar na mene ne kuma?" kasa magana ta yi sai shessheƙar kuka take, Amma dake zaune kujerar dake facing tasu ta dinga kallonta sai kuma ta taɓe baki. Ganin bai ce komai ba ya sanya ta kalleta a ɗan tsawace ta ce"Idan baki da abin faɗa tashi ki bar nan!" Ƙin juyowa ta yi amma tafara rage kukan nata, Alhaji Ahmad ya yi murmushi ya ce"ki yi shiru ki faɗa min me aka yi miki?" Sauke ajiyar zuciya ta dinga yi kafin ta ɗago daga jikinsa tana kallonsa ta ce"Abba kawai nayi missing ɗinka ne fa" girgiza kansa ya yi dan daman ya san kwanan zancen, ya ce"to ba gashi kin dawo ba Nana? Uhm, yanzu kukan na mene ne?" Tura baki ta yi ta ce"Abba shikenan yanzu na bar Aun? Duk friends ɗina mun rabu" Abba ya ce"Ai daman haka yake Nana, komai akai kira zai zo ya shige" ta gyaɗa kanta ta ce"Eh haka Mommy ta ce mana, ta ce daman haka rayuwa take" Abba ya jinjina kansa ba tare da ya sake cewa komai ba. Shiru parlon ya ɗauka kafin ta sake gyara zama ta ce"Abba ina alƙawarina?" Tashi ya yi yana gyara zaman hular kansa ya ce"baki manta ba kenan?"
"I'll not"
Ta faɗa tana washe baki.
Hannunsa ya miƙo mata ta ɗora nata a kai ta miƙe tsaye, waje suka nufa Amma ta bisu da kallo kafin ta ce"a haka zata fita?" Sake kallonta ya yi sai kuma ya ce"and what's wrong with her dress?" Amma ta girgiza kanta ba tare da ta sake cewa komai ba, ya juya suka fice daga parlon.
Tafiya suka dinga yi suna hira kamar abokai, yana ɗaya daga abin da ya sanya take son dawowa gida saboda Abbanta. Yanda suke hira dashi koda Amma bata yi, dan ita Amma tana da ɗan zafi wani lokacin, saɓanin Abba da kome take so shi yake yi. Ganin sun nufi gidan kawu ya sanya ta ce"Abba wajen Uncle zamu je?" Eh ya ce mata yana gyara zaman glasses ɗinsa.
****
Bakinsu ɗauke da sallama suka shiga, Ummi dake zaune kan kujera ta tashi tana murmushi ta ce"wa'alaikummusalam, Sannu da zuwa Alhaji" Abba ya jinjina kansa ya ce"Yawwa sannu Maryam, Yaya yana ciki ne?" Ummi ta ce"Eh yana nan, bismillah" Abba ya saki hannun Nana sannan ya nufi hanyar apartment ɗin Alhaji Kabir ɗin. Ummi ta kalli Nana ganin yanda ta tsaya ta ce"Mai sunan Hajiya Babba zo ki zauna mana" To kawai ta ce sannan ta nemi gefen kujera ta zauna, Ummi ta ce"Nayi tunanin ai ba zaki shigo ba, kin dawo babu ko ziyara" ɗan murmushi ta yi ta ce"to ai daman jira nake Abba ya dawo sai na biyoshi" Ummi ta harareta ta ce"da yake bakisan hanyar nan ɗin ba ko" tuntsirewa ta yi dan dariya ganin irin kallon da Ummin ke mata kafin ta ce"Ai Amma ce ta hanani fitowa, cewa ta yi na zauna na huta" ta taɓe baki ta ce"ita Rabi'an?" Ta gyaɗa mata kai, Sallamar da aka yi ya sanya ta ɗaga idanunta ta kalleshi.
Ya ƙaraso parlon ya zauna akan kujera ya ɗan yi baya yana jingina da kujerar ya ce"subhanallah!" Ummi ta kalleshi ta ce"har ka dawo?" Ya gyaɗa mata kai ba tare da ya yi magana ba. Ummi ta mayar da idanunta kan Nana wadda ta haɗe rai kamar ba ita ba, ta ce"zo muje kitchen na baki abu ki kai wa su Papa" kamar jira take ta miƙe tsaye tana cewa"to Ummi" daga haka ta nufi kitchen ɗin ba tare da ta yarda ta kalli inda Sultan yake ba. Sai da yaga duk sun shige kitchen sannan ya ɗago kansa ya kalli hanyar, ya miƙe ya nufi upstairs da sauri. Drinks ta zuba mata akan wani ɗan madaidaicin tray ta miƙa mata tana cewa"kai sai ki dawo ki kai musu abinci" to kawai Nana ta ce ta karɓa sannan ta fita daga kitchen ɗin. Da idanu tabi inda ya zauna da kallo ganin bayanan ya sanya ta taɓe baki, tana gama hawa saman ta kalli hanyar ɗakinsa sai kuma ta shige da sauri.
Zaune ta samesu suna tattaunawa, Ta ajiye tray ɗin a ƙasa sannan ta durƙusa cike da ladabi ta ce"Papa ina yini?" Alhaji Kabeer dake zaune kusada Abba ya yi murmushi ya ce"lafiya kalao Nana, an dawo lafiya?"
"Alhamdulillah"
Ta bashi amsa tana wasa da fingers ɗinta, jinjina kansa ya yi ba tare da ya sake magana ba, ganin haka ya sanya ta tashi ta fice daga ɗakin. Ta dinga kallon ƙofar ɗakin kamar ta shige sai kuma ta ƙarasa, a hankali ta murɗa handle ɗin tana ɗan runtse idonta. Ta ɗan sauke ajiyar zuciya jin ƙofar a buɗe, tura ƙofar ta yi ta shiga, tayi saurin jan numfashi saboda wani irin ƙamshi daya daki hancinta, ga wani irin sanyin ac mai shiga jiki. Ta maida ƙofar ta rufe a hankali a ranta ta ce"ko meyasa yake son sanyi oh!" Ta dinga kallon tsaftace ɗakin wanda yaji luxury furnitures, komai na ɗakin white colour ne, dan ita ce favorite colour nasa, ba zaka taɓa cewa ɗakin namiji bane saboda yanda yake neat dashi, komai a muhallinsa. Ganin baya cikin ɗakin ya sanya ta nufi inda press ɗin kayansa take tana tafiya kamar mara gaskiya, buɗewa ta yi without making any sound, kayan ciki a linke suke kuma a tsaftace, komai an jera shi a inda yake, ta taɓe baki sannan ta fara dube-dube. Above 2mins amma bata samu abin da take nema ba, dan haka kawai ta miƙe ta rufe press ɗin. Drawer dake dressing mirror ta kalla sai kuma ta ƙarasa wajen da sauri ta buɗeta, murmushi ta yi ganin abin da take neman. Ta sanya hannu ta ɗauko empty bottle ɗin ta buɗe, gaba ɗaya ƙamshi ya gauraye ɗakin, ta kai bottle ɗin hancinta ta shanshana sai kuma ta yi murmushi a fili ta ce"A siyan turare kuɗinsa ke ƙarewa" daga haka ta mayar da drawer ta rufe sannan ta janyo babbar kwalbar turaren dake gaban mirror ɗin, buɗewa ta yi ta tsiyaya dayawa a ciki sannan ta mayar ta rufe ta ajiye. Ta ɗauki wanda ta ɗiba ɗin ta rufe shima sannan ta juyo, Tsabar yanda ta tsorata ya sanya ta jefar da kwalbar ta faɗi ƙasa ji ka ke "tass!" Ta tawarwatse a wajen.
Nana ta dinga kallonsa tana haɗiyar miyau dakyar, tsaye yake gabanta daga shi sai ɗan boxer jikinsa sai ɗigar ruwa yake da alama daga wanka ya fito. Ta ƙurawa faffaɗan ƙirjinsa wanda gashi ya rufe shi idanu lokaci ɗaya kuma ta saki ƙara tana rufe fuskarta da hannayenta.
Saurin rufe mata baki ya yi yana mata wani irin kallo, ta dinga zare idanu hawaye na biyo gefen fuskarta, jawota ya yi daga inda take tsayen suka yi very close dashi har suna jin hucin numfashin juna. Ya janye hannunsa daga kan bakinta still looking at her eyes, Sauke numfashi ta dinga yi tana riƙe da ƙirjinta. Cikin kakkausar murya taji ya ce
"Me ki ke yi a ɗakina?"
Yanayin yanda ya yi maganar in a serious tone ya sanya ta yi shiru bakinta na rawa, a tsawace ya ce"I said who brought you here!?"
A mugun rikice ta dinga kallonsa tana girgiza kanta, magana takeson tayi masa amma tsoro ya hanata, ya yi kwafa sannan ya ce"Saboda bakida kunya ko? Haka ki ke shiga ɗakin maza without knocking ko?" Ta sake girgiza kanta. Sake tamke fuska ya yi ya ce"Ba zaki daina gyaɗa min kai kamar kadangaruwa ba" Gyaɗa masa kan ta sake yi ba tare da ta san tayi hakan ba. Wata muguwar tsawa daya daka mata ya sanya ta fadi ƙasa tana fashewa da kuka, ta riƙe ƙafafunsa cikin kuka ta ce"A... Dan...dan Allah Yaya Sultan ka yi haƙuri, daman turare fa zan ɗiba"
Hannu ɗaya ya sanya ya ɗagota yana kallonta ya ce"wa ki ka tambaya da zaki ɗebi turaren?" Ta girgiza kanta sai kuma ta ce"babu kowa" ya ce"oh sata zaki fara kenan?" Muryarta na rawa ta ce"A'a dan Allah kayi haƙuri ba zan sake ba"
Kallonta ya dinga yi ba tare da ya ce komai ba, ta sunkuyar da kanta har sannan tana ɗan shessheƙar kuka. An ɗauki aƙalla mintuna biyar kafin ya janye idanunsa daga kanta, ya bar wajen yana faɗin"bar ɗakin nan" kallonsa ta yi sai kuma ta nufi ƙofa da gudu ya juyo yana kallonta har ta fice, ya girgiza kansa yana wani irin murmushi ya ce"my mumu girl".
****Kallonta Maimoon ta dinga yi ganin yanda take haki, ta ce"Lafiyarki dai?" Kasa magana Nana ta yi sai hanyar ɗakin Sultan data nuna mata, Maimoon ta tuntsire da dariya sai kuma ta ce"ke mene ne ya kai ki ɗakinsa?" Sai da ta saci kallon Ummi da hankalinta ke kan tv sannan ta kalleta murya can ƙasa ta ce"turare naje ɗauka shine ya kamani" Rufe bakinta ta yi da hannunta ta ce"me ya ce miki?" Nana ta ɗan haɗe rai tana kallon gefe ta ce"tsawa ya yimin har sai da na faɗi ƙasa" Maimoon ta dinga dariya kamar zararriya, ganin haka yasa ta sake haɗe rai ta ce"dan baki ga yanda ya yimin bane da sai kin tausaya min" ta ƙare maganar kamar ta yi kuka.
"Nana ɗauka abincin ki kai musu mana"
Maganar Ummi ta katse su, toh kawai ta ce sannan ta nufi kitchen. Maimoon ta bita da idanu, sai da ta ɗebo warmers ɗin da plates sannan ta kalli Maimoon ta ce"help me mana" daga haka ta miƙa mata plates ɗin, amsa ta yi sannan suka nufi saman a tare, Ummi ta bisu da idanu.