← Book details Naanah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 73 OF 125

Sashe 73

Naanah Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Bayan an kammala komai Mama ta miƙe tana shirin wucewa gidanta, Atta ta yi saurin cewa“to idan ki ka tafi kuma wa zai kai yarinyar ɗaki?”. Kafin Mama ta yi magana ya miƙe yana kallonsu fuskarsa a sake saɓanin ɗazu ya ce“no need Atta. Zan tafi da ita” ya yi maganar babu alamar damuwa ko kunya akan fuskarsa, Jinjina kai Papa ya yi ya ce“hakan ma ya yi, ku je kawai Allah ya bada zaman lafiya.”

Da Amin ya amsa sannan ya nufi inda Nana ke zaune, kamar ba zai magana ba sai kuma ya ce“taso mu tafi” ya ƙare maganar yana miƙa mata hannunsa na dama, Ta cikin mayafinta ta ga hannun nasa, amma ta ƙi ɗora nata ta mike tsaye tana kuka ƙasa-ƙasa ta yi gaba. Bin bayanta ya yi bayan ya sake musu sallama, Abba ya lumshe idanunsa yana jin wata nutsuwa na saukar masa, at least dai ya aurar da ƴarsa. Cikin zuciya ya furta

“Alhamdulilah, ur home is blessed Nana.”

A fili kuwa kasa cewa komai ya yi, sai jingina kansa da ya yi da jikin kujera. Atta kuwa haɗe rai ta yi ta tashi ta haye sama dan sam ba haka ta so ba, ta so ne ta je gidan saboda ta ga Zahra. Da idanu Papa ya bita dan ya riga da ya gama gano shirinta ya girgiza kansa yana murmushi, tashi Aliyu ya yi ya musu sallama sannan ya nufi sana sashin. Su kuma suka ci gaba da maganarsu.

Tafiya suka dinga yi yana gaba tana bin sa a baya, gaba ɗaya ta kasa yin sauri, ga matsewar da lace ɗin jikinta ya yi mata, ga kuma gajiya, ga yunwa dan sam bata samu damar cin abincin ba. Ganin yanda ya yi gabs abin sa ya sanyata tsayawa, ta dinga kallon sa ganin ko sau ɗaya bai waiwayo ba, Tana tsaye a wajen har ya murɗa handle ɗin ƙofar ya shige ciki. Silalewa ta yi a wajen ta fashe da kuka, ita wace irin Amarya ce? Babu wanda ya rakota gidanta, sannan kuma shi kansa mijin ba zai iya jiranta ba ballantana ya jera da ita. Ta kifa kanta akan cinyoyinta tana kuka kamar ranta zai fita. Abdusammad na shiga ya mai da ƙofar yana shirin rufewa, sai a sannan ya lura da cewa bata bayansa, ya ɗan ware Idanunsa sai kuma ya saki ƙofar da sauri. Dube-dube ya dinga yi a balcony ni ɗin amma sam bai hangeta ba, dan haka ya fara tafiya yana kalle-kalle. Ya yi nisa ya hangeta tana tafiya a hankali, ya ɗan ja tsaki sannan ya ƙara saurinsa. Gabanta ya sha yana kallonta fuska a haɗe ya ce

“Ke mene ne haka? Ina zaki je?”

Banza ta yi masa, ta matsa ɗaya gefen ta ci gaba da tafiyarta tana kuka fuskarta rufe da mayafinta, Rai ɓace ya sake yin gaba ya jawota ta dawo gabansa yana kallonta fuska babu alamar walwala ya ce

“Yaushe na fara wasa da ke Nana?. Shige mu tafi!”

Cikin kuka ta ce“Wallahi ba zan bika ba, ni gida zan koma. Ai baka sona”

Ta ƙare maganar tana sakin wani marayan kuka, Kallonta ya dinga yi yana mamakin abin da ta ce, can kuma ya saki murmushi ya kamo hannunta ya ce“sai ina son ki zaki bi ni kenan?” ƙoƙarin kwace hannunta take sai dai rikon da ya yi mata bana wasa bane, dan haka ta ci gaba da kukanta tana cewa“Ni wallahi ba zan zauna da ku ba.. Ni wajen Ammata zan koma” ta juya tana shirin tafiya, Dafe kansa ya yi ganin tana son wahalar dashi a banza. Ya juyo da fuskarta ba tare da ya zare mayafin data rufe fuskar ba ya ce“Kina son na makeki anan ne?”

Madadin ta bashi amsa sai kawai ya ga ta zauna a wajen, ta sake rushewa da wani sabon kukan tana ƙoƙarin birgima a ƙasan. Wani dogon tsaki ya ja ganin tana shirin raina masa hankali yasa ya sunkuya kamar zai mata magana kawai taji ya ɗauketa tamkar Baby ya fara tafiya da ita, zille-zille ta fara yi tana son kwace kanta, sai dai sam bai bata wannan damar ba ya sake matseta da jikinsa yana ci gaba da tafiya. Ta dinga kuka tana cilla ƙafafunta har suka ƙarasa gidan, ya murɗa handle ɗin ƙofar da hannunsa ɗaya sannan ya shige ciki da ita.

08106608363
Nanameera.*🌹 NAANAH 🌹*

Arewabooks@Nanameera08
Wattpad@Nanameera08.

Page 45.

A parlon ya direta yana watsa mata wani mugun kallo ya ce“Idan wasa nake miki ki sake fita.” tura baki ta yi, Ta ɗan janye mayafin nata ba sosai ba, ɗaya bayan ɗaya ta dinga ƙarewa komai na parlon kallo. Ko ina tsaf dashi sai tashin ƙamshi yake, Ya nufi hanyar upstairs ba tare da ya sake bi ta kanta ba. Gajiya ta yi da tsaiwar, cikinta ban da ƙugin yunwa babu abin da yake. Ta kalli hanyar upstairs ɗin sai kuma ta nufi wajen da sauri, A corridor ɗin saman ta tsaya, ta dinga ƙarewa ɗakunan kallo dan babu inda bata sani ba. Extra room ɗin ta buɗe ta shiga, kamar yanda ta yi tunani kuwa anan ne aka zuba mata kayan furnitures ɗinta da Abba ya siya mata. Ta ƙarasa ciki tana sauke numfashi, Cire mayafin ta yi ta ajiye a gefen gadon, Ta zame ɗankwalin lace ɗin ta ajiye shima sannan ta hau gadon ta zauna tana sauke numfashi.

Koda ya shiga ɗakin zaune ya sameta gefen gado ta yi shiru tana tunani, tun bayan kiran da Umma ta yi mata taji jikinta ya yi sanyi kalau. Ya karasa ciki yana kallonta ya ce“Zahra"

Ɗago kanta ta yi ta kalleshi da kumburarrun Idanunta wanda suka sauya kala, wata embroidery Atampa ce a jikinta mai pattern, ɗinkin t boubou mai kyau. Sai dai sam babu walwala akan fuskarta, Ya tsaya a gaban gadon yana kallonta ya ce“Tashi muje ƙasa.”

“Sun kawota ne?”

Ta tambaya a sanyaye, Jinjina mata kai ya yi dan bai ji zai iya magana ba. Zahra ta miƙe a sanyaye ta yafa mayafin dake hannunta sannan ta yi gaba. Ya sauke ajiyar zuciya sannan yabi bayanta.

Da mamaki ya dinga kallon parlon ganin wayam babu Nana babu dalilinta, Ya dafe kansa yana tunanin Allah ya sa ba wani wajen ta sake fita ba, gaba ɗaya so take ta wahalar da rayuwarsa. Ɗan tsaki yaja sai kuma ya nufi ƙofa fita daga parlon, Zahra ta bi shi da idanu tana mamakin inda zai je. Babu in da bai duba ba a compound ɗin amma bai samu Nana ba, kuma shi ba zai iya zuwa Apartment ɗin ba yanzu ya ce ina take. Ya tsaya yana tunanin yanda zai yi, Can kuma ya juya ya koma gidan, yana shiga parlon ya tsaya turus ganinta da ya yi tsaye tana rarraba idanu. Ya ƙarasa gabanta da sauri kamar zai daketa ya ce

“Ina ki ka je?”

Hawayen da yake maƙale cikin kurmin idonta ne ya shiga zirarowa kan fuskarta. Ta kwaɓe fuska kamar ƙaramar yarinya ta ce“Uncle cikina”

“Ina miki wata maganar kina min wata? Na ce ina ki ka je.?”

Tura baki gaba ta yi ta ce“Ni fa babu inda naje, ɗakina na tafi.” ya maka mata wata uwar harara sannan ya nufi kujera ya zauna, kamar jira take tabi bayansa ta zauna kusa da shi ta ɗora kanta gefen kafaɗarsa, ƙoƙarin janyeta ya dinga yi amma sam taƙi yarda, ta zura hannayenta duk biyun ta cikin hannunsa ta riƙe shi gam. Zahra ɗauke idanunta ta yi kamar bata gansu ba, Ya sauke numfashi kafin ya yi gyaran murya cikin nutsuwar data gama ratsa shi ya fara musu nasiha, Duk wani abu wanda ya kamata ya sanar musu akan haƙƙin zaman tare sai da ya sanar musu, daga bisani ya yi wa Nana faɗa dan ya san tsaf zata iya nemar fitina. Sannan ita ma Zahra ya yi mata nata faɗan daban, Bayan ya kammala ya sanya suka yi addu'a sannan ya miƙe yana janye Nana daga jikinsa ya ce

“Sai da safe.”

Ya yi maganar yana kallon su duka, Tashi Nana ta yi ta ce“uncle.” kamar ba zai amsa ba sai kuma ya ce“mene ne?”

“Ni ina kazata?”

Ɗan mitsi-mitsi ya yi da idanunsa kafin ya ce“kaza? Kazar me?”
Chapter 73 · 0% Book details