Sashe 25
Naanah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Lumshe idanunsa ya yi sannan ya buɗe su akanta ya ce“lokacin kina ƙarama sosai, kamar kin fi yanzu hankali” juyowa ta yi tana kallonsa fuska a shagwaɓe ta ce“nafi hankali kuma? Ba an ce mutum yana girma yake ƙara hankali ba?” yanda ta yi maganar da zallar gaskiyar ta ya sanya shi murmusawa ya ja kumatunta sannan ya ce”eh wasu ba, amma ke da kin fi hankali” kallonsa ta dinga yi sai kuma ta ce“to me ya sa Abba?”
“saboda da kin fi son Abbanki, da baki ɓata min rai, u're always been my favorite” rungume shi ta yi tana sauke numfashi a hankali ta ce“yanzu ma ina sonka Abba, ni ina sonka, na fi son ka yanzu” shafa kanta kawai ya dinga yi ba tare da ya ce komai, bai san me ya sa kullum yake ƙara jin yarinyar cikin ransa ba, ko dan ita kaɗai gare shi? Ya tambayi kansa. Jan hannunta ya yi har gaban gadon sannan ya miƙo mata katon ledar dake wajen, ta amsa tana murmushi ta ce“Abba me ka siya min? Ko...”
Wani irin ihu ta saki ta ƙanƙameshi tana dariya, dai dai lokacin Amma ta shigo tana kallon su a ɗan kiɗime ta ce“subhanallahi, lafiya dai?” ban da murmushi babu abin da Abba ke yi, ita kuwa sai faman ihu take tana tsalle, ya janyeta daga jikinsa still smiling ya ce“ya isa haka murnar” girgiza kanta ta yi sai kuma ta juya ta ɗauki system ɗin tana dariya ta ce“wow Abba, thank you so much, ashe baka manta ba?”
Jin jina kansa ya yi sannan ya ce“ya za'a yi na manta?”
Ta lumshe idanu tana murmushi ta ce “shiyasa nake sonka sosai” ta ƙare maganar tana kissing ɗinsa a kumatu, dariya kawai ya yi sannan ya bar wajen, ta ƙarasa inda Amma ke tsaye kamar an dasata ta ce“Amma kin kalla Abba ya siya min new system”
Murmushi kawai Amma ta yi dan ta san ƙaunarta da system ta ce“yar gatan Abba, congrats” ta ƙare maganar tana jan kumatunta, Dariya kawai Nana ta yi sannan ta ratsa ta gefenta ta fice daga ɗakin da sauri.
08106608363
Nanameera.*🌹 NAANAH 🌹*
Page 16...
Haka rayuwa ta ci gaba da tafiya har tsawon sati uku, abubuwa suka dinga matsowa kusa, ban da shirye-shirye babu abin da ake ciki estate. Zuwa sannan duk sun haƙura akan zaɓin da aka musu, babu wanda ya sake tada zancen yana so ko baya so. Ranar Alhamis wajejen ƙarfe 12:00 na rana tana zaune cikin daƙinta wayarta ta fara ƙara, kallon screen ɗin wayar ta yi sai kuma ta ci gaba da danna system ɗinta. Kiran na katsewa wani ya sake shigowa, ta ɗan kalla sai kuma ta matse gefen wayar, ko kaɗan bata son ɗaga kiransa, bata son magana dashi, ta riga da ta haƙura dashi ta yarda da zaɓin da aka mata. Duk da ta san abu ne mawuyaci ta iya mantawa da Junaid cikin ranta, ƙarar da wayar ta yi ya sanya ta ɗan ɗago idanunta kamar zata yi kuka, ta kalli wayar kafin ta sanya hannunta na dama ta dauƙa ta kai kunne. Junaid ya sauke nannauyar ajiyar zuciya jin ta ɗaga wayar, muryarsa cike da damuwa ya ce
“Nana”
Shiru ta yi tana tura baki, ya sake faɗin “kina jina?”
Nan ma ta sake masa shiru tana jin kamar ta katse wayar,
“Nana ko dai...”
“ina ji”
Ta ce murya a ɗan kumbure. Jin jina kansa ya yi yana ɗan suɗe laɓɓansa ya ce“kin daina sona ko? Kin yar dani ko?”
Ciro wayar ta yi daga kunnenta ta dinga kallon screen ɗin kafin ta sake mayarwa, Junaid ya ce“Nana wane ya sauya miki tunani? Wane ya baki shawarar rabuwa dani? Ashe daman zaki iya barin a rabamu? Ashe zaki iya mantawa da alƙawarinmu? Kin bani mamaki Nana”
Sosai ta ji jikinta ya yi sanyi, nan da nan hawaye suka kawo idanunta, ta yi shiru ba tare da ta furta koda kalma ɗaya ba. Jan numfashi Junaid ya yi ya ce“shikenan Nana, tun da kin zaɓi rabuwa dani shikenan, zan haƙura dake, amma ina son ki sani ba zan taɓa iya daina sonki ba, ba zan iya mantawa da ke ba Nana, I'll not! Kuma ina son ki sani bani na bar ki ba, ke ce ki ka bar ni”
Ya ƙare maganar hawaye na zubowa kan fuskarsa, shirun da taji ya yi ya sanya ta sauke wayar daga kunnenta, har sannan bai katse kiran ba, tana jin yanda yake sauke numfashi da sauri da sauri, kashe wayar ta yi gaba ɗaya ta yi wurgi da ita kan ƙarshen gadon sannan ta kwanta tana fashewa da wani raunataccen kuka. Tabbas tana son Junaid, kuma tana jin sa a ranta, amma ta riga da ta yi alƙawarin rabuwa dashi domin farin cikin iyayenta. Tana nan kwance har ƙarfe 1:00 tana faman kuka a hankali, agogon da ya buga ƙarfe ɗayan ne ya sanya ta tashi tana goge hawayenta, ta tashi daga wajen ta ƙarasa gaban mirror ɗinta. Kallon kanta ta dinga yi a jikin madubin, kamar ba ita ba, ta rame, idanunta sun yi jajur kuma sun kumbura. Haka ma fuskarta, ta sauke numfashi sannan ta nufi hanyar toilet tana haɗa hanya.
After 10mins ta fito tana goge fuskarta da towel, ta ƙarasa gaban gadonta ta ɗauki prayer mat da hijab ɗin da ta yi salla da asuba ta zura sannan ta shimfiɗa laddumar ta fara gabatar da salla, koda ta ida zama ta yi a wajen ta dinga addu'o'inta har wajen 1:30 na rana, kafin daga bisani ta tashi ta naɗe laddumar ta ajiye inda take sannan ta nufi hanyar fita daga ɗakin sanye da hijabin.
Kallonsu ta dinga yi kafin ta ƙarasa tana murmushi ta ce“laa aunty” ta ƙare maganar zama kusa da Ramlah. Murmushi ita ma Ramlah ta yi ta ce“Amarsu Nana” sunkuyar da kanta ta yi tana ɗan murmushi a hankali. Cikin zolaya Ramlah ta ce“wai sauran kwana nawa kenan?” kamar zata yi kuka ta ce“ni aunty ban so wallahi” dariya Ramlah ta yi ta ce“ƙaryar banza dai, muna nan zaki zo kina cewa Yaya Safwan kaza, wai ke ga me miji” tashi ta yi daga wajen da sauri tana satar kallon Amma da ke zaune gefe ɗaya, ta ɗan kalleta ta ce“Amma zan je wajen Aunty Zahra”
Kamar ba zata yi magana ba sai kuma ta ce“a dawo lafiya” to kawai Nana ta ce sannan ta yi waje da sauri, Ramlah ta bi bayanta da kallo tana murmushi ta ce“abun mamaki wai Nana ce zata yi aure” girgiza kai Amma ta yi ta ce“nima kullum da auren nan nake kwana nake tashi, Allah dai ya bada zaman lafiya” cikin fara'a Ramlah ta ce“to ya za'a yi? Amin ya rabbi”
****
Murmushi kawai Maimoon ta yi ta ce“to ya za'a yi?” Nana da ke tsaye jikin mota ta ce“bari dai naje na dawo sai mu yi maganar”
“okay zan faɗawa Amrah ma”
Wani irin banzan kallo ta watsa mata sai kuma ta ce“to ba zan je ba” murmushi kawai Maimoon ta yi ta ce“ai ko baki isa ba yarinya, wallahi kamar kin je kin gama” gaba Nana ta yi ba tare da ta sake bi ta kanta ba, Maimoon ta dinga kallonta har ta shige apartment ɗin sai kuma ta juya tana murmushi a hankali.
Tura ƙofar parlon ta yi bakinta ɗauke da sallama, Wata babbar mace ce zaune akan kujera ta ci ado da wani ubansu lace mai kyau da tsada, ta yi ɗaurin ture kaga tsiya kitson attachment ya zubo ta ƙasan daurin sai taunar cew gum ta yi tana ƙas ƙas, Nana ta dinga kallonta sai kuma ta sake cewa“Salamu alaikum” ɗago kanta ta yi daga danna wayar da take ta ɗan kalleta babu yabo babu fallasa ta ce“wa'alaiki salamu” daga haka ta sake sauke kanta tana ci gaba da abin da take. Shiru Nana ta yi tana son ta tambayeta ina Zahra take tana kuma jin tsoron yi mata magana. Ganin mintuna biyu sun shuɗe ya sanya ta ce“dan Allah Aunty Zahra fa?”
“Tana ciki” matar ta ce a takaice tana taunar cew gum ɗinta, okay kawai Nana ta ce sannan ta nufi hanyar upstairs tana tafiya a nutse, matar ta ɗago ta bita da kallo sai kuma ta ɗan yi siririn tsaki. Kai tsaye ɗakin Zahra ta buɗe ta dinga kallon ko ina ganin bata ciki ya sanya ta mayar da ƙofar ta rufe, ta juyo tana ɗan kalle-kalle corridor ɗin. Ɗakin Noor ta buɗe nan ma taga babu kowa a ciki dan haka ta dawo downstairs tana tunanin inda Zahra ta yi,
Tsaye ta same su a parlon, Zahra na kallon matar tana faɗin “okay bari na faɗawa Safeena sai ta miki” toh kawai matar ta ce, Nana ta dinga kallonta kafin ta ce“Aunty Zahra” sai a sannan Zahra ta lura da ita, ta yi murmushi tana faɗin “au Nana ke ce?” gyaɗa mata kai ta yi ta ce“na shigo ban sameki ba, shi ne naje na duba daki naga bakya nan”
“Ayyah ina kitchen ne, girki muke, zo ki taya mu”
Zahra ta yi maganar tana murmushi, girgiza kai Nana ta yi ta ce“a'a bari naje gida an jima zan dawo, daman magana nake son muyi” ɗan harararta ta yi ta ce“to ki tsaya na ƙarasa mana sai muyi maganar” satar kallon matar dake zaune Nana ta yi daga yanda ta haɗe rai dan haka ta ɗan yi murmushi ta ce“a'a zan dawo ɗin” okay Zahra ta ce dan bata son ta takura mata, ta juya ta fice daga parlon da sauri. Sai a sannan matar ta ɗago kanta ta kalli Zahra ta ce“wace wannan?”