← Book details Naanah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 125

Sashe 38

Naanah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ɗago kansa ya yi ya kalleta dan bai san ma ta shigo ba, ta sakar masa kyakkyawan murmushi tana ƙarasowa, ta zauna gefensa ta ɗora hannunta kan nasa a sanyaye ta ce“sannu da dawowa” kallonta kawai ya yi sai kuma ya ce“yauwa, ina Noor?” murmushi ta yi ta ce“kai ma kasan tun da muka zo ƙasar nan ba zama take ba, kullum tana apartment ɗin Hajiya Babba” jinjina kansa ya yi hankalinsa na kan system ɗin ya ce“ai ta yi ta gama nan da 3weeks mun koma gida” da sauri ta kalleshi sai kuma ta ce“tafiya zamu yi?” jin yanda ta yi tambaya da damuwa ya sanya ya ɗago kansa ya sake kallonta murya a sake ya ce“lafiya dai?” girgiza kanta ta yi tana kirkiro murmushi ta ce“kawai dai tambaya nayi” ɗauke kansa ya yi ya ce“to tafiya zamu yi, karatunta ya tsaya duk da ana yi mata anan, sannan nima abubuwa sun fara min yawa” a sanyaye ta ce“tom Allah ya kaimu, amma sai bayan biki ko?” gyaɗa mata kai ya yi ya ce“eh Abba ya ce na tsaya a yi, that's why yasa na ce miki 3weeks da next week zamu tafi”

“ai next week ɗin ne bikin right?”

“eh haka ne”

Ya ce yana rufe system ɗin, Zahra ta dinga kallonsa har ya tashi ya ɗauke system ɗin ya mayar inda yake ajiyewa sannan ya nufi toilet.

****
Al-ameen ya kalleshi sai kuma ya ce“da gaske kana ganin wannan zai yi aiki?” Junaid ya ajiye wayar hannunsa ya zauna kan sofa sannan ya ce“eh mana zata yi bari kuma ka ga” dariyar mugunta Al-ameen ya dinga yi sannan ya ce“Allah sarki har ta bani tausayi wlh, yarinyar so calm da ita” harararsa Junaid ya yi dai dai nan aka buɗe ɗakin aka shigo. Wata babbar mata ce mai ƙiba sosai ta dinga kallonsu sai kuma ta ce“kuna nan kuna sana'ar taku ko?” sosa kai suka shiga yi, Al-ameen ya ɗan durƙusa ya ce“Mama ina yini?"

“lafiya kalau Al-ameen ya Mamanka?”

Murmushi ya yi ya ce“tana nan kalau wallahi, ta ce ma na gaisheki” jinjina kanta ta yi ta ce“ina amsawa, ku dai yiwa kan ku faɗa ku fito da matayen aure ku yi aure, wannan zaman babu inda zai kai muku” sunkuyar da kansa ya yi ya ce“tom Mama in sha Allah, Allah ya ƙara girma” Amin kawai ta ce sannan ta mayar da idanunta kan Junaid ta ce“daman Farhana ce ta zo take nemanka” ɗan tura baki ya yi kamar ƙaramin yaro ya ce“Mama dan Allah ki ce bana nan” wani banzan kallo ta masa kafin ta ce“ka fito ina jiranka malam” daga haka ta juya ta rufe musu ƙofar. Kallonsa Al-ameen ya dinga yi sai kuma ya fashe da dariyar yana zamowa daga kan sofa, Junaid ya dinga kallon sa fuskarsa a haɗe sai kuma ya mike yana faɗin “banza mara hankali” ko ta kansa Alameen bai bi ba ya ci gaba da dariyarsa, Ya yi tsaki sannan ya fice daga ɗakin shima..

****
Ƙarfe 5:00 na yamma Amma ta buɗe ɗakin ta shigo, kwance ta sameta ta rufe jikinta da bargo sai numfashi take a hankali, ta ƙaraso ɗakin tana yaye duvet ɗin ta ce“ke Nana” a hankali ta buɗe idanunta wanda take jin sun yi mata wani irin nauyi. Muryarta a sanyaye ta ce“na'am Amma”

“ki taso Hajiya Babba na kiran ku” kamar zata yi kuka ta ce“Amma ki ce banida lafiya wallahi ba zan iya zuwa ƙauye ba” harararta Amma ta yi ta ce“ka da Allah yasa ki iya zuwa sai ki je ki faɗa mata hakan” daga haka ta saki bargon sannan ta juya ta fice daga ɗakin. Dakyar ta tashi zaune ta jingina da fuskar gadon tana hawaye a hankali, wani irin nauyi ta yi ƙirjinta y yi mata, daga jiya zuwa yau ji take kamar zuciyarta zata tarwatse, ban da tunani babu abin da take, she wish ace mutuwa ta zo ta ɗauketa yafi wannan halin da take ciki, she wish ace duk abin da ke faruwa mafarkine ba gaskiya ba, da sai ta yi sallar godiya ga Allah idan ta farka, sai dai ganin lokaci na tafiya ya sanya ta tabbatar da ba mafarkin take ba. A hankali taja idanunta ta rufe wanda hakan ya bawa hawayen dake kurmin idon samun damar zubowa, ta taune down lip ɗinta tana shessheƙar kuka a hankali, kiran sunanta da taji Amma nayi ya sanya ta tashi jiki babu kwari ta nufi toilet, wanka ta yi sannan ta fito ta sanya wata doguwar rigar material sannan ta ɗauka wani gogaggen hijab ta saka wanda ya saukar mata har ƙasa, ko mai bata samu zarafin shafawa fatarta ba ta fice daga ɗakin, tsaye ta samu Maimoon da Hamida sai Amma dake zaune, ta kalleta rai ɓace ta ce

“da kin bari na dawo dakin sai ranki ya ɓaci wallahi”

Bata ce komai ba ita dai, Maimoon ta ce“mu je mu ake jira” har ta fara tafiya sai kuma ta ce“oh i forgot my phone” daga haka ta koma daƙinta da sauri, a gaban mirror ta ɗauki wayar bata tsayawa kunnawa ba ta nufi waje, a compound ɗin gidan Hajiya Babba suka tadda sauran wanda za'a yi tafiyar dasu, domin yana ɗaya daga al'adar gidan duk sanda zasu yi auren ya'ya sai an kai su can Yola ruga sun gaida kakkaninsu na can, Hajiya Babba ce tsaye sai Abdusammad a kusa da ita, sai Safwan, Sultan, Hamid da kuma Aliyu. Matan kuma akwai Zahra dake riƙe da Noor, Juwaira, Hamida, Maimoon, Amrah, sai kuma Nana. Papa da ke gefen Hajiya Babba na dama ya kallesu ya ce“a kula dan Allah, Abdusammad kai ne babba na san ba zaka bari su yi wani wajen ba amma dan Allah su kula sosai” jinjina kansa ya yi a sanyaye ya ce“okay Papa in sha Allah” daga haka ya nufi motarsa. Ɗaya bayan ɗaya suka dinga shigewa mota, ita kuwa Nana taja ta tsaya dan sam bata ji zata iya zuwa ba, ganin kowa ya shige an barta ya sanya Hajiya Babba ta ce“a'a takwara lafiya dai?” kamar zata yi kuka ta ce“Hajiya banida lafiya fa” ƙarasowa inda take ta yi ta dafa jikinta jin babu zafi ya sanya ta ce“to meke damunki?” a sanyaye ta ce“kaina ciwo yake” Papa ne ya ce“to shiga mota idan kun tafi a hanya a siya maki magani” hawaye ne ya fara zubowa kan fuskarta ta ce“Papa ba zan iya zuwa ba wallahi, kaina ciwo yake sosai” haɗe rai ya yi a ɗan tsawace ya ce“kin shige mota ko sai ran ki ya ɓaci Nana!” yanda ya yi maganar cikin fargagi ya sanya ta dafe saitin zuciyarta tana wani irin numfashi, Hajiya Babba na ƙoƙarin magana Abdusammad ya fito daga motar yana kallonsu ya ce“mene ne?”

“wai ba zata je ba”

Papa ya yi maganar rai ɓace, kallonta ya yi sai kuma ya ja hannunta ba tare da ya ce komai ba, ya ƙarasa motar Safwan ya buɗe front seat ɗin ya turata yana mata wani irin mugun kallo ya ce“kar na sake jin bakin ki kin ji” gyaɗa masa kai kawai ta dinga yi dan gaba ɗaya ba'a hayyacinnta take ba, Ya rufe motar sannan ya nufi tasa motar ya shige back seat dan shi da driver zasu tafi suka ja motar suka yi gaba, ɗaya bayan ɗaya motocin suka dinga fita har suka bar cikin estate ɗin sannan kowacce ta fara gudu akan titi.

08106608363
Nanameera.*🌹 NAANAH 🌹*

Arewabooks@Nanameera08
Wattpad@Nanameera08.

Page 24...

Tun da suka fara tafiyar babu wanda ya ce da wani ƙala, kowa da abin da yake tunani cikin ransa, sai da suka ci rabin tafiyar sannan ya ɗan kalleta ta gefen ido, idanunta a lumshe suke sai dai babu tabbacin bacci take ko kuwa idanunta biyu, dan haka ya ɗan yi gyaran murya. Sarai Nana ta ji shi amma bata ko motsa ba ballantana ya saka ran da zata kalleshi, Safwan ya ɗan fara rage gudun da yake murya a sanyaye ya ce“Nana!”

Dakyar ta iya raba laɓɓanta da juna murya can ƙasa ta ce“na'am” sai da ya yi kwana sannan ya sake cewa“meke damun ki na gan ki so quiet kamar ba ke ba?” a hankali ta juyo da idanunta ta ɗan kalleshi sai kuma ta ɗauke ta maida su kan titi tana kallon yanda suke shige bishiyu da tsaunuka ta ce“babu komai” jin yanda ta yi maganar da wata irin muryar wadda bai santa da ita ba ya sanya ya juyo da kansa ya kalleta, ganin ba shi take kallo ba yasa ya mayar da hankalinsa kan tuƙin da yake kafin ya ce

“ko baki son auren nan?”

Kallonsa kawai ta yi amma bata ce komai ba, bai damu da rashin amsawar tata ba ya sake faɗin “ki sanar dani tun yanzu, cause naga yanda yan uwanki ke shirye-shirye ke bakya yi, gaba ɗaya kin zama wata so silent ba kamar yanda ki ke ba, ki faɗa min ba ki da sha'awar aurena or what?”

A hankali ta dinga kallonsa tana jin kamar ta ce masa eh bata so. Sai dai koda wasa ba zata iya furta hakan gare shi ba, dan haka ta yi shiru tana jin yanda bugun zuciyarta ke tsananta. Safwan bai sake cewa komai ba ganin ba amsa masa take ba, dan haka ya mai da hankalinsa gaba ɗaya kan tuƙin da yake, After 15mins ya ɗan saci kallonta ta gefen ido ganin idanunta a lumshe kamar ɗazu ya sanya ya ce

“tun da ba zaki yi magana ni bari na sanar dake abin da ke raina”

Buɗe idanunta ta yi ta ɗan kalleshi ba tare da ta ce komai ba, amma gaba ɗaya hankalinta yana kansa tana son taji shi mene ne nasa ra'ayin akan auren.

Numfasawa ya yi cikin nutsuwar data gama ratsa shi ya fara cewa
Chapter 38 · 0% Book details