Sashe 80
Naanah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Okay kawai Khadijah ta ce sannan ta fice daga kitchen ɗin. Nana tabi ta da kallo, lokaci ɗaya maganganun Khadijah suka fara dawo mata. Murmushi ta yi can kuma kamar wadda ta tuna wani abu ta tura baki. Tana nan tsaye har Khadijahn ta dawo. Ta dinga kallon ta sai kuma ta wuce ta ɗauko wata sabuwar warmer ta ƙaraso wajen tunkuyar ta ce“kina nan tsaye har sai ya dawo ma.”
“To ai ba yanzu yake dawowa ba.”
Nana ta yi maganar a ɗan ƙufule, Sai da ta gama zuba shinkafar a cikin warmern ta mayar da rufe sannan ta ce“to zauna sai ya dawo, dalla ki je ki yi wanka.”
Tura baki ta yi ta ce“nifa wallahi tsoro nake ji.”
Sak Khadijah ta yi tana kallonta, can kuma ta ce“tsoro? Tsoro fa ki ka ce Nana. Kenan duk abin da nayi ya tashi a banza kenan?”
“To dan Allah ya zan yi? Uncle ne fa.”
“Da yake uncle ɗin ki amma yanzu mijinki ne.”
Saurin kallonta Nana ta yi, Ta gyaɗa mata kai fuska babu walwala. Bata sake cewa komai ba ta yi waje, Khadijah ta bita da idanu sai kuma ta girgiza kanta tabi bayanta. Nana ta fita daƙinta ta shige, ta daɗe tsaye a tsakiyar ɗakin kafin daga bisani ta sauke numfashi ta nufi toilet. Wanka ta yi ta fito tana tsane ruwan jikinta da towel, Gaban dresser ɗinta ta ƙarasa ta fara shafe-shafen mayuka. Bayan ta gama ta saka turaren da Amma ta bada aka kawo mata, nan da nan ɗakin ya gauraye da sassayan ƙamshi. Yar simple make-up ta yiwa fuskarta ta shafa lip gloss, Bayan ta gama ta ƙarasa gaban press ɗinta ta buɗe. Shiru ta yi tana kallon jerin kayan da suke cikin press ɗin a jere, Tana nan tsaye aka buɗe ƙofar. Khadijah dake tsaye tun ɗazu tana kallonta ta ce“wai har yanzu baki ga kayan da zaki saka bane?” juyowa ta yi tana kallonta kamar zata yi kuka ta ce“To dan Allah me zan saka?” taɓe baki Khadijah ta yi ta ƙaraso ciki tana kallon ta, tsayawa ta yi kusa da ita tana ƙarewa press ɗin kallon. Ta jima a tsayen can kuma ta jawo wata doguwar riga, Miƙawa Nana ta yi tana murmushi ta ce“ki saka wannan zai miki kyau” amsa Nana ta yi tana shafa rigar, ta juya ta koma toilet. Murmushi kawai Khadijah ta yi sai kuma ta koma kan kujerar dake jigin gadon. Bata jima ba ta fito tana sanye da Egyptian Abayar nude colour, wata mai flower a ƙirji da kuma hannun rigar. Tashi tsaye Khadijah ta yi tana murmushi ta ce
“wowww! Kin ga yanda ki ka yi kyau?”
Murmushi Nana ta yi ta ƙarasa jikin madubi, Ita kanta ta san rigar ta yi mata kyau. Ta kai hannunta ta shafa rigar tana murmushi ta ce“nayi kyau?”
Gyaɗa mata kai Khadijah ta yi, ta karɓi veil ɗin rigar dake hannun Nana ta ce“Zo na ɗaura miki.” To kawai Nana ta ce, Khadijah ta ɗaura mata ɗankwalin mai tuta a gefe. Wani irin kyau ta yi kamar ba ita ba, Khadijah ta ja kumatunta ta ce“Sai dake kyakkyawar matar uncle” wani irin fari Nana ta yi da ido suka tuntsire da dariya a tare.
****
A dai-dai round about ɗin ta tsaya, Ta juya tana kallon Kaddu dake gefenta ta ce“Ba gida zaki yi bane?” girgiza mata kai Kaddu ta yi tana shafa wayarta ta ce“A'a akwai wanda zai zo ya ɗaukeni kawai saukeni anan.” okay Anty Khadijah ta ce, Kaddu ta buɗe motar tana shirin sauka, kamar wadda ta tuna wani abu sai kuma ta koma ta zauna ta ce“Mantawa nayi zan tafi. Yanzu ya za'a yi wai?”
“Yanda muka shirya mana. Dole Zahra ta fito daga gidan, idan Allah ya kaimu gobe zan yi je gidan na kai mata maganin.” Jinjina kai Kaddu ta yi kafin ta ce“Eh ki yi da sauri. Saboda kada su bar ƙasar” wani shu'umin murmushi Anty Khadijah ta yi kafin ta ce“ai idan ki ka ga an bar ƙasar nan to da ni ne bada Zahra ba!”.
08106608363
Nanameera.*🌹 NAANAH 🌹*
Arewabooks@Nanameera08
Wattpad@Nanameera08.
Page 49.
Murmushi Kaddu ta yi ta ce“Nagode ƙawata. Ki ce nan bada jimawa ba zamu fara ƙirga dollars?” Anty Khadijah ta sake murmushi tana cije laɓɓanta ta ce“Ai idan ki ka ce dollars kaɗan ma kenan, Ke idan da abin da yafi kuɗi wallahi sai kin same shi. Ai ko ke zaman ƙasar nan sai ya gagareki, Ballantana kuma ni, Daga Us nayi uk, daga uku na yi Paris, daga Paris nayi Qatar. Woww!”
Tuntsirewa da dariya suka yi a tare. Kaddu ta ce“tom Allah ya tabbatar ya nuna mana” da Amin ta amsa, Kaddu ta sauka daga motar tana murmushi, Anty Khadijah taja motar ta bar wajen. Bata fi 2mins a tsaye ba wata babbar mota ta yi parking a wajen, Kaddu ta gyara tsaiwarta tana murmushi kafin ta nufi inda motar take..
****
Ana shirin kiran sallar magriba suka fito, Khadijah ce a gaba sai Nana dake biye da ita, Sai haɗe rai take. A bakin ƙofar parlon suka tsaye, Khadijah ta dafatan ganin yanda ta haɗe rai ya sanyata murmushi kafin ta ce
“To wai mene abun haɗe ran? Da ban zo bafa”
Kamar zata yi kuka ta ce“To dan Allah ba sai ki kwana ba. Daga zuwanki”
Waro idanu Khadijah ta yi, Ta girgiza kanta ta ce“flight ɗin safe zan bi zuwa Kano. Kin ga ai ba zan kwana ba, Ke dai ki bari nan bada jimawa ba zan zo idan kuma kun tafi US shikenan”
“Ni ba zan bisu ba”
Cewar Nana a shaƙe. Taɓe baki Khadijah ta yi ta ce“To sai ki yi ta zama a gida ai. Ni kin ga tafiyata, ki koma ciki”
“Ba zaki zo na rakaki wajen Maimoon ba?”
Tsayawa Khadijah tayi akan stairs ɗin balcony ɗin, Ta juyo tana kallonta kafin ta ce“To ai baki tambaya ba.”
Tuni Nana ta ware mayafin dake kanta ta yafa ta yi gaba tana cewa“Ke ni ba'a hanani fita ba." Murmushi kawai Khadijah ta yi sai kuma tabi bayanta.
Maimoon na riƙe da turaren wuta aka buɗe kofar parlourn, Duk zatonta Yaya Aliyu ne ya dawo. Ganin su Nana ya sanya ta ajiye kaskon ta nufosu tana murmushi ta ce“Laaa amarya ce da ƙawarta?. Sannunku da zuwa” Murmushi suka yi Nana ta janyeta daga jikinta tana cewa
“Ni bari kar ki shafa min ciki”
Harararsa Maimoon ta yi tana riƙe da hannun Khadijah ta ce“Ai ba sai na shafa miki ba, nan bada jimawa ba zaki ganki dashi”
“Bakin ki ya sari ɗanyen kashi!”
Cewar Nana bayan ta zauna kan ɗaya daga cikin luxury sofa ɗin dake zagaye da parlon. Maimoon bata sake bi ta kanta ba ta shige kitchen, Drinks ta kawo musu sannan ta sake komawa. Nana ta kalli Khadijah wadda ta yi shiru ta ce“Ke kar ki sha”
“A saboda me zaki hanata sha?”
Ta tsinkayi muryar Maimoon ɗin a kanta, Komawa ta yi ta jingina da jikin kujera ta ce“To sai ta cika cikinta da abinci”
“To ina ruwanki?”
Maimoon ɗin ta sake tambayarta a fusace. Harararta Nana ta yi sanin halin jarabarta ta ce“Da ruwana ɗin, Kuma wallahi sai na faɗawa Yaya Aliyu.”
Wani dogon tsaki Maimoon ta ja sannan ta ƙarasa gaban Khadijah da kanta ta zuba mata ruwan a glass cup ta miƙa mata, Khadijah ta karɓa tana murmushi sannan ta sha. Hira suka dinga yi da Khadijahn kasancewar ta santa sosai a Aun, Ita kuwa Nana ko kallon inda suke bata yi ba, hankalinta na kan wani movie da ake haskawa a mbc max. Suna nan zaune har after 15mins Khadijah ta miƙe tana kallon agogon dake maƙale a parlourn ta ce“Bari naje kar dare ya yi min”
Miƙawa Maimoon ta yi ta ce“Ayya daga zuwanki?” murmushi Khadijah ta yi ta ce“Wallahi da shigewa ma fa zan yi, Nana ce ta ce mu zo.” sai a sannan ta mai da Idanunta kan Nana wadda ke kallon tv,Ta yi murmushi kamar ba ita ta gama yi mata masifa ba ta ce“Hajiya Nana irin wannan kwalliya haka? Ki ce amarcin ake zubawa.” ba zaka taɓa cewa da Nana take ba dan ko inda take bata kalla ba, Maimoon ta kalli Khadijah wadda ita ma take kallon Nanar sai kuma ta ce“kin san halin mutuniyar. Ina zuwa Mimi”
Okay kawai Khadijah ta ce, Maimoon ta bar parlour da sauri, Sai a sannan Khadijah ta ƙarasa Kujerar da take ta zauna tana murmushi ta ce“Haba mana Nanar uncle fushi fa ba naki bane”
“Ce miki nayi fushi nayi?”
Ta yi tambayar tana kallonta, Girgiza kai Khadijah ta yi, Nana ta sake ɗauke kanta ba tare da ta sake cewa komai ba. Itama Khadijahn shiru ta yi dan ta fuskanci abun ne ya motsa, ba'a wani jima ba Maimoon ta dawo parlourn hannunta riƙe da wata leda mai ɗan fadi,Ta miƙawa Khadijah dake tsaye ta ce
“Sorry dan Allah ba yawa kin ji.”
Murmushi Khadijah ta yi kafin ta amsa ta ce“Allah sarki Maimoon uwar kyauta. Thank you, Allah ya raba lafiya” Da Amin ta amsa, Nana ta miƙe ta yi waje without say anything. Da idanu duk suka bita, Sai kuma Maimoon ta dafata ta ce“kada ki biye mata kin san halinta” murmushi Khadijah ta yi ta ce“nii I'll not.” Suka sake sallama sannan ta bar parlour, Koda ta fita tsaye ta hangeta gaban motar da aka kawota ta cake a wajen kamar wadda aka dasata, Khadijah ta girgiza kanta sai kuma ta ƙarasa wajen, Buɗe motar ta yi ta shiga bayan Nanar ta matsa, Ta kalleta ta ce“Sai an jima.”
“Ki gaida su Mami”
Ta yi maganar a shaƙe.
“Zasu ji” cewar Khadijah tana rufe motar, drivern ya ja motar suka bar wajen, Da idanu Nana tabi motar tasu har suka ɓacewa ganinta, ta sauke numfashi sannan ta nufi hanyar komawa apartment ɗinta.